Chapter 3
by @prettys01
★BUDURWAR ABBAN MU★
Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️```
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.
PAGE 3️⃣
Wani dogon numfashi ya kuma ja, sannan a hankali ya miƙe yana mai bin hanyar fita ɗan duba halin da Marwa take, duk da yasan zuwa yanzu ta faɗa ma Basma, ita Fauza ta wuce school.............
Ko da ya isa part ɗin su, sai ya iske ba kowa a ciki, murmushin ƙarfin hali ya yi sannan ya nufa compound, Da Bala Mai shuke-shuke ya fara haɗuwa.
“Alhaji Barka da Safiya." Cewan Bala yana riƙe da tiyon ban-ruwa.
“Uhm Alhamdulillah, na ce yaran nan sun fita ne wai?.”
“Eh Alhaji, Hajiya ƙarama ita ta tsufa a school, Hajiya Babba kuma yanzu ta fita, sai Hajiyar Tsakiya, ita kuma ta ɗan jima da fita."
“Ok to shike nan.” ya faɗa yana koma wa ciki.
Kawar da komai ya yi, ya shirya zuwa office Dan suna da meeting yau, already ya yi wanka, wani farin shadda ya fiddo, wanda ya ji aiki sosai, sawa ya yi sannan ya ɗan taje tarin suman kansan mai laushi da sheƙi.
Agogo mai tsaɗa ya ɗaura a hannunsa, sannan ya ɗau carkey da wayarsa. Har ya matsa gaban mirrorw sai ya dawo ya kalla kansa.
Baya tsufa sam, kullum ƙara ƙyau yake, murmushi ya yi sannan ya ɗauki turaruka kala biyar ya feshe jikinsa da shi.
Cikin sauri-sauri yake sauka daga stairs sanna kuma a natse, yana jin yunwa sosai amma dole sai ya fita zai ci, dan yau mai aikin da aka samo mai za ta zo, in su Basma sun amince sai ta fara aiki.
Mota ya shiga sannan ya yi waje, yana tuƙi yana kiran number Miss Ayo, sai dai kira biyar ya yi mata ba ta ɗauka ba, dan haka ya nufa gidan na ta.
Ta isa bakin get ɗin gidan ya gane gidan akwai lock, Dan haka ya nufa Company.
Sai dai yana zuwa ya tarar duk wanda zasu meeting ɗin sun wuce, da yake ba wani nisa da wajen, sai ya koma moto ya ƙara gaba.
Wani madaidaici wajen taro ne, wanda ya haɗa manya-manyan mutanen da za'a yi meeting da su, Alhaji Mubarak kawai ake jira.
Yana shigowa wajen aka tashi dan nuna mai girmamawa, sai da ya nema waje ya zauna bayan ya musu sallama duk sun amsa.
Zama suka yi sannan suka fara abin da ya tara su.
Abba kallon Miss Ayo yayi, wacce ke zaune daga gefansa na dama na operating system, be san me yasa ba matar tana burgesa, ba ta damuwa, ga kawaici da ibadah, a taƙaice ta yi mai 100%, sai dai dole ma ya cireta a ransa, saboda kishin yaran nasa.
Yayi nisa cikin tunani sosai, har aka fara watsewa dan an kammala zaman.
“Sir! Sir!! Sir!!!.” cewan Miss Ayo tana buga wani file a kan table.
Lumshe ido yayi sannan ya kalleta.
“We have to go." Sai ya ɗaya mata kai.
Wucewa ta yi, shima sai ya bi bayanta.
Sai da ya yi da gaske tukun ta yarda ta shiga motarsa, tana mamakin wai yarinyarsa ce wacce take ta hauka ɗazu.
“I'm sorry Sir, na shiga mamaki sosai saboda nasan baka da mata, hmmm haka muke ai." Ta faɗa tana ɗan dariya.
“To gaskiya ba ku yi ba, in dai har kishi ana gado to mata kuna da matsala sosai.” sai suka yi dariya sosai.
Da haka suka sauya hirar duk dai na nishaɗi ne, har suka yi parking a babban Premises na company ɗin, sannan suka jera tana mai riƙe mai da jakka amma jerawa suke yi suna ta dariya.
Ma'aikata gaishesa suke yi yana amsawa da kai, dan har lokacin be dena dariyar labarin da Miss Ayo take ba shi ba, tana mai Hausa tana haɗawa da yarenta Yaruba.
A tare shi da ita suka kai hannunsu kan handle, jin hannunsa kan nata yasa ya yi saurin cirewa yana cewa.
“Sorry." Sai ta yi mai murmushi tana buɗe ƙofar tare da mai alamar girmamawa akan ya shigo.
Ba musu ya shiga cikin officer ɗin yana cewa.
“Ai neman waje za ki yi ki zauna dan sai na ji karshe Labarin.......Marwa! Basma! Me kuke yi nan?.” cewan Abba cikin mamakin ganinsu zaune suna kallonsu.
Miss Ayo ma kallonsu ta yi da ƙyau, a cikin ranta kuwa cewa ta yi.
‘Masha Allah, Allah dai yasa lafiya.’
Marwa ta miƙe daga in da take zaune tana tafa hannunta biyu, sannan ta yi taku uku tana cewa.
“Basma kin gani ko, Abba ya dena son Mom, wata maccen yake kulawa har suna hira cikin nishaɗi, Abba me yasa kake yaudarar wannan matar?, dan kuwa kai mijin mace ɗaya ne tak, wallahi wallahi babu mai yi ma Mom ɗin mu kishiya har abada." Ta kai nan tana ƙare ma Miss Ayo kallon tsana da ƙiyayya.
Abba kuwa cikin sanyi da kwantar da murya ya ce.
“Marwa me yasa har yanzu ba za ku gane cewa idan mutum ya mutu, ya mutu kenan ba, aure nawa na nema kusan 4 amma duk an fasa saboda ku, kuma dan ku zanyi aure......” da sauri Basma dake zaune cikin takaici da masifa, ta miƙe a zabure tana cewa.
“Mu ba yara bane, babu abin da muke buƙata daga wajen wata maccen, mun iya waka, mun iya cin abinci.........Marwa wannan maganar ba ƙarama ba ce, ko kuma daga yanzu mun baka dama ka aura duk wacce kake so, amma wallahi ko kwana biyu ba za ta yi a cikin gidan Mom ba, ruwan acid zamu watsa mata, hmmmm Marwa mu je, ina da class yanzu." Ta kai na tana ɗaukan handbag ɗin ta, sannan ta kalla Abba.
“Abba daga lokacin da ka fara neman wata maccen ka sani daga lokacin za mu fara shafe cewan muna da mahaifi.........ke kuma idan kin shirya mutuwa, ki yi gigin auran mijin wata hmmmmmm.” takai nan tana wani irin mugun murmushi.
Haka Basma take, ba ta magana mai yawa amma in ta furta akwai ɗaci, halinta sak na mahaifiyarta, ba ta ɗaukan wargi bare ɓata lokaci.
Fita suka yi suka rufo mai ƙofa, Miss Ayo neman kujera mafi kusa ta yi ta zauna, tana dafe kanta.
“Haka yaran naka suke? Na ga ko kai basu girmamaka balle ace ka yi auren, har ga Allah, a tarayyata da kai ban taɓa ganin naƙasun ka ba sai yau, wato yaranka, akwai in da ka kuskure a tarbiyyar su, be dace suna maka magana irin haka ba......hmmmm Allah ya ƙyauta kawai, Bara na je office ɗina.” ta kai nan tana tashi taba shi cikin jujjuya maganganunta, tabbas akwai ƙamshin gaskiya a ciki, amma saboda soyayyar da yake musu be gani ba, sai ma ɗaura ma kansa laifi da ya yi, dan da be kula mace ba hakan ba zai faru ba sam............
*Marwa*
Cikin ƙuncin rai ta isa makaranta, sai dai ta kasa fita daga mota, ƙirjinta mugun suya yake yi akan abin da ya faru, ji ta yi dama ta shaƙe matar nan mai duhun fata, gata ƴar duma-duma, da ta samu natsuwar ruhi, take wayarta dake cikin jakkarta ta hau ringing, sai da ta ja dogon tsaki sannan ta ciro wayar tana picking ta kai kunninta.
Wani sanyayyar murya mai taushi da za ƙi ya fara mata amsakuwa da.
“Baby Love ina class, banganki ba, I hope everything's is fine?.”
Furzar da iskan bakin ta tayi sannan ta ce.
“My Love ganin zuwa." Ta faɗa tana kashe kiran, fushinta ta daidaita sannan ta buɗe motar tana fita.
Marwa tana da ƙyau masha Allah, dan kuwa ta haɗa komai da komai na cikakkiyar budurwa mai aji, doguwa ce, gata akwai jiki ba laifi, sannan ga hasken fata.
Yarda take da ƙyau haka tafiyarta ta kasance mai jan hankali, babbar matsalar shine Kishi, kishinta har ya fi na mahaifyarsu Hajiya Karima, haka Allah yayita, shi yasa koda wasa ta tsana ta ga wata da Abbansu.
Department ɗin su ta nufa duk kuwa da tasan ta gama latti, tana isa bakin ajin ta shiga daidai nan idanunta suka sauka kan wani matashin saurayi tsaye suna magana da wata yarinya.
Take ta haɗe rai, ta nufesu cikin zafin rai sosai, tana zuwa ta fizgo ƙaramin vail ɗin dake kafaɗar yarinyar dake gaban saurayinta, take yarinyar ta juya lokaci guda kuma Marwa ta sauke mata wani lafiyayyen mari akan kuncinta.
Da sauri wanan saurayin ya daka ma Marwa tsaya ganin ta kuma ɗaga hannu za ta kai mata wani marin.
“Baby, Merry ce fa." Ya faɗa cikin ɓacin rai yana riƙo budurwar yarinyar da ta kasa magana.
Sai a lokacin Marwa ta kalla fuskar yarinyar, ɗan zaro ido ta yi saboda ganin Merry, wato ƙanwar Al-hussain.
“Al-hussain I'm sorry, Merry please....." Da sauri budurwar ta ɗan ja baya tana girgiza kai, sannan cikin ɓacin rai ta kalla Al-hussain tana cewa.
“Wanan ce budurwar taka?." Sai ya ɗaga mata kai tare da murza yatsun hannunta.
“No! Ban yarda ba, ba ta yi min ba, ban kuma yarda da ka aureta ba, mtwwssss." Ta faɗa tana fizge hannunta sanan ta yi waje da sauri.
Al-hussain dafe kansa ya yi sannan ya riƙe hannun Marwa suka rufa ma Merry baya yana cewa.
“Kema kinsa Ni ban tsayawa da kowacce mace because of you, sannan kinsan dole sai Merry ta amince zan iya aurenki, hakan yasa ta zo dan ta ganki gashi kin ɓata komai.” ya kai nan yana jin babu daɗi a cikin ransa.
Marwa kuwa baki ta ɗan taɓe dan kuwa dama tun kafin ta ga Merry ta ji ta tsaneta saboda duk abin da Al-hussain zai ce sai ya sa Merry, a yarda ta fahimta kamar mahaifiyarsa haka ya ɗauki Merry.
A zaune suka isketa kan wani kujera, ta haɗe fuska tana waya tare da cewa.
“Al-hassan, yanzu zan tawo Company ɗin, eh......na zo ganin budurwar Al-hussain ne sai dai sam.........” shuru ta yi dan ganin Al-hussain ya fizge wayar tare da katse kiran.
Zama ya yi kusa da Merry sanan ya buɗe baki cikin taushi ya ce.
“Tana da zafin kishi ne, amma Marwa yarinyar kirki ce, kuma ita kaɗai nake so, Merry please ki amince." Ya faɗa yana marairaice fuska.
Marwa kuwa tana tsaye tana ganin ikon Allah, sai dai ko kaɗan fuskarta be nuna komai ba sai ladabi.
“Shike nan, ka bamu waje zan yi magana da ita." Cewan Merry tana ƙarema Marwa kallo.
“Thanks." Ya faɗa yana kai mata sumba (Kiss) a forehead ɗin ta. Take Marwa ta haɗiye wani mugun malulun kibiya ɗaya coketa.
Sai dai jin sanyayyar hannun Al-hussain akan na ta yasa ta ɗan dawo daga ɗauke hutan da ta yi.
Yasan ya taɓota dan haka be kalla idanunta ba ya matsar da ita kusa da Merry sannan ya basu waje.
Yana wucewa Merry ta sauke ajiyan zuciya sannan ta kalla Marwa ta ce.
“Sunana Maryam, kuma Ni ce kaɗai ƙanwa ga Tweens, Mahaifiyar mu ta mutu, tare da babban mu muke rayuwa, tun ba yanzu ba nasanki a bakin Al-hussain, yana miki wani irin mugun so wanda baya iya tantance fari ko ɓaci a cikin soyayyar ta ki. A cikin sati rana ɗaya tak Sunday shine baku haɗuwa, amma sauran ranaku kuna tare da juna, daga safe har yamma, Al-hussain ya riga ya baki komai nasa, saboda ke ya aje aikinsa duk da dama be damu da yi ba, ya dawo makarantar da tun sama da 5yrs ya gama a ƙasar waje, duk saboda ke........uhmmm already kinsan komai, da fari na zo ne akan koma wacce na hana auren na ce bata min ba, dan kuwa ba zan so naga Al-hussain ya aura wacce ba ta dace da shi ba, dama Al-hassan ne wannan ko wa ya ce yana so banda matsala, amma Al-hussain kuwa ina da matsala da hakan, amma karki damu na amince saboda kinyi min gaba ɗaya.” tai nan tana ɗaukan eyes-glass ɗin ta ta sanya tana wani irin murmushi wanda Marwa babu abin da ta gane, abu ɗaya ne tak ta fahimta shine, Merry dai ta amince da ita.
Ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba tana rungume Merry, duk da kuwa dana son auren Al-hussain ko ta ƙarfi ko ta bala'i.
Da haka suka rabu, Marwa ta gyara zamanta, ita kuma Merry ta miƙe tana kallon Al-hussain daya iso gabanta.
Ido cikin ido suke kallon juna, kallo mai cike da ma'anoni iri-iri.
“Na amince." Ya ji ta furta cikin sanyin murya, sai ya riƙe mata hannu sannan ya raɗa mata magana a natse.
“Promise.” sai ta yi murmushi sannan ta ce itama.
“Promise.” sai suka tafa hannu, sannan ta wuce.
Tafiya take yi cikin wani irin yanayi, kawai dai tafiyar yake yi, har sai da ta shiga babban motarta ƙiran G.L.K, tana zama sai ta fashe da kuka, tan yi tana girgiza kai.
Ta ɗau kusan 5mnt a haka sannan ta bushe da wani irin dariya sannan ta ce.
“Marwa kike ko? Hmmmm auren Al-hussain zai iya zama babbar masifa a rayuwarki saboda *PROMISE* .” sai ta kunna motar tana nufan get ɗin fita daga makarantar...............✍️
END.
> Akwai Chakwakiyar da zai ɗaure muku hankali amma muje kawai ladies.
> Kuna tunanin abin da nake tunani kuwa!?💃
#LIKES👍
#SHARE👌
#COMMENTS☹️🔥
*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book
📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book
📙 *BARRISTER* Paid book₦300
📕 *THE SLAVE* free book
📒 *ZAMU HAƊU* Free book
📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300
📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300
📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500
📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book
📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_
📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_
📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_
HIKAYOYI kuma sune :
*SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥*
*SARKIN MU🤣*
MOHINA DA MATSAFIYA💀
*RAMUWA💀🔥*