BARRISTER SUHAIL

CHAPTER 29

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----29

Tun bayan wayar da Yaya Mubarak ya yi mata, Iman ta kasa samun nutsuwa Duk da ta yi ƙoƙarin ɓoye damuwarta, zuciyarta na ci gaba da mata nauyi

Ta gama ayyukan gidan kamar yadda ta saba, amma babu walwala a tattare da ita

yana zaune kan dinning yana breakfast kallon ta yake yana lura da yadda ta rame cikin kwanaki ƙadan 

Yadda idanunta suka koma cike da damuwa

Amma duk lokacin da zai yi yunƙurin magana da ita, sai ya rasa ta inda zai fara 

bai taɓa jin yayi nadamar kawo batun auren zeenah ba kamar yau ba ji yake kamar ya ce ya janye amman yana tsoron zuciyar Abba  kar yayi tunanin tun farko wasa da hankalin yake masa

cigaba yayi da cin abincin gaban sa tu ranar da Iman tasan da zancen auren ta chanza masa magana ma ta daina masa amman duk tana a hakan ,bata taɓa kauce rana ba tare da ta girka masa abinda zai ci ba duk da ita wani lokacin ma yana lura da ita bata ci 

haka duk lokacin daya bukaci ta bashi hakkinsa tana biyasa duk da ba wani sake masa jiki take ba 

a lokacin ya fara tunanin anya yayi ma iman Adalci kuwa?

a daddafe ya gama cin abincin ya nufi wajen aiki 

da yamma 

Iman na zaune a falo sanye take da doguwar riga ta material da hula 
Karar ƙararrawar ƙofar ta cika falon

da sauri ta koma daki ta dauko  gyalenta  sanin ba Suhail bane dan shi baya knocking sai da ya saka key ya buɗe

tana buɗe wa da mamaki taga yaya Mubarak

murmushi ya sakar mata 

"yaya Mubarak"

tare suka shigo palorn ta bashi wajen zama 

farin ciki ya kasa boƴuwa a fuskar ta na ganin yayanta Mubarak 

bayan ta gaishe shi ta tambaye Malan da Ammi ya ce"Bama wanda ya faɗa wa zaizo gidan ta"

tashi tayi ta dauko masa drinks da snacks ta ajiye masa 

Mubarak sai binta yake da kallo ganin damuwar da take ciki ta soma bayyana a jikin ta Iman din da ya sani ba ita yake kallo yanzu a gaban sa gaba ba fuskar babu walwala kamar yadda ya saba gani ba komai ke bata mata raina da wuri ba hakan yasa kullum fuskar bata rabuwa da walwala

idanun ta sun kumbura alamar kukan da take sha 

"Iman meke damunki"

da sauri ta saki ƙasar mayafin da take wasa dashi jin tambayar da yaya Mubarak ya watso mata tun shigowar sa take ƙoƙarin boƴe damuwar ta gudun kar ya fuskanci wani abu"

murmushi yaƙe tayi "bakomai yaya"

"Iman yaushe kika fara boƴe min damuwar ki"

"yaya na fada maka babu wani abu"

Mubarak bai matsa mata ba.

To shikenan Amma idan kina da wata damuwa, ki sanar dani baki da wasu mutanen da suka wuce mu nida su Malan dan haka kar ki bar abinda zai Cutar dake A zuciyar ki"

Kai kawai ta jinjina

tashi yayi zai tafi ta ce"yaya baka ci abinda na kawo maka ba"

"na koshi iman,akwai inda zance yanzu"

ta raƙo sa compound kenan motar Suhail na shigowa bayan yayi parking ya nufi inda suke tun da ya shigo yake kallon dariyar da iman keyi da Mubarak a ransa yake tunanin ina ma dashi take wannan walwalar  haka har ya manta rabon da ko murmushi Iman ya gani

har gate ta raka ta koma ciki 

a falo Suhail ya zauna iman na shigowa ta nufi hanyar bedroom din ta 

"Iman" ya kira sunanta  juya ta kallesa idanun suka haɗu ya waje guda ba tare da ta dawo ba 

Wata irin nutsuwa ce ke fita daga gareta duk da damuwar da ke tattare da ita

"Iman ina so nayi magana dake"

ganin bata da niyyar dawowa yasa ya cigaba da maganar sa

"miya chanza ki cikin ƴan kwanakin nan nayi maki wani laifi ne"

haushi Maganar sa ta bata tambaya ma yake yayi mata wani laifi Suhail ya wuce duk tunanin ta 

kallon sa tayi daga sama har ƙasa "ba wani laifi da kamin Wani lokaci mutum idan ya gane ba shi da muhimmanci a rayuwar wani, sai ya bashi waje ya cigaba da Rayuwa da zabin ransa ba wanda aka zaba masa ba"

sai da kwakwalwar Suhail ta daina aiki na wucin gadi tabbas Banda su biyu a gidan zaiyi tunanin wani ya fadi wannan maganar ba iman ba yana ganin shiru shiru ta bai taba zaton zata yanka nashi magana irin haka 

bata jira ya kara magana tayi shigewar ta daki 

a daren Suhail kasa bacci yayi ya jima yana tunani maganar da Iman ta gaya masa 

text message zeenah ya shigo 
Amma abin mamaki, yau bai ji farin cikin da ya saba ji ba.

Sai wani irin tunani da ya hana zuciyarsa sukuni.


tun daga Ranar Iman ta miƙa Al'amarin rayuwar ga Allah cikin Nasara tana samun saukin ciwon zuciyar ta

Haka rayuwa ta cigaba a tsakanin su ta daina sa ran komai daga Suhail bakin dashi ta dafa abinci ta basa idan dare yayi ya nemi hakkin sa ta bashi 


Kwanaki nata tafiya har yazo saura sati guda daurin auren Suhail da zeenah 

Sai dai duk da farin cikin da ke cike da  Zeenah akwai wani sirri da babu wanda ya sani 

Sirrin da idan ya fito zai iya rusa auren tun kafin ranar ɗaurin aure

mami shirye-shirye biki take da gasken gaske har anko ta fitar ita da ƙawayen wanda zasu saka ranae dinner ba ƙananun kuɗade take kashewa wajen gudanar da shagalin bikin a cewar ko dukiyar ta zata kare sai ta fita kunyar manyan baƙin data gayyato zuwa wajen bikin tillon ɗan ta Muhammad Suhail wato mai sunan mahaifin ta.

ya rage saura kwana biyu bikin Takarda suhail ta transfer din wajen aiki ta fito kamar yadda ya nema yana so ya koma Abuja inda a chan ne ya gida babban duplex mai dauke da part biyu inda zai hade matan sa gaba ɗaya.

koda yazo sanarwar mami zasu koma Abuja tare da iman taji ɓacin ci har take fada masa taya zai haɗe"zeenah da ƴar malamai ya barta ta cigaba da zama a Kaduna in yaso sai ya kai ita zeenah Abuja"

suhail ya ce"mami banda ra'ayin raba kan matana dukkan ɗaya suke a wajena" 

ana sauran kwana ɗaya bikin zeenah gaba daya yan uwan suka cika gidan Malan aunty Zarah naima da sauran dangin kusa da na nesa duk sun hallara a gidan 

harda Iman da Suhail ne ya matsa akan lalle sai tazo badan ranta yaso tabi shi suka tafi 

palorn Mami ya kaita wanda ke cike da bakin ta har ƙasa ta gaida kowa na cikin dakin 

mami taji daɗin ganin ta ko bakomai ta samu mai kawo wa bakin ta ruwa 

"ke Iman" Mami ta kira sunan ta

dago manyan idanun ta tayi ta zuba su cikin na mami 

"kije Kitchen akwai ruwa da drinks ki kawo baƙi na"

tashi tayi kamar wanda kwai ya fashewa ta koma Kitchen ta fara kawo ruwa da drinks tana ajiyewa gaban baƙin mami 

ɗaya daga cikin abokan mami ta ce"wai ina kika samu yarinya mai hankali haka"

kwabe baki tayi ta nuna ta da yatsa "Matar Suhail ce"

kowa kallon mamaki yake mata daya daga cikin ta ce"yanzu tsakani da Allah shine zaki maidata ƴar aiki"

murmushi mami tayi ta ce"kar ku damu ta saba ai daga gidan Malamai ya dauko ta cikin masara da miyar kuka kin ga wahala ba bakon abu bane a wajen ta"

Kalmar ta soki zuciyar Iman amma ta yi shiru so take tayi kuka amman ta daure zuciyar ta 

wata dake gefe ta kalle iman ta ce"kinga tashi ki karo min snacks din nan dan bai ishe ni ba"

tashi tayi ta koma Kitchen ta fito da plate din suka hadu da aunty Zarah wanda tun zuwan ta sai yau suka hadu da iman kunyar ta take ji dan gaba daya ta dauki Alhakin kara auren Suhail ta daura sa a kanta 

Da mamaki ta ga Iman tana ɗaukar wata katuwar tire hannunta 

Zarah ta ce"Iman ina zaki da wannan"

murmushi tayi ta ce"zan kaiwa bakin mami"

ido ta zaro tace kadai tun dazu ke ke serving din su amshe tire din tayi 

"aunty Zarah da kin barshi ma na ida"

a tsawace aunty Zarah ta ce"bazan barki ba Iman,taya kina matsayin suruka a gidan ace ke kike serving baƙi a ranar bikin mijinki this is not fair abinda mami take sam bata kyautawa"

hannunta ta kama suka fita da ita daga kitchen 

Kai tsaye suka nufi part ɗin Aunty Fauziya

Aunty Fauziya tana ganin Iman ta tsaya cak ganin duk tayi chanza ba Kamar lokacin bda suka shigo tare da Suhail ba 

Aunty Zarah cikin fushi cikin fushi ta ce

"Wallahi Aunty idan ba ki shiga maganar nan ba, Mami za ta cutar da yarinyar nan" 

taya za'ayi ta maida ta yar aiki fisabillilah zata ji mu ma surukan mu su mana haka ne itama ma tana da iyayen da suke santa kamar yadda itama take san nata miye laifin dan kawai ta Auri danta sai ta cigaba da taka ta "

Aunty Fauziya ta ce"sai haƙuri kinfi kowa sanin halin laila"

fuuu Aunty Zarah ta wuce ta fita aunty Fauziya ta kai Iman Bedroom dinta ta kwanta.

jin shiru Iman bata dawo ta biyo ta ƙasa daidai lokacin Suhail na shigowa 

tunda ya kawo Iman yake  jin kamar hankalin sa bai kwanta ba yana gudun kar mami tayi mata wani abu 

kallon mami yayi ya ce"Ina Iman"

nima ban sani ba ka duba Kitchen 

A dai-dai lokacin Aunty Zarah ta dawo falon

Kallon ɗaya Suhail ya yi ya mata ya fahimci akwai wani abu da ya faru.

“Aunty Zarah lafiya"

Ta kalle shi cikin fushi ta ce

“Ka tambayi mahaifiyarka da ta  maida matarka yar aiki a gaban baƙi ana aikinta kamar baiwar Allah. 

gaban sane ya fadi ya kalli mami cike da tuhuma sanin bata da gaskiya tayi sum-sum ta koma sama 

Fuskar Suhail ta canza gaba ɗaya yaji kunyar kansa 

"tana ina"

"tana Dakin aunty Fauziya"

Ba tare da ya ƙara magana ba ya juya cikin sauri ya nufi part ɗin Aunty Fauziya 

ganin bata falo ya nufi bedroom a can ya tarar da Iman zaune gefen gado

Idanunta sun yi ja saboda kukan da ta yi amma tana ƙoƙarin ɓoyewa

Suka haɗa ido.

babu wanda ya iya magana

Sai Suhail da ya ce cikin murya mai sanyi

"Iman tashi mu koma gida"