Chapter 2
by @reza12
MATAR MAZA
Duk wanda ke buƙatar a tallata masa hajarsa, zai iya mana magana ta wannan number (*** ko +23408100785178)
Chapter 2
Tun tana yi ana kushe wa, wasu ma basa iya ci har zuwa yanzu da take ƴar shekara sha biyar hannunta ya gama faɗa wa, wani lokacin ma idan tayi wani girkin kamar matar gida. Irin nauyin da Azima ta ɗauka akan ƴan uwanta da mahaifiyar ta, irin nauyin da ɗa namiji ke iya ɗauka ne. Wani lokaci Hajiya da kanta take cewa Azima Mace ce da namiji Ubangiji ya haɗe mata a guri guda saboda juriya da kuma ƙwazon da take da shi. Haka kannenta ko makanrta ne sai ta tabbatar da sun tafi kafin ita ta shirya ta tafi nata. Shi kansa Baba Azima tana daga cikin yaran da yafi so, domin ƙoƙarinta da kuma nuna kulawa akan sa. Sau da yawa wani lokaci kawai zai kirata idan zaiyi baƙi yace tai musu abinci, haka idan sunci zai tai mata addu'a da saka mata albarka yana farin ciki. Haka ɓangaren sauran yan uwanta na gidan idan mutum ya so zata zauna da kowa lafiya, idan kuwa akasin haka ne shima zata bi ta yadda aka zo mata. Tana da fushi sosai da zuciya mai munin gaske, shi yasa sau da yawa idan aka ga ana faɗa da ita to itace kawai mara gaskiya, duk da cewa sau da yawa ita ake tsokana, amma masu iya magana na cewa wanda bai jin haƙuri shine mara gaskiya.
Azima ta na fita daga ɗakin nasu bata tsaya a ko ina ba sai ƙofar ɗakin Ammy. Babu sallama ta tura ƙofar ta shiga tana kiran sunan Jidda kaman dai yadda Maryam tayi. Bata tsaya wata-wata ba ta ɗauke bakinta da mari sannan ta buɗe baki zatayi magana Maryam ta mike tsaye ta kai mata mari itama. Ta kauce tana dawo da kallonta gurinta ta ce "Anty Maryam ke kin sani ba tsoron kowa nake ji a gidan nan ba wallahi, babu yadda za'ayi na daki jidda ba tare da dalili ba, mai yasa ke ba zaki tsaya kiji abun da ya faru ba kika hauni da duka, to gata nan ki tambayeta kiji mai ta min?" Ta ƙarasa tana nuna jidda ɗin da ta fashe da kuka. Ammy ce ta buɗe labule daga uwar ɗaka ta shigo tana tambayar abun dake faruwa. Kafin kowa ya bada amsa Sadiya ta buɗe ɗakin da sallama ta ce "Anty Azima Hajiya na kira, tace idan ta isa dake kizo yanzu". Ta na faɗa ta juya bata ko ƙara bi ta kansu ba. Ganin zata fita ne Ammy ta ce "Wa ya daketa take kuka haka?" Maryam ta ce "Gata nan zata fita" Daidai lokacin kuwa sun bar ɗakin. Sadiya na gaba tana binta a baya sai sauri take. Suna shiga ɗakin Hajiya ta ce "Ina kika je, ba dai ɗakin su kika je ba ko?" Ta faɗa ranta a ɓace. Azima tayi shiru sai ƙunƙune take yi ƙasa-ƙasa. "Ba magana nake miki ba kin min shiru?" Hajiya ta faɗa da tsawa. "To mai zaisa ita tazo har ɗakin mu ta dake ni, ko an ce mata b..."Rufe min baki a gurin kafin na ƙaraso na fasa miki shi, wato ke kullum burinki shine ki nunawa duniya cewa ban isa da ke ba ko? Duk wani faɗa sai dai ace Azima Azima, duk wani abun magana Azima, ke ko kunyar ƙannenki ma baki ji ko, kina so damuwarki tayi ajalina ko Azima, kece babba amma kece fitinanniyya ko, ban isa ganin idona yasa ki fasa abun da kikayi niyya ba ko Azima?". Hajiya ta ƙarasa tana hawaye domin tasan wannan abun karshe kanta zai dawo. Ta ce "Kiyi hakuri, ba zan sake ba". Ta na faɗa ta shige cikin uwar dakinsu domin bata son wannan faɗan na rashin dalili, wato so take itama ta zama kamar ita a dake ka a hana ka kuka, to wallahi ita dai ba zata jura ba, muddin da ranta da lafiyar ta, babu wanda zai taka ta bata rama ba, gara ace an mata duka akan ƙwatar hakkin ta, akan dai taja baki tayi shiru. Hajiya ta share hawaye tana bin bayanta da kallo. A ranta ta ce "Da ace ina irga wannan kalmar ta cewa yi ba zan sake ba da Azima take faɗa da yanzu ta cika dakin da suke ciki, amma kullum sai ta sake, har ma fiye da yadda tayi a baya.
Ai kuwa ko minti Uku ba'ayi ba, sai ga Ammy ta fito tana zagin halin Azima ɗin, tana faɗin shigiya yar iskar yarinyar wacce ta gagari uwarta, to wallahi bari Baba ya dawo dole ayi mata iyaka da Jidda, idan kuma ba haka ba, zata sa yaranta maza su ɗaure yar iska su zane ta. Sosai ran Ammy ya ɓaci domin ai ko ba komai da tai mata magana ya dace ta tanka mata. Hajiya na jinta amma bata ce komai ba, itama Azima na cikin ɗakin suna jiyo ta. Ganin mitar yaƙi karewa ne yasa Maryam fitowa tana taya uwar tata.
Misalin ƙarfe takwas suna zaune a palo tana taya ƙannenta aikin gida na makaranta tajiyo ana mata kiran mafarauta. Sarai ta gane mai muryar, amma tayi banza dasu taci gaba da abin da yake yi. Harma Ummi tana sake faɗa mata cewar ana kiranta amma ta harareta taci gaba da nuna musu yadda zasu yi. Maryam ta buɗe ƙofar palon ta shigo. Ganinsu gaba ɗaya a palo yasa ta faɗin "Kan ubancen, yanzu duk wannan uban kiran da nakeyi ba barci kuka ba kuna jina, harda ku Yusra ba zaku amsa ba idan ita tafi ƙarfin amsawa ko?" Ta ƙarasa tana tsaye a ƙofar. Sai lokacin ta ce "To haka ake kiran mutum kamar wanda ya ɓata?" Maryam ta ce "Ba laifinki bane, kiyi abun da kika ga dama, akwai lokacin da zamu haɗu, Baba ne yake kiranki, yana plao, idan kinga dama kizo idan kinga dama karki zo". Tana faɗa ta saki labulen ta fita. Gaban Azima ne ya fadi, har sai da ta dafe ƙirji, domin ba karamin tsoron Baba suke yi ba. Ta miƙe da sauri ta nufi ɗakin Hajiya, dukda kuwa tasan yanzu tayi barci. Ai kuwa tana shiga ta samu tayi barci ɗin, dama da wuri take barci abunta. Ta fito da sauri ta nufi ɗakin Baba tsoro fal ranta. Tana shiga ta samu Jidda da Maryam gaba ɗaya sun kama kunne. Hakan yasa itama tun kafin ayi mata magana ta kama nata kunnen. Ammy ce zaune a ɗaya kujerar tana hararar ta tun da ta shigo. Baba Ya amsa gaisuwar da tayi ya ɗora da faɗin "Wacece wannan a gurinki?" Ya faɗa yana nuna Maryam bayan yasa sun saki kunne.
Da sauri ta ce "Yayata ce".
"Kin san da haka shine kike mata rashin kunya?"
"Wallahi bab..."
Da karfi ya ce "Shatop this your stupid mount" Tuni ta rufe bakin da hannu ɗaya jikinta na rawa.
Ya ca "Bata haƙuri kice ba zaki sake ba". Take ta shiga bata hakuri tana cewa ba zata sake ba. Itama Maryam ɗin ya sake ja mata kunne kuma yace su rungume juna, sannan yace Maryam ta tashi ta tafi. Maryam na fita. Ya dawo kan Jidda. Itama kaman yadda a kaiwa Azima ta bata hakuri. Ya ce su tashi su rungume juna. Haka kuwa suka rungume juna yace suyi murmushi kuma su gaisa. Daga haka yace da jidda ta tafi itama. Ya dawo da kallonsa ga Azima ya ce "Wato ke kullum baki son zaman lafiya ko, babu ranar da zata fito ta fadi ba'a ce min kin yi faɗa da wani ba ko?" Ta girgiza kai. Ya ce "Gobe ina da baki da yamma, zakiyi musu abinci, dan haka ki zauna cikin shiri". Ta amsa, sannan ya bata umarnin tafiya. Ta na fita ta fashe da kukan da take ta riƙewa saboda kawai an sa ta bawa Maryam haƙuri. Har ta isa sashen nasu kuka take yi na zafin rai, dama haka take, idan an mata faɗa sai kuka, ko faɗa suke da mutum aka raba zafin rai yasa ta fara kuka koda kuwa itace tayi nasara, barin ma idan an naimi ta mayar da magana. Bayan sun fita Ammy ta buɗe baki zatayi magana domin ba haka taso ba, amma Baba ya ɗaga mata hannu yace baya son a sake tada maganar.
Kaf yaran gidan wanda aka aurar da na yanzu babu Mace mai farin jini irin na Azima, daga kan samari harda ma baƙi, sannan irin matan nan ne dogaye marasa jiki, fara ce ba irin sosai ɗin nan ba, kasancewar tayi kama da Hajiya yasa bata yanayin da yan gidan nasu, wanda gaba ɗaya kusan kamanninsu ɗaya kasancewar su alhali guda. Tun tana yar shekara sha ɗaya samari ke nuna suna sonta. Sosai take da shiga rai, ko dan rashin haƙurinta da masifarta. Sai dai kuma ita Allah ya bata wani irin zuciya na rashin yarda da Namiji ko nace dogara da namiji. Bata taɓa kawowa ma zata yi Aure ba bare ma har a kai ga soyayya, bata kaunar alaka ya haɗa ta da namiji kwata-kwata. Izuwa yanzu da ta kai sha biyar duk alamun girma na ƴa mace sun nuna a jikinta, sai samari suka ƙara himma, ita kuma har lokacin bata ji sauyi akan abun da ta je a ranta ba. Bata jin zata iya aure ta bar Hajiya a wannan halin, kuma ta yi aure ta bar kannenta a wannan gidan nasu. Har Hajiya na mata faɗa akan rashin kula samarin da take yi, a lokacin sai tace ita sam bama zatayi aure ba, babu namijin da take jin zata iya so, har tana faɗin ita fa babu soyayya a zuciyarta sai soyayyar ƙannenta da kuma Hajiya sai Baba.
Da safe bayan ta shirya kannenta sun fita school, itama cikin sauri ta shirya tayi sallama da Hajiya ta nufi sashen Baba domin amsar kuɗi. Da sallama ta shiga tana sunkuyawa ta gaida shi. Ta ɗago suka gaisa da baƙon da ta gani tare da shi. Ganin kamar gaisuwar rashin sani tai masa yasa Baba faɗin "Azima Musa ne fa yayanki, baki gane shi bane?" Ya faɗa yana dariya. Itama jin haka yasa ta ɗago suka haɗa ido. Ta kafe shi da ido ƙurr! Amma dai bata gane shi ba har lokacin. Sai taji yana faɗin "Wai Azima ce ta girma haka, ai lokacin da na tafi bata girma ba, dama dai Maryam ce zata iya gane ni". Ya ƙarasa har lokacin idanunsa a kanta. Baba ya ce "A'a lokacin kam ai itama da wayonta, kawai dai saboda ba'a nan kake ba". Ya ce "Gaskiya ne, to Azima ya school ɗin, sai yanzu za'a tafi?" Ya faɗa yana cigaba da kallonta, wanda take jin hakan a jikinta. Baba yasa hannu a aljihu ya dauko kuɗi ya bata. Ta sa hannu biyu ta amsa tana mikewa ta bar ɗakin. Har ta dawo daga school bata manta da batun girkin Baba ba, yasa tana dawowa ta je tace masa mai za'a dafa da yake yau yana gida. Abun mamaki har wannan lokacin Mutumin ɗazu yana gidan, sannan ga yayyeta mata biyu tare da shi alamun dai da gaske ɗan gida ne ganin yadda suke manne masa. Sai ta fara mamaki to yaron waye a cikin Ammy da Mama, dama bayan wanda ta sani suna da wasu yaran ne dama. Tuni ta watsr da maganar ta fara ƙoƙarin aikin da aka bata.
Amma abun mamaki abun ya tsaya mata arai har sai da ta tambayi Hajiya. Hajiya ta ce "Sannu uwar shiririta, Musan ne kuma baki sani ba yau da yake da baki rabo da shirme ko, Musa dai yaron Kawunku Mato shine kika manta". Tayi shiru sai cen ta ce "To kuma Baba ya ce "Yayana ne, ke kuma kince yaron kawu Mato ne, nifa nayi tunanin ma ɗan gidan nan wallahi, ashe ma ba dan gidan nan bane Baba harda wani gaida shi da ladabi". Taja tsaki tayi waje, duk da kuwa shi kawo Mato ɗin ƙani ne a gurin Baba. Tuni ta watsar da maganar ta shiga girki. Da yake ranar girkin Ammy ne yasa lokacin da ta kusa karasawa ita kuma ta shigo kiching ɗin. Bata ce mata komai ba ta sauke abincin domin ya nuna. Ta ɗauko kular da zata juye ta ajiye kusa da abincin.
Ammy ta ce "Kin taɓa zubawa Baba abinci a wannan kular dama?"
Ta faɗa tana ɗauketa.
"Yau zan fara". Ta faɗa tana kokarin sauƙe tukunyar.
"Wannan kular ta abincin gida ce, ba na baƙi ba, dan haka idan zaki wanke waccer ki yi amfani da ita to, idan kuma ba zaki wanke ba sai ki hakura". Ta ƙarasa tana rufe kular ta kawar da ita cen gefe guda.
Azima ta ce "Amma dai ai yau abincin da yawa ne, kuma yafi karfin wannan kular, sannan ai ni ce dai zan wanke ko sun gama ba kowa ba".
"Kular ce kawai ba za'ayi amfani da ita ba, ko baki ji bane". Ammy ta sake faɗa tana zare mata ido, domin tsaf zata iya marinta idan ta sake magana.
Azima da ranta ya ƙara ɓaci ta ce "Saboda me?"
Azuciye ta ce "Saboda ba ta uwarki bace, yar iskar yarinya kawai, shegiya, ko uwarki tazo da kula gidan nan ne, ke wallahi ki kiyaye Ni fa". Ta faɗa a fusace.
"A'a ni dai a bar zagin uwata da babu ruwanta ato, uwa bata fi uwa ba".
"An zagi uwar taki dan ubanta, uwar taki har wata tsiyar ce da ba'a zaga ba?".
Budar bakin Azima sai cewa tayi "Wanda ya zagi uwar wani dai ance mana uwarsa ya zaga". Tana faɗa tayi waje abunta, sai gata ta dawo da toka cikin hannunta. Ta buɗe kular da ake magana akai ta juye tokar ta goke ciki da ita. Ta ce "Ga nan kular ku, na ɓata wankewar da nayi, bari naje na dauko tamu". Ta bar Ammy da baki abu de ta kasa maka sai kallonta. Azima na shiga ɗaki Hajiya ta ce "Ga wannan kular injin Baba wai ki ɗibawa yayanki Musa abinci anan ki kai masa palon sa, na baƙin kuma ki kawo nan a ajiye, za'a zo a ɗauka a kai cen gurin aikinsu". Azima ta kalli Hajiya ta kalli kular ta ce "Waye yayana Musa kuma?" Hajiya ta ce "Ohoo, bana son shiririta fa Azima". Tana faɗa ta bar gurin domin ta lura kakarta take son mayar da ita. Sai dai kuma ita Azima har ga Allah da gaske take ta ma manta da wani Musa gaba ɗaya. Yusra ta ce "Yaya Musa mana tun ɗazu yana palon Baba tare dasu Yaya". Ita har ga Allah sai yanzu ma ta tuna, domin tun lokacin da taji bata da alaƙa da shi ta watsar da batun sa, yo to ko tana da alaƙa da shi ma muddin ba ɗan ɗakinsu bane cen shi ta shafa. Ta bi Hajiya ɗaki tana tambayar ina za'a zuba abincin baƙin domin yayi yawa ba zai ɗauki asalin kular da ake zuba masa ba. Hajiya ta ce "Wani lokacin baki da wayo sam, muje naga abincin da ba zai shiga kular ba. Suna shiga kiching ɗin suka tarar da Ammy da Maryam suna ta aikin ɗaura sanwa. Hajiya ta musu sannu da aiki suka isa gurin abincin. Tana buɗewa ta kalli Azima itama ta kalleta. Gaba ɗaya wannan tokar ce da ta zuba a kula aka mayar mata dashi cikin abincin. Da karfi ta ce "Wacce ƴar abu ta kazar uba ce ta min haka"? Tana rufe baki Hajiya ta buge mata shi tana a'uziya. Azima ta ɗora da faɗin "Wallahi zubawa akayi, kuma wallahi ba zan yarda ba, na gama shan wahalar dafa abincin tun ɗazu, wallahi ko wacce shegiya ce sai..." Dai sauri Hajiya ta ɗaga murfin tukunyar zata buga mata taja da baya tana cigaba da kuka da zagi. "Anya Azima babu wanda suke koya miki iya shege a waje, wani irin zagi ne wannan, a ina kika ji shi, waye zai zuba miki abu a cikin abinci idan ba ke a shirmen ki ba"? "Hajiya haka kawai a zuba min toka, to wallahi na san waye kuma sai na rama domin ni dai ba ni na ce wallahi, na rantse da Allah ba zan haƙura ba". Ammy da Maryam basu ce musu ci kanku ba, sunyi kamar basa kiching ɗin. Duk yadda Hajiya taso da Azima tayi shiru taƙi. Haka ta kwashe saman abincin suka zuba a wani kwanan, sannan ta juye sauran a kula. Ganin Hajiya na neman ɗibarwa Musa ne yasa ta ce "Haba dai, duk da abincin ya ragu sai an bashi, kawai ya tsaya ya ci na gida shima, ni dai wallahi ba abinci na ba". Hajiya ta ce "Bana son shirmen banza fa, meye dan ya ci, kuma ba Baba ne yace a bashi ba". "To kuma su idan baƙin basu koshi bafa, shi ba yana gida ba, ni dai wallahi ba zan zuba masa ba, idan kuma zaki kwashe mai tokar a wanke masa ne to". Ta ƙarasa da gaskenta, barin ma da taga kular bata wani cika yadda take so ba. "Bana son wannan shashancin naki fa Azima, kaɗan za'a diba masa ba da yawa ba, yunwa yake ji bai karya ba tun safe?" Ai tuni ta saɓi kular tayi gaba. Hajiya ta bita da kallo. Haka tana kan kular nan har masu ɗauka suka zo suka tafi da ita. Ta koma kiching ɗin ta wanke duk abin da tasan ta ɓata. Tana yi tana satar kallon su Maryam. Har ta gama ta fito. Ita kaɗai tana ta saƙe-saƙen yadda zatayi. Kusan cin karo tayi da shi zai fito daga dakin Hajiya riƙe da plet shaƙe da abincin da ta dafe. Ya kalleta ta kalleshi. Ya ce "Ina ta jira baki kawo min ba shi yasa na biyo ki kar yunwa ta kashe ni, ko kina ce ni baƙo ne a gidan?" Ya faɗa da sigar wasa. Ta bi abincin da kallo tana mamakin yadda har aka ɗiba bata sani ba. Ta ce "Zan wuce?" Ta faɗa a hankali ganin ya tare mata hanya, kuma yana cin abincin a tsaye, sai hakan ya sake bata haushi. Ya ɗan matsa mata kaɗan sannan ya ce "Please ki kawo min ruwa yanzu ina palo". Ya faɗa yana ƙara gaba. Ta ƙarasa ɗakin tana haɗe sama da ta ƙasa. Ganin bata ga Hajiya a palon bane sai kannenta yasa ta nufi ɗakin har kuka ya fara zuwar mata. Tana shiga taga baƙar leda a kan gado shaƙe da kaya Hajiya na ta ƙoƙarin buɗewa. Ta ce "Hajiya wa ya ɗibar min abinci ya bawa w w n.." kukan ya hana ta ƙarasawa ta fashe da shi tana tsaye. Tuni Hajiya ta gane dalilin maganar ta yi dariya ta ce "Babu wanda ya ɗibar miki abinci, kin manta ke da kanki kika ce min na wanke wanda aka saka toka sai na bashi?" Ta faɗa da yar dariya, hadi da mamakin halin Azima. Sai lokacin ta ɗan ji sanyi kaɗan ta ce "To yaushe har kika gyra ban sani ba?" "Wai to dole ne sai na faɗa miki, ina ce tun da kika fita da abincin nan babu wanda kika bari ya taɓa, ko dai ni aljana ce da zan ɗiba baki sani ba"? Ta ƙarasa maganar da faɗa wanda yasa Azima ta fashe da dariya jin dai mai toka aka bashi. Sai kuma ta ce "Wa ya kawo miki kaya Hajiya, wasu kala ne?" Ta faɗa tana share hawaye. "Ban sani ba". Ta bata amsa. Take suka shiga buɗe kayan suna yabawa. A ciki ta samu doguwar riga da kuma abubuwan ci. Tana ta murna da rigar domin tana son irinta.
Misalin takwas na dare Baba ya tura a kirata, ko da tazo yayi mata godiya kamar yadda ya saba idan tayi masa aiki. Ya miƙa mata leda ya ce "Ga shi sunce a baki wannan ladan girki". Ta amsa tana murna. Ya ce "Idan kinje ki turo min Hajiya". Ya faɗa yana dawo da kwallonsa ga wayarsa da ta fara kara. Bayan ya ɗaga ya rage ƙarar tv sannan ya fara magana. Yana cikin maganar Hajiya ta shigo ta samu guri ta zauna a ƙasa kasancewar ba ranar girkinta bane. Bayan sun gaisa ya tambaye ta gida da yara, ta amsa tana masa addu'ar kasuwa mai albarka. Bayan sun gama ya ce "Naso na bari muyi maganar gobe ranar girkinki, amma abun yazo da sauri yasa nace zan faɗa miki domin ki sani. Ya cigaba da ce wa "Mato ya same ni da batun Musa yaga Azima kuma yana so, sannan kuma aure yake so a ɗaura da wuri kafin ya koma, tun a lokacin ma na ce masa na bashi ita, dama a cikin ita ko Maryam nake da burin a haɗa su, to tunda Allah yasa ya ga ita Azima ɗin yana so ai alhamdu lillih, dan haka ki sanar da ita, ta san da batun, a kowanne lokaci za'a iya daura aure kafin ya tafi". Hajiya gabanta ya faɗi wanda har sai da fuskarta ta nuna. ta ce "To Allah ya tabbatar da alkairi yasa abokan zama ne". Ya amsa da amin yana ɗan nazarin ta. Da sauri ta tashi ta fita tuk jikinta yayi sanyi sosai.
Hajiya na shiga ɗaki ta tarar Azima ta buɗe ledar da aka bata suka ga abubuwan ci na zaƙi da kuɗi ɗauri ɗaya na ɗari-ɗari. Hajiya ta zauna tana ta kallonsu. A karon farko tai wa Azima kallo irin na matar aure. Bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba, a ranta tana auna halin Azima da zaman aure. Zuciya, taurin kai, kafiya, rashin ji, rashin kunya, rashin tsoro. Uwa uba rashin hankali. Duk abun da take bata san tana kallonta ba. Ta ce "Hajiya me ya faru, wacece tai miki wata maganar?" Ta faɗa tana dawowa kusa da ita. Hajiya ta sake kallon ta, gata dai yarinya amma ta zama kamar itace Uwar tasu, ta kula da kanta, ta kula da kannenta, sannan ta kula da ita, yanzu idan har tayi aure yaya zasuyi. Take wani tari ya sarketa mai karfi, ta fara yi kamar zata amayo da kayan cikinta. Sosai take yi har sai da ciwonta ya tashi. A daren a asibiti Hajiya ta kwana tare da Musa wanda shine ya kai su. Washegari suka dawo da magunguna, likita na ƙara kafa musu sharuɗa a kan ciwon nata. A lokacin da suka dawo har Azima ta shirya yaran sun tafi makaranta, ita ɗaya ta rage. Tare suka shiga da Baba ɗakin, ya kwantar da ita yana mata sannu. Sannan ya kira Azima ta ya sake nuna mata yadda zata dinga bata maganin. Har ya fito ya dawo ya kirata palo. Tazo. Ya ce "Jiya Hajiya ta miki magana ne?" Ta girgiza kai. Babu wani kwana-kwana ya ce "Dama na zaɓa miki Musa ne ɗan uwanki a matsayin wanda zaki aura, shi ya ganki ya ce yana so, dan haka na yarje masa, ina fatan dai babu matsala ko?"...📝
Kuci gaba da bina a hankali, ina tabbatar muku da cewar labarin na daban ne. Akwai kwamachala mara iyaka a gaba.