RAGAYAR DUTSE

PAGE 16

by @nanahaleema11

*RAGAYAR DUTSE.*


             ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 016.*


Islaha ta riƙo matar  ganinta zube a ƙasa ta ce, "Mama Sannu, baki ji ciwo ba?." 


Daada ta ɗago kai ta kalli Islaha ta ce, "Ba ku yi min komai ba, gajiya ce kawai.”


Islaha ta ce, "To Mama miƙe tsaye, magrib ta yi kina yawo ke kaɗai." 


Ta riƙe Daada suka miƙe tsaye ta ce, "Mama a ina ki ke?." 


Ta kalli Islaha ta ce, "kaina ne ya juye, na rasa ina zan je." 


Islaha ta ce, "mu shiga napep sai a sauke ki a gida." Islaha ta taimaka mata ta shiga sannan itama ta shiga.


Sai da suka fara tafiya sannan Islaha ta ce, “Mama ina za a kai ki?." 


Daada ta yi shiru tana tuna sunan unguwar, sai daga baya ta ce, “Mafi’a.”


Islaha ta ce, “Malam kai mu Mafi’as quarters.”


Daada ta kalli Islaha tana murmushi ta ce, "na gode jikata, ba ko wanne yaran yanzu ake samu masu tausayin tsoho ba. Ya sunanki?." 


Islaha ta yi murmushi ta ce, "Sunana Islaha." 


Daada ta ce, "Ishlaya?." 


Islaha ta ɗan yi dariya jin yadda ta faɗi sunan abin dariya, ta ce, "Is...la...ha" ta faɗa a rarrabe yadda zata gane


Daada itama a rabe kamar yadda Islaha ta yi ta ce, "Ish...la....ya." 


Islaha ta yi dariya ta ce, "ki ce min jikar ki kawai Mama."


Daada ta yi murmushi ta ce, "sunan na yara ne irin ku. Na gode jikata, yaran yanzu ba kowa ne mai tausayi ba. Na ji daɗin taimakon ki sosai." 


Islaha ta yi murmushi ta ce, "babu komai Mama, ai kamar kakata ki ke." 


Daada ta yi dariyar jin daɗi, tana kallon Islaha ta ce, "Gaki nan baƙar bafulatana, kyakyakawa ma sha Allah. Ga kyau ga kirki, ga tarbiyya da sanin darajar tsoho.” Islaha ta sake yin murmushi bata ce komai ba.


Daada ta ce, “Kina da aure?." 


Ta girgiza kai tana murmushi ta ce, "bani dashi Mama."


"ai kuwa na samarwa jikana mata, daman yarinya mai hankali da tarbiyya nake nemar masa, kuma gaki na samu. Shikenan sai a yi bikin a huta.”


Islaha ta kuma yin dariya sosai ta ce, "Hajiya Mama kenan."



"Da gaske nake jikata, daman ina so na samar masa yarinya jinin fulani mai tarbiyya, kuma ga ki na samu."


"Mama ni an kusa bikina."


"Sai a fasa auren da wancan, jikana Muhammad zaki aura ba wani ba." 


Islaha ta sake yin dariya bata ce komai ba, dan bata ɗauki maganar da gaske ba, ta san irin wasan tsofaffi ne da suka saba.


Mai napep ya ce, "mun shigo unguwar." 


Islaha ta ce, "Mama mun shiga unguwar, a ina za a ajjiye ki?." 


Ta kalle ta ta ce, "gidan ɗana AbdulAziz."


"Ina kenan?."


"A nan unguwar ya ke, kawai gidan ɗana." 


Islaha ta girgiza kai ta kalli mai Napep ta ce, "ka san gidan?." 


Ya girgiza kai ya ce, "wallahi ban sani ba." 


Ta ce, "ka ɗan tambaya, ba za a rasa sani ba."


Ya fita ya je wajan wani mai gadin wani gida ya tambaye sa yana nuna masa Hajiya, yana ganinta ya gane ta ya kuma yi masa kwantance estate ɗin.


Ya dawo ya shiga ya ce, "ai mun kusa, gashi layin gidan can." 


Yana karya kwana zai shiga estate ɗin aka hanasu ƙarasawa saboda security da yake wajan. 


Islaha ta kalli Daada ta ce, "Maman hana mu wucewa, wai sai dai mu wuce da ƙafa." 


Sai a lokacin Daada ta kalli wajan ta ce, "in ji ubanwa? Matsa na fita ki gani." 


Islaha ta ce, "A'a Mama ki zauna, bara na yi musu magana."


Daada ta ce, "ke dai bani hanya." Islaha ta fita itama ta fito. 



Daada ta kalli ɗaya daga cikin masu tsaron ta ce, "waye ya ce bazan wuce ba? Na ce waye ya ce bazan wuce na shiga ba?." 


Ya kalle ta ya ce, "Kaka ba a shiga da napep wajan nan, sai dai ku wuce da ƙafa."


"In ji wa? Wallahi da babur ɗin zan shiga har gidan nan, sai naga wanda ya isa ya hana ni."


Islaha ta bita da kallon mamaki, ganin tsohuwa  da ita faɗa da neman rigima kamar bata girma ba. 


Islaha ta riƙe ta ta ce, "Mama ki tsaya, ba a wasa da irin wajan nan, zasu iya harbin ki. Mu je sai in raka ki har cikin gidan." 


Daada ta kalle ta ta ce, "nida gidan ɗana a ace bazan shiga ba? Sun isa su hana ni wuce?." 


Ta kalli mai Napep ɗin ta ce, "Mai babur mu je, sai na ga wanda ya isa ya hana ni shigewa ciki." 


Ɗaya daga cikinsu ya ƙaraso yana ɗaga bindinga sama ya ce, "Mama ki koma, ba a wucewa da keke, sai dai a ƙasa." 


Daada ta tsuguna ta buga ƙasa ta ce, "wallahi sai na shiga da babur ɗin nan, in ban shiga dashi ba ku ce ban haifu ba..." 


Ta kalli ɗaya daga cikinsu ta ce, "Kai shiga gidan nan, ka ce AbdulAziz ya zo in ji ni." 


Shugaban masu gadin gidan ya ƙaraso da sauri ya duƙa mata ya ce, "Daada barka da zuwa." 


Ta kalle shi ta ce, "yauwa Sulaimanu, shiga gida ka kira min AbdulAziz, ka ce yazo ina nemansa." 


Ya duƙa da girmamawa ya ce, "Ba ya nan Daada." 


Ta ƙarasa kan wani tudu na dutse ta zauna ta ce, "zan jira sa a nan, babu inda zan je sai na nuna musu matsayin da nake dashi. Duk sai na saka an kore su, zasu san sun wulaƙanta ni, har suna nuna ni da bindiga."


Islaha ta dafe kai, tana mamakin wannan faɗa na tsohuwa kamar ba babba ba. Ga rigima da ɗorawa kai, in banda rigima ina ita ina faɗa da masu tsaron hanya.


Islaha ta duba agogo ta ga lokacin sallah har ya wuce bata yi sallah ba, ta kalli Daada ta ce, "Mama ni zan wuce, sauri nake yi." 


Ta ta riƙo ta ta ce, "babu inda zaki je, sai kin shiga cikin gidan nan a wannan babur ɗin." 


Mai gadin ne ya yi musu bayanin wacece a gidan, duk sai suka rikice, suka ruɗe, gashi ta ce sai ta saka an kore su. 


Cikin taushin murya guda ɗaya ya ce, "Ki yi haƙuri Hajiya, ba mu san ke bace, duk muna wannan abun ne saboda tsaoron lafiyar ku."


Ta hararesa sannan ta kalli mai gadi ta ce, "jinin indiyawa ya dawo ko?."


"eh ya dawo Hajiya."


"Ai na san sai shi, zuwansa ne kawai zai saka a tsayar daku a wajan nan kamar wani zuwan shugaban ƙasa. Ku je gidan ku kira min Muhammadun, ya zo ya shiga cikin babur ɗin da kansa, mu shiga gidan a  tare."


"Ki yi haƙuri Hajiya."


A fusace ta nuna su ta ce, "kuma duk sai na saka ya kore ku wallahi." 


Suka haɗa baki wajan faɗin, "Ki yi haƙuri Hajiya, shiga babur ɗin sai ku wuce."


Ta harare su ta ce, "Sai da ku ka wulaƙanta ni? Nima sai na wulaƙanta ku sannan zan shiga." 


Suka dinga bata haƙuri tana shan ƙhamshi, daƙyar aka samu Daada ta shiga Napep ɗin nan, Islaha ma ta shiga aka buɗe musu suka wuce aka shiga da Napep ɗin har cikin gidan. 


Islaha tunda suka shiga take kallon gidan saboda girma da kyau, duk da ta taɓa shiga government house, ta shiga manyan gidaje sosai, amma wannan ya fi burge ta akan ko wanne gida. Ga motoci a zube kamar ba a so, ko ina mota ce babba da ƙarama.


Lokaci kaɗan jikokinta suka baibaye wajan, suna haɗa baki suna cewa, "Daada ina ki ka tafi ke kaɗai? Abba yana ta neman ki." 


Islaha ta fito tana kallonsu, musamman Banisha da take ta dariya kanta babu ɗankwali. 


Sai ta ji yarinyar ta burge ta, kana kallon ta ka san ruwa biyu ce, iya gashinta ya gwada hakan, dan bai yi kama da na fulani ba. Islaha ta zuba mata ido tana kallonta, gata yar duma-duma, irin yaran masu kuɗin nan.


Bashisha ta kalle ta ganin tana kallon ta, sai ta ce, "Sannu." 


Islaha ta yi murmushi ta ce, "yauwa." 


Sai kuma ta kalli Islaha ta ce, "kamar na san ki, Islaha ko?."


Islaha ta yi murmsuhi ta ce, "haka ne.”


Ta ɗan buɗe ido ta ce, "Wow, na ji daɗin ganinki. Ina ganin programs ɗinki a tiktok" ta faɗa tana bata hannu alamun su gaisa. 


Islaha ta saka hannunts a cikin na Banisha tana murmushi. 


_Kai, ka ji hannun yarinya da shegen laushi._ 


Islaha ta furta tana sake kallon Banisha tana ayyana Allah ya yi mana arzuƙi a ranta.


 Banisha ta ce, "Sunana Banisha" kafin ta bata amsa ta tafi a guje ta yi cikin gidan tana kwalla ihu kamar ƙaramar yarinya. 


Ta bita da kallo tana murmushi, tana sake maimaita sunan Banisha, tana aiyana su fa ƴaƴa masu kuɗin nan gudu ba komai ne a wajansu ba, duk shekarun mace dan ta yi gudu abu ne mai sauƙi a wajansu.


Islaha ganin Daada ta yi gaba ita da jikokinta, sai ta koma cikin Napep ɗin ta ce, "Yi haƙuri Malam, juya mu koma kawai bana son ɓata lokaci." 


Ya ce, "Hajiya ai da kin shiga, baki san alkhairi da zata yi miki ba."


"In rabona ne zai kira ni, mu je kawai." Bai musa ba ya ja napep ɗin ya juya suka fita daga gidan.


     Daada tana shiga ɓangarenta Abba ya shigo, sai da ta samu waje ta zauna sannan ya ce, "Daada ina ki ka je ke kaɗai? Hankalina ya tashi, tun ɗazu na fita ina neman ki, na rasa inda ki ka nufa." 


Ta yi shiru bata ce komai ba, sai ta kalli ƙofa ta ce, "ina yarinyar da ta dawo dani ta ke?."


Ya kalli ƙofa shima ya ce, "babu kowa a nan."


"Akwai yarinya da mu ka dawo tare, tana ina?." 


Kafin ya yi magana aka shigo da sallaama, ta amsa ta ce, "Ke ina yarinyar da muka shigo da ita a babur?." 


Ta ce, "Daada ai sun tafi, tun kafin ki ƙaraso suka hau babur ɗin suka tafi." 


Daada ta ce, "Sun tafi fa ki ka ce, ta tafi ba tare da mun yi sallama ba? A yi maza a bi bayanta a nemo min ita yanzun nan." 


Janan ta ce, "Daada a ina za a ganta? Ai kawai ki ƙyaleta."


"Bazan ƙyale ta ba, aje a nemo min ita,

ko ni na tashi naje na nemo ta" ta faɗa tana miƙewa. 


Abba ya ce, "A'a, baza a yi haka ba. Janan je ki ki faɗawa drivern Daada, ya bi bayansu ko zai gansu." 


Janan ta juya ta fita tana ƙunƙuni, banda rigima irin ta Daada ko a ina za a gansu oho.


Abba ya ce, "Sannu Daada." Ta ɗaga masa kai tana shan ruwa.


Abba ya ce, "Don girman Allah ki daina fita ke kaɗai, ban san kin fita ba, sai da na tambaya masu gadi suke ce min wai kin fita a keke. Don Allah ki daina fita ke kaɗai, tunda an girma."