GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 9

by @nusybee143

Page 9



Hajiya Zainab ta gyara zamanta tana goge hawayenta, cikin karyewar murya ta ce"na rasa yadda zan yi miki bayani ne yaya Saude 

Abubuwan sai sake lalace min suke yi,ina kewar ƴata, aƙalla ko da a ce ina jin motsin ta zan ji sanyi

A silar wannan abu da ya faru har yanzu ina fuskantar dariya da izgilanci da gori daga wajen kishiyoyi har ma da ƴaƴansu,ga ki ba kya nan yaya Saude,ina cikin wani hali"ta ƙarashe hawaye yana zubo mata sosai

Abin ya taɓa Hajiya Saudat sosai,amma sai ta yi murmushi cikin dattako,ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye,kai tsaye suka nufi dinning area, Hajiya Saudat da kanta ta zuba mata abinci,dama ta saka an dafa abin da ta san ta fi so,sakwara da miyar egusi,ta tura mata gabanta tana faɗin "bismillah auta ta!"

Kallon abincin Hajiya Zainab ta yi,tana shirin yin magana Hajiya Saudat ta ce"kin san bana san musu,na ce ki ci"bata sake yunkurin musantawa ba ta fara tura abincin da ƙyar,Hajiya Saudat ta fara ba ta labarin irin yadda ta yi rayuwa cikin farin ciki a Cairo 

Tuni ƙunci ya fara kwaranyewa daga zuciyar Hajiya Zainab,tana murmushi ta ce"ki ce daɗinki kawai kike sha Hajiya 

Gaba ɗaya kika manta da mu,kika bar mu da kujiba-kujiba"Hajiya Saudat tana murmushi ta ce"bari kawai auta,ai da an fita da Ni na zaga ƙasar zan fara tuna auta,sai na ji kamar na ce a zo a ɗauko min ke mu huta tare,mu ga gari,gari ya ganmu,abun sai wanda ya gani kawai"

Murmushi Hajiya Zainab ta yi tana faɗin "gaskiya dai sai wanda ya gani Hajiya 

Lallai kin more,har wani jaja-jaja kika yi fa"

Hajiya Saudat ta yi ƴar dariya ta ce"ke ma dai gashi nan ai,ba ki yi duhu ba,sai wani ƙara murjewa da kika yi kika yi kyau,da alamu dai Yusufa yana kula da autar Hajiya"

Zainab ta yi yar dariya kawai,amma kallo ɗaya Hajiya Saudat ta yi mata ta gane dariyar ta yaƙe ce,sai dai ba ta tanka mata ba,suka cigaba da cin abincin tana ta tsokanarta 

Bayan sun kammala sai da suka yi sallar azahar da lokacinta ya yi, sannan Hajiya Saudat ta ja hannun Hajiya Zainab zuwa ɗakinta 

Zaunar da ita ta yi, sannan cikin kwantar da murya ta ce"Zainab! fuskance ni mu yi magana!!

Haba Zainab! menene dalilin da ya sa a yanzu za ki nuna raki bayan hakan ba ɗabi'arki ba ce?

Menene dalilin da ya sa za ki nuna rauni alhali ke ɗin ba mai rauni ba ce?

Ganin hawaye a idanunki a yanzu a dalilin ƙaddarar da ta samu yarki ya sa jikina ya yi sanyi, nake jin kamar ba gaza akanki,kamar akwai abin da ban sauke ba,haka ne ko?"

Kuka ya ƙwacewa Zainab,tana kukan ta ce"yaya Saude na kasa jurewa ne,ƴata ta ɓata,a yanzu tausayawa nake buƙata, sannan kuma......"

"Kin iya addu'a?

Kin dogara da Allah?

Kin tabbatar shi zai iya yi Miki komai?

Kin nemi ɗauki daga gare shi?

To ki koma ki jira sakamako, Allah baya taɓa bai wa bawansa wanda ya dogara da shi kunya

Ki zamo baiwar da ta dogara ga Allah,kuma ta tabbatar Allah zai yi mata komai,wallahil azeem babu wani bawa a duniya da zai iya yin galaba akanki ko da da magana ne

Addu'ar uwa akan ɗanta karɓaɓɓiya ce,koma ga Allah,dage da addu'a,ki yi ta gayawa Ubangiji,da izninsa za ku ga kyakykyawan sakamako mafi alkhairi da amfani,wani kuka da damuwa da saka takaici a rai duk ba naki bane Zainab"

Cikin rawar murya ta ce"amma Hajiya yadda suke nuna min fifikon ya'ya yana matuƙar damu na, kiri-kiri suke nuna min cewa ƴaƴansu ne,kuma tawa ƴar rashin tarbiyya ta yi aka kore ta, Sannan kuma ina yi musu hassada akan nasu yaran "

Ƴar dariya Hajiya Saudat ta yi ta ce"to sai me?

Ke dai har gobe ban ce ki cire hannu akan yaran ba, saboda ubansu bai taɓa nuna cewa ba naki bane, sannan a matsayin ki na babba dole sai kin ji kin kawar da kai,babu wanda ya rubuta ƙaddarar da zata same shi 

Sannan batun rashin tarbiyya kuma su ma sun san ƙarya suke yi,kamar yadda ba ki da iko akan halayya da ɗabiun Shaheeda su ma ba su da iko akan halaye da ɗabi'un yaransu 

Babu ruwanki da abin da aka ce, abin da za'a ce ko ake cewa,ki mayar da hankali akan me Allah zai ce?

Allah ya yarda da hakan?wanne sakamakon zan samu a wajen Allah?

Kina rayuwa da mijinki lafiya ƙalau, don Allah ki yi haƙuri ki cigaba da yi masa biyayya, Allah ya tsare Shaheeda ya dawo da ita cikin aminci "a raunane Hajiya Zainab ta ce"Ameen Hajiya 

A nan Hajiya Zainab ta kai yamma, kafin ta yiwa Hajiya Saudat sallama ta tafi gida, Hajiya Saudat ta rako ta tana cigaba da ba ta shawara, Kafin ta shiga mota 





*IBIZA,BALEARIC ISLAND,SPAIN*


*PACHA IBIZA CLUB*

Kamar yadda ta saba a kowane lokaci dogon wando ne baƙi a jikinta, sai dai rigar yau T-shirt ce fara,kan nan nata babu ɗankwali,sai p-cap ɗin da ta ɗora kalar rigar jikinta white 

Gabanta ƙatuwar tukunyar shisha ce ,irin wadda ta saba amfani da ita lokaci lokaci,tana ɗan jan hayaƙin shishar tana lumshe idanu tana buɗewa 

A hankali ta ɗaga kai tana ƙarewa mutanen da suke cikin club ɗin kallo, musamman matan da suke kan dandali suna taka rawa a waƙar Despacito ta su Justin Bieber,a hankali ta mayar da kai ta kwantar a kan kujerar da take zaune tana lumshe idanunta 

"Hi HERMOSA!"da a hankali ta buɗe idanunta da ya canja kala saboda hayaƙin shishar da ta bankawa cikinta,ta zuba su akan matashin baturen da yake tsaye akanta yana kallonta da murmushi a fuskarsa 

"Leonardo! welcome!!"ta faɗa tana gyara zama

Waje ya samu ya zauna,ta miƙa masa hannu Kamar wanda za su gaisa,sai ya sa mata takarda a hannunta, sannan ya yi mata inkiya da idanu, ba tare da ta yi magana ba ta jinjina kai Sannan ta mayar da kanta ta kwantar a jikin kujerar da take zaune

Duk abin da yake faruwa yana daga can gefe yana kallonsu,ya tabbatar akwai abin da suke shiryawa a nan ɗin,don haka sai ya zuba mata idanu ya ga gudun ruwanta 

Ba ta juma a wajen ba ta miƙe don tafiya,shima sai ya fara yunƙurin miƙewa don barin wajen,dama gaba ɗaya ya takura da hayaƙin taba da na shisha, ga warin giya 

Tana daf da shiga mota ta ji ya ce"hi!"

Juyawa ta yi tana kallonshi,ya yi kyau sosai a cikin wasu designer t-shirt da wando, waɗanda suka amshi farar fatarshi,yana murmushi cikin harshen Hausa ya ce"Barka da wannan lokaci babbar yarinya"

"Wanene kai?"ta jefa masa tambayar tana kallon cikin idanunshi 

Murmushi ya yi yana ɗan buɗe idanunsa,ya ce"Nima ɗan Nigeria ne kawai, I'm very happy da na haɗu da ƴar ƙasarmu a wata ƙasar, that's why Babe"

"Wanene ya ce maka ni yar Nigeria ce?"ta jefa masa tambayar tana kallon cikin idanunshi 

Kai tsaye ya amsa mata da faɗin "haba Madam!

Duk inda na ga ɗan'uwa ai zan gane shi

Yanzu dai kaya nake buƙata,kuma ina da tabbacin zan samu a wajenki,ya za'a yi?"

Kallonsa ta tsaya yi kamar mai nazari ,ya yi ɗan murmushi ya ce"kar ki damu babu mai jin me muke cewa,nan a Spain muke,ba Nigeria ba

Still shiru har zuwa yanzu bata da niyyar magana,ya yi murmushi sosai ya ce"ba ki yarda ba?

I'm MUBARAK!and you?"ya miƙa mata hannu don su gaisa 

Daga inda yake yana iya kallon yadda ta razana da jin sunan,duk da kallon tsanaki da take bin shi da shi, wanda yake da tabbacin akwai abin da take son ganowa

Ɗan murmushin da yake yi ne ya sa ta ɗaure fuska ta ce"ka san ina siyar da kaya?amma ba ka san sunana ba?"

"Simple thing madam!

Na ga yadda kike naki business ɗin,kuma da yake mun saba da ƴan harƙalla a duk inda muka gansu muna gane su,ni dai sunana Mubarak,ke fa?"

Kawar da kai ta yi ta ce"tunda ka san aikina sai ka nemi sunan,na san za ka samu"daga nan ta haye kan bike ɗinta ta tayar,a ƴan mintuna ta bula masa ƙura ta bar wajen

Bin ta ya yi da kallo yana murmushi, kafin ya zaro wayarsa ya kira Awwal da suka zo ƙasar tare

Mintuna kaɗan ya fara magana"Awwal!gata nan mun haɗu,mun yi magana,kuma da alamu ma ba zata yi turjiya mai yawa ba za mu samo kanta,be ready, kowanne lokaci daga yanzu zata iya shiga hannu"Awwal ya sara masa a cikin wayar ya ce"best of luck Sir"

Bayan barazanar da ta yi masa na ƙwace wayar drivern Amna Haisam ya sauya taku na bincike akan ta,da kanshi, ba tare da sanin ƴan team ɗin nashi ba ya gano cewa tana shirin barin ƙasa zuwa Spain,sam bata san jirgi ɗaya suka hau da shi ba

Sai dai shi a maimakon Ibiza kai tsaye Barcelona ya nufa,ya cigaba da bincike a sirrance ta hanyar wasu yaran Roxy ɗin da ya ba su wasu kuɗaɗe 

Tsawon kwanaki shida ya ɗauka yana tattara bayanai akan Roxy,sai dai har zuwa yanzu bai samu cikakken tabbacin daga inda Roxy ta fito ba,ya dai samu sunanta,da kuma tabbacin ita ɗin ƴar Nigeria ce 

Ya samu nasarar bincikar inda ya sauka a Ibiza,ya cigaba da bibiyarta,ta yi harƙalla da su Alejandro,asalima abin da ya kawo ta Spain kenan,inda ta damƙa kayan maye danginsu cocain waɗanda darajar su zata kai ta dala miliyan biyu a hannunsu 

Ya kwashi wasu kwanaki yana bibiyarta,har sai da ɗaya daga cikin yaranta, wadanda suke yi masa aiki a sirrance suka sanar masa kwanaki uku ya rage mata a Spain sannan ya tunkare ta bayan fitowarta daga Pacha Ibiza club

Wannan kenan!

💫

Washe gari tun da safe Haisam yake ta cuku-cukun yadda zai yi ya samu kan Roxy, wadda zuwa yanzu ya san sunanta,sai dai ba shi da guarantee akan komai da ya sani daga gare ta,kuma yana fatan bata san shi ba, ballantana hakan ya ba shi matsala,don ya tabbatar sai ya kama ta da ikon Allah 

Da yamma ya gama shirinsa tsaf, yana jiran dare don tafiya club ɗin da suka haɗu da Roxy,ko a cikin boat ɗin da ya tsallakar da shi zuwa Balearic Island bincike da nazari yake yi, don ya san wacece wannan yarinyar wajen kaifin basira da iya taki, shekaru biyu ta ɗauka tana jijjiga hukumar tsaro,babu yadda za'a yi mutum mara basira da fikira ya iya yin hakan saboda ƙwarewa da sanin makamar aiki ta jami'an tsaron Nigeria 

A inda ya saba gano ta ya ganta,tana zaune tana busa hayaƙinta na shisha kamar yadda ya saba, gefenta yaronta David ne,sai Oga boss,sai ƴarinyarta Hanna da suke ta yin hira suna shewa,amma ita hankalinta yana kan shishar da take zuƙa,sai wayar da take dannawa lokaci lokaci 

Kai tsaye wajenta ya nufa yana faɗin "hi! Hermosa!"

Dukkansu ɗagowa suka yi suna kallonsa kusan a tare,ban da ita,da ta ɗago daga baya hankalinta a kwance,ya yi murmushi yana faɗin "Barka!

Sorry za ki ga ina yi miki magana da Hausa,na fi son na rinƙa jin daɗin mu'amala da ɗan ƙasarmu da yaren ƙasarmu"

David da yake bin shi da kallon raini ya ce"wanene kai?"

Kai tsaye Haisam ya ce"ka bari mu gana da uwar ɗakinka,ku ba mu waje"

Kusan a tare suka kalli Roxy wadda ta ja hayaƙin shisha ta fesa shi a fuskar Haisam da take kalla kai tsaye, kafin ta ce

"Ku ba mu waje,mu ji da me ya zo"babu musu suka miƙe suka bar wajen,shi kuma ya samu waje ya zauna yana fuskantar ta

"Beunas tardes!"(Good evening in Spanish)

Kallonshi ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta yi murmushi ta ce "ka gaji da yin yaren naka ne?sai ka ari na wani?"

Ɗan murmushi ya yi shima,ya ce"kin san bahaushe ya ce idan mutum ya je gari ya ga kowa da jela,shima sai ya samu ɗan zirin tsumma ya ɗaura"ta jinjina kai tana faɗin"kenan kai ma ɗaurawa ka yi dai ko?"

Ya ɗan jinjina kai ya ce"kusan haka"

Ta ce"well!

Lafiya dai ko? menene dalilin da ya sa kake bi na?"

Kai tsaye ya ce"kasuwanci nake so mu yi,ina son na shigar da kaya zuwa Nigeria amma na gagara, saboda wahalar da hakan yake ba ni 

Shine na zo na nemi alfarmar hakan daga gare ki,idan ma kina da wani connection ɗin ko dabarar hakan I'm ready ki ba ni,don bana jin daɗin yadda ake kama min kaya,gashi kuɗaɗe da yawa nake asara"






#Nusy_bee