RAGAYAR DUTSE

PAGE 17

by @nanahaleema11

*RAGAYAR DUTSE.*


                ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 017.*


Daada ta bisa shi da harara ta ce, "ɗan laɓuɓu mai zubin mata kawai."A lokacin Mamy ta miƙe zata fita daga falon bata kalli Daada ba.


Daada ta ce, "ko waye zai zuga Muhammadu auren nan dai sai ya yi, kuma yarinyar da na gani ita zai aura." 


Mamy bata juya ba ta fita tana girgiza kanta kawai, dan ta san da ita Daada take.


Daada ta kalli Abba ta ce, "kai ko bani da rai abinda za a yi kenan, ko yau na faɗi na mutu ka tabbatar da wannan yarinyar da na gani ta zama matarsa."


Abba ya bita da kallo kawai, mamakin kalamanta kawai yake yi. Haka kawai daga haɗuwa da yarinya ba tare da ta santa ba ta dinga zancen ita zata aurawa Rehaan? Ba gwara a aura masa ɗaya daga cikin ƴan uwansa na gida ba, amma batu akan auren wacce ba a sani ba ai bai tashi ba. Yana biye mata ne saboda babu yadda zai yi mata, amma shima bazai yarda da auren ba.


Abba ya ce, "shikenan Daada, ki kwantar da hankalinki, za a san duk abinda za a yi." 


Ta kalle shi cike da harara ta ce, "kai a hankalina nake fa, ka daina yi min kallon mahaukaciya ka gane?. Duk abinda nake faɗa na sani, duk abinda zance na san me nake faɗa, ba mahaukaciya bace ba ni."


Abba zai magana aka yi sallama aka shigo. Babban ɗanta wanda suke kira da Abiy ne ya ƙaraso ya zauna a gefen da Abba. 


Abiy ya gaisa da Daada, ta amsa ba tare da ta kalle sa ba, kasancewarsa ɗan fari ko sunansa zata iya kira, kallonsa ma sai an yi da gaske take yi saboda kunya


Abba ya gaisa da shi ya amsa sannan Abiy ya ce, "ɗazu aka ce min Daada ta fita, ba a san inda ta tafi ba." 


Abba ya ce, "wallahi keke ta hau, babu inda ban je nemanta ba amma ban ganta ba. Sai daga baya ta dawo a keke."


Daada ta ce, "Rabon zan haɗu da yarinyar da Muhammad zai aura ne." 


Da mamaki Abiy ya ce, "Rehaan zai yi aure ne?."


"Daada dai ta nemo masa mata. Yarinyar da ta taimake ta, ta dawo da ita gidan nan, ta ce ita zai aura. Kuma babu wanda ya santa, ko sunanta ba a sani ba balle inda take. Amma Hajiya Daada  ta ce itace matar Rehaan." 


Abiy ya yi murmushi dan ya san rigimar babarsu,  ga tsufa ga rigima ya kalle ta ya ce, "Daada a ina take?."


Daada ba tare da ta kalle sa bata ce, "ko a ina take ita za a nemo ya aura, in dai na isa daku." 


Abiy ya ce, "To Daada. Da har ina cewa yaje gida wajan ƴan uwansa ya ɗauki ɗaya, gida bata ƙoshi ba ai ba a kaiwa dawa ba." 


Daada ta ce, "sau nawa ana cewa ya yi hakan, ya aikata ne?. Yana can fararen fata sun ɗauke masa hankali baya girmama yarensa da asalinsa. Dan haka babu batun auren ta gida, tunda ana nuna masa yaƙi ya buɗe idonsa, zan aura masa wannan ko da ba ya so."


Abiy ya ce, "Shikenan Daada, duk yadda ki ka yi daidai ne. Allah ya sa ta gari ce." Ta amsa ba tare da ta kalle sa ba tana ɗauke kanta gefe.


A lokacin aka sake yin sallama aka shigo, mahaifin Jafar Alhaji Ahmad ya shiga da sallama, duk suka amsa suna yi masa barka da zuwa. 


Ya amsa yana gaishe da Daada, ta amsa daƙyar tana ɗauke kai kamar bata so. Su kuwa suka gaisa dashi da fara'a da girmamawa sannan ya yi mata sallama ya tafi.


Daada ta bisa da kallo bayan ya fita ta ce, "ɗan kishiya har wani ɗa ne? Ba dan yarinyar nan Jurwaiyya ta nace ba, ta ya zan haɗa zuri'a da ahlin kishiyata?. Shi kuma Jafar ya maƙalawa Muhammad, komai tare suke yi kamar tare aka haife su." 


Su dai basu ce komai ba, amma suna mamakin wannan kishi na Daada da har yanzu ta kasa mantawa dashi. Duk waɗanda take magana akai sun rasu, ita kaɗai ce ta rage a cikinsu amma har yanzu kishi take da ƴaƴansu.


Kuma gashi mahaifin Jafar yana da kirki da son ƴan uwasa, ya ɗauki Daada kamar babarsa, tunda mahaifiyarsa ta rasu ya mayar da Daada itace uwa a agaresa. Amma ita bata gani ko kaɗan, yadda take nuna masa ne ya saka ya janye jikinsa daga zuwa inda take sosai, sai hanya ta biyo dashi zai shigo su gaisa ya tafi.


Sallama suka yi mata suka fito. Abiy ya kalli Abba ya ce, "Amma baza ka zuba ido ayi wannan auren ba ko?."


"To ya zan yi mata?."


"Ka san yadda zaka yi, amma auren wata yarinya da ba a santa ba bai tashi ba. In ta nace sai ya yi auren, akwai ƴan uwansa mata. Gidana akwai Nana, gidansu Jafar ga Ikram, gidan Jamila akwai Zainab. Dukkansu sa'anin Juwairiyya ne, me zai saka bazai ɗauki ɗaya ba?."


"Gwara Zainab da Nana zata iya amincewa, amma ka ga Ikram, wallahi baza ta yarda ba. Da ya ta amince da auren Jafar da Riyya da za a sake ɗauko wata daga cikin gidan?."


"Gaskiya ka san yadda zaka yi, kar ka bari ayi masa abinda baya so."


"In sha Allah zan yi." Daga nan suka yi sallama ya shiga mota ya tafi.


Abba kai tsayw apartmet ɗinsa ya wuce, ya kira Rehaan a waya ya ce yazo ya same shi shida Babarsa. 


Ba a jima sosai ba Mamy ta fara shiga, kafin ta zauna ya shigo yana tafiya a hankali, ya zauna ya dafe kansa da hannu biyu.


Abba ya ce, "ciwon kan ne?." 


Rehaan ya sauke hannunsa daga kansa ya ce, "Abba meyasa komai ni ake yiwa dole a gidan nan? Meyasa kowa za a barsa ya yi rayuwarsa yadda yake so, amma ni ko yaushe sai ace sai na yi abu dan dole?."


"Ka yi haƙuri Rehaan, babu yadda zan yi da Daada ne. Yadda ka ke yiwa mahaifiyarka biyayya, nima haka nake yiwa tawa."


"Amma Abba meyasa Daada bata son farin cikina? Komai da ta ɗauko sai ta ce ni, komai ni. Akwai abinda nake yi mata wanda bata so ne?. Ko kuma ƙiyayyar da take yiwa Mamy ce ta shafe ni?."


Abba ya kalli Mamy da bata ce komai ba, ya sake kallonsa ganin yadda idanunsa suka yi ja, gashi sun ƙanƙance hakan ya tabbatar masa da ba ƙaramin ciwo yake ji ba. 


Ya tausasa murya ya ce, "ba haka bane Rehaan, ka daina cewa tana nunawa babarka ƙiyayya ko kai, duk ba haka bane. Rikicin tsufa ne kawai Rehaan, kuma kai rashin zaman da baka yi a ƙasar nan shine yake jawo hakan. Tana ganin ka girma ya kamata ka yi aure, kuma ka ga ta baka dama ka je gidan Abiy, ko gidan Jamila ka zaɓi yarinya ka nuna baka so. Shiyasa ta yi haka."


Ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa dan maganar bata da amfani ko kaɗan, ko ya yi Abba bazai taɓa fahimtarsa ba. 


Abba ya ce, "Matso Rehaan." 


Bai musa ba ya matsa kusa dashi, Abba ya dafa sa ya ce, "duk wani mai ɗauke da nasara sai da ya yi faɗa da ƙalubale a rayuwarsa, duk wanda ka gansa a sama ka duba inda ya taka kafin ta je wannan waje. Allah kai ya nuna a kaf ahlinmu, kai ya zaɓa ya yiwa arzuƙin da bai yiwa manyan da suke ciki ba. Sai ka yi haƙuri da abubuwan da zaka dinga fuskanta, akwai masu sonka tsakani da Allah, akwai masu fuska biyu Rehaan. Ka karɓi duk abinda ya zo maka ka yi haƙuri dashi."


Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "Abba..." sai kuma ya yi shiru bai ce komai ba. 


Abba ya ce, "faɗi abinda yake bakin ka Rehaan, ina jinka."


"Zan iya amincewa da komai, amma ban da auren nan. Bazan iya ba, bazan iya ba Abba." 


Abba ya sauke numfashi ya kalli Mamy da bata ce komai ba, ya dawo da kallonsa ga Rehaan ya ce, "nima maganar nan ban ɗauke ta gaske ba, magana take akan yarinyar da bata santa ba, ta ya zata ce ita za a aura maka?."


Ya sunkuyar da kai ƙasa bai ce komai ba, amma a zuciyarsa yana ayyana duk abinda zai faru shi bazai auri zaɓin Daada ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma bazai taɓa amincewa ba.


Abba ya kalli Mamy ya ce, "Nadira ki yi magana mana, ki kwantar masa da hankali."


Mamy ta kalle sa ta ce, "bani da abinda zan ce." 


Abba ya yi shiru dan ya san ba a kyauta mata ita da ƴaƴanta, ba a yi mata abinda take so, a ko yaushe ita da yaranta ake tauyewa kamar bare. Sau ɗaya aka taɓa amincewa da zaɓi daga ɓangarenta. Auren Juwairiyya da Jafar shine kaɗai aka amince dashi, shima dan shida ƴan uwansa sun tsaya kai da fata ne a kai, kuma sun yi addu'a, amma bayan sa babu wani abu daga ɓangaren Mamy da zai fito ta amince dashi. 


Abba ya ce, "Rehaan jikinka ya ɗan yi zafi, ka je ka huta." 


Ya kalli Abban ya ce, "Abba ka yi haƙuri, bazan amince da auren nan ba. Aikina ba a ƙasar nan yake ba, batun dawowata ƙasar nan gabaɗaya bai tashi ba Abba."


Abba ya bisa da kallo, dan kafin ka ji abinda Rehan zai buɗe baki ya musa masa tabbas abun ba ƙarami bane, abin ya kai maƙura a wajan ƙinsa a zuciyarsa. 


Shi ina ya ga lokacin baka amsa ma balle ya yi maka musu? Ko yaushe cikin busy yake, kana magana dashi sauri yake yi ya bar wajan, ko kuma a kira shi a waya. A ko yaushe in ka ambaci sunansa amsar murmushi ce kawai, kafin ya bada amsa ya shiga wata hidimar.


Abba ya ce, "jeka ka huta, daga baya zamu tattauna akan wannan."  Ya miƙe ya fita ba tare da ya ce komai ba.


Bayan ya fita Mamy ta ce, "Me zai hana baza ka barni na koma ƙasata dani da ƴaƴana ba? Tsananin ƙiyayyar da ake yi min ce ta shafe su. Ana tauyewa Rehaan haƙƙinsa sosai, ana yi masa abubuwa wanda baya so. Bai taɓa dawowa nigeria ya rayu lafiya ba, ko yaushe cikin ciwo yake har sai ya bar ƙasar nan. Kana gani dai, yana saka ƙafa a gidan nan ya fara ciwon, ka san ciwon kan nan nasa da naci, in anjima ban san me za a ce ba."


Abba ya sauke numfashi, ya ɗan yi shiru kafin ya tausasa murya ya ce, "Bana so na ji kina cewa ana nuna miki ƙiyayya ke da ƴaƴanki...."


"To ba haka bane? Waye yake ƙaunata a gidan nan?. A ɓangaren ƴan uwansa mata Janan ce kawai take nuna masa so. Duk yadda ya so da su sake dashi, duk yadda yake yawan maganarsu, duk yadda yake ƙoƙarin faranta musu, su kuma baƙinsa suke gani."


"Ɓangaren mazan kuma gasu nan dai, har gwara Zayyad ya kan ɗan sakar masa fuska, sai Salman, shima dan yana da matsalar ƙwaƙwalwa ne da bazai sauraresa ba, bayansu babu kowa kuma. Kawai dan na kasance ƴar wata ƙasar ba jinin fulani ba shine duk abinda ya faru."


Abba ya sake tausasa murya ya ce, "ba sa son Rehaan, amma wa Allah ya ɗaukaka a kansu? Kaf ahlinmu da dangin mu gabaɗaya akawai wanda Allah ya yiwa abinda ya yiwa Rehaan?. Tun daga kanmu iyaynensa har ƙasa, babu wanda Allah ya bawa dama da baiwa irin wacce ya basa. Dole ya dinga fuskantar ƙalubale, dole ya dinga fuskantar abubuwa irin wannan saboda ɗaukakar da Allah ya basa."


"Hmmm! Nima dai bazan amince da auren nan ba, duk abinda za a yi sai dai ayi, amma bazan taɓa bashi goyan bayan ya auri yarinyar da bamu santa ba. Dan kawai bashi da gata, ba a son ya auri yarinyar da yake so kamar kowa?."


"In kuwa auren ya tabbata, jinin nawa da ba a so, jinin nawa da ake ƙyama,tabbas sai na haɗasa da wacce naga dama nima, zan ɗauko mace ɗaya daga dangina na aura masa. Domin ina da iko da shi, ina da iko da ɗana fiye da kowa...." 


Sai kuma ta sassauta murya ta ce, "ka yi haƙuri, amma ana yi min abinda bana jin daɗi a gidan nan."


Abba ya sauke ajiyar zuciya, ya ɗan yi murmushi ya ce, "Nadira in bakya kwantar da hankalinki ta ya hankalin Rehaan zai kwanta? Ki adana damuwar nan, babu wanda ya isa ya yi nasara akaan Rehaan matuƙar Allah bai rubuta ba. Don Allah ki yi haƙuri, kar ki bar komai ya dame ki." 


Mamy dai ta yi ajiyar zuciya tana kallon gefe ɗaya. Ta ɗan girgiza kai bata ce komai ba.


     Ɓangaren Mama tunda ta bar ɓangaren Daada hankalinta yake a tashe, babban tashin hankalinta bai wuce wacece wacce Daada ta gano ba. Sai zagaye take yi a ɗaki, har aka buɗe ɗakin aka shiga. 


Janan ce ta shiga Mama ta bita da kallo ta ce, "yauwa, ɗazu kin ga yarinya da ta dawo da Daada ne?."


Ta ɗan yi jim sannan ta ce, "gaskiya ban ganta ba, da Banisha suka gaisa. Lafiya Mama?." 


Mama ta girgiza kai bata ce komai ba, sai daga baya ya ce, "jeki kawai." Janan ta juya ta fita. 


Mama ta ce, "Wacece yarinyar nan? A ina take?." 


Sai kuma ta girgiza kai ta ce, "bata isa ta auri Rehaan ba, matuƙar ta cika qualities ɗin zama mace ta gari wallahi Allah bazai aure ta ba. Bana so ya auri ta gari, bana so."


Sai kuma ta dafe kai ta ce, "wacce yarinya ce wannan, Wacce yarinya zan samu na haɗa aurensu? Wacce yarinya zan shiga fita, in biyata ta amince da auren nan?." 


Ta furzar da iska ta ce, "sam bazan zaɓo daga ahlina ba, bazai yu na aurawa wata a cikin dangina Rehaan ba. Kaf ƴaƴana babu mai auren matashin mai kuɗi kamar Rehaan, dan haka yarinyar da na sani baza ta taɓa zama matarsa ba wallahi!. Babu ƴar ƙawa, ko maƙoci, ko ƴar ɗan uwa, da suka isa su auri Rehaan wallahi!."


Ta naushi hannunta ta ce, "bazai yu ba wallahi, dole na san abinda zan yi!."


Buɗe ƙofar aka yi aka shigo, ta kalli wacce ta shigo ganin Umma ce sai ta bita da kallo. 


Umma  ta ce, "Mama wai ya abun yake ne? Wacece yarinyar da ake magana akai ne?."


Mama ta ce, "abinda nake so na gano kenan, na kasa fahimtar wacece wannan. Dah ta bani dama na samo wacce  yake so, da ta ce ta bani dama har na fara plan ɗin nemo wata karuwa in biyata domin ta auresa. Amma an ɓata min plan ɗina."


"Yanzu ma bai ɓaci ba, mu cigaba daga inda muka tsaya, in an ganota ɗin, indai bata yi mana ba kar mu sake mu amince, ko ta wanne hali a lalata auren nan."



"haka za a yi, bazai taɓa auren wacce ta dace ya aura ba, shiyasa bazan taɓa bari ya auri wata daga dangi ba. Daga can waje za a samo, itama wacce bata dace ba."


"Dakyau, haka nake so naji. Bara in je na bawa Salman magani na dawo mu cigaba da tattaunawa. Dole mu dage a nemo yarinyar nan da wuri" ta faɗa tana fita daga ɗakin. 


Mama ta bita da harara tana jan tsaki ta ce, "Babar mahaukaci!."


            *******


Islaha kuwa tunda suka bar wajan Daada take ta murmushi ita kaɗai, in ta tuna rigimar matar bata sanin lokacin da take dariya ita kaɗai. 


Musaamma yadda take faɗar sunanta da yadda take cewa zata aura mata jikanta. A haka ta ƙarasa gida, ta biya mai keke kuɗinsa ta shiga cikin gidan.


Tana shiga suka haɗa ido da Umman su Safeera, ta ɗuka ta ce, "Mama ina yini, Umma ina yini" ta faɗa tana niyar wucewa.


Mama ta ce, "tun ƙarfe huɗu na asuba ki ka bar gidan nan, baki dawo ba sai yanzu bayan sallar i'sha. Ace kin je yawon ta zubar ki ce ke ba haka ba." 


Islaha dai bata ce komai ba, tana jin Umma ta ce, "to ke har san tabbatar miki? Ai ko baki faɗa ba kowa yana ganin idanun yarinyar nan ya san ta san maza. Kai tsaye take kallon idon ka ta yi magana, in ba mata irinsu ba babu mai kallon idon na gaba dashi ya yi magana."


Islaha ta shiga ɗaki ta yi alwala ta yi sallah, sai a sannan ta ji tana jin yunwa sosai. 


Ta fito fito a sanyaye tana jin Umma da Mama suna tattaunawa akan tafiya aikatau wata ƙasar. 


Islaha zata gifta Mama ta ce, "ga baiwa kin ajjiye ko? Sai dai ki je yawon ki, ki dawo ki tarar na dafa miki abinci ko? To baki isa ba wallahi, yau ba ki da abinci a gidan nan."


Ta tsaya cak bata…