NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)
CHAPTER 42 ( All of a sudden).
by @deejasmah
CHAPTER 42 ( All of a sudden)
Zaman Sairah gidan Umma kamar wani dama ne suka samu wanda ba su samu ba a baya na b'arje amarci mara mix, don dama ko tana nan a lokuta mantawa ake yi da ita balle ba ta nan. Ba kuma wai ba ta ran su ba ne Aa kullum suna hanyar zuwa Yerwa don ganinta, in ba su je ba kuma zasu kira Umman video call suna tambayar 'yar ta su.
Tafiyarta da bai fi 1 week ba sai ga period d'in ta ya zo, tana office abun ya zo tsaye tayi a toilet tana ta mamakin zuwanshi ba wai don bai kamata ya zo ba sai yanda ta manta da ainihin date d'in da ya kamata ya zo mata. Ba ta tab'a mantawa da date d'in period d'in ta ba sai yau, koda yake ma shekara nawa ne da last period d'in nata? Tun fa tafiyar da Islaam d'in yayi wanda yayi silar farkon haɗuwarsu da juna, number Fatee ta kira ta ce ta kawo mata pad da yake suna ajiyewa a nan office d'in saboda ma'aikatan wajen. Bayan 2 minutes sai ga ta tayi knocking d'in k'ofar office d'in, bud'ewa tayi ta amsa kana ta koma toilet kimtsa kanta ta fito kasancewar yanda take ji ya sa ta had'a kayanta zuwa gida ba wai tana jin ciwo ba ne kawai komai bai mata daɗi ne a hanya ta tsaya ta sai pad kafin ta wuce gida.
Noodles ta had'awa kanta ta samu ta ci ta kwanta, juyi kawai take tayi har Islaam ya dawo gidan d'akinta ya taho kai tsaye ganin motarta a garage. Shiga yayi jikinta yana sauke mata numfashi a wuya, bud'e idanu tayi tana mai dubanshi don barci ya d'an kwasheta kad'an.
Lumshe idanunshi yayi yana d'aga mata gira, murmushi ta saki tana cewa " welcome home Alpha" cikin muryarta da barci ya gama cinyewa. Cewa yayi " Uhmm thanks wife, baccin yamma?" Ya k'arashe cikeda tambaya.
"Kawai ban jin daɗi ne".
"So sorry dear, me yake damunki ne? Ko mu je clinic?".
"I'm okay Yaa, yanzu da na yi baccin nan na ji dad'i".
"Ok, but in kika ji wani abun daban ki yi magana da wuri kar sai dare yayi abu ya tashi".
"Ok, dear" ta amsa tana mik'ewa tsaye mik'a tayi ta wuce kitchen Lemon juice d'in da tayi jiya shi ta zubo a k'aramin dogon jug ta sako ice sai table water guda d'aya da cup ta fito a kan coffee table d'in da yake gabanshi ta ajiye juice d'in ta zuba masa a cup ta mik'a mai kana ta zauna a gefenshi, amsa yayi ya sha k'arawa yayi sai da ya ji ya kai masa iya in da yake buk'ata kafin ya mik'e yana ce mata bari yayi wanka.
Yana wucewa ta mik'e zuwa kitchen tana tunanin abinda zata yi mai sauk'i, sai da ta gama tunanin kafin ta janyo couscous daga locker ta fata had'a musu egg fried couscous da ta had'a da sausage da meat chunks da kidney. Sprite ta ciro ta had'a da lacasera kana ta d'auko mint d'in ta a blender ta had'a su duka sai da suka had'a kan su kafin ta tace, lemon juice kad'an ta yi squeezing a kai ta saka flavour ta juye a jug tana mai saka shi a chiller. Gyara in da tayi aikin tayi ta wanke abinda ta b'ata, peppered chicken ta ciro daga fridge ta saka shi a microwave kana ta wuce d'akinta jin har yanzu bai dawo ba ta san bai wuce yana gun Fareesah ba wanka ta feso ta zura free white shirt da bum shorts kanta ta d'aure ba ta fita parlorn ba sai da aka fito daga masjid d'in maghrib.
Be shigo gidan ba sai da aka yi isha'i da yake yayi sallama da Fareesah tun maghrib ya sa ya wuce na su kawai, a kan kujera ya hangota zaune ta tankwashe k'afafunta cikin jikinta tana danna waya. Tsayawa yayi daga k'ofa yana kallonta duk da ba wai ta bayyana jikinta ba ne but yanda bumshorts d'in ya manne a kan cinyoyinta da yanda ta tufke gashinta wasu suna lilo a side d'in face d'in ga wuyan ta dake shining ne sake ya kunna shi numfashi ya sauke he so much need her sosai fa yake nufi.
D'agowa tayi ta kalleshi da murmushi a face d'in ta tace " har ka dawo?".
Da kai ya amsa mata kana ya taho cikin parlorn properly, a gefenta ya zauna yana jan ta jikinshi kan shi ya sanya a bayan kunnenta yana sauke mata numfashi. Wani irin mik'ewa tsikar jikinta yayi ta lumshe idanu tana karb'ar yanda ya bai wa bayan kunnen ta attention hannunta ta kai jikinshi tana shafawa dukansu idanunsu rufe juyota yayi kan cinyarshi ya had'e bakinsu wuri guda.
Sun d'auki lokaci mai tsayi suna shafar juna kafin ya janye jin cikinta yana k'ara alamun yunwa, komawa gefe yayi yana nishi ita ko tana inda take ko motsi ba ta yi ba ta rasa dalilin da ya sa ko kad'an ba ta gajiya da Islaam da komai na shi. Komawa tayi cikin jikinshi ta sake lafewa sai da suka d'an natsa kafin ya bud'e idanu a kan ɗaurin gashin ta da ya sake sukurkucewa a idanun shi sai ya ga ma tafi kyau kawar da idonshi yayi daga kai yana cewa " mu je ki ci abinci" don in basu tashi ba zai iya yin mai gaba ɗaya, d'agata yayi ya rik'e hannunta suka nufi dining zama yayi ita kuma ta koma kitchen cups da cucumber da ta yanka a bowl ta ciro kana ta d'auko juice d'in daga chiller a kan tray duka ta d'aura su dining ta kai sannan ta dawo ta ciro naman da ta saka a microwave.
Serving d'in shi tayi kana ta yi serving kan ta ta koma ta zauna, tana cin abincin tana matse cikinta don ji tayi kamar almara mararta yana son yin ciwo a haka ta daure suka kammala cin abincin kwashe komai tayi ta maida kitchen wankesu tayi ta goge kowanne ta ajiye a inda ya dace kafin ta fito burinta ta shiga d'aki ta samu pain reliever ta sha amma sai ta faɗa hannun Islaam da burinshi ya cigaba daga abinda ya fara hakan ya sa shi zuwa kitchen d'in don duba abinda take yi da ta dad'e ba ta fito ba.
Tana fitowa ya kinkimeta zuwa d'akin shi tun a hanya ya fara nuna mata abinda yake nufi sai da abu ya d'auki dum'i amma wancan karon yana shirin kai wa inda yake so ya ji tudun pad, bud'e idanunshi da suka k'ank'ance suka canja kala yayi cike da son tabbatarwa yes ba wai wasa ba ne abinda ya fidda rai da sake gani ne dai a jikinta.
Cikin ficewar hayyaci yace " menene a nan?".
"Ina period".
"Miye period?,,,,,,menstrual cycle? Nooo" ya furta a firgice.
Hannunta ta d'aura kan hab'arshi tana mai lallashinshi tace " Sorry Alpha".
"Dama ke kina period ne? Yaushe ya zo?"
"Today ".
"Kuma baki damu ki gaya min ba ko?".
"Sorry".
"Sorry for what? Yanzu fa sai kin yi 8 days ko? Na shiga uku" ya furta da iyakar gaskiyarshi. Rungumeshi tayi cikin jikinta ta fara k'ok'arin sama masa natsuwa bai hanata ba don in bai samu natsuwan da yake buk'ata ba akwai matsala, ta d'auki lokaci tana mai duk abinda ta san zai kwantar masa da hankali duk da ko itama cikinta na ciwo ta kuma san abinda yayi mata ne ya sa cikin ciwo bayan tsayin lokaci ya samu natsuwa rungumeta yayi tsam jikinshi yana sauke numfashi itama numfashin take saukewa tana dafe ciki. Haske ya kunna yana kallonta gani yayi ta dafe cikinta sosai a hankali yace " lafiya?".
"Cikina" ta amsa tana yarfe hannu hannu ya kai marar tata don samar mata natsuwa, ganin ba zai yi ba ya sa ya mik'e zuwa toilet bottle ya d'auka ya ciko da ruwan zafi kan gadon ya dawo ya d'aura kan mararta ya fara yawo da shi a hankali nishi take yi sai da ya lafa mata kafin ta daina nishin ganin haka ya sa ya ajiye bottle d'in ya d'auketa gabad'ayan ta zuwa toilet kayanta ya k'arasa cirewa kana ya sanyata a cikin ruwan zafi pad d'inta ya nad'e da toilet roll kana ya saka a watse bin d'in toilet d'in su kuma kayan ya zuba a cikin washing machine kana ya dubeta yana tambayarta ko tana da pad gaya masa inda yake tayi ya juya ya fita ita ko fita tayi daga cikin bath d'in ruwan ta tsiyaye ya wuce ta sanya wani ruwan da bubble ta koma ciki wanka tayi kafin ta fito wanke bath d'in tayi kana ta wuce shower cap ta d'auka ta sanya a kanta kana ta sakin ma kanta ruwan zafi tana ciki ya dawo da pad da panties a nan gaban bath d'in ya ajiye mata har da towel kafin ya fita kashe showern tayi ta fito kimtsa kan ta tayi kafin ta d'aura towel d'in ta fito.
A kan gado ta hango shi zaune dubanta yayi yana cewa " ya cikin?".
"Alhamdulillah, thanks Alpha".
Da kai ya amsa ya mik'e yana nuna mata nighties d'in ta ya wuce toilet don son yin wanka, zura nighties d'in tayi ta kwanta shi ma yana fitowa daga toilet d'in jikinshi kawai ya goge boxers kawai ya sanya ya taho gadon kashe wuta yayi ya ja ta jikinshi sai barci yau babu kallon news kenan.
Haka ya dinga hidima da ita tun daga ran da ta fara period ko yana d'akin Fareesah in dai ya zo d'akin yi mata sallama sai ya tabbatar da babu abinda yake damunta ta kuma yi wanka ta kwanta kafin ya tafi ran da ta gama period d'in kuwa bai d'aga mata k'afa ba sai da ya fanshe a zuciyarshi yana adduar Allah ya sa yau za a samu mini him.
Shirin babbar sallah aka fara gadan-gadan, Islaam ya ba su enough kud'i don yin hidima kamar yanda ya saba. Kasancewar Lele tana da kaya ba ta siya ba kamar yanda tayi da k'aramar sallah, birkin bags tayi order guda biyu masu matuk'ar kyau sauran ta ajiye abunta a account.
Itama Sairah tayi mata nata kayan Islaam da kan shi ya kai gidan Umma da ya dawo ne yake bata labarin wai Umman ta ce " da ma sun bar shi don sun riga da sun siya mata" ya d'aura da fad'in " ita fa gani take yi na je rara gefe ne ina son a bani ita".
Murmushi ta saki tana cewa " ai kana son a bakan ko?".
"Sosai ma kuwa, ni da kaina na kaita amma yanzu ina son ta dawo walh, gidan babu daɗi da bata nan".
"Hak'uri ya kama ka Yaa".
"Ai duk ke kika ja".
"Yaa ba fa ni nace ka kaita ba, kai ka kai ta da kanka" ta furta tana d'aga hannu alamun ba ruwana, dariya ya saki yana cewa " yea, amma ai ke kika ce kar in mata magana ko? In ta ni ne da 2 weeks ma sun yi yawa zata dawo gida".
"Toh kawai sai ka je kace mata a baka princess?".
"Cewa zan yi mamanta tana buk'atar yarinyar ta, Umma don Allah ki bata kar tayi ta kuka".
"Da na shiga uku" ta fad'i da iyakar gaskiyarta, ai wannan sai a ga rashin kunyarta duk da an san halinta amma yanda Islaam yake da kamewa da tsare gida waye ma zai yarda shi ya had'a zancenshi.
"Ki shiga uku saboda mene?" Ya tambaya yana sake relaxing kan kujera hannunshi yana sake hawa kan k'ugunta yana shafawa a hankali, numfashi ta saki don movement d'in hannunshi a k'ugunta yana sata jin wani iri tace " ka saka a ga ban da kunya, bayan ka san ba rik'eta zasu yi ba mu na zaman mu zasu aiko da ita".
"Lallai ma kike tunanin hakan? D'azu fa da naje zasu fita da Safwaan ko kallo ban isheta ba a na cewa princess ga PaaPaan ki tace wai ' welcome PaaPaa' daga haka ba ta kuma ce mun uffan ba ta wuce wurin Safwaan tana ce mai ya jirata".
Dariya ta saki sosai don tana iya hangen yanda princess ɗin tana abinda yake faɗi, cikin dariyar take cewa " ni kam ina zuwa ta zo ta zauna jikina har da tambayata me na kawo mata wai, sai labari take ba ni wai Umma tayi kaza Abba this maganar Safwaan kuma ta k'i k'arewa a bakinta".
"Ohh lallai ashe ni ne akewa yanga, duk kuma Safwaan ne ya ja min ba kowa ba".
"Ranar nake ce mai kar ya koya mata kwad'ayi,ce min yayi wai ai in dai ni ban koya mata ba toh na shi da sauk'i ka ji fa".
"Ai ba k'arya yayi ba, ba wanda bai san shaharar kwad'ayinki ba".
"Kai Alpha.....!"
"Abi i lie?".
"Rayuwar ne sai da kwad'ayi ai".
"Ni ma kwad'ayin nake ji" ya k'are cikin ƙaramar murya.
Duban shi tayi tana cewa " toh me zan kawo maka?".
Wani kalar juya idanu yayi yace " kin fi kowa sani".
Baki ta bud'e zata yi magana ya had'e da na shi ya fara aiwatar da abinda yake nufi don kwantar da kwad'ayin na shi da ya taso.
A na gobe sallah ya kawo musu duk wasu cefane kamar kuma k'aramar sallah wannan karon ma Umma ta aiko da masu aiki guda biyu, kowa da nata ita dai Fareesah ta k'ara kiran sisternta wanda tunda aka shiga satin sallah ta dawo gidan da zama.
Ranar arfa ba k'aramin kuka Fareesah ta ci ba, tana yi tana wa bakinta Allah ya isa da fa yanzu tana can hajjin amma gajen hak'urinta ya ja mata. Ba ta ga umrahn ba ta ga Hajji, addua kawai take yi Allah ya sa ya sauko bayan sallah in an fara tafiya ya biya mata. Da ta ji shigowarshi d'akin ko sai ta share idanunta ta kwanta lakur, ko da ya shigo k'in motsi tayi hakan ya sa shi tunanin ko tayi bacci ne sai kawai ya fita.
Fitanshi bai fi da 20mins ba sai ga kiran wayar Mamanta, d'agawa tayi cikin sanyin murya tana cewa " Mama ya gida".
"Lafiya Fareesah kuna lafiya? Ya maigidan na ki?".
"Muna lafiya Mama na ji kina cikin nishad'i ne me aka samu ne?".
"Ke dai bari, yanzu mijinki ya aiko da cefane da kuma ragon sallah kai yaron nan d'an albarka ne".
"Lifeline fa? Rago da cefane kuma?".
"Eh fa, ba ki ga kayan ba wlh yanzu na kira Baba ina gaya masa".
"Allah sarki, ya kyauta ai".
"Wlh kuwa, ban tab'a expecting irin haka daga mazajenku ba ga shi an fara tun yanzu".
"Yanzu aka fara in Allah ya yarda, ki ce wannan sallahn akwai d'aga kai".
"Sosai ma kuwa, shiyasa nake son in zaki zo gida ki sako kayan da ya fi kowanne tsada don ban son a raina min ke in nunawa kowa na yi farar haihuwa".
"Baki da case Mama, ai kin san kaf kayan da suka sako min babu na banza".
"Ni ko na san da haka 'yar albarka, bari in barki ki masa godiya".
"Toh Mama" ta furta tana ajiye wayar wani mugun murmushi ta saki tana cewa " Yes Fareesah, lokacin mu ya zo ".
Wayar ta d'ago tana fara dialing number Islaam d'in,
bai d'aga ba sai da ya yanke ya kirata back, cikeda excitement ta d'aga tana cewa " Love".
"Cherrie har kin gama baccin?".
"Dole na in gama Babe, Mama ta kirani take gaya min abun arziki thanks so much sweetheart Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i".
Shiru yayi yana saurarar adduointa gareshi bai taɓa sanin haka take da hankali ba sai yanzu, hakan ya sa shi cewa " ba komai Love".
"I must babe, ka bani mamaki sosai fa".
"Miye a ciki? Sai kace na kai baƙon wurin gidan mu ne fa so ki ma daina maganan ok?".
"I too much love you Babe".
"Love you too, ina driving ne sai na dawo" daga haka ya katse wayar yana jinjina farincikin da take ciki, rabon da a gaya masa ana son shi an kwana biyu wato dai ta san a faranta mata ranta in kayi ba daidai bane a baka daidai da abinda ka yi ɗin.
Ita ko bakinta ya k'i rufuwa yayinda duk yanda take jin haushin Islaam kan abinda yake matan hakan bai sa ta k'i jin wani sabon son shi ba. Ta san ba komai bane a cikin dukiyarshi abinda yayi d'in amma tana jin shi sosai cikin zuciyar ta da k'aramar sallah kud'i ya aika ma Babansu har shagon shi na saida katifa wai yayi cefane sai da ta je gida da sallah take jin labarin ga na wannan karon ma cefanen yayi ya aika aka kai can gidan.
Wani matsayi Islaam ya k'ara a idanunta duk da halayyarshi a baud'e suke amma yana da kyawawan hali masu burgewa ya kuma san hanyar kama mace shi d'in ne ba a sanin in da ya dosa ko kad'an.
Kamar yanda ya aika da kayan cefane da rago gidan su Fareesah haka ya aika gidan Abbu, ba kuma wannan shekarar ba ce ta farko tun da ya auri Nadeefah bai tab'a fashin aika masa da abun azumi da na sallah ba wannan wata al'ada ce mai k'arfi a kyawawan al'adun kanuri. Mijin 'ya yana aika kayan azumi gidan sirikanshi domin neman albarka, so su Fareesah sun shiga ciki wannan karon.
Itama Lelen kiranshi tayi tana masa godiya sosai akan abinda yayi kamar yanda ya shaidawa Fareesah that she should'nt mind haka ya gayawa Lelen itama, murmushi tayi ta ajiye wayar tana mai jin sabon son shi a ranta ko lokacin da yake mata wulak'anci yana girmama iyayenta bai kuma tab'a duba cewa suna da hali ba yake hidimta musu ta sani ta kuma san Islaam daban ne kuma zuma ne ga zak'i ga harbi.
Aikinta ta cigaba da yi time to time tana amsa waya, da yake ita ce da girki ya sa da ta gama aikin sai ta fara had'a abun iftar in da duka wurin biyar ta kammala komai ta jera tayi wanka tayi zaman hutawa.
Islaam bai shigo gidan ba sai ana shirin kiran sallah sun tafi da su Islaam wurin cinikin shanun da za'a yi amfani da shi na sadaka, da aka kawo kuma suka tsaya sai da aka yanka aka rarraba na ma'aikatansu aka fara cirewa sai sauran kuma wainda Allah ya ci da su musamman aka samu drivers aka ba su da kayan abinci da kud'in cefane suka fita tituna mutum yana tafiya a hanya za a yi parking a zuge glass a mik'a masa a hannu su ja motar su yi gaba.
Kasancewar a gajiye yake ya sanya yana shigowa gidan sai da ya fara wanka ya saka kaya, bai ko lek'a part d'in Fareesah ba parlor ya nufa ya zauna gefen Lele yana cewa " har kun gama aikin kenan?".
"Mun gama, sannu da dawowa".
Da kai ya amsa yana bin parlorn da kallo kana yace" but kun yi sauri fa".
"Sure, ya naku? Na ga duk ka gaji ne".
"Sosai ma, k'ishi nake ji sosai ma".
Hannu ta d'an d'aura kan knees d'in shi tayi squeezing kad'an cikeda lallashi, sake lumshe idanu yayi yana relaxing cikin seat d'in da kyau.
Su na a haka aka kira sallah, normal routine d'in shi yayi na bud'a baki kafin ya wuce masjid don yin sallah, ita ma ta wuce na ta room d'in tayi sallah yana dawowa suka yi iftar sai da ya natsa ya lek'a wurin Fareesah in da ya samu har lokacin su na aiki duk da ko ta fi Lele sauri but tana da procastination hakan ne ya sa time kan shige mata. Bai wani jima ba aka kira sallahr ishai hakan ya sa bai kowa part d'in Nadeefah ba daga can ya tafi masallaci ana idar da sallah gida ya yo ya samu cikin kujera ya narke yana zuba shagwab'a ita ko Lele sai lallab'a shi takeyi ko doguwar hira ba su yi ba suka shige ciki yau baccin wuri suka yi.
Washe gari daga masallaci ba su wuce Yerwa ba gida suka koma saboda aiki, ai ko sun ji jiki sosai don duka suka yi aikinsu lokaci d'aya suka wuce wurin. Tana samu ta gama aikin ta yi wanka ta kwanta Allah ma ya taimaketa yau ta fita daga girkin, so room d'in Fareesah ya wuce shi ma bayan ya dawo daga can gidansu.
The following day ma ba ta fita ba sai Fareesah ce ta fita, in da shi ma kusan zuhr ya tafi gidan Umma ya aro musu princess. Sosai ta ji dad'in d'aukotan da yayi nan suka shiririce da hira da 'yar ta su suna kuma yin bak'i ba laifi, a nan ta kwana da Lele sai da suka je meeting ne suka maida ta wurin Umma. D'ayan washegarin ita d'aya ta yi wucewarta gidan Adnan, ta d'an dad'e kafin ta tafi zuwa gidan friends d'in ta masu aure ta yi yawo sosai sai yamma ta koma gidan.
Tun da aka yi sallah aka gama ta fara fama da mura da zazzab'i kamar me. Tashin farko ya mata pt ya nuna negative bai yarda ba ya kaita BAY wurin Dr. Bose ta duddubata ita ma ta tabbatar da babu cikin sai dai fever ce ta kamata, allurai akai mata da magunguna suna dawowa sai ga period d'in ta ma yazo haushi ya rufe shi ya dinga k'unk'uni don ya riga da ya saka rai da ciki ne da ita, tana daga kwancen ta dinga masa dariya don ita har mamakin shi take yi kamar wani yaro.
Jinyar da take yi sai da kusan kowa na Yerwa ya zo dubata kai kace wani ciwon a zo a gani ne, da Ainah ta zo kuwa har da cewa " wannan cikin d'an fallasa ne, ita cikin wancan babu wanda ya ji sai gani aka yi".
Kallonta take yi da mamaki sai kuma ta saka dariya tana cewa " toh ai yanzu ma ba cikin ba ne just malaria ce i think".
"Ai ke kullum zancenki wai baki da ciki" Najwaah ta fad'i tana harararta dariya tayi ba ta amsa ba sai Zulfaa ce ta amsa da cewa " kuma fa bai dad'ewa yake nuna kan shi".
"Yanzu dai ba shi bane uwar sa ido" ta fad'i har da murgud'a baki, baki ta rufe tana cewa " maman taki ce fa?".
Hannu ta d'aura kan bakin tana cewa " Laaa, sorry Uomm Little" dariya suka kwashe da shi duka Fareesah da ba ta dad'e da shigowa ba ta mik'e tana cewa " Allah ya k'aro sauk'i Mom Princess" Ameen duka suka amsa suna bin ta da ido sai da ta fita kafin Ainah tace " ba ta so a ce kina da ciki ne fa".
"Ba kin ce tana da ciki ba?" Fad'in Fadwaah tana danne dariyarta.
"Babu wani ciki fa a nan, maganar Ainah ne fa" Ya Budu ta fad'i Bahajja tace " ni ma abinda na ce kenan". Dariya aka saka kowa yana maganarshi daban duk akan Aunty Ainahr, sun dad'e suna maganar kafin kowa ya saki zancen aka d'auko wata kuma.
Kwana biyu tsakani ta samu sauk'i ta warware har da zuwa meeting wanda a can ma sai da aka sake mata ya jiki, ita har mamakin yanda suke d'aura mata ciki take yi ita kanta tana son yin ciki but ta ina zata samu bayan tana period?. Ita dai bata biye su ba sai d'aukar Sairah da ta ga ta sake girma tayi tana sake gasgata zancen Islaam na su Umma ba zasu ba su yarinyar ba duk yanda take son ta amshi abunta but kawaici da kunya yana mata shinge tana fatan su ba su ita a sanda suka ga dama. Ranar tare suka yini a can gidan Ummu sai da zasu wuce ne suka ajiyeta ya d'auki Fareesah zuwa gida.
Some weeks later.
Juyi take yi cikeda kasala tana son tashi amma jikinta yana sake gaya mata " 10 more minutes" wanda shi ne yake sakata sake shigewa cikin duvet d'in wanda duk da tana da matuk'ar son barci amma na 'yan kwanakin nan yayi yawa ta zama lazy, tura k'ofar d'akinta aka yi ba ta juyo ba don ta san ko waye yana shigowa k'amshinshi ya cika mata hanci.
Zama yayi a bakin gadon yana d'aga duvet d'in kai tsaye ya zare shi gabad'aya, sai yanzu ta juyo tana dubanshi yayi kyau cikin 3 pieces suit d'in shi kan nan ya gyaru da kyau ya ji mai tsaf sai k'yalli yake yi. Ido ta lumshe ta bud'e a kan shi tana cewa " good morning Alpha" gira d'aya ya d'aga yana cewa " har yanzu?".
"Na gaji ne sosai".
"Today is monday fa, jiya ina kika je da zaki gaji?" Ya tambaya da mamaki.
Numfashi ta sauke tana cewa " dole in koma gym, jikina yayi nauyi sosai".
"Da buƙatar hakan, ba zaki fita ba kenan?".
"Zan fita sai anjima zan duba quaterly records".
"Ok then, ni dai na tafi" ya fad'i yana k'ok'arin mik'ewa matso shi tayi tana k'ank'antar da idanu ta ce " d'an tsam min".
"What...?" Had'e bakinsu da tayi shi ya hana shi maganar sai da tayi kissing d'in shi iya son ran ta kafin ta zare bakin tana cewa " a dawo lafiya" sake janyota yayi ya lashe baki yace " yau ɗanɗanon ki yayi daban".
"Huh?".
"Yes ofcourse, yafi kullum daɗi".
Murmushi tayi tana juya idanunta tace " kai Yaa".
"Gaskiya na fad'i fa, kar ki hana ni fita wife bye".
Bye ta amsa tana sake kwanciya da murmushi a fuskarta sai da ta d'an natsa kafin ta mik'e gidan ta gyara wanda da k'yar ta iya gamawa saboda yunwa, tea ta had'a a gaggauce ta sha tayi wanka shiryawa ta yi ta fita da k'yar ta iya k'arasawa Yerwa complex d'in saboda yunwar da take ji har da hajijiya. Fruits ta siya a wajen masu fruits d'in bakin gate d'in su kana ta shige ciki, ba ta yi parking a inda ta saba ba a k'ofar shiga Yerwa cuisine ta tsaya shiga ciki tayi ta samu wuri ta zauna tana duba menun su a cikin breakfast d'in su tayi ordern Ayamese noodles da plantain da egg sai tea mai zafi.
Ji tayi ya d'auki time kafin aka kawo mata abinda tayi order, nan ko duka bai fi 10 minutes ba. Abincin ta fara ci a gaggauce tana yi tana korawa da tean sai da ta yi kusan rabi kafin natsuwarta ta fara dawowa, ga mamakinta kuma sai da ta cinye duka tas kafin ta ji dai-dai tissue ta sa tana goge baki tashi tayi ta isa counter ta biya kafin ta fito motarta ta ja zuwa in da ta saba parking kafin ta haye saman.
Tana tsaka da ayyukanta ta kuma jin yunwa kallon agogo tayi ta ga duka bai fi 2 hours da cin abincinta ba 10 da kusan 13 tayi breakfast yanzu kuma 12:36, tsaki tayi ta janyo ledan fruits d'in gabanta ta fara ci tana duba records ya d'an taimaketa but tana yin zuhr a kan daddumar ta yi placing order bai taking time ba aka kawo mata har k'ofar office amsa tayi ta koma ta zauna ta cinye tsaf ta sha ruwa kafin ta samu jikinta ya daina rawa har ta maida hankalinta kan aikin gabanta, kamar almara sai da ta k'ara da milkcake (tres leeches) kafin ta bar office d'in hakan ya sa ta gane tsutsar ciki ke damuntaya zamar mata dole ta sha magani
Kafin ta kai gida sai da ta tsaya a Yerwa Gardens and grills ta siya balangu kana ta wuce, tana shiga viel d'in ta ta ajiye da bag kawai ta shiga kitchen tana d'aura girki.
Tun tana d'aukar abun kamar wasa sai ga abu ya zama gaske a yanzu sai ta ci abinci kusan sau 10 a rana kama daga kan small chops da ba ta rabuwa da su a gida zuwa snacks, desserts har kan abinci, fruits da chocolate k'arin mamakin kuma tana cin su bata dad'ewa take jin yunwa. Har tsakar dare take farkawa taci abinci ta koma ta kwanta, da asuba ko kafin tayi komai sai ta had'a tea ta sha kafin ta samu tayi sallah sai ta kwanta baccin da bata gajiya da shi wanda a cikinshi zata ji ana mintsilinta sai ta farka ta had'a tea kafin ta samu ta iya had'a breakfast ma su.
Duk abinda take yi Islaam na lura da ita da yayi mata magana tace worms ne suke damunta dole ta sha magani, da kan shi ya kawo mata drugs d'in da zata yi amfani da shi sai dai tana sha cikinta ya fara bala'in murd'awa sai amai nan ta dinga kelaya shi Islaam yana rik'e da ita tana kammalawa ya d'auketa ya sakata a bath tayi wanka shi kuma ya gyara wurin.
Ba sai zazzab'i mai zafi ya lullub'eta ba ga kuma yunwa nan fa jikinta ya fara kakkarwa, da sauri ya fita yana d'auko mata abinda zata ci zaunar da ita yayi a jikinshi ya bata a baki ta ci ta k'oshi tsaf kana ya bata paracetamol ta koma jikinshi ta lafe don bayan abinci sai Islaam tana matuk'ar son kasancewa tare da shi duk ranar da bata da girki har ji take yi kamar tayi hauka don ma bacci yana saurin d'aukarta da ta haukace.
Yanzu ma shi ya d'auketan hakan ya sa shi kwantar da ita ya lullub'eta ya tsura mata idanu yana mamakin yanda ta koma, duk wannan uban abincin da take ci ba abinda ya kara mata na k'iba duk da ko har da junks take had'awa kanta sai wanda ba a rasa ba sai dai ya fito mata da shape ɗin da ya dad'e yana fata ta samu komai ya ciko tsaf. Kuma ba ta iya gymming saboda tana farawa take gajiya sai sake d'ashewa take yi haskenta na k'aruwa tana kyau, wuyanta ya zuba ma idanu ganin yanda yake haske har da d'aukar ido ga k'yalli da yake yi. Kai ya gyad'a tuno yanda yanzu take haukacewa a kanshi ɗan taɓa ta da yayi zata zurma, hannunta ya bud'e yana dubawa k'irjinshi na bugawa bai son ya saka high expectations akan ciki ne da ita amma duk wasu alamu sun nuna tana da cikin ne.
Da sauri ya mik'e tsaye waje ya fita yana duba sauran abincin da ya rage ya tabbatar zai isheta kana ya dubi agogo don lissafa adadin hours d'n da ya rage mata kafin ta tashi. Duba roastern clinic d'in yayi don ganin wata Doctor ce zata yi afternoon a yau Saturday, cikin sa'a Bose ce ajiyar zuciya ya sauke yana sake kwanciya cikin kujerar ana kiran Asr tana fitowa daga cikin room d'in ta hannunta kan cikinta tana shafawa gira ya d'aga yana dubanta tura baki tayi ta nufi dining ba tare da ta lura da shi ba abinci ta sako da coconut and pineapple juice d'in da tayi ta dawo kan kujera ta zauna sai lokacin ta lura da shi washe baki tayi tana cewa "barka da hutawa Yaa".
"Yawwa barka da cin abinci wife".
Murmushinta ta fad'ad'a tana cewa " wlh yunwa nake ji sosai fa".
"Ci abincinki ki k'oshi in na dawo masjid zamu fita da ke".
"Ok" ta amsa tana d'an jin ba ta son fitan da yace za suyi don so tayi ta samu time tare da shi da yamman nan tunda yau ne zai komawa Fareesah, sai dai ta share ta fara cin abincin shi ko mik'ewa yayi don zuwa masjid kasancewar an fara shiga masallaci. Tana cinyewa ta mik'e ta koma ciki alwala tayi ta canja kaya tana tsaye a gaban madubi tana kallon kanta, tayi kyau abunta duk da bata shafa ko mai ba a fuskarta. Haskenta ya k'aru sosai ga kuma k'ibar da ta ga tayi a fuska, tab'e baki tayi cikeda jin haushi don babu abinda ta tsana duniya kamar tayi k'iba. Kuma fa ba k'ibar da tayi kawai murjewa ta sake yi sai lips d'in ta da ya k'ara ja sosai, shape d'in da ba ta da shi a yanzu ya fito boobs d'in ta ya ciko sosai ga hips ya bud'e sai dai cikinta da wurin mararta da ya d'an tasa kad'an hakan ne kuma ya saka take jin kamar tayi k'iba sosai don ita ba ta da tumbi. (Irin jikin Nadeefah irin wainda in za su shekara suna ciye-ciye babu abinda zasu k'ara sai dai su murje, irin mu ma we go explain tire kafin a yarda muna cin abinci 😭).
Tana tsayen nan ya shigo yana kallonta da mamaki don har ruwan alwalarta ya bushe babu kuma alamun tayi sallah, dafata yayi da sauri ta waigo yace " lafiya?".
"Yaaa duk nayi k'iba ko?".
"Babu k'ibar da kika yi, komai cif yayi".
K'ara kallon mirrorn tayi tana cewa "but..."
"No buts madam ki daina tunanukan da basu taimake ki ba, ki je kiyi sallah ko kinyi ne?".
Kai ta girgiza masa kawai praying space d'in ta ya nuna mata da hannu ba tare da yayi magana ba, wucewa yayi ta d'auki hijab ta hau dadduma ta tada sallah tana idarwa ta zauna sai da tayi lazumi duk yana tsaye yana jiranta. Sai da ta idar ta cire hijab d'in a wurin ta ajiye tana tasowa veil ta yafa kan rigarta wetlips kawai ta shafa mara k'yalli ta dube shi tana cewa "i'm ready" hannunta ya rik'e suka nufi waje motarshi suka shiga ya ja suka bar gidan a bakin gate suka had'u da Fareesah zata shigo hannu ya d'aga mata ta d'an yi murmushi ta shige su kuma suka fita.
BAY ya nufa kai tsaye Dr. Bosen ya samu a duty sawa yayi tayi mata duk gwajin da ya kamata, urine test ta fara mata saboda shi ne sharp-sharp nan da nan kuwa sai ga sakamako ya fito rad'am Lele tana da ciki. Gwaje-gwajen da ta kuma mata ya sa ta gano kwananin cikin wanda yake 9 weeks 4 days sosai Islaam ya nuna farin cikinshi inda da zasu dawo ya siya mata duk wasu abu da zata buk'ata da gaggawa
Tun da ta gane ciki ne da ita sai kwad'ayinta da yunwan ya k'aru ainun, komai ta gani sai ta ji tana son ci ranar rogo ta gani sai da ta siyo dafaffe ta ko ci da yawa. Da ta fita sai sai ga ta da d'anyen rogon ta zo ta kuma dafawa da sauce, Islaam yayi mamakin yanda ya sameta tana cin don shi bai tab'a ci ba duk da yana yawan ganinshi a hanya ita ko tana ci a gidan Hajjah har k'osan rogo Yaana ke musu. Da yamma ma kiran Yaanah tayi tana tambayarta yanda ake yi ta gaya mata nan ko ta tashi ta had'a da yawa ta soya, ta ci kuwa har sai da ya fita daga kanta da ya shigo shi ma ya ci sosai har yana ce mata dama breakfast tayi musu da shi.
Ranar da dare tana scrolling a tiktok ta ga wata foodblogger ta yi kwad'on garin kwaki har da saka masa tsire saboda tana da tsire sai ta mik'e ta shiga kitchen garin da take eba da shi ta jik'a ta yi yanda ita wancan bloggern tayi ya mata dad'i kuwa ta zauna kan rug nan parlor tana ci sai ga shi ya shigo, tsayawa yayi cak yana kallonta ya tambayeta menene wannan ce mai tayi wai bata san sunanshi ba ce wa yayi " wannan ciye-ciyen naki fa kar ki je ki yi poisoning kanki ba komai da kike gani ba ne ake kai wa baki".
"Wannan dai ana ci wallahi Alpha ba ka san dad'inshi ba ne shiyasa".
"Ina fa zan san dad'in shi? Ke dai ki kiyaye".
Kamar ko yayi mata baki cikin dari ta tashi cikinta yana mata ciwo ga heartburn saboda tsaminshi da yayi yawa sai da ta sha antacid kafin ta samu sauk'i da flagyl da safe ko bata ba shi labari ba ta yi gum da bakinta don ta san sai yayi mata dariya in ma bai saka dokar kar ta sake ci ba ita ko daga abinda ta ji ta gwammaci ta ci abunta in yaso ta sha maganin daga baya.
Yau tun asuba ta tashi da kwad'ayin waina ba wai normal waina da muke yi ba Aa ta semo kuma stuffed one ta sha da tea, daga kan dadduma straight kitchen ta wuce ruwa ta d'an yi warming ta zuba a blender ta kunna ta saka yeast a ciki da nono ta saka butter kana ta zuba garin ciki sai da ya had'e ta k'ara ruwan a ciki ta kashe blender. A k'aton bowl ta juye ta yi grating tarugu ta yanka bell pepper da onions ta zuba a ciki rufe shi tayi ta ajiye gefe, minced meat ta ciro ta had'a da kayan miya ta soya shi da kyau ba da mai sosai ba ya had'a jikinshi ta sa carrot a ciki yana had'e kan shi ta ajiye gefe.
Islaam da zai wuce gym don dawowarshi daga masjid kenan ya hangota tsaye tana juya abu a bowl lek'owa yayi ta window yana cewa " me kuma kike yi da sassafiyar nan?".
D'agowa tayi ta dube shi tayi murmushi tace " Good morning Alpha".
"Morning, me kike yi?".
"Masa zan yi".
"Yau ita Baby yake so kenan?".
"Wlh Yaa, har na had'a battern ma jira nake yi ta tashi in soya".
"Da miya ne?".
"Nope seasoning d'in shi zanyi, da yaji zan ci".
"Bakin nan naki da son yaji ko?".
"Allah ya shi nake jin kwad'ayi".
"Ok tohm, za'a tsammin ko?".
"Sure, sai in maka warming stew".
"Okay wife" daga haka yayi wucewarshi bai dad'e da tafiya ba ta fara suyan wanda ta d'auko yajin ta zuba a plate tana suya tana ci, sai da ta ci iya gejin da take buk'ata kafin ta sha orange juice ta cigaba da aikin don dama da yawa ta kwab'a saboda cikin nan ya koya mata jin abu bai isanta gani take yi zata iya cinye abu duk yawan shi kuma ba ta kan ci d'in sai in kwad'ayin ya taso ta nemi wani abun.
A haka take fama da kwad'ayinta Islaam kuma yana biye mata ko fita yayi ta kan kirashi ya kawo mata wani abun, online vendors ma suna shan cinikinta akwai wata Hussys_kitchen da ta sa awararta a gaba da ci ko ba ta yi niyyan yi ba in Nadeefah ta saka naci sai tayi wani lokacin ma d'anyen take siya tayi nata sauce d'in. Shi dai Islaam kullum hannunshi a bud'e yake duk sanda ta buk'aci abu koina yake sai ya kawo mata hankalinshi ke kwanciya.
A tsakankanin kuma damuwa ya had'u ya wa Fareesah yawa don abinda Islaam yake mata yayi yawa ba fa yana mata wani abu ba ne but ita a wurinta bai ba ta abinda take nema daga gare shi. Ga shi itama tana fama da zazzab'i a tsaitsaye wanda take fatan ya zama ciki ne da ita duk da bata sanar da kowa ba, ita d'aya take fama da lalurarta da yake bata amai zazzab'in ne kawai shi ma na dare ne shi ma sai can tsakar dare lokacin sun yi barci sai kawai ta zare jikinta ta koma gefe sai asuba yake sauka.
Hanci ta ja cikeda bak'in ciki tana duban agogo girkinta ne amma Islaam har yanzu bai dawo gidan ba ma, a k'aida bai wuce magrib a waje amma yanzu ga shi nan ana shirin kiran isha'i babu alamun dawowar shi. Bakinta ta cije ciki tana lissafin kalan rashin kunyar da zata yi masa, don ai ba haka ya saba dawowa a ranakun girkin Lele ba na ta ranakun ne ya raina kuma ba yau ya fara ba so babu wanda ya isa ya hana ta d'aukan mataki.
Duk fa wannan abinda take yi ko flashing bata masa ba balle a sa ran zata kira shi ta ji inda ya tsaya, ko me ya faru amma babu kalan alwashin da bata ci a kan shi ba. Kiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata mugun tunanin da take yi, d'agawa tayi tana kallon mai kiran Bestie ne yake nunawa a kan screen d'in da sauri ta d'aga tana cewa " Gadon zinari".
"Ammatas yaya dai, kun yi magana da shi?".
"Nope bamu yi ba, har yanzu bai dawo ba".
"Toh ki kwantar da hankalinki dai kar ki b'ata masa rai ya hanaki tafiyan nan".
"Da wallahi jiranshi nake yi ya dawo in wanke shi sama har k'asa, saboda na tsani rainin hankali".
"Thank god na kiraki da kin watsa komai, in da kin kuskura kin yi haka da ya za'a yi bayan kin san yanda tafiyar nan yake da muhimmanci".
"Okay, ya ci arzikin tafiya ya shirye-shiryen ta b'angarensu?".
"Nothing special babu wani partyn da za'a yi walima ce kawai".
"Ahh ustaziya" ta fad'i cikeda isgili tana kwashewa da dariya, itama dariyar ta saka sai da suka yi mai isansu kafin tace " kin san in an tuba, ba a komawa inda aka fito".
"Saura ke ai, ki samu miji ki yi aurenki".
"A tunaninki zan iya aure ni a yanzu? Ina ganiyar cin zamani na ta'b ai sai in duniyar ta fara gaya mana ba dai-dai ba tukun".
"Kar dai ki jira sai time d'in, madam".
"Ba fa zan iya yin aure yanzu ba haka kawai namiji ya saka mini takunkumi da karan tsana ni mai saka maza kuka? Kina fa jin yanda mijinki ke treating d'in ki kamar kashi ina ban iyawa".
"Ba kowa ke haka ba, nima kuma ba laifinshi ba ne 'yar iskar matarshi ce take kawar mai da hankali daga kaina ba komai ba".
"Ko ma miye ni dai ki ji da shi ki samu ya bar ki zuwa bikin nan atleast ke ma zaki samu ki d'an ga k'awaye a d'an gyagije".
"Ok babe 3 days ko?".
"Yeah, 3-4 days".
"Ok zan kira ki da safe".
"Oya na good night" ta furta tana kashe wayar daga can sashen, shiru tayi kasak'e da wayar a hannunta tana juya kalaman k'awar tata ta san ita ba irinta ba ce duk son da take wa namiji ba shi zai sa ta zauna ya dinga juyata iya son ranshi ba ba shi zai saka ta d'auki shirmen ko wani d'a namiji ba ne balle ita yanzu tana lokaci manyan 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati take harka da su tabbas ba zata iya zama da mutum irin Islaam a aure gani take yi kud'in shi bai kai ba wanda ita ma Fareesah farko ba wai kud'in ne ya ja ta ba sai kyanshi mai kwantar da zuciya sai daga baya ta gane yana da kud'in sosai shiyasa ta sanya k'afar cin kud'in shi babu d'aga k'afa.
Tana wannan tunanin ta ji shigowarshi cikin gidan mik'ewa tayi da sauri ta shiga bedroom, wanka ta shiga saboda ta san shi da son wanka.
Da yake dare yayi ya san Lele ta kwanta don last kiran da tayi masa ta shaida masa ta kwanta ya sa bai shiga wajenta ba direct d'akin Fareesah ya wuce, a mugun gajiye yake don daga 44 ya wuce BAY sakamakon accident d'in da wata mata mai tsohon ciki tayi daga staircase ta fad'o hakan ya sa ta samu karaya a cinya ga kuma nak'uda da ya taso gadan-gadan an samu an d'aura ta yanzu haka kuma ta sauka lafiya sai fatan Allah ya bata sauk'i.
Wanka ya shiga yayi yana fitowa bai ko goge jikinshi ba da robe d'in ya nufi bedroom d'in Fareesah, a tsaye ya ganta gaban madubi tana shafa turare kallonta yayi da murmushin wankan da tayi juyowa tayi tana dubanshi itama da murmushin bud'e mata hannunshi yayi da sauri ta fad'a ciki ya rungumeta tsam don ya gaji yana neman hutu sosai.
Tana rungume da shi tace " welcome back".
''Thanks Cherrie baki yi bacci ba?".
"Ina zan iya bacci baka dawo ba? Na damu da shirun da kayi sosai " ta fad'i tana narkewa jikinshi hmm kawai yace don ko beep d'in ta bai gani ba balle yace da gaske ta yi missing d'in shi sai yanzu take wannan maganar but yayi mamakin yanda ba ta yi k'orafi ba tunda ya san halinta ba zata jira yayi explaining kan shi ba.
Hakan ya sa shi cewa " na zaci ma fushi kike da ni ai".
"Don me zan yi fushi babe? Na shiga damuwa ne ganin ba ka tab'a kaiwa after 8 a waje ba alhamdulillah da ka dawo".
"Uhmm, shi ne ko sau ɗaya baki kira ni ba".
''I called you, number ne bai shiga shiyasa".
"I'm sorry na ɗaga muku hankali, emergency ne aka kawo kuma mai matuk'ar hatsari but Alhamdulillah yanzu patient d'in tana lafiya".
"Subhanah! Me ya faru?".
Labarin abinda ya faru da condition d'in patient d'in ya bata nan ta dinga salati duk jikinta yayi sanyi har tana cewa ta godewa Allah ba upstairs yayi mata ba, dariya yayi yana jan hancinta yace " shi accident ga mai ciki ai ba sai a kan stairs ba, a koina ana iya samu itama ta ci sa'a da ba a kan cikin ta fad'a ba da yanzu wani maganar ake yi".
"Allah ya tsare gaba, ya bata lafiya".
"Ameen ya rabb".
"Babe ba zaka ci abinci ba ne?".
"Dare yayi da yawa, akwai fura right?" Ya tambaya don jiya ya kawo musu har Nadeefah tayi masa wani damu mai coconut da apple a ciki da dabino da gyaɗa.
"Yes akwai, a dama ne?".
"Sure, na ma shigo da nama yana room d'ina".
Ok ta amsa tare suka fito ita ta wuce kitchen shi kuma ya nufi d'akinshi, furar ta dama masa ta k'ara condensed milk a ciki sai bata saka sugar ba sai d'an zuma kad'an a bowl ta saka masa da spoon kana ta d'auko wani plate ta had'a a kan tray ta fito.
Sanda ta shiga d'akin ya riga da ya shirya cikin kayan barci, kan carpet ta ajiye masa ya mik'a mata naman tare da Lele ya siyo but ya saka nata a fridge d'in shi in yaso da safe tayi microwaving d'in shi. A tsanake suka ci abincin yana lura da ita sai taune bakinta take yi alamun akwai magana a bakin nata hana kanta take yi, dubanta yayi kai tsaye yana cewa " uhum? Tell me mana".
Kallonshi tayi tace " what?".
"Abunda kike son gaya min, just tell me".
"Nothing fa".
"Akwai magana a bakinki, kar ki ji komai just tell me".
"Ai na ga ka gaji ne, i'd tell you in the morning".
"Kar ki damu Babe, yeah i'm tired but ban yi gajiyar da zan kasa jin me kike tafe da shi ba just tell me ok?".
"Uhmm dama Mama ne ta kira ni kan maganar tafiyar da zamu yi biki a Kano, ni na ma manta da bikin sai d'azu take gaya min shi ne tace in nemi izini".
"Kano kuma? Da ma kuna da family a Kano? I thought duka suna Zaria".
"Yea ita kad'ai ce take aure a can Kanon, cousin d'in Mama ce ta zo bikinmu ma Maman ba zata samu zuwa ba ne suna wani biki a nan shi ne tace ni da Aunty Aseeyah zamu je a madadin ta".
Shiru yayi yana nazari haka nan ya ji bai son barinta zuwa bikin sai kuma yayi tunanin idan Nadeefah ne zai hanata? Nan take gaya masa akwai bikin da zasu je a Sudan da k'arshen shekara lokacin ta haihu kuma ya yarda ta tafi sai ita ne zai hana? Bayan nan ma an masa raino mai girma a kan zumunci duk k'ank'antar dangartakar da yake tsakaninku a familyn haka ake tsayuwa tsayin daka ayi maka hidima kan jiki kan k'arfi toh shi sai yace ba zai barta ba? Dama dai na k'awaye ne ba zai bari har a je wani gari ba, in dai ya wuce Kadunan nan toh a bar shi haka nan.
Gyaran murya ya sauke yana cewa " yaushe zaku tafi?".
"Thursday a dawo Sunday".
"3days?".
"Eh may be mu kai 4 days".
"Aa ba zaku wuce 3days ba".
"Meaning ka bar ni?".
"Yes na bar ki, flight zaku bi ne?".
"No mota ne zamu tafi da wasu 'yan family".
"Allah ya tsare,gobe zan tura miki kud'i ku saka mai a mota ki kai na gudunmawa ko akwai wani abinda kike buk'ata?".
"Zan amso d'inkin bikin gobe".
"Nawa ne?".
"70k".
"Ok zan tura da shi, shikenan ko?".
"Eh Babe Allah ya saka, ya k'ara bud'i".
"Ameen sweetheart" daga haka ya mik'e zuwa kujera yana duba wayarshi bai ma jira sai goben ba a take ya tura mata ganin kudin da ya turan sai da ya bata mamaki ainun ta san ba komai ba ne a abinda yake da shi amma ta ji wani mugun dad'i ta tabbatar zai isheta facaka ta nunawa k'awayenta itama ta auri mai hannu da mai, ƙasan ranta kuma tana jin babu dad'in k'aryar da tayi masa sai dai kuma ta san ko da wa take yawo ba zai bar ta na friends ba ko zuwa gidan bai cika son suna yi ba amma 'yan uwa ko mutum nawa ne su zo bai damu ba yanzu dole ne tayiwa Mamanta bayani ta san ba zata k'i goya mata baya ba musamman in ta d'an bata nata kason da itama yayarta Aseeyah.
Godiya ta fara masa wanda daga haka ya juye zuwa karatun da ita da shi suke matuk'ar so, basu yi k'asa a guiwa ba suka fad'a duniyar da suke mararin maganar tafiya kuma bata sake tashi ba.
Da safe bayan fitanshi school ta nufa dama lectures d'aya take da shi 11 to 1 daga can ta tsaya ta karb'i d'inkin ta wuce gidansu, bayanin komai ta ma Mamanta kai tsaye ta goya mata baya har da kiran Islaam d'in tana mai godiyan kud'in da ya bata tayi gudunmawa a cewarta ita aka bawa, kana ta kira Aseeyah ta shaida mata me yake faruwa da farko ta so nuna musu rashin yardarta sai da itama aka mata alk'awarin 50k kafin ta yi shiru. Ta jima a gida uwar na sake nuna mata wasu hanyoyin na karb'ar kud'i kafin ta dawo gida.
Washegari da zai wuce office ne ya kai ta wajen Lele tayi mata sallama kafin d'auketa zuwa gidan Aunty Aseeyahr, bai ko shiga ciki ba a gate ya ajiyeta ta ja jakarta zuwa ciki shi kuma ya wuce. A zaune ta tarda Yayar tata zaune a k'ofar parlorn ta ajiye jakar tana dubanta tace " Aunty ina kwana?".
"Lafiya lau, ya maigidan naki?".
"Yana lafiya, yanzu ya sauke ni ma".
"Ni yanzu kin saka ni a tsaka mai wuya da mijinkin nan? What if ya gan ni a cikin gari?".
"Shi ba gwanin yawo ba ne ai, sai kiyi one week kina bin garin nan ba ku had'u ba".
"In kuma tsautsayi ya had'a mu fa?".
"Haba Aunty mana".
"Ban son abinda zai saka shi zarginki ki na zaman-zamanki aurenki ya lalace a banza".
"In shaa Allahu ma ba zai faru ba, zan je in dawo lafiya".
"Yanzu da ita B queen d'in zaku je?".
"Yes motar ta ma zamu bi, me ya faru?".
"Ki tafi da su Badiyya mana".
"Why?".
"Kin san yarinyar nan ba natsuwa ne da ita ba,tun tuni ta kwashe kayanta ta bar gida tana zaman kanta. Ni ban ma san ya aka yi kike mu'amala da ita ba".
"Aunty ni fa irin lifestyle d'in ta ba wai yana birge ni ba ne sai dai ba ka isa ka shirya kowa ba sai wanda Allah ya shiryar mu ma da muka yi auren muka zauna gidan miji ba wayo ko dabarar mu ba ne yin sa ne da ikonsa so mu gode masa mu daina ganin wasu".
"Ai fa tunda an kira k'anwar uwarki mai gado".
"Kai Aunty...ni fa kawai ban son zagin da ake yawan mata ne mu yi addua kawai In shaa Allahu zata shiryu yanzu ba ga ita Nafeesahr zata yi auren ba? Ina babu kalar rashin jin da ba su yi tare da Bee ba? Komai lokaci ne sai ki ga itama kamar ba a yi ba".
"Ki ma daina had'a rashin jinsu da Bee, ita Nafeesah ta so ta shiryun ne sai Allah ya taimaketa ita ko wannan yarinyar ba abun ne a ranta ba tun da dai kin ce a bar maganar an barta Allah ya dawo da ku lafiya".
"Ameen Auntyna" ba ta kai ga ko rufe baki ba Bestien ta kuma kiranta, d'aga wayar tayi ta shaida mata tana daga waje gata nan ta fad'i ta ajiye wayar ta dubi Yayar tana cewa " toh sai mun dawo".
"Allah ya tsare, ki dai san inda kike ki kuma dinga tuna ke matar aure ce".
"In shaa Allah Aunty bye" ta amsa daga haka ta fita motar ta samu parke a booth ta saka kayan kana ta bud'e gaba ta shiga yarinyar da ke jan motar ta ja ta fiii da matsiyacin gudu don tana son su isa da wuri kasancewar yau zasu fara gabatar da bikin na su, ga sauran tsare-tsaren da suke da shi wanda shi ne ma mak'asudin zuwan na su.
Tafiyar tata wani babin honeymoon aka bud'e a gidan kai kace sabbin aure dama ga shi a lokacin Lele bata da burin da ya wuce jin ta jikinshi sai kawai ya samu damar juyata duk iya yanda ya so, motsi mai k'arfi ba sa yi sai jikin juna gefe guda kuma suna waya da matar tashi ran da zata dawo take shaida masa da tana fama da zazzab'i so ba zata iya hawa mota ba hakan ya sa shi cewa ta kwana washegari ta hawo jirgi haka kuwa aka yi washegari ta sai ticket zuwa kd shi ya je ya d'aukota zuwa gidan har yake tambayarta Yayar tata sai tace ai ita jiya ta dawo gida ita d'aya suka bari cewa yayi " da na san haka da a gidan Baba Prof. Zaki kwana sai Muttee ya kawoki or ya kai ki airport ki dawo ( Muttee autan Baba Prof. ne sunanshi Mukhtar wato sunan Babansu Umma Ameer ake ce masa but ya fi son Muttee kafin a kira Ameer d'in ma sai dai iyayen kamar yanda Suke kiran Sadeeq da Baana)".
Cewa tayi " Ayya da ko mun yi zumunci ka ga dama ban tab'a zuwa gidan ba".
"Sai wani lokacin" ya amsa yana focusing akan titi.
Da suka dawo Lele ce ta had'a dinner ta kai mata tana mata barka da dawowa, godiya tayi mata sosai inda ta ji 'yar kunyar Lelen don ita ba ta yi tunanin ba ta abinci ba da ta dawo daga Umrah sai da ya d'auketa suka fita kafin ta ji babu dad'i. Ta tabbatar ko ita ce Lelen ta hana abincin zai iya d'aukarta su fita ta ciwo abinci, ajiyar zuciya ta sauke suka ci abincin washe gari da ta wanke kwanon har da saka mata chin-chin da dubulan a ciki da ma gurasa wai tsaraba. Godiya tayi mata sosai duk yanda ta so ci ta kasa ji tayi zuciyarta tana tashi abinda ba ta tab'a ba a cikin nan sai ta bayar da chin-chin d'in gurasar ce ma ta kwad'a wacce ta tada mata da k'wadayi washegari sai da ta kuma yin wata a gida ta ci sosai har Islaam yana cewa da ta yi magana da Fareesah ta siyo mata.
2days tsakani Fareesah ta fara ciwo k'ak'as daga zazzab'i abu ya koma ciwon mara, ga shi ita d'aya ce a gidan da ta ji azaba ne ta kirawo Islaam nan da nan ya taho gidan kafin nan ta galabaita ya kinkimeta zuwa mota before ma su isa clinic d'in har jini ya fara zuba mata suna isa aka d'auketa zuwa ciki sosai hankalinshi ya tashi don ya gane me yake damunta b'arin cikin da bai ma san da shi ba tayi. Sun yi mata duk abinda ya dace sukai mata wankin mara kana aka gungurata zuwa d'akin hutu haka su Drs. D'in clinic d'in suka rufe shi suna bashi hak'uri don ko ta rasa jinjirin cikinta da yake 7weeks wanda ko ita ma bata sani ba zato kawai take yi amma bata san da akwai ba.
D'akin da aka kwantar da ita ya shiga yana kallonta tana baccin wuya duk ta sauka sai hasken da tayi masa, goshinta ya shafa cikeda jin tausayinta sosai yake son yara duk da bai san tana da ciki ba but ya ji zafin rashin shi. Nadeefah ya fara kira ya shaida mata da suna asibiti kana ya kira Umma itama ya gaya mata sai Mamanta. Kan kace kwabo ko clinic d'in ya d'inke da mutane kowa ya zo ana ta jimami, ko da ta farka aka gaya mata kuka tai tayi sai da aka lallasheta kafin ta hak'ura amma har ranta ta so rik'e babyn Burhaan a hannunta wa ma ya sani ko namiji zata haifa?.
Haka 'yan familyn suka dinga hidimar abinci ga masu zuwa don 'yan gidansu ba sa kawo komai, Lele ko kullum ita ke kawo abinda zata ci tun safe har dare wanda sai Fareesahr ta kai zuciya nesa take iya ci musamman idan ta dubeta da cikinta da yake cikin wata na hud'u duk ya fara nuna kan shi sosai har ji take dama ita ma na tan ya b'are duk ayi biyu babu.
Kwanansu biyar aka sallameta da Mamanta ta so ta ta fi da ita gida, amma Islaam ya k'i hakan ya sa ta hak'ura sai aka bar mata Adama don ta taya ta zama. Ko da suka dawon Lele ba ta daina hidima da ita ba,tsaye da ba gani suke yi ba sai ta kawo su kushe though ba a gabanta suke yi ba su biyu suke kayansu duk da ko tana dawowa gida ta amshi mijinta bai sa ta daina ba sai da ta warware ta fara zuwa school kafin ta daina tayi focusing a kan kanta don ita ma ba wai ta cika lafiya ba ne.
Tun da cikinta ya kai wata na hud'u ta fara jin canjin yanayi, son jikin Islaam da take yi yanzu duk ya sire mata a kai. Ba ta son ya rab'eta ko ya zo kusa da ita sai dai tana jurewa ainun don bata son duk abinda zai b'ata masa rai,amma kullum abun yana ƙara zaman mata azaba don har k'amshin na shi ma bata so in ya taba ta yana fita sai tayi amai.
Yau tun da ta tashi take jin k'yank'yani komai na d'akinta bai mata ba, gyaran d'akin tayi ta canja turaren humidifier ba ta saka na tsinke ba sai wani halud da shi d'aya ne ya mata dad'i sai ta saka shi a burner ta turare d'akunan. Ta shiga gyaran d'akinshi ne ta ji kanta na mugun juyawa jin k'amshin turarenshi da ya game d'akin, abu ta ja ta rufe hancin ta fara gyaran duk da ko ta rufe hancin da k'yar ta iya kammalawa lafiya tattarawa tayi ta fita ta zauna a parlor tana maida numfashi sai da ta samu ya saketa kafin ta tashi tayi wanka ta wuce office a can ma ba ta sauya zani ba don k'in zuwa d'akin da suke had'a turare tayi ta zauna a office d'in ta da aka kawo mata wainda aka gama ta duba fatattakarsu tayi waje suka dinga mamaki don babu abinda take so duniya da ya fi k'amshin turare.
A haka ta yini 4 ta kwashi jiki zuwa gida don yau Islaam zai dawo yayi tafiya zuwa Lagos wani conference kwanansu biyu, kuma ya fad'o ita ke da girki tana dawowa ta fara hada-hadar girki steamed rice ta dafa da green veggie sauce da ta ji kifi. Tamarind juice ta had'a da salad ta danka komai kan dining ta shiga tayi wanka,ba su shigo da wuri ba sai kusan 9pm Safwaan ne ya d'auko shi yau ko shigowa bai yi ba ya juya.
Tana jin shigowarshi ta nufi d'akinshi da azama, sai dai k'amshin da ba ta so ne ya daki hancinta dakatawa tayi ta d'auki serviette dake kan dining d'in ta ta shiga d'akin bakinta da sallama. A tsaye ta same shi tsakar d'akin alamun yana jiranta ne don ya saba yana tafiya take tararshi with so much longiness kai kace wacce tayi shekara ba ta ganshi ba, tana shigowa ta fad'a jikinshi wanda a take ta ji kamar tayi amai but ta daure ta cije tana cewa " welcome home Husband".
"Thanks Wifey,kina lafiya?".
Da kai ta amsa don bakinta ya cika da miyau sosai, ja baya yayi yana cewa " lafiya dai ko?".
Da kan ta sake amsa masa, bai damu ba yace " bari in yi wanka,ki jira".
Yana shiga d'akin da sauri ta juya zuwa parlor toilet ta fad'a ta fara yin amai, sai da ta amayar da komai na cikinta kafin ta fito lokacin ya fito shi ma k'anakun kaya ya saka ya nufi part d'in Fareesah Adama ya samu kawai tana kallo a Arewa24 gaishe shi tayi ya amsa direct d'akin Fareesah ya nufa waya take yi yana shigowa tace " bestie, mijina ya dawo zan kira ki da safe" daga haka ta katse wayar, baki ta washe tana cewa " welcome back baby" rungumeta yayi tsam yana cewa " ba ki yi missing d'ina ba kenan".
"In ji waye, nayi missing ɗin ka wlh".
"Missing me a baki ba? Kullum sai ki ce you are missing me but ba kya kirana".
"Kana fa kiran mu Lifeline, ban son shiga lokacin aikin ka ne shiyasa".
"Uhmm" ya amsa tana jikinshi, kusan 5 minutes kafin ya janye jikinta yana cewa " bari in je in kwanta".
"Okay, good night Sweetheart Allah ya huta gajiya".
"Night" daga haka ya juya ya fita, part d'in su ya koma parlor ya nufa don yana jin yunwa and he's very sure Nadeefah ta had'a masa the best dinner ever. A kan kujera ya tarda ta tana numfashi hannu ya kai zai tab'ata ta mik'e tana cewa " lemme serve you".
"Wannan zai iya jira, barin fara jin ɗumin ki first".
"Ba zan iya ganin ka a haka kana jin yunwa ba mu je ka ci abinci ina nan ba zan gudu ba ai".
Dariya yayi a tunaninshi ko tana jin tsoron in ya tab'ata ba zai ci abincin ba sai ya samu natsuwa, matsalarshi kawai toshe hancin nan da take yi ne bai san me yake damunta ba. Ko a wajen cin abincin ma haka tayi ta yi da suka gama ko ya buk'aci abinda aka alk'awarta masa nan fa ta fara masa wala-wala da ya matsa mata kuwa sai ga hawaye yana zuba hakan ya sa ya k'yaleta tunaninshi ko akwai inda yake mata ciwo sai kawai yace su tafi su kwanta nan ma ya zama d'an zani don cewa tayi ya tafi na shi d'akin ya kwanta.
Zuwa lokacin kam ran shi ya fara b'aci don ga zahiri nan gudun shi take yi, juyawa yayi ya bar mata d'akin kawai. Na shi ya tafi ya kwanta cike da kewa, haka ya dinga juyi yana tsaki itako hankalinta kwance tayi barcinta sai asuba ta tashi yau ko abincin tsakar dare ba ta tashi ci ba.
Da safe normal suka tashi bai nuna mata komai ba, duk da har lokacin hancinta a toshe yake da tissue. Ko da tayi serving d'in shi abincin komawa tayi kan kujera ta zauna da ya gama daga kan dining ya juya ya fita a k'asan ran shi yana imagining abinda yake damunta.
Tun daga ranar bai sake attempting tab'ata ba, duk kwad'ayin shi ya tarkata zuwa wajen Fareesah duk da dauriya kawai yake yi ba ta kashe masa k'ishin da yake fama da shi amma tunda ita wacce yake muradin ba ta so sai ya tsura mata idanu. Ganin bai damunta ya sanya ta kwantar da hankalinta a nata tunanin ya fahimci mai yake damunta ne shiyasa ya sakin mata mara shi ko d'an bawan Allah bai san ana yi ba wai kunu a wani gida.
Yau kam abun ya isheshi don sosai yake da buk'atarta, tana gama serving d'in shi ta mik'e don komawa cikin parlor da niyyar idan ya gama sai ta zo ta ci. Hannunta ya rik'e yana nuna mata ta zauna zaman tayi kawai ta duk'ar da kanta k'asa hannunta kan hancinta hawaye yana zuba, abincin kawai yake ci yana ayyanawa a ranshi yau sai ya kawo k'arshen saɓanin da ke tsakaninsu a na shi tunanin ko laifi yayi mata bai sani ba.
Da ya kammala tashi yayi ya bar mata table d'in, sai lokacin ta saki hancin abincin ta zuba tana ci tana mai jin kewarshi da son kasancewa da mijin nata turarenshi ne kawai matsalarta bata kuma san yanda zata gaya masa ba. Tana gamawa ta kwashe kayan ta kai kitchen wankesu tayi ta jera ta dawo parlorn ganin yana zaune ya sa ta nufi d'aki hannu ya sa ya janyota zuwa jikinshi, idanunta ta bud'e tana kallonshi kallonta shima yake yi d'ukawa yayi yana had'e bakinsu waje d'aya kissing d'in ta yayi da duk wani abinda yake da shi sai da ya tabbatar ya samu sukunin kewar lips d'in ta da yake ji kafin ya sake ta, sakin nata da yayi dai-dai da sakin wani uban amai a kan jikinshi yi take yi tana k'arawa tsayawa yayi cak yana kallonta.
Wai yau Nadeefah ce ke amai don yayi kissing d'in ta? Baki ya bud'e yana cewa " amai fa kike yi wife just saboda nayi kissing ɗin ki?".
Baki ta bud'e zata bashi amsa wani aman ya sake zuwan mata ta sake sakin mai don duk abinda suke yin bai saketa ko na second d'aya ba, ba ma zai iya sakintan ba don duk da abinda tayi ya zafe shi ba zai iya sakinta ba ganin yanda take shaking kamar ta k'arar da kayan cikinta a waje...........
Wannan yaron na Lele akwai tsurfa wallah, ji yanda yake gudun babanshi kamar mugun abu🙄?
Deejasmah 🎭