CHAPTER 30
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----30
Iman ta share hawayenta sannan ta ɗago ta kalli Suhail
"ba inda zanje"
"kin fiso ki zauna a maidake baiwa"
"ai na jima da amsa wannan sunan,dan haka kaje ka cigaba da shirin bikin ka"
Aunty Fauziya da shigowar kenan Dakin ta ce"Suhail leave her Please tunda tace bazata ba"
ba a san ransa ya tafi ya bar taba sosai zuciyarsa ke jin nauyin abinda yayi mata chanjin ba a iya Iman ya tsaya ba har aunty Fauziya ma yaga hakan a fuskar ta
zama tayi kusa da iman ta kamo hannun ta saka cikin nata "Iman kiyi haƙuri i know the pain you are going through ,Amman ina so ki sani duk wani dan adam baya wuce ƙaddarar sa ki dauki hakan a matsayin jarrabawa ina da yaƙinin nan da wani ɗan lokaci komai zai wuce akwai ciwo amman kiyi haƙuri duk da nasan a cikin abubuwan dake faru ba'ayi maki adalci"
Ta share hawayen da ke gangarowa daga fuskar Iman
"bana son wannan kukan Bana son ki bari duniya ta ga rauninki cikin sauƙi inaso ki zama jaruma kamar ko wacce mace a gidan auren ta"
Kuka Iman ta saki a hankali
A hankali Aunty Fauziya ta rungume ta
jinta take tamkar ƴar da ta haifa a cikin ta.
sakin aunty Fauziya tayi ta ce"Bara naje na duba girki"
tana fita ta gamu da Amatullah a falo ta dawo daga raka Naima saloon tana riƙe da Ayla ta tambayi aunty Fauziya "ina Iman"
"tana bedroom"
da gudu ta shiga dakin bakin gado ta zauna tana sakar mata Murmushi fara'ar dake kan fuskar ta ya gushe ganin alamun hawaye kan fuskar iman
ajiye Ayla tayi a gefe ta kalli iman"aunty kuka kike"
girgiza kai tayi tare da yin murmushi ta ce"Amatullah i'm not crying"
"aunty karya babu kyau gashin kina kuka are You crying saboda Uncle zai ƙara aure"
"Amatullah i'm feeling headache"
Ayla ta dauka "let me get you medicine from momy"
ba bata lokaci ta dawo hannun ta riƙe da paracetamol ta miƙa mata da robar swan
bayan ta sha miƙa mata sauran
kusan minti biyu ba wanda yayi magana Amatullah ta ce"Aunty dama Uncle baya sanki ya aure ki shiyasa zai kara miki kishiya just seven weeks to You weeding wallahi naji ma na daina son shi kamar ɗa "
bata karasa maganar ba ta rufe mata baki "kar in kara jin kin fadi haka,kuma ai ba laifi bane dan ya kara aure ko baki je isilamiya ba Namiji yana da right din da zai auri mata har hudu"
Amatullah ta bata rai ta ce"na sani Amman aunty Uncle bai maki Adalci ba it's to earlier ya yi aure kinga ko daddy ma baiwa momy kishiya haka aunty Naima"
Aunty Zarah ce ta shigo rike da junaid kallo iman tayi ta ce"ya jikin naki Amatullah ta ce kan ki na ciwo"
murmushi tayi ta ce"Aunty da sauki ma sossai"
"to Allah ya sauwake"
kallon Amatullah tayi ta ce"kije dakin mami ga mai lalle chan zata maki"
Amatullah ta ce"momy za'ayi ma aunty Iman ma"
"idan ta gama maku sai tazo nan tayi mata"
suna fita iman ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita
Zeenah ce zaune a dakin mummy an gama yi mata jan lalle whatapp massage ya shigo wayar ta sabuwar lamba ta gan an turo da wasu videos har guda ukku
Hannunta ya fara rawa, numfashinta ya ɗauke na ɗan lokaci yayin da take kallon video na farko Da ta kunna na biyu, sai da ta dafe kirjinta jin zuciyartar na kokarin fitowa daga kirjinta
wani ihu ta saki bayan ta gama ganin videos din da aka turo mata gaba daya hankalin Mutanen dakin ya dawo kanta
Kanwar mummy nusaiba ta matsa kusa da ita "Zeenah lafiyar ki kuwa kike wa mutane ihu haka"
ƙoƙarin amsar wayar take zeenah ta taƙi badawa "Aunty bakomai kawai wani abu ne ya bani tsoro a cikin wayar"
tsaki yayar Alhaji ibrahim dake gefe taja cikin faɗa ta ce"Zeenah wai yaushe zakiyi hankali dan abu ya baki tsoro maimakon ki kira sunan Allah shine zaki sakar wa mutane ihu"
bata cikin nutsuwar da zata maida mata martani maganar da tayi mata gyalenta ta dauka ta fita falon ƙasa mummy na zaune a falo tare da abokan ta ko tan su bata bi ba ta fita
a yadda ta fita ba nutsuwar kasan ba lafiya Mummy a tattare da ita tabi bayan ta amman bata ganta ba
cikin fulawowi ta shiga ta boƴe ta kira lambar da aka turo mata videos dariya aka saki "Hajiya Zeenatu Ibrahim makama"
nasan zaki kira ai daman amaryar Barrister suhail
kuka zeenah ta fashe dashi "haba Khalid miyasa zaka min haka ka cuceni ai duk abinda ya faruwa tsakanin da kai ka dauke ni video Allah ya isa tsakanina dakai Khalid kaci Amanata na saki jiki dakai shine kake neman tozartani"
dariya Khalid ya saki ya ce"Zeenah ashe kinsan Allah,Kin manta alkawarin da kika min kenan Zeenah? Yanzu saboda kuɗin Suhail zaki yaudare ni"
cikin kuka ta ce"Khalid kasan i'm not after his money inason suhail tsakani ni da Allah badan wani abu ba na roƙe ka goge wannan videos kar ka rusamin ranar da na jima ina daukin ta kar ka kawo dalilin fasa aure na Suhail"
kuka take sossai
Khalid ya ce"Abu biyu ne zai ceceki daga ganin videos dinki a Social media na farko kiyi transfer din three million zuwa account dina na biyu kuma i need to make some love with you a daren nan"
gaban tane ya fadi jin bukatar sa ta biyu tayi ƙasa da murya ta ce"zan tura maka five million Khalid amman bazan sami damar zuwa inda kake ba ko ka manta gobe daurin aure nane duk idanun Mutanen gidan nan akaina yake"
"okay haka ma zaki ce to ki shirya shiga tashin hankali nan da awa daya kuma nasan matukar videos din ki suka kai ga Suhail babi abinda zai hana ya fasa auren ki dan ba abinda zaiyi da lalatacciya irin ki kura da fatar Akuya"
katse wayar yayi
zama taji dirshen tana sake kallon videos
Wayar ta faɗi daga hannunta
Hawaye suka cika idanunta a karo na farko tun bayan da aka saka ranar aurenta, Zeenah ta ji tsoron rasa Suhail miyasa tun farko ta saki jiki da Khalid har ta sakar masa ragamar jikin ta yake sarrafa tamkar matar sa da iya sakayyar da zai mata kenan hatta motar da yake hawa ita ce ta siya masa amman ya rasa sakayyar da zai mata sai dai yayi recording nude din ta ya rinka mata barazana dashi
Ta rufe idanunta tana girgiza kai.
bata da sani option illa kawai taje ta samu Khalid duk ma Abinda yaga zai iya yayi da ita,ita dai kar auren da Suhail ya fasu
"Zeenah da wa ki ke waya"
Muryar mahaifiyar ta daƙi kunnen ta da saurii ta saki wayar hannun ta cikin rawar murya ta ce"mummy Suhail ne"
kallon da mummy tayi mata yasa ta shiga tashin hankali alamun ta gane karya take
"duk fadin gidan nan ki rasa inda zakiyi waya da shi sai garden"
"mummy ina bukatar sirri ne"
yayi idan kin gama sai koma ciki mai dilka na jiranki
wayar ta dauko koma ciki
an fara dilkan kenan massage din Khalid na sake shigowa
"don't waste my time zeenah"
a gaggauce ta mai dilkan ta gama sakamakon matsawar da zeenah tayi da kyar ta bari aka kammala
mayafin ta dauka da key din motar ta ta bi ta kofar baya ta fita bayanbta kira Khalid ya tura mata da address din da zata same shi
Gaskiya idan bakwa comment yadda ya kamata zai rinka yin page guda guda a rinƙa like kuma