Chapter --- 15
Bismillahir Rahmanir Raheem.
***Namiji Ƙanin Ajali***
Written By
Amdeey Tejj d'Unique.
Page -- 15.
Tafiya kawai nake, ni kai na bazan ce ga halin da nake ciki ba balle inda na dosa,na rasa kuka zanyi ne ko jimami,abin dai yana bani mamaki yadda matar nan ta koreni lokaci guda ba tare da wani dalili ba,taya mutumin da ya taimake ka batare ka roƙa ba,yayi maka karamci irin wannan, lokaci guda kuma yayi maka haka,to ko dai dama ƙarya take min,kai batayi kama da waɗanda zasuyi hakan ba,duk da baka nagari a ido, idan tayi min ƙarya meye ribarta,amma zaiyi wuya ace zatayi min ƙarya,to idan ita ta min shi wanda mukaje karɓar kuɗin a wajen sa fa?,iya tunani da hasashe na na kasa gano komai,abu ɗaya na fahimta a cikin idanunta shine firgici, akwai firgici da tsoro a idanunta amma tayi ƙoƙarin ɓoye shi, amma bayan nan duk iya hasashena ban gano komai ba,da irin waɗannan tunanin da bansan malamar su ba na tari keke napep na shiga gwiwata a mugun sage,a ɗazu ina da ƙwarin gwiwa na fuskantar Habibu, amma bazance ga halin da nake ciki ba ma, na gayawa me keken inda zai kai ni muka ɗau hanya bayan ya gaya min kuɗinshi na bashi.....
A bakin ƙofar shiga tashar ya tsaya na sauka,ban tsaya ba kasancewar na riga na biyashi na nufo ƙofa,a wajen na tarar da Habibu na kai ka dawo hannun sa rataye a bayanshi , gabana ya faɗi amma sai na dake nayi ƙoƙarin aro jarumta na yafa,na ƙarasa inda yake a hankali na kira sunan shi,jin muryata a fusace y juyo ya hau sauke min kwandon bala'in da yayi dakonshi yake jiran in sauke mai,inda yake shiga ba nan yake fita ba, ina naje na zauna,a cikin faɗan na shi ne na fahimci ashe jikin Hajja ne ya tashi aka faɗa mai,raina ya ɓaci,ya zai zo yana min faɗa a bakin shiga tasha kamar ba matar bariki ba matarsa ba,na rasa inda Habibu ya koyo wannan halin na duk inda ya sameni sai ya hau magana ko da na ɓacin rai ne,ko kuma wanda ya kamata daga ni sai shi ne,duk da na gane dalilin ɓacin ran nasa, amma ai ba hujjar da zai min faɗa a bakin kasuwa bane tunda ba a gida muke ba, kuma nima fafutuka naje yi dan wannan matsalar amma a haka bai tambayi dalilin da yasa na kai wannan lokaci ba,ƙalau nake ko matsala aka samu,ya hau diri yana masifa abin takaicin ma shine a bakin tasha kamar wasu ƴan bariki, wannan tunani yasa raina ya ƙara ɓaci,shigewa nayi ban ce mishi komai ba,da haka ya ɗauki fushi,a inda maza suke sallah ya kwana,ni kuma a inda muke kwana,dan mita ya cigaba dayi wai na maida shi mahaukaci yana min magana amma na share shi,nan ma bance mishi ci kanka ba har yayi ya gama,sai kuma ya hau fushi,ko takanshi nima ban bi ba.
Washe gari muka tashi bai kula ni ba,nima ɗin dai gaishe shi kawai nayi,bai amsa ba sai ce min da yayi na shirya yau zamu koma,yayi maganar kamar an cusa mai tsumma a baki,amsa mishi nayi ban mishi banza kamar yadda ya min, kasancewar tsakanin Lafia da Shabo ba nisa suke dashi ba yasa muka tari keke napep ya ɗauke mu,muka miƙa hanya.........
Halima.
Ina zaune a bakin murhu na,na gama hura wuta kenan wajajen ƙarfe biyar saura,ban hura da wuri ba yau,dan shinkafa kawai zan dafa fara ina da miya,Hassana tana bakin ƙofar ta tana soya-soyen kaji tana waƙe-waƙen da ta saba na habaice - habaicen da nake rasa da wa takeyi, kamar ba yammaci ne ya ƙarato ba da ya kamata ace kowace mace tana ƙofarta tana ƙoƙarin ɗora abun da zasu ci da iyalanta ba,amma maimakon hakan ga wasu daga cikin matan gidan suna zaune a ƙofar Hassana suna ran gadin ayi a ɓalla musu,sammarwar da da Hassana tana halin yaɗawa kowa yaji a garin da anyi kowa yasan ta samma musu nama ,a basu azo ana musu gori amma bashi zaisa gobe suƙi zuwa ba, duk da ba kowa ke cin abun hannun Hassana ba saboda gori,dan mutum mai zuciya ba dan Musulunci ba to da ko sannun fatan baki ba zai sake haɗa ka da Hassana ba,amma su Ladiyo da Lantana kam ko dukansu zatayi kafin ta basu sai sai sunci balle kuma gorin da da baki za'ayi shi, kamar baƙin cin nama.
Ina zaune a wajen Bature ya shigo ,a kafa yake da alama a waje ya ajiye mashin ɗin tunda ba lokacin dawowarsa bane yayi,koda yake yadda yake ji da mashin ɗin nan yau ne kawai yayi ra'ayin ajiyewa acan,
amma ko mantuwa yayi ya dawo to sai kawo mashin ɗin har ƙofar ɗaki kafin ya faka.
"Halima"naji ya kira sunana bayan ya shiga ɗaki,na amsa na bi bayan shi,tsaye na same shi a tsakar ɗakin,kallo ɗaya na mai na kau da kai dan har ga Allah ni yanzu a dole nake kallon Bature kusa dani,kamar baƙin kumurci nake kallon shi,yayi man abubuwa da yawa a rayuwata, wanda bazan iya mantawa dasu ba balle in yafe.
Maganar sa ce ta katse min tunani ''me ya haɗa ki da Sabuwa har kika mata rashin kunya?,ɗazu ina kasuwa Malam Na Sidi yazo ya same wai kin yiwa matarsa rashin kunya"
Numfashi na kawo na sauke,dama nasan sai sun kai ƙarata ko wajen shi ko wajen umma,na buɗe baki zanyi magana kenan tashi maganar ta katse ni.
"Yanzu ke koda kuɗi sai ki buɗe baki ki zagi wannan mata?,koda bata haife ki ta girme ki,tunda zatayi sa'ar margayiya maman Fareesa,wato abun naki ya wuce kaina ya kai har maƙota da ƴan unguwa ma,dama ni bakya gani na daraja to wallahi ki shiga taitayinki dan bazan ɗauki wannan iskanci da rashin tarbiyyar ba"magana yake kamar zai kai min duka,kai kace tashi mahaifiyar sa na zaga.
Da nayi niyyar na bar mai ɗakin tunda hukunci yazo yankewa ba bin ba'asi ba,amma rashin tarbiyyar da ya kira gidan mu dashi yasa naji bazan iya ba dan bazan iya jure ji yana cin mutuncin gidan mu ba,dan haka na juyo na kalle shi a nutse dan maganar zai kwana yana tunawa nake so nagaya mai dan haka ina buƙatar nutsuwa"ay dana san hukunci kazo yankewa da ban ɓata lokaci na wajen sauraren ka ba,da nace kayi abun da ya kawo ka kawai kai tsaye, rashin kunya kuma ai shi yayi min ado har ka ganni kace kana so,tunda idan ban manta bani nace ina sonka ba,kai kace kana sona,to kaga ashe kaima shi ya burge kenan har ka auro ni, rashin ganin daraja kuma da kace bana ganinka dashi komai ya samu shamuwa ai watan bakwai yaja mata, tarbiyya kuma da kake maganar bani dashi kai kasan ko da girgiza kurna ta ɗara magarya,dan ko maƙi gani bazai wa gidan mu wannan shaidar ba,kuma gidan rashin tarbiyya ya maka rana ai,ko kamanta In tuna maka?,ka kiyaye ni Bature tam''daga na fice daga ɗakin na barshi baki sake,ina fita ban tsaya a wajen ba dama nagama dafa shinkafar har na kwashe a kula ruwa ne a wutan, kular kawai na ɗauka na bar wajen kafin ya farga dan na fahimci yayi suman tsaye,dan ban taɓa gaya mai magana irin haka ba,dan haka kafin ya farfaɗo gara bar wajen,dan zai iya biyoni ba damuwar shi bane ayi uwar watsi a gaban kowa,kuma idan ya fito yaga abinci na ba kunya ne dashi ba sai ya ɗauka ya cinye ba abun da ya mai zafi, hakan yasa na ɗauke kular abinci na tafi da shi.
A ɗakin Inna Lami na yiwa kular masauki,ban tsaya ba na fice daga gidan,da yake jikina fes yake ba kace aiki nake na fito ba,dan bana zama da ƙazanta ko kaɗan,tafiya kawai nake ina tunani wai nice har nake gayawa Bature magana haka, tunda nake hasaso rayuwar auren mu kafin na shiga dama bayan na shiga ban taɓa hasaso wannan rayuwarce zata wanzu tsakanin mu ba,na tuno soyayyar mu, wahala da gwagwarmayar da muka sha ko ince nasha dan sai yanzu ma wani abun yake gifta min akaina,nake ganin irin ganganci da wautar da nayi, ajiyar zuciya kawai na ke saukewa,bansan inda zani ba, amma ko hauka nake bazan nufi gidan mu ba,dan ko da asiri naje umma ba zata goyi bayana ba, kuma ko bayan haka ma na ɗauki alƙawarin ni bazan taɓa yin yaji ba,sai dai idan saki na yayi, gidan ƙawata wasila na wuce kai tsaye da yake ba nisa tsakanin mu,anan na ƙarasa yammacin sai bayan Isha na dawo,a raina ina ta mamakin yadda suke kulawa da juna ba gajiyawa,kamar basu shekara goma sha da aure ba, kamar ba auren ƙiyayya ba,sai soyayya da kulawa suke nunawa junansu kamar basu suka haifi yara shida ba,nan na baro su da tazo rakoni kuwa na hau mata tsiya wadda kamar al'ada muddin naje sai na mata nakan ce mata"oh wasila mamaki kike bani idan naga yadda kike ɓare-ɓare akan Halliru, kullum naga haka sai na tuna ranar da muka kawo gidan nan"
dariya kawai takeyi duk sanda na mata wannan tsokanar tace “kuma yanzu a haka nake son abuna”,da haka take kashe bakina, kenan nima da na auri tanimu da ban kasance a haka ba,kai amma har abada bazan taɓa iya auren Tanimu ba ko na bar Bature,ba dan komai yasa bana son Tanimu ba sai kasancewarsa tsoho,duk da bai sa'an baban mu ba,amma ba yaro bane, daɗin daɗawa ga muni,ni kuma bana son tsoho bana son mummunan namiji a rayuwata, waɗannan dalilai su suka naƙi shi,duk da wasu suna cewa duk munin namiji inda kuɗin sa kyakkyawa ne,ni kuma ba kuɗi bane a gabana, iyayena ma nasan ba saboda kuɗin sa suka so in aure shi ba,sai dan sun hango min abun da ni na rufe idona daga hango shi saboda soyayya, iyayena masu rufin asiri ne, sannan suna da wadatar zuci, wannan turbar da suka raine mu akai,nakomai ka samu a rayuwa komai ƙanƙantarsa kace alhmdllh, yasa ban damu da kuɗin Tanimu ba,nabi soyayya ta,batare da nasan kara da kiyashi na ɗauka ba.........
Toh ku gafarce ni,zan huta anan muhaɗu a next page.
Naku Amdeey Tejj d'Unique.....