Chapter 27
Chapter 27
Fitar Firdausi da wuya, aka ji ƙarar mota a compound, Farida ce ta leƙa ta window sannan ta juya da sauri ta haura sama
A hankali ta buga ƙofar ɗakin Zahra.
"Anty..."
Zahra ta ɗago kanta
"Na'am?"
"Mama ce." Cewar Farida
Zahra ta haɗe gira
"Wace Mama?"
"Maman Alhaji Khalil."
Nan take Zahra ta miƙe ta ce
"Ina zuwa"
Toilet ta shiga ta wanke fuskarta da ruwan ɗumi, ta goge ta da towel sannan ta gyara scarf ɗinta kafin ta fito, hijab ta saka sannan sannan ta fita
A parlorn ƙasa ta same ta zaune, da alama daga gida take saboda babu alamar gajiya a jikinta
Zahra ta ƙarasa ta zauna
"Ina kwana Mama."
"Lafiya lau" Ta amsa
Sannan ta ɗan yi murmushi.
"Na zo ne ina son na wuce office, nace Khalil ya kai min ke. Shine kuma nace bari na zo kawai da Kai na dan Ina da program da yanma"
Sai ta ɗan yi shiru.
"Amma na ji kun samu matsala har shekaran jiya ya kwana a can gida?"
Zahra ta sunkuyar da kai, fingers ɗinta take wasa da su,
A da can zata iya ɓoye mata, amma yanzu? Bata ga dalilin yin hakan ba kawai gwara ta fada ko data koma gida karta ga bakinta
Sai ta ɗago kai, a hankali ta fara bata labarin komai, tun daga Pretty, har zuwa Lovie Dovie, har zuwa yadda Khalil yake fita da daddare baya kwana a gida, har zuwa hotunan da ta gani tare da kawarta
Maman ta saurare ta ba tare da ta katse ta ba, sai da Zahra ta gama, ta yi shiru na wasu dakiku, sannan tace,
"Ai duk maza haka suke Zahra"
Zahra ta ɗago kai ta kalleta Jin me tace
Mama ta ci gaba
"Kuma ke ma kin yi laifi, gaba daya nan laifin ki ne Fatima"
"Ni?" Zahra ta tambaya cikin mamaki, bata ma sanda ta furta Ni din ba
"Eh." Mama ta gyada kai.
"Wani ya ce miki ki dinga taba wayar mijinki?"
Zahra tayi shiru tana kallon wani waje sai kuma ta ce
"Amma ai Mama sai daya daina kwana a gida shine na fara taba wayar dan ganin menene"
"Baki da wannan right ɗin" Mama ta katse ta
Zahra ta kasa magana.
Mama ta ɗora
"Da baki shiga wayarsa ba ma da baki ga komai ba."
Wani irin mamaki ne ya rufe Zahra, ta zaci ko da kaɗan ne za ta ji tausayinta, ko ta yi Allah wadai da abin da ɗanta yake yi, sai dai akasin haka ne.
Mama ta ci gaba da kare Khalil
"Khalil bai taso cikin kunci ba, ki yi ƙoƙari kina faranta masa rai sbd Namiji idan baya samun nutsuwa a gida ai zai fita waje ne"
Zahra ta haɗe hannayenta cikin juna tana kallon ikon Allah
Mama ta ɗora
"Shi kaɗai gare ni Fatima, ba zan yarda wata mace ta saka shi gaba ba, Idan kina son zaman lafiya ki bi mijinki"
Daga haka ta miƙe tsaye
"Toh ni zan wuce" Ta faɗa, ba tare da ta jira amsa ba ta fice
Zahra ta bita da kallo har ta fita, sai kuma ta furta a hankali
"Sai dai idan wata matar ce zata bi sa..."
Ta girgiza kai "Amma ba Zahra ba"
Ta miƙe tsaye, kai tsaye sama ta haura, ta ƙarasa tattara sauran kayanta, da ta gama ta sauko ƙasa.
Farida ta fito da sauri
"Anty bari na zuba miki abinci."
Zahra ta so cewa a'a, sai kuma ta taji kamar yunwa take ji, ta gyada kai
Farida ta zubo mata abinci, ta zauna a parlon tana ci a hankali ta ɗauki wayarta, ta kira Ya Umar
Yana shiga bai daɗe ba ya ɗaga
"Hello Baby."
Ya faɗa da fara'a.
Zahra ta ɗan yi murmushi.
"Yaya."
"Uhm Zahrah."
"Barka da aiki."
"Yauwa. Ya jikin?"
"Da sauƙi."
Sai ta ɗan yi shiru.
"Yaya ƙarfe nawa zaka koma gida?"
"Maybe wajen biyu" Ya amsa.
"Me ya faru?"
"A'a." Ta girgiza kai duk da baya ganinta.
"Nima ina zuwa ne, na fitson idan zan tafi kana gidan ne"
Ya Umar ya yi shiru na ɗan lokaci.
Sai yace "Toh can't wait to see you"
Daga haka suka yi sallama, a kashe wayar.
Sai ta buɗe Instagram. Tun da ta yanke hukunci rabuwa, tana son goge duk wani abu da ya haɗata da Khalil a page dinsa
Ta shiga profile ɗinsa, da niyyar fara goge hotunansu, selecting tayi ta goge su tass, ta fita zata shiga chats dinta da shi
Sai dai kafin ta yi wani abu...
Wani post ya faɗo mata a timeline, da farko bata kula ba, sai kuma ta sake kallon hoton
Nan take gabanta ya faɗi, ta matso da wayar kusa da fuskarta
"What...?" Ta furta a hankali.
Sai taga notifications suna ta shigowa, ga uban tags
Da sauri tayi switching to acc dinta, Tana shiga mutane suna ta tagging ɗinta
Da sauri ta shiga post ɗin, zaro Idanu tayi, ta miƙe tsaye ba tare da ta san tayi hakan ba
Cokalin da ke hannunta ya faɗi ƙasa, numfashinta ya fara canzawa, zufa ta fara keto mata
Comments suna ta shiga babu ƙaƙƙautawa, Likes suna ƙaruwa a seconds, shares suna ta karuwa
Ga uban maganar da mutane suke yi, sosai ta hada zufa, mutane suna ta mamaki, wasu suna ta tambaya, abu ne da ya isa hannun dubban mutane cikin ƙanƙanin lokaci.
Zahra ta dafe bakinta, ta kasa ko magana.
Domin abin da take gani a screen ɗin wayarta... bata taɓa tsammanin zai fito duniya ba
"Wai ya akayi...?"Ta furta a hankali.
"Ya akayi wannan ya fito?"
Yatsunta na rawa ta shiga comment section.
Comments kuwa sai shigowa suke yi
"Saudat is evil wallahi."
"How can you do this to your friend?"
"This is betrayal"
"Poor Zahra"
"Na shiga page ɗin Zahra yanzu ma. Ashe friends ne tun secondary school"
"Kai duniya" "Allah ya isa"
Wani ya saka screenshots na hotunan Saudat da Zahra da suke tare a Instagram, mutane suna ta ɗauka suna resharing post, suna nuna yadda suke fita tare,yadda Zahra take kiranta sister, yadda suke comment a posts ɗin juna, abin da ya ƙara dagula mutane kenan
Wasu na zagin Saudat, wasu na tausayin Zahra, wasu kuma na zagin Khalil
"Wife like Zahra kuma ka je ka bi kawarta?"
"Khalil should be ashamed of himself."
"This man is shameless."
"No wonder she looks unhappy these days."
"Men can be wicked."
Kowane refresh da Zahra take yi sai ta ga sabon zagi, sabon comment, sabon repost.
Zahra ta zauna a hankali kan kujera, wayar na hannunta, amma gaba ɗaya jikinta ya mutu
Abu ɗaya kawai yake yawo a ranta, waye ya fitar da wannan? Ta yaya ya samu?
Saboda hotunan da ta gani a wayar Khalil... ba kowa ne zai iya samunsu ba, sai wanda ya shiga wayarsa, wanda ya samu access ɗinsa
Can ta ji ƙarar buɗe gate, amma ko kallon kofar parlon bata yi ba, hankalinta gaba ɗaya yana kan screen ɗin wayarta
Har aka buɗe ƙofar parlorn, bata ɗago kai ba, har aka yi taku zuwa ciki
Sai kawai taji wata tsawar murya.
"KEE!"
A firgice ta ɗago kai
Khalil ne, fuskarsa a hade kamar kunu Idanunsa sun yi ja, numfashinsa ma a bayyane yake saboda tsananin fushi
Tun daga ƙofar parlorn yake nuna ta da yatsa.
"ME KIKE SO KI MAYAR DA RAYUWATA NE?!"
Zahra ta zuba masa ido kawai, Khalil ya ƙaraso gabanta
"Dan uban ki baki ji Ina miki magana bane?" Ya faɗa cikin tsawa.
"Saboda baki samu abin da kike so ba sai kika je kika watsa ni a duniya ko?!"
Zahra ta ci gaba da kallonsa, kamar ma ba ita yake yi wa magana ba
Abin ne ya ƙara ɓata masa rai
"Kin yi hauka ne?!" Ya daka mata tsawa
"Dama plan dinki kenan ba? Ke da wannan ƙawar taki marar tarbiyyar!"
Nan ya fara zaginta itakam tama shiga shock ne
Khalil ya tsaya gabanta yana huci,
"Ke kika yi wannan ba!"Ya sake faɗa.