Chapter 28
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 28
Ya fi mintuna goma yana kallon rubuce rubucen da ke cikin memo ɗin, tare da baje su a faifan tunaninsa, ya shiga nazartarsu daki daki. Sosai rubutun ya ja hankalinsa, sai dai ya kasa tantance salon magana ce ko waƙa ya rubuta, ya san dai koma mene ne an tsara shi cike da baiwa da kwarewa. Abin da ya iya fahimta kawai, labarin soyayyarsa ce ya bayar a takaice, tun daga ranar da ya fara ganin yarinyar har zuwa kan abinda ya faru tsananinsu a safiyar yau, wanda a fahimtarsa shine musabbabin da ya jefa sa a halin da yake ciki yanzu. lumshe idonu AA ya yi, yana jin kamar zuciyarsa na narkewa, labarin soyayyar Suraj da ya karanta ya tasar masa da wani tsohon mikin da ya gaza warkewa tsayin shekaru a zuciyarsa, cakwakiyar da ke cikin tasa soyayyar da Noorie ya fi karfin a rubuta shi a cikin 'yan wasu ƙayyadaddun kalmomi irin wannan. Wani irin tausayin yaron ya ji ya kama shi, duka duka shekarunsa nawa ma wai tukunna? Ya aiyana a ransa, Girgiza kai ya yi “ hmm... soyayya!” ya furta akan laɓɓansa, tare da taune lips ɗin kaɗan, sai kuma ya rufe littafin, ya nemi waje kusa da Suraj da har lokacin bai sake ɗagowa ya kallesa ba ya zauna, ya daura masa littafin a kan cinyarsa, “Surajuddeen!” ya kira sunansa da wani amo na musamman da ya tilasta masa ɗago kansa kaɗan ya kallesa, “Soyayya ce ko?” Ya sake faɗa da sigar tambaya. Gyaɗa masa kai Suraj ya yi, sai kuma ya faɗa jikinsa da sauri ya kwantar da kansa a kafadarsa ya saki kuka, tallafe bayansa AA ya yi yana dariya, “Kai shashasha mene ne haka, be a man mana.” “Let me Ya B, let me cry on your shoulder, kar ka hana ni please.” Shiru AA ya yi, yana jin kukanshi na taɓa masa zuciya, wannan wacce irin yarinya ce haka, da ta sanya masa baby kuka, shi kuwa ko da lu'u lu'u da murjani aka ƙerata sai sun mallaketa, ko zuciyarta ta karfe ce, sai ta so Surajudeen soyayya mara iyaka, ya dauƙi wannan alkawarin. Be hana shi kukan ba kamar yadda ya roƙa har sai da ya yi mai isarsa ya yi shiru, yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya ɗago shi ya zaunar da kyau, “Kalle ni Suraj.” Ya furta a tausahshe. A hankali ya ɗago ya zuba masa manyan idanunsa da suka ƙara rinewa, fuskarsa dauke da danshin hawaye. AA ya girgiza kai a hankali, yana kallonsa da wani irin tausayi da kuma ɗan tsauri a lokaci guda. “Is this how weak you are?” Ya faɗa a ɗan kausashe. Da sauri Suraj ya girgiza kai, alamar A'a, lokaci guda wasu hawayen suka sake ziraro masa, da sauri ya saka hannu ya share. “A haka dama ka ke tunanin ta so ka, kana kuka kamar mace?.” ya sake girgiza kai. Ajiyar zuciya AA ya sauke sai kuma ya tausasa murya kafin ya ci gaba da cewa “Haƙiƙa na ji kunya Surajudeen. Shin ina mazantakarka take? Ya ɗan sahirta yana kallon cikin idanunsa, kafin ya daura “Ka sani kuka ba shine mafita ba, kuka gazawa ce rauni ce a soyayya, kai ba rago ba ne, domin ba ka fito daga tsatson ragwaye ba, ka je ka bincika tarihin soyayyar Mother da mahaifinka as an assignment.” Ya ɗora hannunsa a kafaɗarsa, ya ɗan bubbuga “Idan har kana sonta da gaske. to ka tsaya tsayin daka. Ka jajurce. Ka yi yaƙi tuƙuru, ka mallaki abinda ka ke so da karfi da jarumtarka.” Ya ɗauke hannunsa a kafaɗansa, ya kama haɓarsa ya ɗan ɗago kaɗan. “Kar ka sake bari hawaye su zama makamin ka. Ka mai da zuciyarka ta ƙarfe, ta yadda za ta iya jure duk wani gwagwarmaya, ba tare da ta tarwatse ba, ina so ka min alƙawarin ba za ka sare ba, ba za ka janye ba, babu gudu babu ja da baya har sai ka yi nasara, ina tare da kai zan tallafeka, ba zan taɓa bari ka faɗi ba.”
Kallonsa kawai Suraj ke yi, yayinda zuciyarsa ke wani irin buɗawa, duk wata kalmar da yake faɗa tana shiga kasan zuciyarsa kai tsaye tana tasiri, tare da samun Kyakkyawar matsuguni. Take duk wani tsoro da raunin da suka soma tasiri a kansa suka juye zuwa jarumta, hawayen da ke gudana a idanunsa suka ƙafe. Murmushi AA ya saki, saboda fahimtar da ya yi wutar da ya kunna ta soma ruruwa. “Ka nuna mata kai ba ƙaramin yaro ba ne, daga ranar irinta ta yau, ina son ka yi min alƙawarin ba za ka sake zubar da hawaye akan ta ba, ba za ka sake kuka kamar mace ba, kada ka sake nunawa kowa rauninka akanta.” Lumshe idanu Suraj ya yi a hankali ya buɗe akan fuskar yayan nasa, kafin ya gyaɗa masa kai, ya kara da faɗin, “I promise Ya B, Amma ina neman alfarma, ka bani dama duk lokacin da na ji ina buƙatar yin kuka zan zo in da kake zan yi a gabanka.” murmushinsa ne ya faɗaɗa ba tare da ya shirya ba, ya shafa kumatunsa, ya ce “ Na baka wannan damar ƙanina, ina maraba da kai a kowanne lokaci, ina yi maka fatan nasara.” Ta shi ya yi ya rungumesa, “Thank you, Ya B, I really love you.” “ I love you too, kanina Romeo baban soyayya, Oh ya Rab! Wai har baby Surajudeen ya girma har ma ya balaga, ya fara neman aure.” Da sauri ya sake shi ya yi baya, sai kuma ya kwashe da dariya tare da rufe fuska da tafukansa irin ya ji kunya. Shima ɗan murmushi ya yi.
“Wace ce, surukar tawa?”
“Sunanta Salmah Mu'az, yar uwar tagwaitakar abokina Salman.”
“Wonderful! kana nufin Salman dai da na sani.”
“E shi, Yayarsa ce, ita ce Hassana shi Hussaininta.”
“Kai kai kai ka ce yayarku ce,da gaske fa ka yi mata yaro Surajo magana ta domin Allah.” Ya yi maganar cike da zolaya. Dariya Suraj ya yi, a zuciyarsa ya ce, “Sai kun aura min ita za ku samu tabbacin wannan amsar ba yanzu ba.” A fili kuwa cewa ya yi, “Ba komai na ji, na amince, zan bata girmanta zan yi mata biyayya, in bita sau da kafa, ko kara ta ajiye ba zan tsallake in Sha Allah.” Sosai zancensa ya bawa AA dariya, ai kuwa suka hau darawa a tare kamar ba babu mai wata damuwa a cikinsu.
Dai dai wannan time ɗin Mother ta turo kofar dakin ta shigo. Tana can zaune a falo in da AA ya barota cikin alhini da tsumayen sakkowansa ta ji abinda ke faruwa, sai dai shiru kamar malam ya ci shirwa ba shi ba dalilinsa tun tana irga mintuns tana kallon agogo har ta sare, ganin wankin hula na neman kai ta dare yasa ta mike ta biyo bayansa, sai dai me? Tun da ta sharo kwanar dakin take jin dariyarsu na tashi, hakan yasa ta kara da gudu har tana tuntuɓe.
Ja ta yi ta tsaya a bakin kofa tana binsu da kallo baki sake. Hakan ya karawa dariyar tasu power sai ta hau tafa hannu tana sallallami, “Allah Ubangiji ya shirya min ku.” ta furta kafin ta girgiza kai ta fice, tana hamdala a zuciyarsa, lokaci guda kuma duk wani nauyin da zuciyarta ya yi a dazu ya shiga yayewa kaɗan kaɗan....
******
A can asibiti kuwa, wunin ranar ya zamto na musamman a gare su, saboda kasancewar Ya Anas a tare da su. Yanayi ne da suka jima suna kewa. A kallo ɗaya idan ka yi wa fuskokinsu za ka shaida haka, ba ga Ammie ba, ga ba 'ya'yan nata ba, hatta Aysha da ke halin jinya, jin yau ɗin take na dabam, duk da tarin fargabar da ganin nasa ya haifar mata.
Hakan ya yi tasiri matuƙa wajen rage mata nauyin damuwar da ya haifar mata da jinya.
Da takura da lallashi cikin salonsa na barkwanci ta samu ta ci abincin da Salmah ta kawo, wanda rabonta da shi har ta manta.
Cikin Hukuncin Ubangiji kafin yamma sai gata a zaune tana hira harda dariya.
Sosai Ammie ta ji daɗin hakan, musamman da ta gama fahimtar sauyin na tattare da wanzuwar Anas ne, wanda tun daga irin kallon da taga yana yi wa Ayshar, ta tsinci kanta cikin wani irin farin ciki da annashuwa irin wanda ta dade ba ta yi ba, amma sai ta dake ta yi kamar bata gane abinda ke faruwa ba, saɓanin Salman da baya iya gani ya kyale sai da ya tofa. Sai da ya bari Ammie ta ɗan fita, ya kallesu a lokacin Anas na zaune a gafenta rike da plate ɗin abincin da yasa Salmah ta zuba mata, yana rarrashinta akan ta daure ta kara koda cokali biyu ne.
“Ya Anas…” Ya kira sunansa yana sakin murmushin tsokana.
“Salmanu...” Ya amsa ba tare da ya juyo ya kallesa ba.
“Hope ba wata special treatment ake yi a nan ba? Because this level of care, it feels like something more.” Ya ƙarasa yana ɗan dariya.
Muƙut! Aysha ta hadiye abincin dake bakinta ba tare da ta shirya ba. Shi ko Anas kyakkyawar murmushi ya saki, ya kashewa ƙanin nasa ido tare da daga mai gira.
“Oshey!! Looks like we are having a good time a nan, ko?” Ya faɗa cike da tsantsar farin ciki.
Duk yadda gabatanta ke faduwa dakewa ta yi, cike da borin kunya ta watsa masa harara, “Kai dai wallahi ka cika surutu Allah, Ya Anas ɗin mu ne fa, ko ka manta ne.”
“Ina kuwa zan manta, ai na gane shi.” Ya amsa mata cikin gatse yana dariya, Ammar da Salmah na taya shi, sai dai ita nata dariyar na yake ne da tashin hankali.
Cikin dariya Ammar ya ce “Kash! Kai kuwa Salman ya lamarinka da haka, lamari na Ya da Ƙanwa, ai ya fi gaban wasa.”
“Ai na fahimta Ya Ammar na janye.” Ya kare da dage hannu alamar surrender.
Zamewa Aysha ta yi ta kwanta, tare da rintse ido duk kunya ta cikata, godiyarta daya Ammie bata ɗakin.
Ci gaba suka ka yi da jan zancen shi da Ammar, Shi dai Anas bai tofa ba illah murmushi da yake binsu da shi, shi kaɗai yasan yanayin da zuciyarsa ke ciki.
Shigowar Ammie tare da Dr Lukman ne ya katse musu yanayin. Sun gaisa da Dr cike da girmamawa kasancewarsa abokin aikin Ammie, ya bukaci da su ba shi guri ya duba mara lafiya.
“Ai Ammie bari na tafi gaba daya kawai, yamma ta riga ta yi gashi har karfe biyar ake nema.” Ammar ne ya yi maganar yana kallon agogon hannunsa bayan ya miƙe.
“Toh Ammar, a sauka lafiya, mun gode sosai Allah ya yi albarka, ka gaida Turan.” Sai kuma ta kalli Anas da shima ya riga ya miƙe, don cika umarnin Dr “Ka bishi ya sauke ka, a gida ka huta ɗan fice gajiyar hanya mana.” Dan yamutsa fuska ya yi, kafin ya amsa da “To Ammie.” ya yi maganar idanu da dukkan hankalinsa na kan Aysha, yana kokarin haɗa ido da ita, ta ƙi basa damar hakan. Shi kansa yasan hana bukatar hutun, to amma buƙatar zuciyarsa ta rinjayi ta gangar jikin.
“Yawwa Yaya mu je, na tayaka hutawa.” cewar Salman, Caraf Salmah ta cafke, “ Ka hana shi hutawa dai.” Wani banzan kallo ya wullo mata, ya yi gwafa tare da shigewa zai fice.
“Ya haka Salman? Daga fadar gaskiya.” Ammar da bai san yadda su ke ba ya yi maganar.
“Rabu da ita Ya Ammar, ba ka san abinda yarinyar nan ta aikata ba ne yau, wallahi ba ƙaramin haushinta na ke ji ba, kuma in sha Allah, you will pay for it.”
Tsaki ta ja, ita sai a lokacinma, take tunawa da abinda ya faru tsabar bata saka shi akai ba.
“Tsaki ko? Ki ci gaba dai.”
“Zo nan Salman, me ya faru?” Ammar da hankalinsa ya fara tashi da sa'insar tasu tun da ba wai ya saba gani ba ne, ya faɗa tare da rike hannunsa ya jasa suka fice daga ɗakin.
“Oummu Salamaaah!” Anas ya kira sunan Salmah yana binta da wani irin kallo, wanda ita kaɗai ta san ma'anarsa.
Dariya ta saka, “Wallahi Yaya ban yi masa komai ba kawai bala'i yake ji da ji kai ma kasan halinsa, ka tambayi Aysha ka ji Allah bana faɗa da shi yanzu na daina.” Girgiza kai kawai ya yi ya kalli Ammie, “Sai na dawo zuwa dare in sha Allah.” “Okey Allah ya tsare.” Idanun Ammie da ke kansa ya hanasa sake juyawa ya kalli Aysha, duk da umarnin da zuciyarsa ke ba shi kenan, haka ya dake ya sa kai ya fice.
A bakin mota ya samu Salman da Ammar, suna magana, yanayin Ammar ya canja lokaci gudu, kuma hakan ya faru ne sanadin labarin Suraj da Salman ya ke basa a takaice, zuwa kan abinda ta aikata yau ɗin.
Dr Lukman ya ji daɗin ganin yadda jikin Aysha ya yi kyau sosai sabanin yadda ya barta da safe. “Alhmdlh 'yar gidan Ammie jiki ya yi kyau.” Ta yi murmushi kawai. “ To Masha Allah, zuwa gobe zan duba idan da yiwuwar ki je gida, in sha Allah.” Ta gyaɗa kai. Ammie ya yi wa bayanin ci gaban da aka samu, kafin ya yi musu sallama.
Da dare tare suka dawo asibitin su uku, harda Abie, wanda ya fara biyawa ta gida ya yi wanka saboda gajiyar hanyar da ya kwaso, sannan kuma don ya yi tozali da ɗan nasa, da yake matukar kewa, wanda tunda rana da ya samu labarin zuwansa, a bakin Salman bai sake sukuni ba. Tare su ka yi sallar magriba da isha da samarin nasa kafin su wuto asibitin. Ya ji daɗin ganin yadda jikin Aysha ya yi kyau, murnarsa ta kasa ɓoyuwa ya yi ta mata sannu harda yar zolaya, a kunyace ta yi ƙasa da kai, tana yar dariya, haka kurum ta sinci kanta da kasa sakewa da shi kamar kullum, musamman da ta daga kai idanunta suka sauka a cikin na Anas.
Ya kula da sauyin amma bai kawo komai a ransa ba, face yanayi irinta masara lafiya rashin son magana, balle ga Aysha da bata da hayaniya.
Wai wajen goma da rabi suka yi niyyar barin asibitin gaba dayansu harda Salmah.
Ammie ta yi musu rakiya har wajen mota, sai da ta bari sun shige sun zazzauna, sannan ta nemi ganin Abie, daga ɗan nisa da motar suka tsaya in da take da tabbacin yaran ba za su jiyo su ba.
“Ya aka yi ne My Dr?”
Murmushin ta yi, ta ce, “Wani abu ke tsungulin zuciyata na ke son na raba shi da kai.”
“Umhh really! To ina jin ki Allah yasa ba wanda zai hana ni barcin daren yau ba ne.”
Ƴar dariyar da ya kara bayyana yanayin farin cikin da take ciki ta saki, kafin ta shiga bashi labarin abinda take hasashe tsakanin Aysha da Anas.
Kallonta kawai Abie yake yi yana sakin murmushi tare da murza saisayayyen gemunsa mara tsayi, mai dauke da farin gashi da tsilli tsillin baƙi.
“Ba ka ce komai ba fa.”
“Ai bakin ne ya mutu murus Dr. Na dade ina tunanin mijin da zan kai wa Aysha wanda ba zai wulakanta min ita ba, kullum ina cikin fargabar rashin amincewar Anas game da zaɓin da na yi masa, Allah ya sani ina jin tausayin yarinyar nan sosai Dr.”
“Mu yi wa Allah godiya Brr. Allah ya tabbatar mana da dukkan alkharin da ke cikin wannan al'amari.”
Lumshe ido ya yi a hankali ya bude alamar amsawa. Kusan mintuna goma suka kwashe suna ci gaba da tattaunawa game da wani muhimmin abu wanda ya kasance sirri a tsakanin su. Kafin daga bisani su ka yi sallama, ya tafi zuciyarsa fari tas tas.....
Saura 2 Pages mu kammala book 1, bisa ga rokon da ku ka yi akan a kara 5 pages, kafin mu kammala ga duk wacce ta shirya biya, ta saka 800₦ a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya, a turo min shaidar biya ta nan ***.