NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 44 ( What could it be?)

by @deejasmah

Last chapter 

Kamar wasa fa wai k'aramar magana ta fara zama babba,don fushin da Islaam ya ce yana yi da Lelen da gaske yake yi don a yanzu ya fara sassautawa Fareesah duk da dai ba kamar yanda yake mata a baya ba. 


Lelen ce dai ya d'inkewa bai shiga shirginta d'akin na shi ma da take gyarawa ya daina barin mata shi a bud'e balle ta shiga ciki, duk ya gama sauyawa ya koma Islaam d'in shi da sani na farkon aurensu mara wasa da sakin fuska.

Har yanzu dai yana kwana a d'akin musamman ranar girkinta don bai kwashe k'afafunshi gabad'aya daga part d'in ba duk a k'ok'arinshi na kar ya bawa Fareesah wani dama da zata san me yake faruwa tsakaninsu da Lele wanda a banza yake yi don a yanzu ta fara suspecting ba lafiya ba don duk wani soyayye-soyayye da k'auna da suke damunta da shi yanzu babu ko shi mai isar da matana kaza matata that bai mata sai bak'in izzarshi da ba abinda ya ragu sai ma wanda ya k'aru hakan ne ma yake hanata focusing kan gulmar duk kuwa yanda take son bin diddigi ta kasa hakan ya sa ta hak'ura har take ma ganin ko cikin ne ya saka haka.


A hankali rayuwa yake tafiya cikin nata yana k'ara kwanaki tana k'ara samun sauyuka masu yawa, yanzu haka dai ta daina jin abinda take ji a kanshi sai ma wani masifaffen kewa da sha'awarshi ce take kamata tun tana jurewa har ta gaza ta fara neman hanyar da zasu shirya da juna sai dai aikin banza ne don izuwa yanzu yayi nisan da bai jin kira a kan matsalarshi da ita.



Tsaye tayi a bakin k'ofar part d'in shi tana knocking amma tsit ba a amsa ba balle tayi tunanin ko zai bud'e mata, tsaki tayi a karo na barkatai tana dafe kan ta ina ma tana da dama da ta hak'ura da ganin na shi amma ba zata iya ba. 

Mugun son ganin shi take yi kamar ta bi hanya, ta sanar da duk duniya halin da take ciki. Ta san yana a cikin d'akin don ta jiyo motsin shigar shi ita ce kuma da girki balle ta ce yana wurin Fareesah, hanya d'aya ta rage mata wato ta bi ta main k'ofar shi ta garage don tana da yak'inin samunta a bud'e in ma kuma tayi knocking ba lallai ya k'i bud'e mata ba.


Ajiyar zuciya ta sauke tana mai matsawa daga bak'in k'ofar don bin umarnin zuciyarta wurin aikata abinda ta saka ta, duban kanta tayi tsaf da ita cikin doguwar riga kalar purple wacce ta lafe a cikinta ta baiwa d'an madaidaicin cikinta da ya tasa don a yanzu yana cikin wata biyar zuwa na shida haka damar fitowa sai hula fara tas da ya tamke kanta da gashinta da ya sha gyara ya kwanta luf har ana iya ganin shi ta gaban hulan haka za ya kwanta a wuyanta har bayanta.

Komawa d'aki tayi ta d'auko gyalen rigar tana mai k'ara turare, wayarta ta d'auka da key ta fita datse kofar tayi da kyau kana ta nufi k'ofar d'akinshi.

Knocking tayi ba a bata izinin shigowa ba bata yi k'asa a guiwa ba ta kuma knocking, shi ma dai ba a bud'e ba ba kuma ayi magana ba har ta juya zata koma inda ta fito aka bud'e k'ofar waigowa tayi nan tayi arba a abun mamaki.

Fareesah ce taye sanye da bubun da take yawan sakawa kalar ash da d'an cream, tsaye ta yi cak ta kasa motsawa ko nan da can. Murmushin kissa Fareesahn tayi tana cewa " Mommy princess, yanzu kika shigo gidan halan".

Saita fuskarta tayi tana cewa " nope, dama ina ciki yana nan kuwa?".

"Sure, ki shigo please".

"Nope, dama na ji motsi ne a ciki na zaci ko bai dawo ba ne shi ne na zo dubawa" ta fad'i tana mai juyawa gabaɗaya don ba zata iya shiga d'akin Fareesah na ciki ba, ya ma zata shiga bayan ba shiri suke yi ba haka nan tana shiga ya kunyatata a gabanta ta fad'i babu nauyi. Haka za ma tana mai jin haushin shigarta d'akin ba kuma wai saboda ba ta kai ta shiga ba sai dan abu guda d'aya, kowa tana da d'akinshi a part d'inta so bata ga dalilin da zata zo d'akinshi dake part d'in ta ba sai in shi ya buk'aci ganinta.

A take zuciyarta ta kwab'eta da cewa " kika sani ko shi ya buk'aci ganin nata?" Ba ta kai ga ba da amsa ba ta jiyo muryar Islaam yana cewa " cherrie ke da waye?".

"Mom princess ce" ta ba shi amsa duk bata ko kalle su ba duk da tana jiyo kaifin maganan shi a kanta, sauri ma take yi bata ko jira ko reply d'in shi ba tana mai ganin duhu yana mamaye mata idanu kenan duk knocking d'in da take yi daga nan parlornta suna ji shi da Fareesah. Kenan a gabanta ya wulak'antata ya nuna mata bai son ganinta da k'yar ta iya bud'e k'ofar waiting room ba ta ko ganin gabanta ba ta ko iya zare keyn ba ta fad'a kan sofar dake parlorn tana sanya kuka.


Duban shi tayi bayan wucewarta tana cewa " ina ga magana take son ku yi".

"Hmm, sai ki tafi tunda kin gama next time in kina son magana da ni ba sai kin zo ba just call me".

"I did called you ba kayi picking ba shiyasa na zo".

Alright ya amsa yana bata hanya kayan takaddunta da ta shigo da su ta kwashe dama maganar project ya shigo da ita, so sun gama har ma ya nuna mata yanda za ta yi godiya ta masa tana fita murmushi ta saki a ranta tana ayyana " da alamu suna fad'a ne, naji daɗin da samuna da ta yi itama ta ji in da dad'i" ta k'arashe tana sakin k'aramar dariya.

Shi ko tana fita ya runtse idanu yana mai jin wani kala, duk yanda ya kai ga jin dad'in ganinta amma bai ji ɗoki kamar yanda yake ji a baya saboda ganinta ya tuna masa da kalar mugun gashin da take yi masa. Bud'e idanun yayi yana mai jin kamar ya bi ta but wani abu yana hana shi kai infact ko ganinta ma ba ya son yi, dafe kan shi yayi yana komawa ya zauna yana cije lips bai san abinda yake damunshi ba amma ya tabbatar ko miye ba abu ne mai kyau ba.


Kukanta tayi ma'ishi na tsantsar kishi da jin zafin k'in biyota da bai yi ba, yayinda zuciyarta babu kalar abinda bai raya ma ta ba. Gani take yi kamar shi ya kirata don ya nuna mata ya daina yayinta, ko dan ya wulak'antata wata kuma tana gaya mata daman ai ba sonta yake yi ba sha'warta ce yake yi.

Kuma ya da'de da maida miyan kwad'ayinshi a kan kanta, tunda har d'iya sun haifa ta ma godewa Allah ta kai wannan lokacin. Hannu ta kai tana share hawayen idanunta sannan ta tattara jikinta ta mik'e sai lokacin ta zaro keyn ta ta datse k'ofar da kyau ta wuce ciki, wuri ta k'ara samu ta cure tana mai jin babu dad'i a ranta amma kaso mafi yawa na zuciyarta tana tsumayar zuwan Islaam gareta ko kuma kiran na shi sai dai har zuwa kiran magriba babu shi babu alamunshi wanda a lokacin ma har zazzab'i ya fara kamata da k'yar ma ta iya ta shi tayi sallah yau ko abincin ma ba ta dafa ba da yunwan ta sark'afeta tea ta had'a ta sha ta sake kwanciya.

Haka washegari ta tashi duk ranta, zuciya da gangar jikinta babu lafiya, kasa fita koina tayi tana kwance sai da rana ta fito sosai kafin ta mik'e ta yi wanka madara ta d'umama ta sha da wasu magunguna kafin ta iya d'an gyaran gidan ta yi girki ta ci ta koma ta kwanta.

Ta idar da sallahr Asr tana kan dadduma kiran Zulfaa ya shigo wayarta, d'agawa tayi a kasalce tace "hello".

"Kina ina haka?" Zulfaa ta tambaya daga can gefen, tura baki tayi tana cewa " home".

"Au ba ma ki san me ake yi ba kenan?".

"Whaa?" Ta tambaya tana gyara zama.

"Gamu a clinic da Suleim tana labor".

Ji tayi d'an damuwarta ta kau da sauri tace " haba don Allah? Wani clinic?".

"BAY mana".

"Barin fito yanzu Allah sarki sweetheart".


"Oya naa, sai kin zo" ta k'arashe tana kashe wayar gabad'aya, da sauri ta mik'e hijabin ta cire kasancewar k'ananun kaya ne a jikinta ya sa ta nufi wardrobe doguwar rigar material mai d'an kauri khaki green ta ciro inner wears ta fara sanyawa kana ta zura rigar a jikinta. Mint green jersey veil ta yane kanta da shi bata ko d'auki bag ba keys kawai ta d'auka da wayoyinta ta zura crocs mai taushi na Nike bak'i ta fita rufe d'akinta tayi ta shiga mota.

Message ta turawa Islaam akan za ta asibiti wurin Suleim kafin ta ja motar ta bar gidan, a dai-dai kwanar unguwarsu ta k'arshe suka had'u da Fareesah ta dawo hannu kawai ta d'aga mata kana ta ja motarta tayi gaba.


A dai-dai parking lot ta had'u da Adnan yana k'ok'arin shiga mota da alamu zai tafi gida ne, ganinta ya sanya shi fasa shiga motar yana washe baki. Gyara parking tayi ta fito itama tana sausauta fuskarta, "Abban Shukra".

Murmushinshi ya fad'ad'a yana cewa " da kuma unborn ba".

"Ba dai ta kusa sauka ba?".

"Mun kusa dai samu don ma baku son zumunci ke da mutumin nawa".

"Haba dai Abban Shukra sau nawa ma na je gidan ba ka nan, ya aikin?".

"Aiki Alhamdulillah, ya jiki-jiki ya kuma abokina?".

"Duka Alhamdulillah".

"Har da abokin nawa?" Ya tambaya with much concern, ajiyar zuciya ta sauke bai kamata ta tona cikinta da wuri har haka ba. Duk da ta san yafi kowa sanin halinda suke ciki tun da can balle kuma a yanzu, ganin yanda tayi shiru ya d'an sa ya saki fuskar yana cewa " da matsala ne?".

"A'a, babu wata matsala".


''Uhmm, ban san inyi katsalandan a tsakaninku but ina son please ki gaya min abinda Islaam ya miki da kika zab'i azabtar da shi da rashin kulawarki. Duk ya bi ya susuce kamar ba shi ba, duk kuma saboda ke".

Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa " na gaya masa babu abinda yayi min bai kuma ba ni damar da zan masa bayanin abinda yake damun nawa ba".

"Ko zaki iya gaya min? Kar ki ɗauke ni a abokin shi, ki d'aukeni kamar yayanki just tell me".

"Pregnancy hormones ne, na kuma zaci shi yafi cancanta da ya gane hakan amma ya k'i fahimtata ko kad'an. Ni kuma ban san yanda zan masa bayani ba".

"Nima na gayan masa hakan, yace ya fi bada dai laifi ya miki kika zab'i gasa shi ta wannan hanyar. Bari in gaya miki abinda baki sani ba Nadeefah Burhaan yana son ki ko da shi bai gane hakan ba wallahi yana matuk'ar sonki don a tsayin shekarun da na san shi ban tab'a ganin ya damu da wata kamar yanda ya damu da ke ba har wainda ya tab'a ik'irarin yana so kuwa, ki sauko ki saurarashi ki masa bayanin komai please duk ya bi ya koma kamar wani zararre akan yanda kike masa".

Shiru ta yi ta kasa ko da motsi yayinda mamakin maganganunshi yake nuk'urk'usanta yana kuma dad'a narkar da k'arfin halin da ta aro ta yafa a hanyarta na zuwa asibitin.

Gyaran murya ya kuma mata da sauri ta dubeshi cikeda mamaki tace " ni fa Abban Shukra sai nake ganin kamar hasashe ne kawai, Yaa Islaam bai taɓa so na ba....."


"Ki bar ganin haka Nadeefah, wallahi yana sonki so mai tsanani kuwa ke ce kuma ya kamata ki gane haka kafin kowa".

"Amma in da yana so na mai yasa ya kasa fahimtar yanayi na, meyasa ya kasa min uzuri har ya gina k'atuwar katangar k'arfe a tsakanina da shi yanzu fa ko wayata bai d'agawa bai cin abincina bai ko zuwa inda nake shin wannan duk cikin so ne? Kai i doubt". Ta k'arashe da bayyanannen d'aci a kan harshenta, shiru yayi yana mai son fassara kalamanta in dai ya canka dai-dai tana nufin duk bayan maganarsa da shi ne ya fara aikata hakan? To meyasa in suka had'u yake kuma nuna masa zafin rashinta da yake fama da shi in har ya san shi ma da sa hannun shi ga hakan? Kai akwai wani abun don Burhaan ba zai tab'a yin haka ba.

Da sauri ya dubeta yana cewa "ƙila misunderstanding ne".

"Maganar yana sona ko? Ni ma haka nake gani ".

"Ba wannan ba, na katangar da kike maganar ya saka a tsakaninku but zan masa magana in shaa Allah".

"Ba komai fa".

"Da komai Nadeefah ki yi hak'uri please".

"Nagode sosai".

"Ba komai, ba ri in barki kin shiga ciki".

"Aha ka gaida Aunty Salmah".

"Zasu ji" ya amsa yana shigewa motarshi cikeda tausayinta, itama wucewa ciki tayi can hanyar labour room.

A dogon parlorn wurin ta tarda su tsaye, kusan duka matan familyn sun zo maza ko daga ElSadeeq sai Farhaan da yake gefenshi yana d'an kwantar masa da hankali, gaishe su ta yi sama-sama ta d'auki Little yarinyar Zulfaa ta samu wuri ta zauna daga d'an nesa da su.


Zamanta bai fi da 5 minutes ba Islaam ya zo wajen, gefen su Farhaan ya zauna shi ma cikin nuna damuwa duk da bai yi magana ba kamar yanda Farhaan yake yi. Amma shi ma dai ya d'an damun don ta d'an samu zuban jini ne kafin haihuwar hakan ne ya sa akai rushing d'inta zuwa hospital d'in.


Duba d'aya yayi wa gefen da Lele take ya d'auke kai, itama ba ta ko kalle shi ba banda kallon farkon ta cigaba da salati a ranta tana jiran tsammani. Cikin ikon Allah gab da magrib Allah ya sauki Suleim lafiya bayan ta ci kwakwa ba k'arama ba babba sosai, itama mace ta haifa kamar Zulfaa. Kimtsa yarinyar aka yi aka fito musu da ita nan fa wuri ya d'inke da hayaniyar su ta gado kai ka ce ba su suka yi kasak'e d'azu kamar wainda akai wa rasuwa ba, musamman da Elsadeeq ya rungume yarinyar ya k'i sakinta sai da su Najwaah suka rufe shi da tsokana kafin ya ba su suka d'auka shi da su Islaam suka wuce masjid.


Sai lokacin ne suka samu sharafin d'aukar yarinyar, kyakkyawa ce sosai mai tsananin kama da su Nadeefah. Don yanda ka san Lelen ce ma ta haifeta tsabar kamanninsu har ta fi Sairah yin kama da ita don ita Princess akwai kamannin Islaam a fuskarta amma wannan yarinyar sak su Lele, babu abinda ta d'auko na Mamanta ko kad'an gwara ma shi ElSadeeq d'in tunda yana d'ibar kama da Lelen.

Mommy Hafsat ce ta saka gud'a tana cewa " wannan yarinyar yanda ka san Ummunku ta haifeta, ba ta bar komai nata ba".

Ammi tace " wallahi, nima haka na gani kamar fa yanda aka haifi Nadeefah''.

Murmushi Umma ta saki tana cewa " sosai kam, kamar ma har ta b'aci ko fa Sairah ba tayi kama da ita haka ba".

Ita dai Lele sai sake washe baki ta ke yi jin maganar da ake yi, a take kuma so da k'aunar yarinyar ya sake rufeta kamar yanda take jin Sairah a ranta. Sai da kowa ya d'add'auka sannan aka bawa Zulfaa inda ita ma ta juya kan Lele cikeda tsokana tace " ke dai kin cika had'ama matar nan ba ki k'yale su Sairah ba kin fara bi har dangi".

Gwalo tayi mata tana cewa " ai so nake mu k'ara yawa a dangi, ko ita ma little ai da ni ta so yin kama Yaa Farhaan ne ya b'atata".

Dariya maganar ya bawa kowa har ita da tayi ai ko suka d'inga k'yalk'yatawa sai da suka natsa kafin Mommy Hafsat tace " ai gwara da ya b'ata tan, gashi nan ta k'ara kyau".

Ita ko Zulfaa duban gefen da Mommy take tayi ganin kamar hankalinta ba ya wurin don waya take yi da Ummu suna wa juna barka. Yasa tace '' idan baki yi ba ai sai an tambayeki,ban san meyasa bakinki yake son kiran Farhaan ba kam".

"Shi ne kad'ai abokin wasa na" ta amsa tana murgud'a baki zata d'auki babyn hanata Zulfaa tayi tana mai cewa " ko allon nasarar ki ba, baki ga in kika kira sunan har wani natsuwa kike yi ba".

"Allah ya kyauta, wannan ai sai dai ke" ta k'arashe tana mai sake kai hannu don d'aukar yarinyar, k'asa da murya tace " sai ni kuwa, shi ne nasarata in gaya miki" ta amsa a hankali ba su san Mommy Hafsat da ke gefensu da Ainah sun ji ba sai Mommyn ce tace "ai mun sani rasai''.

Da sauri ta rufe ido Lele ta yi caraf tace " ai in gaya miki Mommy Zulfaa ta dad'e da bin hanya".

Harararta tayi tana cewa " ai duk layinku guda, in kika samu dama babu abinda ba ki fad'i kan Islaam toh me muka ce?".

"Don ma ba kiga yanda take ta wani narke fuska ba da yake zaune shikuma sai wani kallonta yake a kaikaice" Ainah ta fad'i cikeda tsegumi, salati suka sanya a tare Aunty Fareedah tace " ke kam Ainah kina yanayi har yaushe aka yi hakan?".

Dariya su ka sake fecewa da shi Ainah kam ko a jikinta tace" gata nan ta musa mu ji".

Narke idanu tayi tace " ai ni kam Aunty Ainah kin fi k'arfina" ta k'arashe tana mik'ewa don shiga can room d'in da aka shaida musu an maida Suleim d'in, su ma duk sauran duk mik'ewa suka yi.

Ko da suka shiga Suleim d'in barci take yi don haka kwantar da babyn suka yi suka fara gabatar da farali.

Ba ita ta farka ba sai bayan isha'i a lokacin kam d'akin ya cika ya batse da 'yan barka duk sannu da jiki suka mata kafin aka bata wuri suka nufi toilet ita da Mommy Hafsat ta tayata ta kimtsa jiki tayi wanka suka fito. 

Dr. Ce ta sake zuwa ta duddubata da ta tabbatar da komai normal suka bata sallama around 9 pm direct gidanta suka nufa da ita har da tsohuwar da aka nemo ma ta saboda tayata zama, ko da suka shiga gidan babu wanda ya zauna sallama aka yi mata aka barta domin ta samu ta huta.

Haihuwar Suleim shi ya kawar mata da damuwar Islaam gabad'aya, kamar yanda ya bata space haka itama ta bashi fili mai girma ko don kwanciyar hankalinta gudun matsala gareta da abinda zata haifa. Ba wai kuma don bai damunta ba sai don damun nata bai da wani fa'ida sai ma matsala gareta.

Kamar kuma yanda Adnan yace zai masa magana yayi masan sai dai bai bari ma maganar ta shige shi ba gani yake kamar wani salon ne take son tsirowa da shi, shiru yayi masa da ya gaji da maganar shi ma shiru yayi yana cewa " ya na ji kayi min shiru? Kamar ba ka fahimci me nake nufi ba?".

"Dama ya za'a yi in fahimci me kake nufi? Ehn bayan ni ban ma san inda ka dosa ba gabad'aya".

"Bam gane ba ka san inda na dosa ba? Maganar Nadeefah fa nake maka kana son maida ni kamar wani d'an iska".

"Ni dai ake shirin maidawa haka Adnan, in dai kamar abinda ka fad'i ne meyasa a randa na tambayeta ba zata iya fad'a min ba? Da bakinta fa tace min tana jin ƙyama ta bata son in zo inda take ba ta son ganina haba Buddy kayi lissafi mana".


"Tabbas ba ta kyauta ba, ayi mata hak'uri toh please" ya furta don ya san kafiya da dagiyar Islaam . Hmm shi ma ya amsa da shi yana maida hankalinshi ga system d'in gabanshi alamun ya gama maganar, tsaki yayi cike da jin haushin halin na shi ya fita ya bar masa ofishin shi ko raka shi yayi da idanu yana jin ina ma zai iya yarda da zancen Adnan d'in? Amma ba zai iya ba tunda da kanta ta fad'i masa abinda take ji a kanshi wanda yake akasin abinda ta faɗawa Adnan, shi kuma maganar da ka fara fad'a masa da shi yake amfani kuma bai son 'kumbiya-k'umbiya kuma shi ya ƙara lalata komai in da ta fad'in masa ainihin abinda take ji ko sau d'aya ne da yanzu ba wannan zancen ake yi ba.

Bayan haka ma bai san dalilin da ya sa ba zata iya gaya masa me yake damunta ba sai Adnan, ko shi take aure ne ohon mata.

Haka dai yayi ta lissafin dake sake daguwa kwanciyar hankalinshi, da k'yar ya samu ya yakice tunanin yana sake k'arfafawa kan shi guiwan cewa sai ta zo tana kuka tana fad'in maganar da bakinta kafin ya hak'ura.

Don shi ma fa yayi iya k'ok'arin da zai iya a kansu amma ta nuna bata san wannan batu ba, babu kalan ban hak'urin da bai mata ba duk a tunanin ko ya mata laifi ne but tayi masa banza shi akwai ma macen da ta isa ya mata abinda yayi wa Lele? Shi fa da mace ta nuna masa ta gaji da shi zai fita hanyarta fita kuma ta har abada Nadeefahn ce dai bai iyawa shiyasa har yanzu yake da yak'inin zai iya saukowa su daidaita amma sai ta kuma ji a jikinta. Kashe system d'in yayi ya tattara kayakin shi ya rufe office d'in zuwa gida, ba kuma gidan ya wuce kai tsaye ba sai da ya fara tsayawa a sahadstores yayi musu cefanen duk abinda suka k'are ko suka yi k'asa har da turawa Lele kud'i masu yawa izuwa account d'in ta da note"kuɗin cefane".


San da ya koma gidan ba ta nan sai kawai ya ajiye mata, komai a cikin kitchen kana ya koma waje ya shigar wa da Fareeesah da nata kayan itama.


Tana zaune cikin su Zulfaa a tsakiyar gadon Suleim tana maida bayani message d'in ya shigo, bata duba ko na menene ba ta cigaba da zancenta bakin nan fil-fil. Duka yau kwanan Suleim uku da haihuwa, Ainah ce ta lek'o d'akin tana cewa " ga amaryarki nan ta dawo barka".

Kafin ta d'ago ta ba da amsa sai ga ta ta turo kai tana shigowa da d'an murmushi kan fuskarta, a gefen Fadwaah ta zauna suka gaisa a mutunce tana sake tambayar Suleim jikinta don ta zo washe garin haihuwar yau ma ta kuma dawowa ne, amsawa tayi da d'an murmushi duban Nadeefah ta yi tana cewa " Mommy princess ya gajiya?".

"Alhamdulillah, ya naku?".

"Wlh Alhamdulillah daga school ma na dawo wlh".

"Ayya, sannu da k'ok'ari".

"Yawwa" ta amsa tana mik'ewa tsaye, tana cewa " bari in k'arasa dawowata kenan ban ma kai ga shiga ciki ba". Godiya suka kuma mata har ta fice daga parlorn don dama suna zaune ne a part d'in Suleim su Ainah ne suke main parlor suma suna ta su hirar.

Da harara Zulfaa ta rakata tana cewa " kin ganta kamar wata ta Allah".

"Toh wa yace ba ta Allah ba ce ba?" Tambayar Fadwaah tana dubanta,baki ta tab'e tana cewa " wlh babu wata ta Allah a nan".

"Me tayi miki?".

"Ni sai ta min wani abu? Ai duniya babu wata kishiya ta Allah duk 'yan iska ne" girgiza kai Fadwaah tayi don ta san kishi ne yake d'awainiya da ita ba komai ba, ita ma dai ba wai tana son ganin Fareesahr bane don duk sanda zata gan ta sai ta ji kamar in mijinta yana ganinta zai iya zuwa itama ya kinkimo mata wata a kishiya.

Lele ce tace " ba sai kin shiga sabgar su za su miki ba? Besides ita dai wannan ba kalolin kishiyoyin nan ba ne".

"Ke ba a yabon kishiya fa, na rabaki" fad'in Ainah da ta dawo d'akin.

Dubanta tayi tana cewa " nima ba wai ina yabonta ba ne, kawai abinda na sani na fad'i in ma tana da wani halinda ban sani ba toh wannan kam damuwarta ne ko a gefen gyalena".

'Yan d'akin gabad'aya suka d'auka da fad'in " dama wa ke da lokacin wata kishiya?".

Ahh toh ta fad'i tana mai kawar da maganar da wata, daga haka ma aka saki zancen suka kama wata. Ba ita ta bar gidan ba sai after isha'i sai da ta tabbatar da taci abinci ta k'oshi kafin ta tattara kayanta a lokacin ne ma ta tuna da message d'in da ya shigo mata, duba wayar tayi nan ta ci karo da kud'in da Islaam ya saba tura duk wata cizon bakinta tayi ta yi wato dai yana sane da ita wulak'ancin shi ne ya sa yake shareta, murmushin takaici ta saki message d'in godiya ta tura masa tana maida wayar cikin jakarta tare suka fito da su Ainah su mota suka shiga ita Zulfaa da Farhaan suka taka tare da ita suna fita suka yi k'asa ita kuma ta yi d'an sama kad'an don gidanta yana daga farko sai na ElSadeeq sai na Yaya Mahfuz sai na su Farhaan d'in.

Tura k'ofa tayi ta shiga Umara ya taso yana mata barka da dawowa, cikin sakin fuska ta amsa shi kana ta nufi part d'in ta. Wanka ta fara yi ta zura kayan barci har ta kwanta ta tuna ba ta da ruwa a d'aki mik'ewa tayi ta nufi kitchen.

Wuta ta kunna nan ta ci karo da kaya a ajiye a gabanta, murmushi ta kuma saki kawai tana duban kayan. Har da ruwa da cartons d'in drinks da su fruits da sauran kayan buk'atun gida bubbud'e su tayi ta sanya kowanne a inda ya kamace shi kafin ta wanke hannayenta, ruwa ta d'auka ta kashe wutan ta koma d'aki kwanciya tayi tana mai sake jin matsalarta na washewa ta san ba za'a dad'e ba zai karkato gareta ita kuma ba zata yi wasa da wannan damar ba zata kuma rik'e mijinta don ita d'aya ta san wahalar da ta sha na rashinshi.

A haka suka cigaba da rarrafa rayuwa har zuwa ranar da aka yi sunan babyn Suleim da aka sanyawa sunan Mommy wato Zainab, wanda kai tsaye suka rad'awa suna Aleenah. Mommy ta ji dad'in karar da aka mata don duk sauran yaran babu wanda yayi mata takwara, don sun fi son saka suna kai tsaye ba na takwara ba shi ko ElSadeeq yana matuk'ar son 'ya'yan shi su ci sunan wani ko don shi ma takwara akawa Aji Garwa oho. Nadeefah ma tana matuk'ar son takwara kawai dai don Islaam bai so ne ya sa ta hak'ura.

Sosai sunan yayi armashi an ci an sha mai jego da baby sun yi kyau kamar ka sace su sun kuma samu kaya masha Allahu, ko Lele ma tayi nata k'ok'arin yanda ta saba inda shi Islaam sai bayan isha'i ya kawo na shi kayan masu matuk'ar kyau a irin wainda yake siya ne wurin YaBudu na haihuwar Lele ba tare da itama ta san da su ba ne ya kawo.

Godiya suka saka masa ainun sai da Lele da Zulfaa suka tayata suka jera kayakin a inda ya dace, suka gyara gidan tsaf kafin suka wuce gida. Yau kam tayi baccin wuya da gajiya don ba k'aramin hidima aka yi na sunan ba, washe gari ba ita ta iya tashi ba sai kusan 10 wanka tayi ta gyara gidanta ta sake komawa gidan Suleim.


Su na gama zaryan gidan kuma damuwarta ta fara dawowa sabuwa, hana hakan tayi da maida hankalinta ga business d'in ta dake kuma samun karb'uwa in kuma ta dawo ta shiga d'akin arts d'in ta inda sai ta kai dare tana yi musamman da cikinta ya fara tsufa ya shiga wata na 6 zuwa 7 sai baccin ya fara d'auke mata kamar irin na Sairah.

Sallah ta ke yin kayanta a zaune da 'yan adduointa kana ta wuce can arts room d'in nata inda a can take k'arasa sauran daren sai tayi sallahn asuba take iya bacci wanda ko ma tayi ba ta iya wuce 10 in ta tashi ta tattare gidan ta had'a breakfast ta ci tai wanka anytime around 12 take wucewa office.

Duk wannan halin da take ciki da Islaam ba ta tab'a gigin gayawa kowa ba har Hajjah kuwa balle su Ummu, tana da yak'ini mai k'arfi a ranta zata iya jure komai ba kuma ta daina zuwa cikin Yerwa ba har abincinta na Friday ba ta fasa ba tana kaiwa tana kuma zuwa meeting ita d'aya ba tare da su ba. Zulfaa ce ta fara mata magana akan hakan sai ta nuna mata babu komai kawai ita ce bata son suna jiranta don yanzu ba ta iya barci da dare da safe ne take iyawa so ba ta iya ta shi da wuri.

Tausaya mata tayi ainun don ta san me rashin barci yake nufi ga mai ciki, toh kina samun barcin ma ya aka cika balle baki samu. Umma ma samun Islaam d'in tayi da maganar a kan a wani dalilin ne bai zuwa meeting da Lele sai da Fareesah bayan kowa in zai je meeting tarkata familynshi yake yi har da su da suka manyanta 'yan kame-kamen shi yayi yana cewa ita Lelen ce take cewa su yi gaba, fad'a tayi masa sosai akan don ta ce suyi gaba sai su tafi su bartan kamar mara gata?.

Da Nadeefahn ta zo gidan duba Sairah kamar yanda ta saba itama tayi mata maganar, ba ta yi k'asa a guiwa ba ta mata irin bayanin da tayi wa Zulfaa ta kuma gamsu ainun inda ta tausaya mata sosai. 

A haka ta cigaba da lallab'a rayuwar cikinta tana zuwa ante-natal ran da tayi scanning ta ga gendern da zata haifa sai da tayi kuka sosai don ta tuno ranar da suka yi scanning d'in Sairah yanda suka dinga murna da farinciki kamar za su cinye junansu don dad'i. Haka ta yini har washe gari ba ta jin dad'in ranta da zuciya, gidan Hajjah ta tafi a can ta wuni sai dare kafin ta wuce gida inda da ta so tace zata kwana ne but tuno cewa ba zata barta ba ya sa ta hak'ura. Abinda ko bata sani ba shi ne a yanzu Hajjah ba zata hanata kwana a gidan ba musamman da take ganin damuwa a fuskarta wanda ta k'i  sanar da ita, da farko ta yi tunanin ba mai girma ba ne matsalar don ta san in dai har matsalar ta yi yawa sai Lelen ta gaya mata ko zata samu sauk'inshi a rai da rayuwarta. Sai daga baya ne tayi tunanin ko irin damuwar nan ne ta masu tsohon ciki da zaka dinga ganinsu cikin damuwa har sai randa suka haihu tukunna komai yake daidaita, don haka ma zata so su kwanan ko zata samu ta d'an kwantar mata da hankali ko yaya ne musamman ma da yanzu tana da kishiya zata iya kwana a gidan ba kamar da da take ita d'aya ba.

Still dai bata bar ta ta tafi ita d'aya ba sai da ta had'ata da Mele ya maidata gidan sannan hankalinta ya iya kwanciya. Washe gari da wuri ta wuce office wanda rabinshi a kwance ta yi shi ba ma ta kai yamman da ta saba ba ta koma gida, tana shiga ta ci karo da kaya masu matuk'ar yawa na jarirai a parlornta.

Cak ta tsaya ta kasa gaba ko baya, gani take yi kamar almara ne ko wasa sai da ta d'auki lokaci kafin ta ja jikinta zuwa gaban kayan. Bubbud'e su tayi dukansu kaya ne designers masu kyau da inganci haka za duk wani abun buk'atu ga mai jego da babynta an tanade su a cikin kayan, babu ce kawai ba a saka ba ko ita ce ta je siyayyar kayan haihuwa k'arshen mak'urar zab'enta kenan zama tayi yarab a kan kujera tana d'aukar takardar da ya ajiye mata a gefe short note ne ya rubuta mata akan ta duba abinda babu ta tura masa ta message.


Wayarta ta d'auka tana tura masa message d'in komai akwai tagode kuma sosai amma shin zata iya ganin shi?. Bai dawo da message d'in ba hakan ya sa ko da ta kai kayan ta ajiye su a inda ya kamace su bata zauna a ciki ba, yau parlor ta dawo ta zauna tana dakon jiranshi sai dai tsit kamar an aiki bawa garinsu don ko babu shi babu dalilinshi ko mostinshi ma bata jiyo ba balle ta san ran zai zo d'akin nata abun mamaki kuma shi ne barcin da ya kwasheta bayan isha'i ba ita ta iya farkawa ba sai to 2 wanda kuma tunda ta farka ba ta iya komawa ba sai kawai ta shiga cikin d'akin ta yi wanka ta tada sallahrta a zaune yau saboda ba ta ma iya tsayuwa sai ba ta je artroom d'in ba zaman duba records tayi da reshuffling abubuwa zuwa yanda ya kamata da ta kammala ma ta koma gadon ta kwanta duk da ba bacci tayi ba tunanukanta take yi tana lissafin kwanakin da ya rage mata ta haihu ko kusa ba ta son ta haihu suna a irin wannan yanayin da Islaam don ta tabbatar in dai har ta haihu a haka ba k'aramin tonuwa asirinta zai yi ba agogo ta kuma kalla ta san yanzu ya dad'e da yin barci in ma ba wai yana shirin farkawa ba tana ta wannan lissafin ta kwance wannan ta k'ulla wancan har ta gaji da kwanciyar mik'ewa tayi kawai ta fara gyaran gidan ta yau ba ma ta jira sai da safe ba kafin a kira asubah babu abinda ba ta yi ba har ta jik'a shinkafar da take son yin sinasir da ita da safe sai da tayi sallah tayi wanka ta kwanta.

Tun sanda ta kunna vacuum cleaner ya farka daga barci, duban agogo yayi yana duban lokaci zaro idanu yayi cikeda mamakin aikin da take yi a wannan lokaci. Sai kuma ya sa hannu ya janyo wayarshi yana sake duba message d'in ta na buk'atar ganinshi da take yi, a take kuma wani sabon tausayinta ya rufe shi kenan ba ta iya barci ba ne ko me?.

Numberta ya fara dialing sai dai bai kai ga shiga ba ya katse yana cije baki, sau kusan uku ya sake gwada kiran numberta yana katsewa in as much as yana son yin magana da ita amma bai son jin muryarta. Mik'ewa yayi tsaye ya zura takalmanshi ya nufi parlor har ya murza knob d'in k'ofar sai ya kasa, wani mugun zafi ne yake cika masa rai yake kuma jin kamar ana rik'e masa k'afafu ko in yaje wajenta wani mugun abu ne zai iya samun shi. Runtse idanu yayi cikeda takaici yana jingina da k'ofar yana mai jin dukkan motsinta, a ranshi kuma yana jinta a kusa da shi amma tayi masa nisa kamar an d'auki duk wani feelings da emotions d'in shi a kanta an saka a k'asan dutse mai nauyi a can cikin zuciyarshi duk yanda su emotions d'in suke k'ok'arin su d'aga dutsen amma basu da k'arfin da zasu iya kawar da shi daga kan su gabaɗaya hakan ne ma ya sanya suke dambe su da dutsen shi yasa yake d'an jin motsinsu a ran shi amma da sun yi k'ok'arin motsa kambunsu sai su gaza. Ba shi ya bar wurin ba sai da aka fara kiran sallah a massalaci barin wurin yayi ya shiga ciki wanka yayi ya fito ya zura riga zuwa masjid, ko da ya dawo shi ma gaza baccin yayi sai kawai ya wuce gym d'in shi a can ya samu ya wartsake gajiyarshi ya dawo d'akin shi a sabon espresso machine d'in da ya siyo ya had'a Iced Americano mai matsakaicin k'arfi ya shanye yayi wanka ya bar gidan ko wurin gimbiyarshi bai lek'a ba.


Tun daga wannan ranar ba ta wani cika lafiya ba, rashin yin barcinta ya k'aru ainun kafin ka ce miye duk ya nuna a fuskarta k'asan idanunta duk sun yi bak'i alamun rashin barci hakaza fuskarta ya tasa sosai dul tayi d'anye-d'anye kamar ba ta jini. Hajjah ce ta fara lura da hakan in da ta sanya mata salati da sallallami duk ta firgitata, ba ta kai ko ga zaman da tazo yi ba ta juya sai asibiti.


Tsura mata idanu Dr. Bose tayi tana dubanta bayan gama karanto mata matsalarta, kai tsaye tace su fara yin PCV da kuma gwajin Bp duk da dai duk zuwa sai an mata shi. Ita da kanta ta d'ibi jinin ta tafi da shi lab, tana dawowa ta fara mata gwajin bpn kafin su gama running test d'in. 

Ta tsorata da ganin yanda jininta ya hau wanda dama masu ciki suna fama da matsalar hawan jini balle ita kuma mai fama da rashin barci ga damuwa, tausarta tayi-tayi a kan ta kwantar da hankalinta ko ma me take tunani zai daidaita yanda ta haifi wancan lafiya haka ma zata haifi wannan don ita a tunaninta ko tsoron haihuwarce ya sa jinin ya hau sosai har haka. Ita dai jinta take yi kawai tana gyad'a mata kai, ko da aka kawo result ɗin test d'in PCVn ta babu wata matsala yana normal range kawai matsalar bpn ne, maguguna ta sake d'aurata a kai ta amsa tana godiya ta koma gida. Ta na zuwa sai da ta kira Hajjah tana mata shagwab'ar wai ta tsoratata to ba wai bata da jini ba ne bp ne ya hau, ajiyar zuciya hajjahn ta sauke inda ta d'aura da nata lallashin akan ta kwantar da hankalinta don Allah ta bar saka damuwa in kuma ta k'i da kanta zata zo ta d'auketa ta maidata gidanta har sai ta haihu har ta so ta hanata zuwa office kai tsaye ta k'i yarda don shi ne kawai abinda ke d'ebe mata kewa amma zaman gidan duk ya bi ya gundureta.


Yau dai da yake ta sha magani tun 10 ta fara barci ba ita ta tashi ba sai da aka kira sallah, sosai ko taji ta sakayau fiyeda sauran kwanakin baya. Tun daga nan ko ta fara samun sauk'i da sukunin yin barci duk da dai in ta tashin to komawarta yana matuk'ar zama mata wahala.

Wani mahaukacin fitsari ne ya tada ta daga barcin da tayi, da sauri ta mik'e tana dafe mara cikeda mamakin yanda fitsarin ya don ita ba gwanar fitsari sosai ba ne musamman da ya kasance ta yi da zata kwanta ba kuma ta sha ruwa ba. Sai dai kuma tuno yanda marar masu ciki take a sake ya sa ta lallab'a ta sauka daga gadon bayan ta kunna hasken d'akin ya gauraya tar da haske, tun kafin ta kai bayin ta fara jin ruwa yana bi mata k'afa take k'irjinta ya buga ba dai fitsarin ta fara yi a jikinta ba?.

Kai wannan ba fitsari ba ne sai dai a ce faya ta fashe mata bata sani ba, a gaggauce ta shige toilet d'in ta hau kan sit tana mai sakin fitsarin kamar an bud'e shower. Tayi fitsarin mai yawa wanda yake fita da abinda yake fitar mata, tsarki tayi tana mik'ewa daga seat d'in flushing tayi tana d'ago kai k'irjinta yana bugawa da mugun k'arfi sakamakon arba da tayi da wani bak'in k'adangare a dai-dai windown toilet d'in da yake a bud'e alamun mantawa tayi ba ta rufe ba don ta kan d'an bud'e don iska ya shigo.

Tsureta da idanu shi kad'angaren yayi yana gyad'a kai yana jiran ta ce arr ya arce, ita ko da ba ta ma san kallon tsoro yake mata ba juya a gaggauce da niyyar barin bayin ta manta da cewa da k'yar ta iya kawo kanta saboda k'afafunta da suka fara nauyi. Ai ko tayi missing step sai ji kike yi kif ta fad'a a kan cikinta wani razanannen k'ara ta saki, tana dafe mararta da ta tsinke a take jini ya fara bin farin tile d'in da ke k'asan bayin a take kuma idanuwanta suka rufe ruf tana somewa gabad'aya.............


Toh fah!! Akwai matsala!

Shin suma kawai Nadeefah tayi ko ma mutuwa tayi ko kuwa dai mafarki tayi ba gaske ba ne?.

In mafarki ne miye makomar aurenta da Islaam?
Miye ma yake damunshi ne takamaimai?

Amsan na book 2 wanda yake paid ba free ba ne. 

Akwai sadaki madaidaici ga book d'in wanda yake akan 1k kacal kuma zaku iya samun shi complete a WhatsApp ƴan Arewa kuma In Shaa Allah gobe za mu ɗaura daga inda muka tsaya.

To subscribe to book 2 kindly pay 1k to 
9042522373
Khadija Ismail 
Moniepoint 
Sai ku tura min evidence of payment ta WhatsApp on ***
Nagode sosai
Sai na jiku

Love y'all

Deejasmah🎭.