Chapter 3
by @reza12
MATAR MAZA
Chapter 3
Azima ta ɗago tai masa kallo ɗaya ta girgiza kai kawai a lamar babu matsala. Ya ce "Allah yayi miki albarka, ki zauna cikin shiri a kowanne lokaci za'a iya daurawa". Ya na faɗa yayi waje hankalinsa kwance. Ya na fita ta zauna daɓas ta na bin bayan Baba da kallo. Gaba ɗaya taji ita ba kuka ba kuma ba haushi ba kuma ba komai ba, kamar dai mamaki ne ya kashe ta a zaune a gurin, domin dai wallahi bata ma san me take yi ba a ɗan wannan lokacin. Ta kai minti goma a haka ko matsi ta kasa yi domin ji take kamar gaske kamar mafarki, kamar kuma ba ita Azimar Baba yake nufi ba. Sai kuma ta furta kalmar auren kamar mai jin tsoro. Tashi tayi ta shiga cikin ɗakin sai suka haɗa ido da Hajiya. Har zata kurma ihun kuka ta faɗa kanta, amma ta tuna bata da lafiya, sai ta toshe bakin da hannu ɗaya ta koma da baya zuciyarta na zafi, ta dawo palo ta fashe da kuka mai ƙarfin gask8. Kenan Baba yana nufin tayi aure ta bar Hajiya a cikin wannan gidan nasu, aure fa, a wannan shekarun nata, baga Maryam ba, mai zai hana ba za'a bashi ba sai ita. Sai lokacin ma ta tuno da wanda za'a aura mata ɗin. Da karfi ta tofar da yawo tana cigaba da kuka, take ta ji duk duniya ba wanda ta tsanar kamar shi, domin dai ai da bai zo yace yana sonta ba da ba'a kai har wannan lokacin ba. Sai da tayi mai isar ta, a ranta tana jin ina ma tana da ƙwarin guiwar da zata iya roƙon Baba kar a mata aure, bata son aure, bata son aure, bata ko son jin kalmar aure gaba ɗaya a rayuwarta. Tashi tayi ta wanke idanunta ta koma ɗakin ta samu Hajiya ta lumshe ido. Amma tana jin motsinta ta buɗe tana kallonta. Suna haɗa ido Azima ta sakar mata murmushi tana karasowa gurin da take ta ce "Sorry Hajiya, Allah ya baki lafiya". Ta faɗa tana shafa kanta. Ta amsa da amin. Sai binta da kallo take yi domin duk kukan da take tana jinta. Ta tashi ta rage mata gudun fanka, ta sauke mata labule, sannan ta kunna mata tsintsiyar ƙamshi kaman yadda ta saba. Har zata fita ta ce "Azima" Ta kirata da wata murya mai kama da ta bankwana. Ta juyo ba tare da ta amsa ba". Ta ce "Nagode". Ta faɗa tana mata murmushi. Itama tayi murmushi kafin ta fita. Palon Baba take son zuwa domin amsar kayan girkin rana domin sune da girki yau. Tana jin yadda ake ta mayar da batun auren nata, harda yaran gidan, abun dai kamar tsokana kamar kuma taya murna, to ita dai ta kasa gane musu. Har zata shiga palon Baba taji anyi sallama a gidan kuma ana kiran sunta. Balki ce ƙawarta sanye da kayan makaranta. Ta tsaya har ta karaso gurin da take. Ta ce "Zo ki gani, gurinki aka zo" ta faɗa tana kamo hannunta suka yo waje. Ta biyota da mamakin hakan. Suna fitowa taga taron yan school ɗin sune suka zo gaida Hajiya dalilin Yusra ta faɗa wa Balik abun da ya hana yayar tasu zuwa. Ta musu iso har cikin palo, ta shiga ta samu Hajiya batayi barci ba. Ta ce su shigo cikin ɗakin su duba ta. Haka suka dinga shigowa suna gaidata. Sosai taji daɗin abun da sukai mata. Bayan sun fito taji suna tsokanar ta da amarya. Abun ya bata mamaki, kenan suma har sunji. Suka kama hanya. Ta dawo cikin gidan, har yanzu jikinta a mace domin gaba ɗaya idan taji batun aure sosai take fita a haiyacinta. Duk yadda ta kai da rashin hakuri haka yau bata bi ta kan kowa ba har ta gama girki. Sai gashi ta kasa cin komai, har sai da kowa ya gane Azima ba lau ba. Babu irin tambayar da kannenta basu mata ba amma tace musu ba komai. Haka girkin dare ma tayi shi a daddafe ta gama. Tana zaune a bakin dakinsu kamar ance ta ɗago ta hango shi tsaye a ƙofar shigowa gidan yana ta kallonta kamar tsohon maye. Har cikin ranta ta rasa gane tsakanin shi da kuma auran wa tafi tsana ne. Kasancewa gidan a kwai haske yasa itama tsaf ta kare masa kallo a karon farko. Da hannu yayi mata alama da tazo, harda murmushi, sai itama ta mai alama da yazo da hannun kamar yadda yayi mata. Ya waro ido yana kallonta da mamaki yana nuna kansa alamar shine zai zo ɗin. Ji take kamar tai masa daƙuwa tsabar yadda take jin haushin sa, amma ga mutane da yawa a tsakar gidan, kuma Baba ma yana gida. Ganin yana zuwa ɗin ne yasa ta tashi da sauri ta shige ɗakin ta rufe gabanta na cigaba da faduwa. Tana jin yana buga ƙofar yana kiran sunanta amma ta share shi. Gaba ɗaya yau rabi da rabi tayi barci, sai ta fara sai ta fara tunanin wai an ɗaura mata aure sai ta farka da ihun kuka. Tayi haka ya kai sau biyar tana farkawa. Daga karshe dai haka barcin yayi nasarar kidnaping ɗin ta ba tare da ta sani ba.
Yau da suka tashi jikin Hajiya da sauƙi, dan har ta taya su Sadiya shirywa. Hakan yasa ta ɗan samu kuzari ta shirya itama. Bata ko bi ta gun Baba ba ta tafi makanta duk jiki a kasalance. Bata san mai yasa abun ya taɓa ta har haka ba. Motsi kaɗan tunanin ne ke damunta, ƴar karama da ita amma duk tunani da damuwa sun addabeta. Acen makarantar ne ma ƙawayenta suka dameta da tambayoyi akan auran da suka ji za'ayi mata. Nan ta faɗa musu abun da ta sani, take kuwa suka fara murna jin cewar dai da gaske ne za'ayi. Ko ba komai sun ɗebe mata kewa dan lokacin da ta dawo ta samu Hajiya ta gama girkin rana, ga Kuma baƙi da yawa a gidan dangin Baba harda mahaifiyar Musa matar Kawu Mato. Bata cewa kowa komai ba ta shiga dakin su. Sai taji an rangaɗa guɗa mai karfi. Hakan yasa gabanta sake faɗuwa. Sai ta kasa cire kayan makarantar ta tsaya a gurin kamar mai jiran zuwan wani. A haka ta kwanta a kan gadon ɗakin ita ba kuka ba ita ba lau ba. Minti biyar ta tashi ta cire kayan ta sa na zaman gida kafin ta fito Palo ta samu kannenta suna cin abinci, kasancewar basu san ta dawo ba yasa suke ta kallonta kamar wata baƙuwa. Ta zauna a cikinsu tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin su. Sadiya ce babba, saboda ita ce ke binta, sai Yusra, sai kuma Ummi itace karama. Dukkan su sun ɗan tasa domin Sadiya shekarar ta sha ɗaya, Yusra takwas sai auta mai biyar. Sai dai gaba dayansu ba mai wayo kwatakwata, dan har mamakin yadda suke da sanyi kamar dai Hajiya takeyi. Wani lokaci sai ta rasa gane to mai yasa gaba ɗaya babu wacce ta dauko Irin halinta na kuzari da kazar-kazar.
Yusra ta ce "Anty Zima wai aure zakiyi?" Ta faɗa da farinciki.
"Waye ya faɗa miki haka?"
"Hajiya ce, kuma gashi a gida ma ana ta faɗa, yanzu idan kikayi aure zamu dinga zuwa gidan ki ko, Kema zaki samu gida naki ke ɗaya, sai mu dinga zuwa muna gani ki ko". Ta ƙarasa da dariya.
Ummi ma ta ɗora da nata. Azima ta ce "Yanzu kuna so nayi Aure na tafi na barku a gidan nan?"
Ummi ta ce "A'a bana so ki tafi"
Yusra ta ce "Ai idan muna son ganinki zamu zo ko?"
Sadiya ce ta ce "Anty kuma kina son Yaya Musa ɗin, naga baki murna gaba ɗaya?"
Azima ta share hawayen da ya gangaro mata ta ce "Baba ya riga ya bashi, so ko ina so ko bana so babu abun da zan iya, kawai dai Sadiya ki min addu'a kinji". Sai gaba dayansu suka tsaya da cin abincin jikinsu ya mutu ganin tana hawaye.
Sadiya ta ce "Yi haƙuri Anty Anty, zan tai miki addu'a akan Yaya Musa ya so ki".
To Sadiya na gode, kuci abincin ku, ba kuka nake yi ba fa". Ta faɗa tana halittar murmushi a fuskar ta ganin sun zuba mata ido.
Suna cikin ɗaki suna jin yadda baƙi ke cigaba da zuwa, Azima na mamakin to me za'ayi a gidan haka, Hajiya ta leƙo ta kira Sadiya. Bayan ta fita ne Azima ta tashi da sauri tabi bayanta. Ta tsaya turus da mamaki. Bata san lokacin da wata abokiyar wasan su ta ƙaraso gurin da take tana kamo hannunta tana sakin guɗa ba. Wata daga cikin yayyenta mata da sukayi aure ta ce "Yau dai zamu huta da annoba a gida, Allah na gode maka da yasa miji daidai da irin halinta ta samu". Da karfi ta kwace hannunta ta ce "Malama sakar min hannu dalla". Ta koma ɗaki ta dauki hijjabi tayi hanyar waje. Hajiya ta kwaɗa mata kira amma ko a jikinta, tana zuwa kofar gida taji ana shafa fatiha ga kuma dandazon mutane. Ta tsaya a gurin tana kallon yadda ake tarwatsewa daga gurin. Ta juyo ta dawo ciki kanta na juyawa. Tana shiga cikin gidan aka fara mata tafi da ihu da guɗa hakan yasa kanta yayi zafi, ga tsoron da ya shigeta, ga ihun da suke mata hakan ya jawo mata rashin ingantaccen numfashi daga kirjinta, take numfashin nata ya tsaya mata hakan yasa ta sulale a gurin bata ko motsi. Bata sake sanin a ina take ba sai washegari, koda ta farka kirjinta ne ke mata ciwo, ga wani sarawa da kanta ke yi. Hajiya ta fashe da kuka tana kiran sunanta. A hankali ta miƙe ta wanke baki kafin aka haɗa mata Shayi. Tana cikin sha Baba ya shigo dalilin faɗa masa da akayi cewar ta farko. Yayi mata sannu yana taɓa jikinta. Haka ya ɗan dade a dakin yana kwantar mata da hankali kafin ya sanar mata cewar nan da sati ɗaya zata tare. Tun daga lokacin Azima ta fara rashin lafiya domin da gaske bata son maganar aure, kuma duk a dalilin halin da zata bar Hajiya da kannenta ne, da kuma yadda gaba ɗaya auran kansa tsoro yake bata, saboda ita a irin hali da ɗabi'arta ba zata iya yin ladabi da kuma haƙuri ga wanda take ganin bai isa ba. Haka dole Hajiya ta zage ta fara koyar da ita rayuwar aure, domin dai babu abun da Azima ta sani, tabbas idan har ta kaita gidan miji a haka to a kwai matsala ƙatotuwar ma kuwa wallahi mai zaman kanta, saboda bayan girki bata jin akwai abun da Azima zata iya tsira da shi na zamantakewar aure. Duk da ba lafiya gareta ba, bai sa ta kawar da kai akan wasu abubuwan ba, shi kansa Musa ya fahimci akwai matsala a wannan auran, dan duk zuwan da yake yi basa wanyewa lafiya, gashi har wani rama yaga tayi, dama gata ba wani aukin kirki ba kamar kuɗin guzirin maitafiya Libiya. Hajiya ta ce "Azima ina so ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurare ni, yanzu ke matar aure ce, dole ne yadda suna da matsyinki ya sauya to halaiya da ɗabiunki suma su sauya, zaki bar gabanmu ki tafi cen gurin da ba kowa, halinki shine zai ƙwace ki, kuma ni sheda ce muddin kika je da wannan halin naki wallahi zaki sha wahala, dan Allah Az..." Da karfi ta sake fashewa da kuka tana riƙe Hajiya, domin sai take jin kamar sun rabu ne har abada. Ta ce "Wallahi bana son aure Hajiya, nafi son zama daku, dan Allah Hajiya ki faɗawa Baba ya barni tare da ke, na tsani aure, bana so, dan Allah ki fahimce ni, zan iya mutuwa wallahi". Ganin irin kukan da take yi ne yasa Hajiya ta ɗan fara wani tunanin daban, ko dai tana da aljanin da yake hana Mace son aure ne, ko kuma dai akwai wani abu, ko kuma Aljanin ya aureta ne. Da sauri ta kawar da wannan tunanin domin dai yadda Azima ta taso dole ne taji ba daɗi lokaci ɗaya ace zatayi nisa da gida. Yarinyar da bata san komai ba sai hidimar gida, da kuma rikicin yan uba, da tashin hankalin kishiyoyin uwa.
Sai ana gobe za'a tare ne ma ta san cewar ashe ba ita ɗaya ce kawai aka daurawa are ba, ita da Maryam ce, sai dai Maryam wanda take so aka aura mata, gashi ma sai murna take yi tana ta dariya abunta. Duk wani abu da Hajiya tasan zata mata tayi iya yinta, sauran kuwa ta barwa Allah komai, domin yadda ake ta yada mata da magana akan in sha Allah ko sati ba zata yi ba za'a korota domin halinta dai kam ba mai iyawa da shi, babu namijin da zai iya zama da irin wannan halin na Azima ko waye kuwa, dan haka sun bawa wannan auran sati ɗaya ko kuma kwana biyar zai tarwatse. kalmar tayi mata zafi har sai da hakan ya nuna a fuskarta, itama haka Azima sauran yaran gidan ke tai mata fatan idan taje a sake ta a ranar. Abun dai ba daɗi, duk yadda take jin bata son auran, kuma ita idan za'a yankata bata san cewar ma saki wani abun ƙi bane, har tana amsa addu'ar domin idan dai har zata dawo gida gurin yan uwanta ne idan aka sake ta, to zata so hakan ko da yanzu ne ma. Su biyun ne durƙushe a gaban Baba kowacce kanta na kasa, yayin da Azima ke kuka kamar ranta zai fita, saboda da ta tabbatar da cewar yau dai sai ta bar gidan nan ko tana so ko bata so. Ya cigaba da faɗin "Sanin kanku ne har gida nake bin yarinyar da taiwa mijinta iya shege na zane ta, to wallahi tallahi kar naji kar na gani, ba ma saki ba, yaji idan har ya kawo wata gidan nan sai na mata dukan da gobe ba zata dawo ba, ku zauna kuyi zaman aure, duk abun da kuka tambayi mazanjenku suka ce basu da shi to ku sanar dani, banda rashin kunya, banda rashin kunya"? Ya maimaita yana kallon Azima. Ya ce "ko a kwai mai magana?" Suka girgiza kai gaba dayansu. "To Allah ya muku albarka, ya bada zaman lafiya yasa mutuwa ce kawai zata raba, ku tashi ku tafi". Yana faɗa Maryam ta miƙe, Azima ta kasa tashi, ya kalleta ya ce "Ko kina da magana ne?" Ta girgiza kai ta sake yunkurin tashi amma ta kasa. Ya ƙaraso ya daga ta, sai ta faɗa jikinsa ta fashe da wani irin kukan da yasa jikinsa yayi sanyi. Yayi shiru yana jin tausayinta har cikin ransa amma tabbas wannan shine karshen gatan da zai iya mata, yasan halin Azima shi yasa ya samu miji mai hakuri da sauƙin kai, wanda yasan zata fahimta zuwa gaba, domin idan ba shi ɗin ba, baya jin anan kusa za'a samu wanda zai iya da ita. A hankali ya ce "Kiyi hakuri Azima, ki zauna da mijinki lafiya, zaki yi alfahari da hakan ko bayan raina, na tabbatar miki da cewar Musa yana sonki, kuma zai kula dake in sha Allah". Bata iya cewa komai ba har masu tafiya da ita suka zo.
Nan fa ta fara ihu tana kiran Hajiya da Sadiya, ita kanta Hajiya daki ta koma tana kukan tausayin kansu. Sosai take ihu ana janta tana ƙwacewa, har tana cire ɗan kwalli da gyalan jikinta. An kai minti goma ana fama da ita, har masu kai Maryam sun dawo da yake gidan ta ba nisa. Kusan minti ashirin kowa ya kasa fita da ita domin ihu take yi bilhakki da gaskiyar ta kamar wacce ake yankar naman jikinta. Jin haka yasa Baba ya fito wanda dama yana jinsu, kawai tausayinta ne ya hana shi fitowa, shi kansa yayi mata uzuri domin bata taɓa yin nesa da yan uwanta haka ba, sai idan zata je garin kakarta, shima tare suke zuwa gaba ɗaya. Ai kuwa tana ganinsa tayi tsit kaman anyi ruwa an ɗauke. Yana zuwa ya kama hannunta ya saka ta a cikin motar kowa na mamakin yadda ta tsayar da kukan kamar ba ita ba. Ya ce "Ina wanda zasu rakata?" Suka shiga sauran motocin suka tafi. Motar na fara tafiya ta sake baro wani sabon kukan, har aka ƙarasa gidan bata daina kuka ba. Aka kamo hannunta suka fito da ita daga cikin motar. Duk wanda ya kalleta dole ya tausaya mata da irin yadda ta koma abar tausayi kamar ba amarya ba. Abun kamar wacce a kaiwa faɗa, haka ta fara binsu har cikin gidan da an saka mata komai. Har cikin daki suka kaita aka zaunar da ita akan gado. Wasu manyan mata suka fara mata faɗa da nasiha da jan kunne. Har suka gama bata ɗago ta kallesu ba. Aka tafi aka barta daga ita sai wata yayarta da tayi aure mai Suna Asabe, basa shiri da ita kwata-kwata, ko yanzu ma Baba ne ya umarce ta da ta biyota ba dan haka ba da babu abun da zai kawo ta nan. Haka ta karaci Zaman babu wacce tayi magana har ango ya shigo. Yana shigowa kuwa ta ce "To ango ga dai amarya an kawo maka, sai Kaita hakuri, duk da an faɗa maka hankalinta kace kaji ka gani, Allah ya bamu alkairi, rashin kunya da hauka ne dai sai ka sha su, idan ka iya jurewa to, idan kuma ka kasa ma dai duk kai ka sani, na barku lafiya". Tana faɗa tayi gaba abunta. Musa ya rakota har waje kafin ya rufe gidan ya dawo ɗakin idonsa akan amaryar tasa. Ya ajiye ledar da yazo da ita ya hau kan gadon yana kiran sunanta a hankali haɗi da ƙoƙarin buɗe mata rufin da tayi...📝
Please like and shering and comments.