BARRISTER SUHAIL

CHAPTER 31

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----31

Har tayi niyyar fita da motar Sai ta fasa matukar ta fita da ita za’a gane kuma mummy Sai ta tanbaye ta Ina taje

A Kafa ta taka har ta isa bakin titi kasancewar Unguwarsu ba kasafai abun hawa ya cika shiga ba

Adaidata sahu ta tara bata damu da kudin da ya gaya mata ba burinta kawai taje wajen Khalid 

A kofar Wani karamin hotel ya ajiye ta bashi kudin sa ta shiga ciki 

Kiran Khalid tayi “Ina reception “

Dariyarsa ta karade mata kunnen zeenah 

“Ashe kina son kanki zeenah hau bene na biyu room 207”

Katse wa wayar yayi 

Zeenah ta lumshe idanunta tana neman kwarin gwiwa 

A hankali ta fara takawa

Duk wani taku da take yi kamar ana yankar zuciyarta ne 

Har ta kai bakin kofar dakin  Hannunta na rawa ta daga zata kwankwasa har ta manta Rabon da ta tsinci kanta a hotel tun suna tare da khalid kusan shekaru shidda baya tun tana shekaru goma sha tara da haihuwa

Khalid ne tsaye bakin kofa sanye da singlet da guntun wando

Murmushin yake mai cike da mugunta 

“Welcome to my room amaryar Barrister Suhail” 

Kuka ne ya kwace mata  hade hannayen ta tayi waje Guda tana rokon sa “Khalid dan Allah ka tausayamin ka tuna hallacin da Nayi maka a rayuwa”

Ya kama hannunta ya jata ciki kan gado ya wurga ta babu abinda ke cikin Sai warin taba da shisha da Khalid ke sha 

Matsawa yake dap da ita tasa hannu ta kare “Kada ka taba ni”

Dariya yayi ya ce”Yanzu na zama abin kyama kenan”

Zeenah ta ce”Khalid mı kake nufi Dani ne Nace ban Baka kudi kace a’a ka fadamin abinda kake nema Dani”

“Zeenah all I want is you body you know I miss it badly I miss this you too”

Hannu ta Kai ta done kunnuwanta jin irin maganganun banzar da Khalid keyi mata 

“Khalid don Allah”

Hannu ya daga mata 

Ya kalle ta daga sama har kasa.

“Yanzu kin tabbatar na fi Suhail muhimmanci a rayuwar ki”

Tunda Ina da abinda kike tsoron duniya ta sani a kanki 

Cikin fada zeenah ta ce”impossible dan iska irin ka bazai taba zama mai mahimmaci fiye da Suhail ba Khalid idan ka manta Bari na tuna maka nice na zama gatan ka ,a lokacin da duniya tayi maka zafi abincin da zaka ci yake Neman ya gagagare ka ni na soka a lokacin da duniya ke maka kallan Abu marar amfani shege da wanda baida Asali lokacin da mutuwa ke neman Rayuwar ka ido biyu

Ni tsaya wa karatun duk a lokacin ma cutata kake da sunan kana Karatu kuskure mafi girma da na aikatawa rayuwata shine sanin ka da Nayi Khalid Duk Wannan abin da Nayi ka tasa mi zaka yi Sai kayi recording nude Dina ka rinƙa threating dina da shi  hakan da kayi ka gasgatar wannan ya tabbatar min da cewa ba ka san darajar alkhairi ba Khalid"


hannu ya daga daga zai mari zeenah sai kuma ya ƙasa duka abinda ta faɗa ba karya bane tayi ba banda shigowor zeenah Rayuwar sa da tuni ya jima a ƙabari 

zeenah ta hadu da Khalid wata rana ta raka mahaifiyar ta Asibitin da take aiki taga khalid kwance a ƙasa yana ta juye juye zai mutu an rasa wanda zai tambaye shi miya same shi ita ta roƙi  mahaifiyar akan ta sa a duba shi tun daga lokacin yake samun kulawa daga gare ta hatta abinci daga gidan aka kawo masa sun saba sossai inda ya bata labarin Rayuwar kaf ba tare da ya boye mata komai ba 


ta tausaya masa bayan an sallameshi ba tare da sanin kowa ba ta kama masa gidan haya ta biya kudin shekara biyu ta kuma maida shi makaranta kamar yadda ya buƙata Khalid mutun ne mai   hazaka amma rayuwarsa cike take da ƙalubale Zeenah ce ta fara taimaka masa da kuɗin handout, daga baya ta biya masa registration, har ma ta siya masa waya ,Soyayyar da ta fara a matsayin tausayi ta koma soyayya ta gaskiya Sai dai abin da Zeenah bata sani ba shi ne, Khalid yana tattara sirrinta ne domin wata rana ya yi amfani da su a kanta 

Daga baya soyayya ta yi ƙarfi a tsakaninsu har suka shiga rayuwar da ta sa Zeenah ta amince da shi fiye da kima, zeenah irin mutanen da baza su iya Rayuwa ba tare da Namiji a kusa dasu ba 

tun lokacin da zeenah ta tafi makaranta ta fara ja baya da Khalid sakamakon ta hadu da Suhail duk da tana aji ɗaya shi kuma yana aji ukku ko hutu ta dawo bata neman khalid


ta daina basa duk wani taimako har akazo kudin hanyar sa ya kare aka kore sa daga gidan tundaga lokacin rayuwarsa ta kara shiga wani hali ya fara sace sace har aka kamasa yayi shekara biyar a gidan yari bayan ya dawo yake samun labarin auren zeenah da Barrister suhail hakan yasa ya dawo da videos dinta da ya jima yana ajiye dasu ko dan wata rana


Zeenah ta ce"ka mare ni Khalid"

ai duk wani abu da zakamin bazan ji ciwo ba domin ka jima kana marin Rayuwa ta

shishar dake gaban sa ya zuƙa ya busa mata hayakin 

cikin kakkausar murya ya ce"tura min kudi na ki kama gaban ki"

jikin ta har rawa yake ya karanto mata account Number din sa ta tura masa kudin tashi tayi zata bita 

Khalid ya ce"kinga kin manta jakar ki"
dawo wa yayi ta dauka ta fita da gudu

comment Kadai zai saka ku sami update din dare