PAGE 18
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 018.*
Umma tana fita daga gidansu Saheer gidan ƙawarta Atika ta shiga, aminiyarta kuma abokiyar sirri. Tana shiga ta ɗauki kujera ta zauna a tsakar gida ta ce, "Atika kina ina?."
Tana daga ɗaki ta fito ta ce, "Gani nan, aminiya ta samu ne?" Ta faɗa tana fitowa ta zauna akan kujera itama.
Umma ta ce, "ta samu, ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa ƙawata."
"Ina jinki, meya faru?."
"batun tafiya Saudia aikin nan ne, kin ji kuɗin da ake samu?."
"Allah ƙawata?."
"Bari kawai ƙawata. Ga gidan aikin an samu a hannu, kawai ma'aikaci ake nema."
Atika ta ce, "ba kin ce Safeera za ki tura ba?."
Umma ta ce, "Yarinyar baza ta yarda ba, kin san tana tare da Islaha, kullum cikin kushe abin suke. Babanta ma ya ce indai shi ya haife ta bazata je ba. Shine nace masa amma ni ai ba shi ya haife ni ba, zan dire su in yi tafiyata."
Atika ta ce, "abinda zan ce miki kenan, da ƙarfin ki da lafiyarki ki tsaya ana ɓata miki rai da lokaci?. Meye amfanin ki, meye amfaninki in ba ki je ba?."
Umma ta ce, "Atika ba Baban Safeera nake ji ba, mutanen Katsina nake ji. Baza su ɗaga min ƙafa akan haka ba, Yayanmu fata-fata zai yi min."
"In sun sani ba, sai ki tafi ba tare da sun sani ba. In dai kin je ba shikenan ba?."
Umma ta ɗan ti jimm alamun tunani kafin ta ce, "Ina son zuwan nan wallahi, amma ban san ya zan yi ba."
"Maimuna ki daina tunani, ki ajjiye ƴaƴan nan ki, ki je ki tara kuɗin auren Safeera. An kawo kuɗinta fa, ko yaushe za a iya maganar aurenta. Me Baban nata yake dashi, ke me ki ka tara da zaki aurar da ita?."
"Babu Atika."
"Amma kin samu dama zaki bari ta gudu?in wannan damar ta kubce mana a ina zamu samo kamar ta?."
"Babu."
"Ki rufe ido kawai ki yi, indai kin je ɗin dai ba shikenan ba? Duk faɗan da za a yi sai ayi, tunda kin je ai komai ya ƙare. Shi kuma Baban in ya sake ki fa shikenan."
Umma ta buɗe ido ta ce, "Saki Atika! Da girmana?."
"To sai ki zauna ai. Kin san in da aurensa a kan ki bazai bari ki tafi ba, in kuwa ya sake ki ba shikenn kin huta ba, ki yi tafiyar ki babu nauyin kowa a kan ki."
Umma ta ce, "Gaskiya ne wannan, kin ƙara min ƙarfin guiwa sosai Atika."
"Ahto, akan me zaki bari Baban Safeera yana juya ki? Dan ya hana ƴarsa ke ai bai haife ki ba."
"Gaskiya ne wannan, kuma zan iya tafiyata mutanen Katsina basu san na tafi ba."
"Daɗina dake akwai ɗaukar haske."
"Bara in je na same shi" ta faɗa tana miƙewa ta fita ta nufi gidanta.
Tana zuwa ta samu Baba ya dawo, ta zauna tana sake yi masa magana a kai.
Baba ya bi Umma da kallo ya ce, "amma na faɗa miki bana son wannan maganar ko? Na faɗa miki kar ki sake gangancin yi min irin wannan maganar ko Maimuna?."
Umma ta ce, "kuɗin nan fa in an samu ba ni kaɗai zan saka a gaba na cinye ba, amfani zamu yi dasu in auren Safeera ya tashi. Baka dashi, kuma baka da hanyar samu, laifi ne dan na nemo mafita domin gaba?."
Bab ya ce, "to baza a yi ba, babu inda Safeera ko wani a gidan nan zai je, wallahi."
Umma ta kalle sa cike da mamaki ta ce, "harda wallahi?."
"Wallahi Allah baza su je ba, matuƙar ni na haifesu babu wacce zaki ɗauka ki kai wata ƙasar neman kuɗi."
Umma ta girgiza kai ta ce, "na ji, kai ka haifesu kana da iko dasu. Amma ni ai ba kai ka haife ni ba ko?."
Baba ya bita da kallon mamaki jin abinda ta ce, ya gyara zama ya ce, "bani na haife ki ba, amma akwai aurena a kanki. Yadda na isa da ƴaƴana haka na isa dake, kafin na samu ƴaƴan ke na samu, kafin na faɗa su ji, ke zan fara faɗawa ki ji. Dan haka kema babu inda zaka je."
"Ai kuma baka isa ba, wallahi baka isa ba. Ka hana ƴaƴana zuwa nima ka hana ni? Kaima ka san ai bazai yu ba. Ƴaƴanka ka ke da iko dasu amma bani ba, ƴaƴanka zaka hana tafiya bani ba. Aure da ka ke magana aki kalma uku zata warwaresa, daga nan babu komai tsakanina da kai, zan je duk inda na ga dama."
Baba ya bita da kallo, jin tana maganar saki har haka, har tana cewa kalm uku ce ta raba auren ya ce, "shikenan Maimuna, Allah ya taimaka" ya faɗa yana miƙewa ya bar mata wajan, kar zuciya ta tunzurasa ya aikata wani abun da zai yi danasani.
Safeera ta shigo falon a sanyaye ta ce, "Haba Umma, me ki ke aikatawa haka? Ina ke ina tafiya wata ƙasar aiki?."
Ta bi ta da harara, cikin faɗa ta ce, "ba kin biyewa ubanki ba?."
"Umma ko Baba hana ba, wallahi ni bazan je ba."
"Kar ki je Safeera, kar ki je ɗin mana. Ƴar iskar yarinya mai taurin kan tsiya, wacce bata son abinda uwarta take so. Matsa ki bani waje ko na tsinka miki mari!" Ta faɗa a fusace tana kallon Safeera.
Safeera ta ja gefe ta tsaya tana kallon Umma da ɗubun mamaki. Bata ɗauka abin Umman ya kai haka ba, bata ɗauka lamarin Umman ya kai wannan matakin ba sai yanzu. Akan zuwa wannan aiki wat ƙasa take ce mata ƴar iska, har take cewa zata mare ta?.
Umma ta ce, "in baki je ba ai ni zan iya zuwa ko? Ina da ƙarfi da lafiyar da zan iya yin ko wanne aiki ne. Ki zauna Safeera, ni zan je, bazan taɓa ganin arzuƙi yana tunkaro ni n tsallake ba. Zan bar gidan nan in tafi, sai ki zauna ki cigaba da kula da ƴan uwanki, amma wallahi sai na je!."
Baba ne ya shigo ya dawo ɗaukar wayarsa da ya bari, ya ji kalaman Umma. Sai ya ga Safeera ta zube a ƙasa tana kuka, ta ce, "don girman Allah Umma ki rufa mana asiri, Umma don Allah kar ki tsallaka ki bar mu a nan. Ki zauna a tare damu, kar ki tafi wata ƙasar saboda neman abin duniya. Da yawan aikin nan yaudara ce, wahala ake zuwa a sha a can."
Baba ya ce, "ƙyaleta Safeera, matuƙar da aurena a kanta babu inda zata je wallahi!."
A fusace Umma ta ce, "idan na kashe auren fa? In ka sake ni ba shikenan ba!?."
"Sai dai hakan, dan in dai kin ga kin bar ƙasar nan tabbas babu aurena a kanki!."
"Ai daman sakina zaka yi, bazan zauna da auren ka ba nima.."
Safeera ta fashe da kuka ta ce, "Umma na yarda zan je, na yarda zan je ɗin. Ki daina faɗar wannan maganar don Allah, ni zan je na samo miki duk abinda ki ke so!. Ki zauna dasu Rukayya, ni zan js na samo duk abinda ki ke so ki samo a can"
Cikin tsawa Baba ya ɗago Safeera ta miƙe tsaye, ya ce, "wallahi baza ki je ba! Ni na haife ki, ina da ikon saka ki ko na hana ki, babu wanda zai yi miki dole akan wanann. Baza ki je Safeera, ita dai tunda bani na haife ta ba ki ƙyaleta ta je!."
Umma ta ce, "nima ai ban ce ta je ba, ta yi zamanta ita da kai, zan je na yi abinda nake so. Sai ka zauna dasu su maye maka gurbina" tana faɗar hakan ta fita daga falon.
Safeera kuka take yi sosai, murya tana rawa ta ce, "Baba don Allah ka bar ni in je, ka ji!."
Baba ya kalle ta cikin sigar kwantar da hankali ya ce, "ki kwantar da hankalinki, barazana take yi miki dan ki ce zaki je, amma babu inda zata je. Ki daina kuka."
Safeera ta goge ido ta ce, "Baba Umma da gaske take, ban taɓa ganinta cikin irin wannan yanayin ba sai yau, ni ka bari in je don Allah, ka ƙyale ni na tafi don Allah!."
Baba ya girgiz kai ya ce, "babu inda zaki je wallahi, ki bar maganar nan dan ba yuwa zata yi ba."
Ta yi ajiyar zuciya tana goge hawaye, ta juya ta kalli ƙannenta mata guda uku duka mata.
Rukayya da ta kasance babba mai bin Safeera, ta ƙaraso ta ce, "Adda ina Umma zata je?."
Baba ya ce, "Rukayya ki zauna da ƴar uwarki, ina zuwa" ya faɗa yana fita daga falon.
Safeera kuwa bata iya amsawa Ruky ba, kuka kawai take yi tana tunanin ya zama dole ta je Katsina dangin Umma ta faɗa musu halin da ake ciki, dan gaskiya baza ta bari Umma ta aikata wannan ɓarnar ba.
*******
Suna zaune a compond ɗin gidan, ta saka hijjab har ƙasa shi kuma yana gefenta a zaune. Suna ta hira cikin nishaɗi da soyayya.
Saheer ya ce, "na fito dake bayan na san a gajiye ki ke."
Islaha ta ɗan murmusa ta ce, "Babu komai, ai na ɗan huta kaɗan."
"To ya aikin? Kin samu ganin Mr Ray ɗin?."
"A'a, amma mun ga Mr Jafaar, ko yaushe ance suna tare."
"Good. Sai aka yi ya kenan?."
Ta ɗan kalle sa ta ce, "dashi mu ka yi magana, ya tabbatar min da kansa zai neme ni in lokacin hirar ya zo. Amma a yanzu ya faɗa min hira dashi bazai yu ba, dan ya faɗa min gaskiya bai rufe ni ba."
Saheer ya ce, "hakan yana dakyau, Allah ya taimaka matar Hamma."
Ta yi murmushi ta ce, "Amin ya rabbi Hamma."
Sai ta ja numfashi ta ce, "ka san me na gani?."
Ya girgiza kai ya ce, "sai kin faɗa."
Islaha ta ce, "Hafsa na gani a hotel ɗin fa, kuma da ita kaɗai na gani da sauƙi, zan iya cewa wani abun ne ya kai ta, amma ita da wani ne har na ga sun shiga ɗaki."
Ya buɗe ido cikin firgici ya ce, "Hafsa dai ta orpahange?."
Ta ɗaga kai ta ce, "ita fa. Lokacin da na gansu mu kuma lokacin mun fito, sai hankalina bai kwanta ba, sai na koma daga baya. Ka ga" ta faɗa tana nuna masa hoton da ta ɗauka na Hafsa.
Ya karɓi wayar ya yi zooming yana kallon fuskar Hafsa, cike da mamaki ya ce, "ai kam itace. Amma me ya kai ta hotel su da ba a barinsu su fita past six?."
"Ashe ka fahimci abinda yake a raina. Kuma kasan na je gidan, an tabbatr min da kwanan Hafsa biyu bata nan."
Ya bata wayarta sannan ya ce, "waye ya faɗa miki?."
"Zainab ce, kuma tana cikin faɗa min Fadwa tazo ta hanata, sai hakan ya sake jefa min zargi a zuciyata Hamma."
"Zargin me ki ke yi?."
Ta kalle sa suka haɗa ido ta ce, "ina zargin ana aikata mummunan abu a gidan nan, zuciyata tana bani ana fitar ƴan matan gidan a kai su inda bai kamata ba."
Saheer ya girgiza kai cike da gamsuwa ya ce, "gaskiya ne wannan, nima kaina yanzu na fahimci zarginki. Amma meyasa da ki ka ƙi faɗa min?."
Ta rausayar da kai ta ce, "zargi ne ai shiyasa, yanzu da na samu hujja ai na faɗa maka."
Ya girgiza kai ya ce, "yanzu what next?."
Ta sauke numfashi sannan ta ce, "zan sake samun evidance mai girma, daga nan sai na yaɗa maganar zuwa gaba."
Ya kalle ta kaɗan ya ce, "amma in hakan ya tabbata sun ci amana wallahi, Allah ya ba su amana suna ci."
Sai kuwa ta ta sake fusata, ta fara magana cikin kaushi ta ce, "bari kawai, na rantse da Allah babu wanda zan sassautawa, wallahi ko waye yake da hannu a lamarin nan sai na tabbatar da ya tafi gidan yari."
"zan baki goyan baya ɗari bisa ɗari. Allah ya kare min ke, ya cigaba da baki nasaraa a rayuwarki."
Ta yi murmushi tana kallonsa, ƙaunarsa na sake shiga cikin zuciyarta.
Ta sunkuyar da kai tana blushing ta ce, "Amin Hammana."
Murmushi ya yi ya ce, "ina ji kamar na...." Sai bai ƙarasa ba ya zuba mata ido kamar yadda ta ɗago tana kallonsa.
Ganin kallon da yake yi mata sai ya bata kunya, ta sunkuyar da kai tare da rufe fusksrta da tafukan hannunta masu matuƙar kyau.
Hannunta ya bi ta kallo, muryarsa a ƙasa ya ce, "zaki jira ni in je ɗaki na dawo?." Ta ɗaga kai bata buɗe fuska ba.
Ya miƙe ya shiga ciki ta bisa da kallo cikin ƙauna da soyayyar da take yi masa. Ta sauke ajiyar zuciya, domin kuwa Hamma ya cancanci soyayyarta mai girma, ya zamar mata komai a rayuwarta, bata da wani sai shi ɗin kawai.
A lokacin ta hangosa yana tahowa, ta tsaya tana ƙare matsa kallon yadda yake takawa kamar baya so. Hammanta duniya ne a wajan kyau, kai da ka gansa ka ga jinin fulani gaba da baya. Yana da kyaun fulani, ga kwantaccen gashi baƙi irin nasu.
A nutse ya ƙaraso ya zauna kusa da ita, ya ɗaga mata gira ganin yadda take kallonsa kamar bata gane shi ba. Sai ya sake ya bata kunya, ta sunkuyar da kai tana murmushi.
Ya yi murmushi ya ce, "ƴan mata wannan kallon fa?."