PAGE 19
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 019.*
Hankalin Jafar ya tashi sosai, sai kai kawo yake yi a tsakanin ɗakin da aka shigar da Ray dan a basa taimakon gaggawa.
Mamy kam tana zaune ta yi tagumi, ta yi kuka har ta gaji, fuskarta ta yi ja sosai, kana ganinta ka san ta yi kuka ba ɗan kaɗan ba.
Abba ma yana zaune ya yi shiru bai ce komai ba, hankalinsa yana kan halin da Rehaan ɗin yake ciki, dan yadda aka fito dashi yanayin ba mai kyau bane.
Mintinansu arba'in a wajan suna jira, sai a lokacin Dr Munib ya fito daga ɗakin yana cire nosemask ɗinsa.
Jafar ne ya ƙarasa inda yake ya ce, "Dr ya jikin Rehaan?."
Ya kalli Jafar, ya kalli Mamy da Abba da suke jiran amsarsa ya ce, "Alhamdu lillah, an samu an daidai matsalar."
Jafar ya ce, "Alhamdu lillah!. Amma bai taɓa irin wannan ciwon cikin ba, duk da ka san ciwon ciki cutarsa ce, amma ba ya yin wrost haka."
Dr Munib ya ɗan sauke numfashi ya ce, "Mr Jafar zan iya ganin abinda ya ci ko ya sha, wanda ya kasance na ƙarshe?."
Jafar ya bi sa da kallo ya ce, "ban gane ba."
Abba ya ce, "Dr Munib ka yi mana bayani yadda zamu fahimta."
Cike da girmamawa ya ce, "i'm sorry to say, Mr Rehaan was poisoned!."
Mamy ta yi baya kamar zata faɗi, Abba ya yi saurin riƙo ta, ta janye jikinta ta taho wajan Dr, a gice ta ce, "guda ka ce! Guba ya ci?."
Ganin ta gigice ya sai Dr ya ce, "calm down Mamy! Ba abinda zaki ɗaga hankalin ki bane."
Mamy hankalin ta a tashe ta ce, "ina so in ganshi, ka faɗa min in ya mutu Dr."
Dr ya ce, ""Wallahi bai mutu ba Mamy, ki kwantar da hankalinki. Bacci yake yi yanzu."
Abba ya riƙe ta suka zauna, ya ce, "Don Allah ki nutsu, asibiti ne nan ba gida ba."
Jazy ya ce, "yanzu ya jikinsa?."
"Gudar bata da ƙarfi ko kaɗan, kuma kaɗan ya ci ko ya sha a cikin abinda aka yi poisining ɗinsa. Yanzu ina so a samo min abinda ya zama last a cikinsa, zamu yi gwaji dan mu tabbatar."
Jazy ya ce, "in kana ganin baza ka iya kai kaɗai ba, mu sake kiran toxicologist ku yi handling case ɗin nan."
Ya yi murmushi ya ce, "don't worry mr Jafar, zan yi duk abinda ya kamata a kai. A fara kawo min abinda ya ci na ƙarshe."
Abba ya ce, "to me ya ci?."
Jazy ya ce, "ya sha coconut drink a gabana, kuma yana gama sha bai jima ya fara reacting. In zuwa" ya faɗa yana barin wajan da sauri.
Mamy ta ce, "coconut drink kuma? Ta ya za a yi poisining ɗinsa a coconut drink bayan Riyya ce ta haɗa masa? Sai dai in wani abun ya sha ba shi ba."
Dr ya ce, "ba abin damuwa bane, zai samu sauƙi in sha Allah." Abba ne kawai ya amsa ya buɗe ƙofar falon da suke zaune ya fita.
Jazy bayan ya ɗauko drink ɗin suka haɗu da Riyya, sai ya ɓoye sa a aljihunsa dan ya san itace ta haɗa, in ta ji a ciki ya sha guba hankalinta zai tashi sosai. Ya san yadda suke son Rehaan kamar su goya shi, in bashi da lafiya kamar su ɗauko ciwon su dawo dashi jikinsu haka suke ji.
Riyya ta kalle sa da idanunta da ta sha kuka ta ce, "Ya jikinsa?."
Ya zuba mata ido sannan ya ce, "ya ji sauƙi, bacci yake yi."
"Me ya same shi?."
"Ciwon ciki, kin san kuma yana yi.
"Amma wannan ya yi yawa, unconsiouly aka fita dashi fa."
"Kar ki damu, ina tabbatar miki da ya ji sauƙi, bacci ma yake yi."
Ta yi shiru bata ce komai ba, ta ɗago taga ita yake kallo sai ta ce, "don Allah zan bi ka in je, ina ao naga halin da yake ciki, please!."
Ya ɗan sauke numfashi yana kallon ta ya ce, "gobe kina da school fa."
Cike da shagwaɓa ta ce, "msc nake yi fa, i'm not a small girl. Ka yarda mu je ka yi Hamma Jazy!."
Yadda ta yi maganar ya saka shi yin murmushi ya ce, "ki je ki rufe gashin nan na ki sai mu tafi. Na ce ki daina zama babu hula bakya ji ko?."
Ta yi murmushi ta shafa kanta, sai a lokacin ta ji ashe ma babu ɗankwali a kanta, ta koma ciki shi kuma ya shiga mota yana jiranta.
Babu jimawa ta dawo, Janan da take ta hangosu ta ƙaraso suka tafi gabaɗaya..
Bayan ya sauke su shi kaɗai ya kaiwa Dr Coconut drink ɗin, su kuma suka je wajan da Mamy suke a zaune.
Riyya ta zauna a kusa da Mamy, ta fara hawaye ta ce, "Mamy me ya samesa? Ciwon cikin da yake yi ne?."
Abba ya ce, "ki kwantar da hankalinki Juwariyya, babu abinda ya same sa. Zai ji sauƙi in sha Allah."
A lokacin Jafar ya dawo, Abba ya kalle sa ya ce, "Jafar ka kai masa?."
Ya ɗaga kai ya ce, "na kai Abba, sun shiga lab za a duba."
Mamy dai ta kasa cewa komai hawaye kawai take yi, bata son zaman Rehaan a Nigeria, amma mahaifinsa ya kasa fahimtar haka. Gashi daga dawowarsa har an fara ƙoƙarin kashe mata shi.
Babu jimawa Dr ya ƙaraso wajan da result a hannunsa. Ya daidaita nutsuwarsa, yana kallonsu dan baya so ya yi wani kuskure. Mai asibiti gabaɗaya babu lafiya dole a nutsu, kuma Rehaan ba ya ɗaukar mistake ko kaɗan.
Ya ɗauko ragowar drink ɗin ya ce, "Abba a cikin wannan drink ɗin ya sha guba."
Abba ya ce, "innalillahi wa'inna ilairhir raji'un! Da gaske dai gubar ya sha?."
Dr ya ce, "da gaske ne Abba, guba ce amma bata da ƙarfi sosai. Kuma Mr Jafar ya faɗa min ɗan kaɗan ya yi sipping ba da yawa ba, shiyasa bata shiga jikinsa sosai ba."
Mamy ta ce, "ta ya zai sha guba a wannan drink ɗin?."
Ta kalli Riyya da take zare idanu ta ce, "Ƙanwarsa ce ta jini ta haɗa masa, ta ya za a ce akwai poison a ciki?."
Dr ya ce, "tabbas akwai guba a ciki Mamy, a ciki ya sha gubar."
Riyya ta fara girgiza kai ta ce, "wallahi ni kaɗai na yi aikina, kuma ni ban saka masa poison ba, ta ya zan iya sakawa Hamma Rehaan poison? Ta ya zan yi ƙoƙarin kashe sa?."
Abba ya riƙe hannunta ya ce, "calm down Juwairiyya, babu wanda ya ce kin zuba masa guba. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki."
Abba ya kalli Dr ya ce, "ka tabbatar a ciki aka zuba masa?."
Ya ɗaga kai ya ce, "na tabbatar yallaɓai."
Mamy ta kalli Juwariyya da take kuka ta ce, "Ke da wa ku ka yi aikin? Ke da wa ku ka haɗa drink ɗin?."
Muryarta tana cracking ta ce, "ni....kaɗai....ce" ta faɗa tana sake fashewa da kuka mai sauti.
Mamy ta dafa bayanta ta ce, "shikenan ya wuce, ai babu abinda ya same sa. Ki daina kuka."
"Amma Mamy ni kaɗai na haɗa komai, ta ya aka samu poison a ciki?."
Abba ya ce, "akace ki bar maganar, kar ki damu tunda babu abinda ya same shi sai mu godewa Allah. Dr ya jikinsa?."
"Da sauƙi sosai, in sha Allah gubar baza ta yi wani tasiri a jikinsa ba. Yanzu bacci yake yi, zai iya kawai gobe kamar haka yana bacci. Za ku iya shiga ku gan shi."
Abba ya ɗaga kai ya ce, "Dr waye ka ce ma?."
"Dr Munib Sir."
"Thank you Dr Munib."
"My pleasure Sir" ya faɗa tana murmushin jin daɗi ya fita. So yake ya yi abinda za a gode masa daman, iyayen Rehaan ba abin wasa bane. Gashi kuma Rehaan ɗin ne da kansa a kwance, dole a nutsu a yi aiki dakyau.
Abba ya kalli Juwariyya ganin ta ƙi daina kukan ya ce, "zo."
Bata musa ba ta koma kusa dashi, ya dafata ya ce, "ki kwantar da hankalinki, babu abinda zai samesa."
Ta ɗaga kai alamun to, Abba ya kalli Janan ya ce, "Janan ku koma gida dare ya yi sosai."
Jafar ya ce, "Abba zan kai ku na dawo, sai na zauna dashi."
Mamy ta ce, "In bashi da lafiya a jikina kaɗai yake iya yin bacci, zan zauna dashi Jafar, ku koma gida."
Jafar ya ce, "Mamy ku je gida kawai, ni zan zauma dashi a nan."
Abba ya ce, "Jafar baka huta ba, ka dawo daga tafiya baka sosai ba."
Ya murmusa ya ce, "babu komai Abba. Riyya mu je na mayar daku gida, Abba mu je driver ya mayar daku."
Basu musa ba duk suka miƙe, suka shiga ɗakin da yake kwance suka ga an saka amsa ruwa yana shiga jikinsa.
Abba ya dafa kansa ya ce, "Allah ya baka lafiya Muhammad."
Mamy ta shafa kwantaccen gashinsa wanda ya zube akan pillow. Sai kuma ta saka hannu ta cire band ɗin da ta ɗaure gashinta, ta kama gashinsa ta ɗaure masa, sannan ta yi masa peck a goshi tana shafa bread ɗinsa.
Ta sake ajiyar zuciya ta ce, "Allah kar ya bawa maƙiyanka ikon ganin bayan ka, Allah ya cigaba da kare ka a duk inda ka ke Rehaan!."
Suka amsa da amin, Riyya ma ta ƙaraso ta yi pecking ɗinsa tana kuka.
Janan ma kuka take yi tana kallonsa a haka suka fito.
Lokacin da suka fito security guard guda biyu ne a ƙofar ɗakim, duk da asibitin na Rehaan ne, amma dole a saka masu kula dashi.
Mamy ta kalli Jafar da yake tafiya ta ce, "Jafar." Ya kalle ta ya ce, "Na'am Mamy."
"Barin guard ɗin nan babu damuwa? Ka ga fa babu kowa a wajansa, za a iya biyansu kuɗi su cutar dashi."
Abba ya yi murmushi yana girgiza kansa, wato in kana so ka ga wacce bata iya ɓoye son da take yiwa yaranta aka samu Mamy an gama.
Abba ya ce, "Nadira babu abinda zasu yi masa, akwai cctv a nan, babu wanda ya isa ya cutar dashi. Ki nutsu don Allah."
Ta sake kallon guard ɗin bata ce komai ba suka yi gaba. Abba da Mamy motar driver suka shiga, Juwariyya da Janan suka shiga motar Jafar.
Janan da Riyya dukkansu kuka suke yi, Jafar ya yi musu bai ce komai ba har suka je gida. Janan ta buɗe ta fita da gudu tana kuka.
Riyya zata buɗe ya riƙo hannunta ya ce, "Riyya!."
Kamar jira take ya yi mata magana, ta fashe da kuka mai sauti wanda ya fi na farko.
Ya sake riƙe hannunta sosai ya ce, "ki daina kuka Riyya, zai samu sauƙi in sha Allah."
Ta kalle sa da jar fuskarta ta ce, "Guba fa ya sha, guba aka zuba masa a abinda ni na yi making ɗinsa na kai masa da kaina."
Calmly ya ce, "ki nutsu! Babu abinda zai same shi."
"amma a cikin abinda na bashi aka bashi poison."
"Amma kowa ya san bake bace ba."
"Ku ne zaku ce haka, amma mutane da yawa zasu ce ni na bashi guba" ta faɗa hawaye yana sakkowa daga idonta.
"Kowa ya san ba ke bace ba Riyya, an yi amfani da damar da aka samu daga wajan ki ne shiyaasa haka. Amma ki daina kukan nan bana so."
Ta goge fuskar ta ta ce, "waye yake son kashe mana shi?."
"Kawai ki cigaba da taya shi da addu'a, in sha Allah komai zai zama daidai."
Ta yi ajiyar zuciya ta kalle shi ta ce, "Kar ka bar komai ya same shi, ka ji?."