Sawun Giwa

04

by @ammimalami99


~~

EL YAKOUB

Cikin iko na ubangiji ciwon kirjin nasa ya sauka bacci ya sace sa batareda ya samu damar gyara kwanciyarsa ba dan haka yayi baccin a zaune har lokacin tashinsa yayi. Wannan ne abunda ya haddasa masa ciwon wuyan da har lokacinda yayi shirin office ya wuto bai tafi ba, wani abu da ya saka yanayinsa na ranar gabaki daya ba dai dai yake ba. 

Shiyasa lokacinda Aisha ta bude kofar nan ta shigo da sallama ya kasa juya kai ya kalleta daga inda yake zaune saman doguwar kujerar nan dake tsakiyar office dinsa yayinda Habeeb yake zaune a kujerar dake kallon sa suna wani lissafi akan gine ginen da suke kokarin farawa. Habeeb ya daga kai ya kalleta yana amsa sallamar da tayi data samu nasarar isowa garesu dukda yanda tayita ahankali. 

Tsayawa kawai tayi ta rasa ma shin komawa zatayi sai sun gama koh kuwa tsayawa zatayi ta jirasa ya gama din. Habeeb da ya lura da hakan sai kawai yace mata 

"Karaso mana". 

Ta sauke numfashi dan tsakani da Allah wannan nervousness din data rabu dashi jiya sake dawowa yakeyi yana wanketa daga kai har kafa. Barinma yanda tagan sabon ogan nata koh dagowa baiyi ya kalleta ba sai kawai maganganun matan nan na jiya suka dawo kanta na cewar yanada tsauri. Toh koh dai yanada tsaurin dagaske tunda jiya a lokacinda ya fadi wannan maganar na addu'an Inna kadai ne taga gilmawar wani abu mai kama da murmushi a fuskarsa bayan wannan kuwa sam bazama ka kallesa ba kace yana murmushin koh kuma wani abu mai kama dashi. Ta tako kafarta ciki kuma saida ta iso daidai katon carpet dinnan tukunna ta tsaya ta gaishe su. 

Habeeb wanda taga alamar yana da raha kadai ne ya amsata yana mata sannu da zuwa kuma bai karasa kokarin nuna mata wajen zaman da yakeyi ba ta jiyo wannan muryar ta El Yakoub yana fadan wasu kalaman da batayi tsammanin zuwansu ba koh kadan. 

"I'll need your email Aisha". ( Zan bukaci email dinki Aisha )

Maganar tasa ta rudar da ita lokaci daya dan sai da taji zuciyarta ta sake wannan kakkarwar data shigo dashi kafin ta baiwa kanta kwarin gwiwar kai idanunwanta kansa inda yake zaune cikin farar rigar suit dinsa da ya nannade hannunta yatsun hanunsa na rike da wani biro da ya koma d'an karami acikin nasa hannun mai fadi. 

"Na'am" Ta samu nasarar furtawa dan duk cikin maganar da yayi ita kalmar sunanta kadai ta fahimta aciki. 

Habeeb yagan yanda ta rude lokaci daya kafin ya d'an murmusa ahankali dan dama yasani yarinyar nan zata sha wahalar aiki da Saraki tun farko. In dai ba wai ta jajirce bane ba lallai su ji dadin aiki da juna ba. 

"Yana nufin kije ki saka masa email dinki a na'urarsa". 

Ya fada yana daga hannunsa ya nuna mata teburin El Yakoub din dake chan karshen dakin. Ta gyada kanta alamar ta fahimta wani nauyi na zagaye kirjinta bayan ta sake satar kallon El Yakoub dinda ke zaune har a lokacin idanuwansa na bin layin rubutun takardar dake hannunsa. Teburin nasa ta karasa, ta zagaya wajen kujerarsa kamshin turaren rigarsa dake rataye a wajen ya daki hancinta yana kwantar da hargitsin dake faruwa a cikin kwanyar ta. Na'urar a kunne take kuma sai bayan ta daga hannunta ta dorasa a mouse dinnan tana kokarin nemo inda email din nasa yake tukunna ta lura cewa hannunta kakkarwa yakeyi. Sai kawai ta lumshe idanuwanta ahankali tana fitar da iska ta bakinta tana tunatar da kanta cewa wannan fargabar fa ba zata kaita ko'ina ba saidai ma ta tayata bata al'amura dan haka dole ta ajiye komai gefe ta fuskanci aikin nan. Wannan ne abunda ya taimaka mata ta samu natsuwar da ta bata damar shiga email din nasa ta shigar da nata ta bar masa shi a wajen yanda idan yazo kawai zai tura mata abunda zai tura mata koh ya barshi a drafts har zuwa lokacinda zai bukace sa. 

Ta dawo wajen Habeeb yana nuna mata wajen zama a kan doguwar kujerar da El Yakoub yake zaune dan kujerar dake kusa da Habeeb din tulin takardun da ya shigo dasu ne dan hatta teburin dake tsakiyar su wasu takardun ne tareda na'urar El Yakoub din. Ta zauna ahankali tana dora jakarta a kafafuwanta da take jinsu kamar hanjin ligidi. Mintina kusan biyar suka wuce Habeeb na yi masa wasu bayanan shikuma yana basa amsa kai tsaye wanda acikin wannan maganar tasu ce ta tsinci sunan da Habeeb din yake kiransa dashi wato 'Saraki'. Ta maimaita sunan a ranta tana shaida cewar yayi kama da sarakin koh a gaske. Toh ko dai yana da hadi da sarautar ne bata sani ba. A cikin wannan tunane tunanen nata ne Habeeb ya juyo gareta ya fara mata bayanin yadda aikin nata zai kasance. Ya fada mata dukkan wasu abubuwan da zata fara yi da yanda zata gudanar da komai. Kuma sai alokacin itama ta sake jinjina cewar aikin babba ne kamar yaddda Nurse Hadiza ta fada tun farko dan har binsa zata ringa yi idan zaije site inspection. Abubuwan dayawa dan har saida ta kusa bacewa a lissafin. 

Habeeb din yace mata akwai komai a office dinta duk abunda take bukata zata iya yiwa El Yakoub magana ayi mata providing. Yanxu ta tashi taje ta shigar da email dinta a desktop dinta za'a turo mata da aikin da zata fara dashi yanxu. Tayi masa godiya ta mike ahankali ta fice batareda ta sake kallon sashen ogan nata ba wanda duk a wannan lokacin da Habeeb ke mata bayanan nan yana zaune ne kawai yana karance karance da danne dannensa. 

Sai bayan kofar ta rufe a bayanta tukunna ta samu sararin sakin numfashi tana jinjina yawan aikin. Motsin data ji ne ya fargar da ita ta dago ganinta zuwa ga wata kofa dake a bude wadda sam koh a zuwanta jiya bata lura da ita ba. Wata mata ta fito daga cikin bandakin da wani bokiti a hannunta na shara tana rufo kofar itama kuma sai a lokacin ta lura da Aishar. 

"Sannu Hajiya" matar ta gaisheta. 

Kalmar Hajiyan nan tayiwa Aisha nauyi dan ko da lalube ka lalaba kasan cewa matar ta haifi Aishar. Ta gaisheda matar suka gaisa cikin mutuntawa kafin matar tatafi ita kuwa taja kujerarta ta zauna da bisimillah tana sake karanto addu'oi kafin ta kunna komai tayi setting up email dinta. Mintina uku basu cika ba kuwa tagan tulin files dinda ya turo mata yace ta mai sorting shikenan ta hau aiki. Aikin da har yanxu da awanni biyu suka wuce bata samu gamasa ba. 

Ita rubutun keyboard dinne ma yafi wahalar da ita dan abune da bata saba dashi ba, rabonta da amfani da computer ma ai tun tana makaranta wannan shine dalilin da ya saka aikin ya dauketa lokaci sosai kafin ta gama ta tura masa ta fara na biyun da ya aiko mata. Sha daya da kusan mintina goma kofar office dinsa ta bude, ta dago kanta daga inda take zaune idanuwanta suka sauka cikin nasa. 

Yayi saurin dauke idonsa daga kanta yana gyara rigar suit dinda ke jikinsa. Aisha itama ta yakice idonda daga kansa kafin ta tura kujerarta ahankali ta mike saboda dama Habeeb ya gaya mata akwai meeting dinda za'ayi karfe sha daya da duka staff din kamfanin. Doguwar rigar material ce a jikinta launin green mai duhu data bude daga waist dinta zuwa kasa dan kusan duka kayakinsu haka suke a bude ba wadda za'a dauko ace ta kame. Sai gyalen datayi rolling dinsa jersey scarf cream mai laushi. Kayan sun matukar karbarta idanuwanta suna sake fitowa saboda zanen layin kwallin data saka wanda shi kadai ne a fuskarta bayan Vaseline dinda ta shafa a fuskar dan hatta labbanta mantawa tayi bata shafa musu shi ba. 

Ta bi bayansa lokacinda ya fice daga office din suka sauka kasa zuwa second floor dan har yanxu ba'a kammala elevator ba Ayo na biyo bayansu. Koh da suka isa katon hall din kusan kowa ya hallara dan hatta cleaners din kamfanin saida aka tattaro su dan El Yakoub cewa yayi meeting din na kowa da kowa ne da ya kasance ma'aikaci. Habeeb ne ya gabatar da kansa matsayin babban mataimakin mai kamfanin wato chief operating officer ( COO ). Yayi karamin jawabi akan yanda tsarin aikin zai tafi da yanda sukeso kowa yayi kokari sosai ya jajirce wajen aikinsa da dai sauransu kafin ya mika abin maganar ga El Yakoub. Aisha tana tsaye a gefensa lokacinda ya mike tsaye daga kan kujerar da aka basa bayan ya shigo. Yayi y'ar karamar gyaran murya kafin ya fara magana bayan ya kashe abin maganar ya ajiye alamar dake nuna bazaiyi amfani dashi ba kenan. Kuma yadda muryarsa mai zurfi ta fara zagaye hall din da yayi tsit lokacinda ya mike tsaye ya saka Aisha gyara tsayuwarta batareda ta shirya ba. 

Cikin natsuwa yake magana yana karawa kan maganar da Habeeb din yayi na bukatar kowa yayi kokari wajen badda himma a aikinsa. Sannan duk idan sunada wata matsala kada su ji kyashin gabatar da ita ga na gaba dasu. Yayinda kowa ke mamakin ganinsa a matsayin mai kamfanin sabanin yanda sukaji a labari Aisha nata tananin ya ta'allaka ne a karamcin da El Yakoub ya nunawa ma'aikatansa. Yanda ya saka aka tattara kowa da kowa har cleaners ya kuma yi addressing dinsu matsayin abu daya batareda ya banbance ba tunda dukkaninsu suna aiki a karkashinsa ne abun ya burgeta matuka da gaske. 

Ta dago kanta tana karewa y'an hall din kallo daga inda take tsaye kafin su sauka kan wa'ennan y'an matan guda biyu da taji suna maganarsa jiya lokacinda tazo interview dinta. Wani murmushi ya kubuce a bakinta sanda tagan yanda suka zare ido da baki suna kallon El Yakoub wanda jiyan jiyan nan suka gama gulmar cewa tsoho ne ya haura hamsin. Matan nan sun bata dariya sosai har bata san sanda ta saki y'ar siririyar dariya ba lokacinda suka fito daga hall din bayan an kammala meeting din suna haurawa sama. Dariyar ta shiga kunnen El Yakoub lokaci daya dan ita kanta da tayita bata san cewa zata fito da sauti bane. 

Ayo ta juyo ta kalli Aisha tana dage mata gira daya alamar tambaya. Sai kawai ta girgiza kanta tana saita kanta sanin cewa El Yakoub ya jita. Dole zai jita mana yanxu da suke gab da gab dan ta riga ta gama sanin wannan kunnen maciji garesa dan idan ba kunnen maciji ba ta rasa yadda za'ayi ace yaji wayar da tayi da Inna jiya. Allah sa kar yayi tunani da shi take ta fada a ranta kuma addu'ar tata ta karbu dan shi sabanin son sanin dalilin dariyar tata yadda dadin sautin dariyar yake kawai ya jinjina a ransa. 

Sukayi sallama da Ayo ta shige office dinta inda ta iske dogayen kafafuwansa har sun shige dashi nasa office din ta zauna ta cigaba da aikinta kuma batayi mintina goma ba tagan ya sake fitowa wannan karon ya tube jacket din suit din ya sake tattare hannayen rigar. Ya nufi wajen counter dinnan kafin ya bude cupboard yana fito da kofi. Dama tunda ta kallesa bayan ya fito ta dauke idonta sai dai kiran sunanta da yayi ne ya saka ba shiri ta sake dago idanuwan nata ta saukesu a bayan sa zuciyarta na kakkarwar jin yanda ya fadi sunan. 

"Aisha" muryarsa ta ratsa tazarar dake tsakaninsu. 

"Sir" Ta amsa sa. 

"Come here" 

Maganar ta daketa irin sosai dinnan dan har sai da taji cikinta ya d'an murda. Ta tura kujerarta kan ta mike ta taka zuwa inda yake tsaye ta tsaya dai dai lokacinda yake dibar koren garin matcha yana zubawa cikin wani karamin kofin da ya dakko. Baice mata komai ba, ita ma kuma bata ce komai ba kawai tayi tsaye tana jiran ya bata wani umarnin koh ya sakata wani aikin. Ya tara kofin gaban dispenser ya zuba ruwa mai dumi kafin ya sake mika dogon hannunsa cikin cupboard din ya dakko karamin whisk. Ta zubawa hannunsa ido yanda yake jujjuya whisk din. Fatar sa ja ce sosai kamar ka danna jini ya fito. Hannayensa manya ne kuma karfafa dan har wasu layin jijiyoyi ne kwance samansu. Ta d'an dauke idonta da sauri ta kalli gefe kafin ta sake juyawa lokacinda yake juye hadin da yayi cikin babban kofinsa. Ya sake tara sa kankara na zubowa kafin ya bude fridge ya fitoda madara mai sanyi ya zuba a ciki ya mayar. 

Sai da ya gama tukunna ya dago ya kalleta kuma sai da ya tabbatar itama ta dago ta kallesan tukunna yace 

"Kinga yanda na hada ai koh?"

Aisha ta gyada kanta tana maida dubanta kan kofin dake hannunsa inda koren matchan yake hadewa da farar madarar da ya zuba. 

"Good, I'll need you to make this for me everyday at 11".  

Ya fada yana cigaba da kallon karamar fuskarta da sai yanxu yake samun damar kare mata kallo gabaki daya dan tana tsaye a gefensa ne lokacinda ya juyo hakanne ya saka suke fuskantar juna. 

"Okay sir". Siririyar muryarta ta fito tana shiga kunnensa. 

Sai kawai ya gyada kansa ya bi ta gefenta ya tura kofarsa ya shiga da matchar a hannunsa. Ta dauki kayan da yayi amfani dasu ta dauraye ta mayar kan ta koma mazauninta ta cigaba da aikinta. Lokacin sallahr azahar yayi ta shiga bandakin nan da komai yake fes fes tayi alwala a ranta tana tunanin inda zata samu darduma tayi sallah. Ba halin tambayar Ayo tunda ba musulma bace. Tayi tunanin tambayarsa amma duk yanda ta ringa fadawa kanta tura kofar kawai zatayi ta shiga kasawa tayi sai kawai ta fito waje taje wajen Ayo ta tambayeta ina zata samu abin sallah. Ayo na kokarin bata amsa Habeeb yana fitowa daga wata kofa dake wajen wadda ashe nanne office dinsa. Da murmushi yake tambayeta idan akwai wata matsala sai take ce masa abin sallah take nema. Yace mata ta shiga office dinsa ta tambayi secretary zai bata. Ta masa godiya kafin ta nufi kofar ta tura ta shiga da sallama. Office din sak nata hatta da su fridge da cupboard dinnan duk akwai. Suka gaisa da Ameer ta fada masa abunda ya kawota. Ya bata dardumar ya kuma nuna mata inda zata kalla. Ta masa godiya ta wuto zuwa nata office din inda ta shimfida dardumar ta gabatar da sallahrta. 

Ta gama ta ninke ta ajiye kafin ta cigaba da aikinta wanda El Yakoub sai lodo mata su yakeyi dan duk ayyukan da ba'ayi masa bane kwana biyu saboda rashin secretary yake tuttura mata. Bata jima da farawa ba telephone dinda ke jikin teburinta ta dauki kara. Zuciyarta ta harba lokaci daya dan bata san mai kiran ba. Shin shine koh kuwa a'a wani babba ne daga cikin kamfanin. Da bisimillah ta dauka ta dora wayar a kunnenta sai taji ashe ma Ayo ce. Suka gaisa take ce mata lunch break dinsu ne fa yanxu idan tanaso tazo suje su siya abinci a waje. 

Tace mata toh gata nan zuwa dan sai karfe biyar zasu tashi kuma tasan ma koh bataji yunwa yanxu ba zataji anjima. Ta dauki y'ar purse dinta ta fito suka sauka kasa itada Ayo suna d'an hiran aikin. Saida suka shiga keke sukayi tafiyan kusan mintina biyar kafin suka iso wani wajen siyarda abinci. Tsabtar wajen ya saka Aisha ta iya sayen shinkafar su tace a saka mata kifi guda biyu ta kaiwa Khausar dan Allah ya dora mata son kifi kafin suka dawo. 

Haka dai ranar ta kare a aiki dan bata samu cin abincin ba ma sai can kusan la'asar. Tayi sallah ta mayarwa Ameer dardumarsa tukunna ta dawo ta karasa aikinta. Tun kafin biyar ta gama aikin da ya bata ta zauna jimm taga koh zai sake bata wani aiki koh ya kirata amma shiru. Shiyasa biyar din tanayi ta dauki jakarta kafin ta karasa kofarsa ta kwankwasa ta tura ta shiga. 

Yana tsaye ne gaban katuwar shelf dinnan wani file a hannunsa yana dubawa. Da farko ya dauka Habeeb ne shiyasa ma bai dago ba sai da ya jiyo siriririyar muryar nan ta Aisha tana cewa 

"Zan wuce sir" tukunna ya juyo kansa ya kalleta da yanda tayi tsaye dab da kujerar nan ta rike jakarta dake rataye a kafadarta da hannyenta biyu idanuwanta akansa. 

"Okay" ya furta mata kawai ya juya yana cigaba da aikin da yakeyi. 

Ta jinjina kai itama ta fice tana hamdala ga Allah da ya nuna mata karewa lafiya yau dinnan. Tayi sallama da Ayo dake kokarin tattara nata kayan itama dan anguwarsu ma ba hanya daya bace. Gida straight keken ta ajiye ta. Ta mika masa kudinsa ta shiga ciki da sallama dan bata ma tsaya kofar dakin Mallam ba tunda tasan baya nan kasancewar yana fita la'asar baya dawowa sai bayan Isha dan mafi yawanci ma a can ake kai masa abincin dare acan wata katuwar rumfa da akayi gefen masallaci inda manyan malaman ke zama da kuma tsofaffin y'an anguwa. 

Juwaira ta iske a kitchen ta dora tuwon alkama saboda Inna ke da girki har a ranar ma tunda kwanaki biyu biyu sukeyi. 

"Ma'aikaciyar ofishi ce ta dawo kenan" 

Juwairar ke tsokananta lokacinda ta karaso kofar kitchen din ta tsaya. 

Aisha tayi dariya tace "Ke kika san ma'aikaciyar ofishi hannuna gabaki daya a kage yake" ta karasa tana lankwasa tsintsiyar hannunta. 

Juwaira tace "Sannu, zaki saba ai in sha Allah"

"Allah yasa"

"Ki shafa man zafin Inna anjima zai daina". 

Aisha ta gyada kanta kafin ta waiga kofar dakin Maman Nana data gani a rufe tace 

"Ya naji gidan shiru ne". 

Juwaira na fififita wutar murhun tace 

"Sunje makota dubiya Hajiya Zulai ce ta zame a bandaki har asibiti aka kaita aka mata hoton baya". 

"Subhanallahi garin yaya" 

"Wallahi bansani ba mu ma dazu da Asma'u ta shigo take fada mana shine fa su Inna suka tafi dubiyarta". 

Aisha ta girgiza kai "Kai toh Allah ya kawo sauki ya kuma kiyaye gaba". 

"Ameen". 

Ta karasa dakin Inna ta ajiye jakarta batareda tabi takan wayarta ba dake ta hasken shigowar kiran Mu'azzam kasancewar tun a office ta sakata silent. Ta tube rigarta ta shanya ta jikin kofar durowar su kafin ta saka wata riga y'ar kanti ta zaman gida mai fadi ta fito zuwa kitchen tana taya Juwaira girkin sunayi tana bata labarin tulin ayyukan da tayi yau. Sai dab da maghriba su Inna suka dawo Khausar ta leko kitchen din tana gaisheda Aishan. 

"Jiki yayi sauki kenan" Aisha ta fada. 

Khausar ta tsugunna gaban kofar tana baiwa Aisha labarin da Asma'u jikar Hajiya Zulai ta bata akan makaranta tunda makarantar su d'aya kafin ta jiyo Inna na fadan ba ta hanata tsugunnen bakin kofa ba da maghariba su kuwa su Aishan sun zuba mata ido suna kallonta bazasu mata magana ta tashi ba koh. Khausar na ture turen baki ta mike zuwa daki. Bata jima ba kuma ta fito zuwa alwala suma kuma duk sukayi alwalar sukayi sallah nan waje inda suka shimfida babbar tabarmar su dan dama a wajen suke zama a irin wannan lokacin in dai babu wutar Nepa. Suna hirarsu karar kukan raguna da kajin Mallam na taya su. Saida suka gama abincin tukunna aka zubowa kowa suka zauna suka ci Aisha na baiwa Khausar kifin data siyo mata. Khausar dadi harda rungume Aisha. 

A irin wannan lokacin Maman Nana tana zaune ne a wajen tare dasu amma sai lokacinda Juwaira ta kai mata tata kular abincin tace kanta ke ciwo hutawa takeyi. Sukam suna zaune waje abunsu suna hirarsu har lokacin Isha. Suna gama Isha Inna tace Aisha taje ta kaiwa Mallam abincinsa. Dama wani sa'in Khausar ake aika amma sai ta lafe wai ita batajin dadi Aisha ta girgiza kai kawai dan son jikin khausar din dama yawa ne dashi. Bata chanja hijabin sallahrta ba ta dauki abincin ta fita. Tafiya ce kadan zuwa wajen. Taje ta kai masa kafin ta juyo zuwa gida iskar daren mai dadi tana kada hijabinta. 

Tun daga nesa ta hango motar Mu'azzam dake pake gaban gidansu. Taji ranta ya baci lokaci guda ganin yanda yayi wani tsaye gefen motar yana danna wayar dake hannunsa hasken screen din yana haske kyakkyawar fuskarsa. Wato wayar tasa ma na hannunsa kawai kashe ta yayi koh. Tana isowa wajen kuwa tayi kamar bata san da zaman sa a wajen ba tayi hanyar cikin gida. Mu'azzam na ganinta ya mayar da wayar aljihu kafin ya d'an tako da sauri yasha gabanta mayen turarensa na shigar mata hanci lokaci daya. 

"Haba babe" Ya furta ahankali cikin muryar nan tasa da Aisha bata son ji idan ranta ya baci dan duk yanda zaiyi ya sakko da ita yasani. Saidai a yanda zuciyarta ke tafarfasa bata tunanin akwai wani salonsa da zaisa ta sakko yau. 

Ta gifta ta gefensa zata wuce ya sake shan gabanta. 

"Please mana ki tsaya ki saurareni". 

Sai a lokacin ta dago ta kallesa kuma dama abunda yakeso kenan dan lokaci daya ya narke mata da kyakkyawar fuskar nan tasa kafin ya hade hannayensa waje daya alamar roko. 

"Please please my love, kinsan ni banason wannan fushin naki ai" 

Ya cigaba da fada yana murza hannayensa. Aisha ta kautar da kanta gefe wani hucin takaici na fita bakinta. Ya sake juyowa gefen data matsar da kan nata 

"Kiyi hakuri please". 

"Wani excuse kuma kazo dashi wannan karon" 

Ta fada garesa muryarta ba alamar wasa a cikinta kwata kwata. Mu'azzam yaji sanyin iskar dake kadawa na kama kafafuwansa dan baya tunanin ya taba ganin fushin Aisha haka. 

"Babe kinaji sace mun waya akayi wallahi". 

Aisha ta jinjina kanta tana cije lebenta na kasa. 

"And so" ta furta. 

Girar Mu'azzam ta tattare waje daya cikin mamakin jin abunda ta fada. Wai koh dai an sauya mai Aishansa ne. Allah ya gani yana son yarinyar nan har cikin zuciyarsa. Dan tun gani na farko da ya mata a wani bikin kawarsu ya karbi numberta wajen amaryar. Haka kawai yaji  ta kwanta masa a rai shiyasa yayi yanda zaiyi ya karkato hankalinta garesa duk yawo da hankalin data ringa masa da farko. Yes yasani akwai abubuwa da dama gameda rayuwarsa da Aisha bata kaiga sani ba, baya fata kuma ta taba sanin su har izuwa lokacinda zai gama karantunsa suyi aurensu kamar yanda ya tsara a ransa kenan. 
Shiyasa duk yanda zaiyi ya bata hakuri ta sakko idan ya bace mata na kwanaki tana nemansa yi yakeyi. Dan a yanda yakejinta a ransa koh cewa tayi ya yita mulmula a kasa ne yana bata hakuri Allah zaiyi. 

"Ban siya wani ba sai yau babe". 

Ya fada yana fitoda wayar daga aljihunsa ya nuna mata. Sabuwar ce kamar yanda ya fada din. Sai kawai Aisha ta budi baki ta fara amayo mai abubuwan dake ranta wanda in sun tabasa ma toh kamar yanda mutum yake daga hannunsa a iska ne batareda ya tabo komai ba. Ya ringa jera mata ban hakuri da tsararrun kalamai wanda suka saka dole bayan sun jima a wajen ta hakura. Shima yasan bata gama sakkowa bane dan yasan halin kayarsa. Zai bita a sannu ne har zuwa lokacinda zata sakko. 

Ta basa labarin aikin data samu ya tayata murna sosai kuma suna tsaye a wajen Khausar ta leko kanta daga kofar gidan dan Inna ce ta aiko ta kan cewa tazo ta leko Aishar tunda tun dazu ta fita bata dawo ba. Shima kuma dama da yazo yanata kiran Aishan bata dauka ba kuma bai samu yaron da zai tura cikin gidan ba lokacinda tazo wucewa shiyasa y'an cikin gidan basu san da zuwansa ba. 

Yayiwa Khausar alama da tazo. Ta fito din kuwa tana gyara zaman dankwalin dake kanta data yafo na Inna. Ta gaishesa yanai mata ya jiki tunda Aishar ta gaya masa ai Khausar din ta kwanta jiya ma aka sallamo su. Ya bude motarsa ya baiwa Khausar ledar siyen siyen da yayiwa Aisha kan hanyarsa na zuwa. Ta karba da godiya ta shiga dasu ciki. Itama Aishar bata jima ba sukayi sallama. 

Ta iske ledar a kan tabarma inda Khausar ta ajiyeta bayan tayi tayi Inna ta bari ta bude tace bazata bude ba tunda ba ita aka kawowa ba. Har Khausar din ke cewa ai ita ya baiwa Inna tace tagan hannunta a ledar sai ta kwade ta tukunna tayi shiru tana Allah Allah Aishar ta shigo su bude ledar dan duk lokacinda Mu'azzam ya kawowa Aishar wani abu toh abun dadi ne.

"Allah yayi yazo kenan" Juwaira ta fada ga Aishar data tube hijabinta ta zauna tana nadesa. 

"Eh wai wayarsa ta lallace"

"Kuma bai samu wata ya kiraki da ita har tsawon kwanaki uku koh kuma yazo?" Juwaira ta sake aiko mata wata tambayar. 

Inna ta tabe baki tana saurarensu dan ita Allah ya gani Mu'azzam dinnan ba wani kwanta mata yayi a rai ba. A takaice ma Aisha bata taba wani saurayin da Inna taji ya kwanta mata ba kwata kwata musamman wannan Mu'azzam din data rasa ina ma alqiblarsa take. 

"Ke tashi dakko mun radio na" 

Ta fada taba bubbuga kafadar Khausar datayi matashi ta kafafuwanta. 

Khausar tace "Inna toh ki bari ta bude ledar mugani". 

"Banace kar na sake jin maganar ledar nan ba" 

Inna ta fada tana bubbuga kafarta wanda ya saka ba shiri Khausar din ta mike tsaye ta shige daki tana laluben mirrorn Inna inda ake ajiye radion dan koh fitilar da Juwaira ke miko mata bata karba ba. Ta mikawa Inna radion lokacinda Aisha ta bude ledar kuma kamar yanda Khausar tayi tunani Ice cream ne na FanIce babbar roba guda biyu tareda tulin chakulet da kayan kwalama. Khausar kunne har baki dan da gudu taje ta dakko spoons ta kawo musu suka d'an tattaba kafin Aisha ta dauki dayar robar ta saka a fridge din Maman Nana.

Inna dai kin sha tayi dan Allah na tuba me zatayi da wani Ice Cream. Allah dai ya zabawa Aishar mafi alkhairi ita shine add'uarta. Ta kunna radionta suka fara sauraren labaransu anayi ana taba hira yayinda Maman Nana ke zaune dakinta zuciyarta na tafarfarsa da hassadar da bata san yaushe ta girgije ta zama katuwar bishiya ba a cikin zuciyarta. 
Aisha ta kasa ta tsare, haba. Ya za'ayi ace ga aikin kamfani ga kuma saurayi mai mota da kuma abin hannunsa tunda dukda dai bai gama makaranta ba ai iyayen nasa nada rufin asiri tunda gashi har mota garesa yayinda ita kuma tata y'ar tana can tana yawon ta zubar. Ina dole ne tasan yadda zata bullowa wannan al'amari dan wallahi bazata bari Aisha tayi gaba ta bar y'arta a baya ba. 

Na nawa kuma jama'aaa????


Sawun Giwa
Ammi Malami🌸