Namiji Ƙanin Ajali (Book 01)

Chapter --- 16

by @amdeeytejjdunique587

Bismillahir Rahmanir Raheem.







*Namiji Ƙanin Ajali*










Written By

Amdeey Tejj d'Unique.










Page 16️⃣.






Ina wannan karatun zucin ne na iso gidan,kai tsaye ƙofar Inna Lami na wuce dan na ɗauki abinci na,dan koda Wasila ta bani abinci banci ba,na tarar Layla har tayi bacci,Husna ne ke cin tuwo da ƙarago kamar yadda ta saba, Inna Lami ne tace''Layla tayi bacci ta gama rigima kenan ita baza taci tuwo ba sai madara zata sha, Malam ya ba Mustapha kuɗi ya siyo mata,ta gama sha kenan ta ɓungure sai bacci gata can''tayi maganar tana nuna min inda Laylan take,ɗan murmushin da iyakansa laɓɓana nayi kawai bance komai ba na shige ɗakinta na ɗau kula na fito,Husna ta maƙale sai ta bi ni,na ɗauke ta muka wuce.

Ban samu shi uban  gayyar a ɗakin ba, sai dadduma a shimfiɗe alamar yayi sallah kenan bai daɗe da fita ba,na ayyana,na ajiye Husna na fita waje tattare kayayyakin da na tafi na bari ɗazu,da na gama na koma ciki naci nawa abincin dan banci komai ba a gidan Wasila,tayi min tayi naƙi ci,na gyara ma Husna jikin ta na sa mata pampas na kwantar da ita,bata jima tayi bacci nima har ya fara ɗaukata naji maganar Bature a kaina"ki tashi ki tafi gidan ku''naji ya furta yana haurin ƙafata da tasa ƙafar.

A hankali na na buɗe idona na miƙe a nutse dan bana son hayaniya ya tada min yarinya,kafin nace"a matsayin me zanje gidan mu?,ka sake ko yaya?, idan ba haka ba kaima kasan na gaya maka babu batun yaji a lamari na, idan gidan mu kake so inje,kafi kowa sanin abin da ya dace kayi, amma ni bazan je bansan matsayina ba"ina gama faɗin hakan na juya nayi kwanciya ta ban sake bi takan shi ba,ban san yaya ƙarasa ba,nidai na farka da asuba ban ganshi a inda na barshi tsaye ba,naso tashi sallar dare amma bacci yayi gaba dani sai asuba na farka.








Bayan ɗan ayyukana na safe kamar yadda na saba na shirya Layla ta tafi makaranta,jiran wankin Sa'idu nakeyi wani yaron anguwar da ya min magana tun jiya nace ya kawo yau, amma har yanzu bai kawo ba,sallamar Imrana naji ina kwance daga bakin ƙofar ɗaki,na amsa ya gaisheni na amsa sannan nace"Imrana ya akayi ina ka fito?''

"Daga gida nake yaya, umma ce tace nazo na kiraki''ya bani amsa

"Umman ce tace ka kira ni?,amma lafiya?,ko jikinta ne?"na tambaye shi a rikice,dan iya abun da yazo kaina kenan.

"A a ba jikin bane, jiki kam yana nan yadda kika sani,yaya Bature ne yaje suka yi magana,sai ta fito tace inzo in kira ki"

"Ƙarata yakai kenan,wato dan ba mahaifiyarsa bace,shiyasa yakai mata ƙara dan ya ɗaga mata hankali duk da yasan halin da take ciki"

"Kun samu matsala ne?"Imrana ya tambaya 

"Eh"nan gaya mai komai,dan cikin ƴan uwana bayan yaya Asma'u mai rasuwa, Imrana ne kawai nake faɗa mai damuwata, saboda yana da kyakkyawar fahimta, duk da yana da ƙarancin shekaru amma akwai hikima da hangen nesa,ga hankali.

''Imrana hakuri na ya ƙare,bari inje sai ya faɗa min dalilin da yasa yaje yake son ɗagawa mahaifiyata hankali bayan yasan halin da take ciki”

Da sauri Imrana ya riƙo hannu na"haba yaya Halima,ina hankalinki yaje ne?,yanzu kema kina zuwa a haka mai zakiyi bayan sake ɗaga mata hankalin, yanzu ina da tabbacin komai gaskiyar ki umma laifinki take gani,dan ba baki gaskiya zatayi ba, balle kuma kinje a haka, idan shi bai san darajar ta ba ai ke kin sani"

Nayi murmushi ina jinjina kaifin basira irin na shi, addu'ar alkhairi na mai a raina sannan nace"muje"kawai daga haka muka fice.

Muna isa umma bata tsaya saurare na ba ta hauni da faɗa,inda take shiga ba nan take fita ba faɗa kawai take yi, dama kuma umma akwai faɗa kamar jira takeyi ace ga laifin ka,ni tausayi ma ta bani,yayin da wutar tsanar Bature ke ƙara ruruwa a raina,duba da bata da lafiya amma bai ko yi duba da hakan ba yazo ya sata tana ta maganar da nasan ƙarshe sai ciwon ya tashi,ko da ta gama faɗan ta haƙuri kawai na basu,a raina ina ta addu'ar Allah yasa kada tace na ba Sabuwa haƙuri,sai dai zaren tunanin nawa bai gama war-warewa ba naji tana bani umarnin na ba sabuwa haƙuri, abin ya min ciwo amma ko a fuska ban nuna ba bare naci musu dan nasan ko nayi hakan ma ba aiki zaiyi ba,nasan tunda tayi wannan magana to umarni ne, bayan ta gama faɗa tayi mana nasiha sannan tace mu tashi mu tafi,ni kuma kafin na shiga gida na fara shiga na ba Sabuwa haƙuri,da haka muka fito raina ba daɗi.

Kamar yadda ta umurce ni ban shiga gida ba sai da naje na ba Sabuwa haƙuri.

Nan zaman ya sake caɓewa tsakanina da shi,a wannan karon bai hana mu abinci ba,zai bayar amma ganin damar shi dan shi kansa yasan kuɗin da yake bayarwa ko kusa bazasu isa ba,haka dai nake karɓa in cika inyi kuma insa mishi yaci har da neman ɗumame,ban damu ba,ba haƙuri ake cewa nayi ba,to ina kai Allah ya bani wuyan ɗauka,in kuma shine silar kawo ƙarshen numfashi na Allah yasa in cika da imani,ita kuwa Sabuwa kamar ƴar gwamnar jahar data lashe zaɓe,sai yayatawa takeyi a unguwa ta karya alƙadarina,ta kau da jijji da kan da nake ji dashi,ai har gida naje bata haƙuri da kyar ta yafe ma,har kuka sai da nayi,kai kace sarkine yaba bafaje haƙuri,duk maganar da takeyi na dawowa kunne na, amma ko in daga kai in kalleta,Ni Wallahi dariya ma take bani wani lokaci kuma mamaki har cewa nake kodai dama tana ƙullace dani ne akan abin da bansan meye ba.


Ranar ina kwance daga bakin ƙofa karatu littafi nakeyi wanda jiya na karɓo haya a wani shagon da ake renting ɗin Novel,ban cika karɓa haya ba nafi saya, saboda wani idan yamin daɗi sosai na kan sake karantawa,ina karatun inajin hirarrakin su Hassana da sukeyi a bakin ƙofarta,a hirar tasu ce naji an kira sunana hakan yasa na tsaya da abun da nake yi ina sauransu inji me zasu ce,nasan ba su san ina nan ba,ko kuma suna tunanin bacci nakeyi,dan na tura ƙofar ɗakin kamar yadda na saba,kuma takalmana ma suna ciki akan wani tsumma daga bakin ƙofa, idan nayi hakan akan ɗauka bana gidan,dan idan banga dama ko zasu ɗaga gidan da masifa idan bom ɗin gulmar su ta fashe,ko leƙe daga ɗaki banayi balle ya dameni,dama ni sam ban iya leƙe ba,sai idan na fito wacca gulmar ke cinta a ƙasanta tazo ta bani labari, idan nasan bata san sanda na fito daga ɗaki ba nace ai bana nan ne,maganar da naji Lantana tanayi yasa na aje wannan tunanin ina saurarensu dan tunda suke hirar su ban mai da hankali wajen ba dan ba damuwa ta bane, idan zaki samin wuƙa a wuya bazan ɗorar da kanun labari ɗaya daga cikin wanda sukayi ba.

''sai kuma kuka ji Halima tayi bakam,duk maganganun da Sabuwa takeyi tayi gum kamar bata nan''cewar Lantana

''Nima dai abun ya dame ni,nace to dama ta raina Ladiyo ne kenan? ko kuma kurwar Sabuwar ce ta danne Tata?''naji muryar Reashida wata maƙociyarmu

"A a fah,muyi maganar gaskiya,dan ni tsegumi na kawai ake kallo ba a duba da akan gaskiya nake magana wani lokaci''dariya suka kwashe da
a tare suka haɗa baki wajen faɗin''Hassana kece mai faɗar gskyr?''

''Bansan iskanci dama maƙaryaciya kuka ɗaukeni,to yanzu ma gskyr zan faɗa dan wallahi kuma kunsan kaf unguwar nan da kewayenta,ba wanda bai san Halima bata faɗa akan ɗanta, asali ma idan faɗa ya haɗa ɗanka da yaranta, dukansu take haɗawa tayi musu hukunci bayan ta gama ta basu alawa,kaf unguwar nan ba me yin haka tun daga mu yara har manyan mu,kowa ana taɓa mata ɗa ko jika kamar jira take zata hau tijara,ni na sani bana wajen abun ya faru amma nasan taga an zalunci da akayiwa yaranta yayi yawa ne yasa tayi magana dan kar a ɗauka tsoro ne,kuma kowa yasan ba wadda Halima take shayinta a unguwar nan, sabuwa kuma kowa yasanta da faɗan rashin gaskiya musamman akan wannan mummunar jikar tata mai kama da jinjirar jaki''sukayi dariya gaba ɗaya

Rashida tace''ai ni wallahi banso faɗan ya tsaya a haka ba,na so ai ta cin uwar sabada''

''To ai kinsanta da dakar kunne,kamar jinjirar da aka haifa kan kunne''cewar Lantana.

Hassana tace''to ai ko Ladiyo ma ba a farkon farin yi ne ta kulata ba,sai da ta kaita bango kafin aka fara wasan,kai!!! ni ɗayar biyun,naga bala'in da ya girmi kakata a wannan shekarar, tsakiyar d......''

maganar tasu ta katse sakamakon fitowa ta dan maganar sun ta isheni ta hanani mai da hankali akan abun da nake yi,gara inzo in taka musu burki...


Toomasu karatu ko ya zata kaya,mu haɗu daku a page na gaba.

Nagode da bani lokutanku,kada ku manta kuyi comment da share.

See 👁️ you next time 🕜... 

Goodbye👋.

Naku Amdeey.....