GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 10

by @nusybee143

Page 10


Da kallo ta bi shi har ya gama jawabinsa ba tare da ta ce uffan ba,sai hayaƙin shishar da take cigaba da zuƙa tana fesarwa,sun kwashi kusan mintuna biyu cikakku a haka,bata yi magana ba,ta zuba masa idanu kawai tana cigaba da shan hayaƙinta,shi kuma ya yi shiru yana jiran amsarta

Zuwa can ta dube shi,kallon ƙasan idanu,ta ce"menene dalilin da ya sa ka fara business ba tare da kana da dabarun yin hakan ba?"

Murmushi ya yi yana gyara zama,ya ce"ai da ni da ke bambancin ya kai tsawon sama da ƙasa ranki ya daɗe 

Ku ne manyan yan kasuwa,ku ne iyayen gidanmu a wannan harkar,why not ki yi min jagora,i bet za ki iya tsallakar min da kaya na"

Ɗauke kai ta yi daga kallonsa tana jinjina kai,a hankali ta ce"yaushe ka shirya fita da kayan?"

Kamar mai jira ya ba ta amsa a ɗokance"duk lokacin da kika tsara, yanzu feedback daga gare ki nake jira,ki gaya min maximum abin da za ki ɗaukar min da abin da zan biya"

Miƙewa ta yi ba tare da ta kalle shi ba ta ce"mu yi magana next time, David zai karɓi phone number ɗinka,za ku yi magana da shi,akwai gidana na sirri da nake ganawa da baƙi, za'a kawo ka zuwa gobe, because I'm leaving this country in less than 48 hours "

Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa,ya ce"alright, thanks very much ma!"bata kula shi ba,ta yi hanyar ficewa daga club ɗin,ya bi ta da kallo yana murmushi, kafin ya fito da wayarsa

David ne ya ƙaraso inda yake, ba tare da ya yi masa magana ba ya miƙa masa hannu yana galla masa harara, Haisam ya miƙa masa complementary card ɗinsa ba tare da ya kalle shi ba, sannan ya miƙe ya nufi hanyar fita daga club ɗin 

Washe gari tun da sassafe yake dakon kiran wayar Roxy,amma shiru babu wanda ya kira shi,har wajen sha ɗaya na safe,a lokacin ya gama magana da su Awwal,sun yi shiri cif 

Sai wajen ƙarfe biyu wayarshi ta yi ƙara,ya ɗaga yana duban wayar, unknown number ya gani,ba tare da damuwa ba ya ɗaga wayar

David ne a daƙile ya ce"kana ina ne?"

Kallon restaurant ɗin da yake ya yi,ya ce"ina wani restaurant ne"

"Ya sunan restaurant ɗin?"Haisam ya gaya masa 

David ya ce "okay to yanzu ka fito zuwa bakin titi,ka bi hannunka na dama bayan ka tsallaka titi,ka yi doguwar tafiya,za ka same mu,sai mu karasa wajenta "

"Okay babu damuwa "ya faɗa yana miƙewa don ficewa daga wajen 

Yana fita,ta cikin earbuds da suke kunnensa, ƙasa ƙasa ya furta"get ready Men!"suka amsa kusan a tare "yes sir!"

Kamar yadda David ya gaya masa,babu ɓata lokaci ya bi hanyar da ya kwatanta masa ba tare da tunanin komai ba,yana tafiya yana bin hanyar da kallo,don babu mutane

Daga can nesa ya hango David yana ɗaga masa hannu,kai tsaye ya miƙe don isa gare shi,amma me?

Kafin ya ƙarasa wani mutum da fuskarsa take a rufe ya dira a gabansa,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya hura masa wata powder a fuskarsa,babu ɓata lokaci ya sulale a wajen cikin fitar hayyaci, wanda shi kansa ba zai ce ga halin da ya shiga ba

Ba zai iya tuna lokacin da ya ɗauka a wannan halin ba, kafin Allah ya nufe shi da farfaɗowa,sai dai tun kafin ya gama wartsakewa ya ji shi a ɗaure gam gam, yadda numfashi ma sai da ƙyar yake iya yi

Dishi-dishi ya fara ganin mutane akansa,a hankali kuma ganinsa ya dawo tar-tar,ya ƙarewa kanshi kallo,inda yake ɗaure da wata ƙatuwar igiya, kafin ya kalli inda mutane suke

Su shida ne, Roxy da yaranta biyar, cikin su har da David da Hanna,sai kuma waɗanda ya biya kuɗi don su fallasa masa sirrin Roxy 

Tasowa ta yi tana taku ɗaiɗai,tana murmushi,ta ƙaraso gabanshi ta durƙusa kusa da kanshi tana kallonsa tana sake waro kyawawan idanunta 

"Hi!

Barka!!

Sunana Roxy,shahararriyar ƴar safarar miyagun ƙwayoyi daga ƙasa zuwa ƙasa, sannan kuma babbar ƴar yahoo, wadda jami'an tsaro suke nemanta ruwa a jallo 

Yau dai gata ga jami'in tsaro, jami'in DSS"ta juya tana kallon su David tana murmushi,ya sunan nashi ma?"suka kusa haɗa baki"CSO Haisam Abdulmalik Madaka!"suka kwashe da dariya

Haisam dai yana kwance a ɗaɗɗaure yana kallonsu,gaba ɗaya ji yake yi ya muzanta,don tun daga yanzu ya fara ƙyanƙyaso cewa matar nan ta raina masa hankali ne,bai gama tunani ba ta cigaba da magana bayan ta miƙe tsaye tana aika masa wani irin kallo

"Na san jami'an tsaro suna nemana sama da shekaru,a tunaninka ni wawiya ce zan zuba idanu ina zuƙar shisha da fasa accounts ɗin mutane ina shagali?then you are mistaken dude!!

Yadda kuke bibiya ta haka nake bibiyarku. Tun lokacin da ka amshi wannan case ɗin,ka ce a ba ka wata guda don ka kama ni nake bibiyarka,gashi watan yana so ya ƙare,amma har yanzu babu labarin kama ni, infact,don ma na sa ka ji ka kusa cimma burinka ya sa na haɗa maka wannan trap ɗin 

Na san kana cikin jirgin da na biyo zuwa Spain,amma da muka sauka a Barcelona kai sai ba ka biyo ni Ibiza ba, kafin ka ƙaraso izuwa Pacha Ibiza club ranar farko akwai yarana da suke kular min da shige da ficenka sun sanar da ni, lokacin da ka zo,muka haɗu a farko na saka an sake yi min bincike akanka,har yaran da ka zo da su, Finally, lokacin da kake waya kana communicating da naka yaran na yi hacking wayar, na ji komai,don haka na bari ka gama shirinka, sannan nima na zo da nawa shirin, wanda ya fi naka

Yarana da suka ba ka hint akaina don ka kama ni ni na ba su umarnin su yi hakan,don ka haƙa ramin da zan jefa ka da kanka,kuma gashi a ƙarshe na yi nasara

I repeated proudly N-

O-

C-C-M!!! Ka je ka cigaba da bincike akan waɗannan letters ɗin da ka fara before,ina ga da ka gano ma'anarsu da ba ka sake attempting shiga gona ta ba, David,yi masa allurar nan"babu ɓata lokaci David ya yi masa allurar,a take kuma jikinsa ya saki,wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi

A ranar Roxy ta bar Spain zuwa Mexico,inda ta gama shirin sake order na wasu kayan,daga nan zata sake komawa Nigeria don ta rabawa distributors dinta 

Har ta bar Spain ranta yana a ɓace saboda ji kimarta da take jin Haisam ya taɓa,ta yi wasa da manyansa,shi wanene da yake jin zai iya biyo ta har inda take ya ce wai zai kama ta,ta ja tsaki ya fi sau a ƙirga





*HAISAM*

Yana zaune a garden ɗin da yake kusa da masaukinsu ya yi shiru yana kallon waje ɗaya,amma da alamu hankalinsa ba ya kan inda yake kalla, tunani yake akan wulaƙanci da tozarcin da Roxy ta yi masa,wanda tun da ya zo duniya ba'a taɓa yi masa makamancin irin wannan cin mutuncin ba

Bayan Roxy ta gama yi masa bayanin da ya zauna masa akai,don tabbas zai yi amfani da su ya karya alkadarinta,ta sanya aka yi masa allura,ta saka aka cire masa kaya aka bar shi daga shi sai shortneakers,ko arzikin singlet babu, sannan aka kawo shi gefen gari aka ajiye shi cikin dare

Sai da ya samu ya koma masaukinsa,ya sake lalubensu Awwal,Awwal ya shaida masa cewa lokacin da suke cikin magana da shi,ba su san abin da ya faru ba suka ji network ɗinsa ya katse, ƙarshe sun yi laluben duniya ba su same shi ba

Tunda yake a wajen aiki ba'a taɓa yi masa illa an lalata masa aiki irin wannan karon ba,sai yanzu ya gane dalilin da ya sa Roxy take ba wa jami'an tsaro wahala, tamkar wadda aka yiwa training,tana aiki da lissafi sosai

Amma kuma wannan abu da ta yi masa shine ya sa yake jin dole ma ya kai ta ƙasa ko ta wanne hali,zai san yadda zai yi da ita

Miƙewa ya yi ya fice daga garden ɗin,a ranshi yana raya ta hanyar da zai bi ya rusa wannan yarinyar da ya kira annoba 

Da yamma ya kammala komai da shi da team ɗinshi,suka bar Spain zuwa Nigeria 






*KANO*

"Arfa!ba Ni wayata!"

"Wacece wannan da kake kallon hotonta?

Malam ka gaya min ko ka ga bala'i a gidan nan wallahi!"

"Arfa na ce ki bani wayata ko?"ya faɗa cikin ɗaga murya 

"Wacece wannan da kullum kake kallon hotonta?

To wallahi ba zan bayar da wayar nan ba sai ka gaya min wacece!

Okay!na gane!wato yanzu hotonta kake kalla ko?wato ina murnar na rabu da ƙaddara amma ashe tana liƙe da ni ko?ko tsine maka aka yi ne da har yanzu Kai kake sonta bayan kowa ya kama kanshi kanta?"

"Oh seriously!ashe dai kin san wacece kike wahalar da kanki wajen tambaya?ba ni wayata dalla malama!"

A maimakon ta ba shi wayar sai ta buga ta da ƙasa,sakin baki ya yi yana kallonta cikin mamaki da takaici,ta yi ta buga wayar da ƙasa har ta yi kwatsa-kwatsa da ita, sannan ta ɗaga jajayen idanunta ta ce"Muyassar!

Na fi ƙarfin ka ci amanata saboda kilaki,ragowar arne!!!"

Da wani irin ɓacin rai da hargowa ya ce"Arfa!

Watch your tongue!ina yi miki gargaɗi da babbar murya kar na sake jin kin kira ta da kilaki,akwai kilaki da ta wuce ki ne? wadda ta gama tambaɗewa kafin a cuce ni a liƙa min?"

"Muyassar!na za ka yiwa ƙazafi?don na kama ka kana kallon hotunan kilaki shine za kayi min ƙazafi!tsawon shekarun da muka ɗauka da kai baka taɓa tunanin ka yi min ƙazafi ba sai yanzu?

Innalillahi wa inna ilayhi rajiun!!

Allah ya yi min sakayya da kai,wa ya sani ma ko kaine ka fara nuna mata hanyar lalacewar shiyasa za ka......."

"Arfa!"ya daka mata tsawar da ta kaɗa ƴan hanjinta,yana huci cikin tsananin ɓacin rai ya ce"do your worst Arfa,ki yi duk abin da ya zo ranki, lokacin ki ne,amma kar ki sake kiran Shaheeda da karuwa,ba ki sani ba,bari na sake nanata miki,I LOVE HER!I LOVE HER MORE THAN HOW I LOVE MYSELF!

Kar ki sake haɗa wata ke da Shaheeda, Shaheeda ba sa'arki ba ce!!!

Ki yi duk abin da za ki yi, lokacinki ne,amma idan kika sake aibata ta komai zai iya faruwa, ciki kuwa har da tafiyarki gidanku, diot!!!"yana gama magana ya ja tsaki ya juya ya fice daga ɗakin cikin tsananin ɓacin rai,yana jin zuciyarsa tana tafasa,ya rasa wanne irin zafi yake ji,ji yake ya yiwa Arfa dukan mutuwa ma,ko zai samu ya huce wannan abin baƙin cikin da ta cusa masa

Ya sani soyayyar Shaheeda wani sashe ce ta rayuwarsa,da numfashinsa take bugawa,babu yadda za'a yi daidai da second ɗaya ya iya mantawa da ita,ko ta bar tunaninsa,a kowanne hali,a kowanne lokaci da ita yake kwana yake tashi,ya sani soyayyar Shaheeda da ita zai bar duniya, kuma har zuwa yanzu ba ya jin ya karaya,yana da kyakkyawan fatan ko ba daɗe ko ba juma zai mallake ta a matsayin matarsa 

Ita kuwa Arfa a wajen ta zube tana wani gunjin kuka mai motsa rai,ta daɗe tana zargin Muyassar yana tare da soyayyar Shaheeda,a da gani take yi ta haye,bata tare da kowacce matsala,amma sai ta tarfa Muyassar yana bacci yana sambatun kiran sunan Fatima Shaheeda,hakan ne ya tayar mata da hankali,ta so ta tuhume shi a wancan lokacin,amma ta san wanene Muyassar, mutum ne tsayayye wanda baya son wargi,hakan ne ya sa ta kasa fito masa gaba da gaba,ta fara bincikensa ta ƙarƙashin ƙasa 

A yau dai ta kama shi red handed tana kallon hoton Shaheeda,hakan ya sa ta fizge wayar,har suka yi rikici ya kai su ga haka

Tana kuka sosai ta miƙe ta nufi inda wayarta take,tana ɗauka kai tsaye ta kira yayarta Hajiya Ruƙayya 

Hajiya Ruƙayya tana ɗagawa Arfa ta fashe da kuka sosai, Hajiya Ruƙayya da take zaune tana cin abinci sai da ta kusa ƙwarewa,a ɗan firgice ta ce"Arfa lafiya dai ko?

Me aka yi miki kike irin wannan kukan?"

Cikin hargowar kuka ta ce"Aunty na gaji!na gaji wallahi,na kasa gane ɗabiun da abban Zuhra ya ɓullo min da su kwanannan,ashe wai har yanzu yana son wannan matsiyaciyar ƙaruwar yarinyar,don Allah Aunty ki yi wani abu akai, wallahi ina tsananin kishin miji na,ba zan iya haɗa shi da wata mace ba,don Allah Aunty na!"






#Nusy_bee