32
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----32
har ta kusa fita daga kofar hotel din
"Zeenah"taji an kira sunan
sai da gaban ya fadi da kyar ta iya waiga wa bata kara shiga damuwa ba sai taga Sameer yana nufo ta
da mamaki yake kallon ta miya Kawo zeenah da daren nan hotel dan har an fara Sallar magariba
da murmushi ya ƙaraso inda take"Amaryar mu"
da kyar ta iya masa magana"Sameer ya kake"
"lafiya qlau zeenah wani abu kike zo yi"
inda inda ta fara "ehhh.... nazo duba wasu friends dina da suka zo daga Abuja"
jinjina ka yayi ya ce"okay,nima na zo duba ball din da zamuyi reception gobe"
tare suka fita ganin alamar kamar bada mota tazo ba ya ce"muje in sauke ki ko"
ta kofar baya ya ajiye ta ,ta shiga ciki
mutanen dake gidan duk sun rage babu kowa sai dagin na kusa
Mummy ta shiga daƙin Zeenah nusaiba ce kadai kwance akan gado"nusaiba ina zeenatu kuwa"
Mummy nima tun dazu nake neman ta na duba ko ina ban ganta na kuma kira wayar ta a kashe
gaban mummy sai ya fadi jin abinda nusaiba ta ce tun daga yadda taga Zeenah na waya a garden hankalin ta bai kyauta ba amman yanzu tsoron ta kar taje wani abu ne ke shirin faruwa da zeenah
zata fita daga ɗakin kenan Zeenah na shigowa
mummy ta bita da kallon tuhuma
"zeenah daga ina kike"
cikin rawar murya ta ce"mummy daga wajen tailor nake naje amso ko dinki na"
"karya kike zeenah miyasa baku je tare da nusaiba ba kuma idan ma zuwa zakiyi miyasa baki fita da mota ba"
marai recewa tayi ta ce"Mummy ki yarda dani kuma,key din motar na duba ban gansa ba shiyasa"
Mummy ta kafe Zeenah da ido
“Key ɗin motar ma ya ɓace kenan, wayarki kuma a kashe take, Zeenah me kike ɓoye min?”
Gabanta ya sake faɗuwa
Da kyar ta ke haɗiye yawu
“Mummy wallahi babu komai”
Mummy ta jinjina kai
“Allah yasa haka ne”
Ta juya ta fita daga ɗakin amma hankalinta bai kwanta ba ko kaɗan
da sauri zeenah ta karasa bakin gado ta zauna jin ƙafafuwan sun kasa daukar ta
dubanta takai ga Nusaiba dake ɗan na wayar ta ce"Sister Please ki samo min Abinda zanci yunwa nake ji"
tayi hakan ne dan tasamu damar kiran Khalid taji ko ya goge videos din
Nan take ta sake kiran Khalid taji wayar a kashe tabbas Khalid tarko ya hada mata dan ya cigaba da amsar kudi a hannun ta
Iman na zaune a ɗakin Aunty Fauziya
An gama mata kitso kenan wanda Aunty Zarah ce ta samo mai kitson
Kananan kitson ya zauna mata sosai har ya ƙara fito da kyakkyawar fuskarta
Hannunta kuma cike yake da ja da bakin lalle yayi masifar yi mata kyau
tana zaune tana cin abinci tare da Amatullah Aunty Zarah ta shigo ta miƙa mata waya wai Suhail zai mata magana
Amsa tayi takai wayar kunnen ta"ki kawo min coffe ɗaki na"
sai da gabanta ya fadi ta wai ta kawo masa tea dakin sa mikawa mata wayar tayi
ta kalli aunty Zarah "wai coffe zan kai masa dakin sa"
murmushi aunty Zarah tayi ta ce"ki shiga Kitchen din aunty sai hada ki kai masa"
tana turo baki ta tashi ta fita da kallo aunty Zarah ta bita tana murmushi ganin tsantsar yarinta a wajen Iman wani gefe na zuciyatar na tausaya mata ko ya zatayi Zaman kishi da zeenah wayayya yar boko
"ya Allah” ya fada a fili
Amatullah ta ce”mommy miya faru”
“Bakomai ki gama cin abincin ki fita da plate din Nan”
Cikin yan mintuna iman ta gama hada komai a tray ta fito kenan ta gamu da Amatullah ita ta mata rakiya har kofar dakin Suhail amman taƙi shiga dan har Yanzu haushin sa take ji
knocking tayi sau biyu
suhail dake zaune a falo ya ce"come in"
sanye yake da farar jallabiya yana dan na wayar sa
tunda ta shigo ya ke kallon kunshi hannun ta ga gashin ta da ya fito ta cikin dankwali
ajiye tray din tayi zata fita Suhail ya ce"Iman"
juyawa tayi ta na kallon sa
"kiyi haƙuri akan karyar da na maki wajen abba na jima inaso baki haƙuri in kuma yi maki godiya kare ni da kika yi a gaban sa"
"ka riƙe haƙurin ka zai maka amfani a gaba ban kuma kare ka dan ka gode min ba"
maganganun ta sun shiga zuciyar Suhail
juyawa tayi tayi fitar ta
Washe gari
karfe Biyu na Ranar juma'a aka daura auren Zeenatu Ibrahim makama da Muhammad Suhail munnir Mahmud akan sadaki dubu dari biyar
bayan an gama Suhail ya nufi wajen reception tare da Sameer wanda shi ya hada masu tare da abokan su
bangaren Zeenah ma daga Lagos mummy ta dauko mai make up tayi mata ta saka white wedding gown wanda ta siyo da kudi masu yawa tayi kyau sossai komai nata Unique and classy zeenah akwai son gayu
gidan su Suhail ma mami ta dako masu decoration an gyara mata zata gudanar da walima tare da kawayen ta har makeup ta sa ayi mata
ta dauko hayar masu Abinci daga 711 resturant dan fitar da baƙin ta kunya
ɓangare Iman aunty Zarah ke shirya ta dinkin na musamman ta bada ayi masu irin daya hadda Amatullah ita tasa ayi wa Iman make up ta bata wani dan karamin veil ta yafa ta fita wajen da ake walimar
gaba daya hankalin Mutanen dake wajen yayo kanta kowa da abinda yake faɗa ko baka kaunar Allah kasan Iman tayi kyau kamar ka sace ta ka gudu
Na'ima na hango ta ,ta wurga mata wata irin harara ta kalli kayan dake jikin duk sai taji ta raina kanta a wajen
tashi tayi zata bar wajen ta gaban iman tabi ta bangaje ta da kafaɗa ta tafi luuu zata fadi da sauri aunty Fauziya ta tare ta duk abinda ya faru a idon mutane wajen har Suhail da shigowarsa kenan yaga abinda na'ima tayiwa Iman
Mami ko sai murmushin take Na'ima tayi abinda ta faranta mata rai
A fusace Suhail yabi bayan na'ima a falon mami suka hadu hannu ya daga ya wanke ta da mari
yatsa ya nuna mata "should be the last time da taɓa mamata a gidan nan useless girl"
hannu tasa a inda ya mare ta "Yaya ni ka mara akan wachan ƴar Malan din"
hawaye ke fito wa daga idanun ta karon farko da Suhail ya taɓa dora hannun sa akan ta tsanar iman ta karu a zuciyatar ta
"zan miki fiye da haka indai akan Iman ne"