Chapter 29
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 29
Washegari, kamar yadda ta kasance jiya, tun bayan sallar asuba Salmah ta shiga gyaran gida, bayan ta gama, kitchen ta koma ta haɗa musu abincin kari mai sauƙi, ta shirya na su Ammie wanda za ta kai asibiti a basket, sai da ta gyara kitchen ɗin tas, kafin ta koma ɗaki ta yi wanka da shirin makaranta a gurguje.
Duk da sai 10 take da lecture, tana so ta bi Abie ya sauketa a asibiti ne, daga can idan lokacin ya yi sai ta wuce, don ba ta son ta jera da Salman, gaba yake yi da ita sosai, da sun haɗa ido sai harara da ƙwafa, ita ma take ta ke mayar masa da martani ta kara da “Aikin banza! Bayan ta ka dogon tsaki. Ta san shakkar Ya Anas ne ya hana shi cewa zai kai hannu jikinta, ba don shi ba yadda gidan babu Ammie wata kila da tuni sun dambace.
Kasancewar Abie fitar sassafe ya yi karfe bakwai da ashirin a cikin asibitin ta yi musu.
Sun tarar da Ammie zaune akan dardumar da ta yi sallah, hannuta rike da carbi tana lazumi.
Ganinsu yasa ta yi addu'a ta shafa, kafin ta gaisar da Abie, ya amsa mata cike da kulawa da soyayya, ya kara da tambayar yadda suka kwana da mai jikin, da ya tarar ta koma barci.
“Alhmdllh. Jiki yana ta kara kyau, in sha Allah muna saka ran samun sallama yau, kamar yadda Dr Lukman ya faɗa.”
Ya gyaɗa kai “Allah ya ƙara sauƙi.”
“Amin ya Rabbi.” Ammie da Salmah suka haɗa baki wajen amsawa.
Dan tattaunawa su ka yi da Ammie akan maganar aikin da ya karɓa mai wahala, wanda ya saka shi gaba, kwata kwata baya samun hutu cikin kwanakin.
Ammie ta nuna tausayinta a gareshi, ta kuma yi masa addu'a da fatan nasara.
Sosai ya ji dadin hakan, ya kara samun kwarin gwiwa akan aikin. Bai wuce minti goma ba ya yi musu sallamah ya tafi.
Sai sannan Ammie ta dawo da hankalinta kan Salmah da tun shigowarsu bayan sun gaisa da Ammie, ta haye wajen zamanta na jiya, ta kwanta ta juya musu baya tana danna waya.
“Ina sauran mutanen gidan? Ya kuka kwana?”
Ta shi ta yi ta zauna, “Lafiya muka barosu Ammie, don lokacin da mu ka fito ma ba su tashi ba.”
“Shi Salman ba shi da lecturen ne?”
Ambaton Salman da Ammie ta yi yasa take yanayinta ya sauya, “Oho masa, nima ban sani ba.” Ta furta cikin yanayin ko in kula.
Harara Ammie watsa mata. Sai ta kyalkyale da dariya, “Ammie wallahi da gaske na ke yi ban sani ba.”
“Me ya haɗa ku jiya?” Ammie ta wurga mata tambayar tana ci gaba da hararanta.
Rass! Gabanta ya faɗi, ko cikin gigin barci ai ba ta ce wa Ammie ga abin da ya faru ba. Muƙut! Ta hadiyi miyau, kafin ta saki murmushin yaƙe, “Uhm... Amm... Kawai fa, Ba komai fa Ammie, kin san halinsa kema dai.” Ta yi maganar cikin inda inda irinta ta rashin gaskiya.
“Baki da gaskiya Salmah.” Ammie ta faɗa kai tsaye tana kallon cikin idanunta.
“Kaii. Wallahi fa Ammie.” sai kuma ta yi shiru tana zare ido.
“Na san halin kowannenku, Salman ba ya fadan rashin gaskiya, na shaide shi da wannan, duk yadda aka je aka zo ke ce ki ka yi masa ba daidai ba.”
Cikin yanayin shagwaɓa, ta na matso kwallar munafurci ta ce, “Kaii Ammie dama kullum ni ce mai laifi a wajen ki, amma Allah ne shaida ni ban masa komai ba.”
“Zan bincika ai, idan na ji saɓanin abinda ki ka fada ranki zai yi mummunar ɓaci na gaya miki.”
Jiki a sanyaye ta gyaɗa kai, gabanta na luguden faduwa.
Motsin Aysha ya ja hankalinsu gareta, “A'a Aysha kin tashi? Sannu ya jikin?” Ammie ta yi maganar tana nufarta domin ta taya ta tashin da take kokarin yi.
Duk da za ta iya tashi don jikin da sauƙi sosai amma Ammie ba ta barta ba, ita ta taimaka mata ta raka ta har toilet ta yi alwala ta yi brush, ta zo ta yi sallah.
Kafin ta idar Salmah ta zuba mata abinci ta haɗa mata tea.
Akan farin kujera ta zauna, kasancewar drip ɗin da aka daura mata tun cikin dare ya kare Ammie ta cire mata, Salmah ta miƙa mata abincin da tea ɗin da ta haɗa mata, ta fara ci kaɗan kaɗan, suna hirar school da Salmah jefi jefi Ammie na saka musu baki.
Karfe tara da minti biyu, Salman, Ya Anas, da Ya Ammar, wanda shine ya dauko su zuwa asibitin suka shigo ɗaki. Idanun Ammar akan Salmah su ka fara sauka, sam jiya bai iya rintsawar kirki ba saboda tunaninta da ya adabi zuciyarsa, ita kuwa kamar ta san kallo ta yake ko da wasa ta ƙi ɗagowa, domin tana jin muryarsa gabanta ya hau faduwa for no reason.
Sai bayan sun gaisa da Ammie da Aysha, sannan ta dago cike da aji ta gaishe su a tare gaba ɗaya. Cike da ɗokin ganinta ya amsa mata, daga haka suka zauna su ka shiga tattaunawa da Ammie, batu ne mai muhimmanci hakan yasa ta basu dukkan hankalinta.
Ganin haka yasa Salman ya koma kusa da Aysha ya zauna suka hau tasu hirar, yayinda Salmah ta duƙufa kan waya.
kimanin mintuna talatin suka kwashe kafin Ammar ya miƙe yana kallon Agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa.
“Anas, we should go now, it’s getting late.”
“Ok let's go.” Ya amsa shima yana miƙewa.
Addu'a da fatan dawowa lafiya Ammie ta shiga yi musu, hakan ya janyo hankalin su Salman kan su, ganin sun mike za su fita yasa ya diro da sauri.
“Ya Ammar, please let me come with you, you can drop me at school.”
“Okey, ba matsala mu je, kan hanyarmu ne dama.”
Kallon Salmah Ammie ta yi, “Ke ma ba na ji kin ce kina da lecture 10 ba?”
Kamar za ta fashe da kuma ta gyaɗa alamar e.
“To tashi ki bi su?” Ba tare da sake tankawa ta mike ta dauki jakarta na baya karama irinta yan gayu matasan 'yan jami'a, ta goya akan dogon hijab ɗinta irin wanda ake ya yi, wanda ake yiwa laƙabi da me capacity wani mai yanayi da riga, sannan ta rufa musu baya, tana tafiya a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Kafin ta isa har sun shiga mota sun tayar ita suke jira, baya ta buɗe ta shiga, ta zauna kusa da Salman da ko kallonta bai yi ba, Ammar ya ja motar ya rufe suka ɗauki hanya.
Tafiya mintunar da ba su wuce ashirin ba ya kawo su school ɗin, har cikin makarantar Ammar ya shiga da su, ko da ya sauke su, kuɗi ya debo masu yawa ya fito ya bawa Salman, sannan ya miƙawa Salmah nada har ta fara tafiya itama, dai da ta kalli kuɗin kafin ta daga kai a hankali ta kallesa ba tare da ta karɓa ba. Idanunsu ya hadu cikin na juna, gyaɗa mata kai ya yi, sai ta samu kanta da girgiza masa kai, alamar A'a, ya sake gyaɗa mata kai, ta sake girgiza, ya sake a karo na uku itama ta sake girgizawa, sai kawai suka saka dariya a tare.
“Come on, take it my Friend! Na yi kama da abokin wasan ki ko? Idan Anas ne ya baki ai ba za ki karɓa ba.”
Hannu ta miƙa ta karɓa, tare da faɗin.
“Thank You.”
“You’re welcome… but don’t do that next time. I don’t like being refused.”
Murmushi kawai ta yi, ba tare da ce komai ba ta juya ta fara tafiya, bayanta ya bi da kallo na sakwanni goma, yana shafa sumar kanshi, kafin ya saki murmushi ya juya ya shiga motarsa ya tayar suka fice daga harabar school ɗin a guje........