KUSKURE 29
*KUSKURE*
By maman shaheed
Shafi Na Ashirin d tara
Safwan dai mamaki ya dingayi ,da tambaya kanshi" yaushe aka d'auki wanan hotunan a wayar shi ?"
Can ya tuno lokacin da Noor ta karban Mai waya wai zatayi game anan wato ta dinga Mai wasa da waya ta dinga d'aukan Mai kowa a waya haka.
Can Kuma ya Cigaba da duba hotunan Yana cewa Ai gwanda adauki pics din indo da a daukan Mai hotuton Huzna Mara tarbiya sakarya da Yanzu duk ta sake sire Mai.
Kaf sai da ya gama duba hotunan Babu ita sanan yace ,da andauka da ya goge, dan be gane inda noor ta ɗauke da be fito ba ma.
Zuciyar shi ta tmby shi to Damme baze goge n indon ba ?.
Sai yaba zuciyar shi amsa da "kodan su Noor" baze goge ba Kuma wasu ma ai tare suka d'auka Ya Nuno wani hoton ndon ita kad'ai tayi kyau kamar asace ta a gudu, kamar dama ta shirya ma hoton tana murmushi dama gata uwar fara'a musamman in tana tare da yaran.
Y fara kare Mata kalo cikin wani siga ,Yana tunani da hasashen ko girma ta karayi yaga kamar....Da sauri ganin zuciyar sa da kwakwalwar sa zasu Kai shi inda Bai yi niyar zuwa ba yasa yayi saurin dawowa ya tsaida tunanin sa.
Yaga indai Bai ajiye wayar ba baze bar ganin indon ba ,Dan haka ya ajiye wayar ya shiga wani dogon nazari.
***********
Indo ta Isa gidan Inna lpy ,taba Inna sak'on Ammy ,Inna nata MA Ammy Addu'a.
Bayan ta huta taje gidan su nawara ta gaishe da momyn ta bayan sun danyi Hira ta rakota gidan Inna sun Sha Hira , sosai.
Har nawara take cema indo "waye Wanda ya kawo ku kwanaki?"
Indo tace "shine uban gidana Wanda nake Aiki a gidan shi dadyn su Noor"
Nawara tayi dariya tace, "Kai Amman Akwai fahimta a tsakanin ki da yaranshi ,Amman shima da fahimta tsakanin ki dashi ko?"
Indo tace "kamar ya me wata fahimta kuma?".
Nawara tace" kamar yadda na tmby ki, kar ki raina min hankaki"
Indo tace"aiko na raina miki dan ohon Miki ni ban fahimce ki ba ,keda hidaya in kunso gulmar ku bazaku fitoma mutum da Abu barobaro ba sai kuta sashi a duhu"
Nawara tayi dariya tace"laa ban tambaye ki kawar mu hidaya b?"
Indo tace" Yar gulma kamar ki ba ,Tana lafiya tun shekaranjiya rabon da mu hadu".
" mune masu gulma ko ?" nawara ta firta.
" eh Mana ,in ba gulma ba kudinga min magana da zan fahimce ku Mana ,Amman sai ku dinga kudindine magana"
Nawara tace "hmmm shikenan barin kyaleki sai ƙamshin hasashena ya fara yawaita da har yan gari kowa zai sani ,na ɗora daga inda Kika dakatar Dani" tana hararar ta da mata murmushi.
" ke kikasan wanan karatun ,Ni ban gane ba"
Suka bar wanan hiran ,nawara ta faraba Indo labarin saurayinta da zata aura ,Tana Gaya Mata yadda yake nuna Mata so da k'auna Mai tsafta ga kulawa da yake Bata.
Lokaci na farko a tarihin Rayuwar Indo da hasashen wani da namiji ya bijiro cikin tsarin Rayuwar ta , Fara tunanin" shin zatayi soyaya? To inzatayi da wama zatayi shin zata samu Wanda zai sota fiye da tunanin ta Kuma zai taimaka Mata wajen cikar burikan ta ?"
Nawara nata ma Indo magana ,Indo an Lula duniyar gano amsar tabayarta.
Sai da nawara ta taɓata sanan Indo ta dawo hayyacin ta .
Nawwara tace" ƙawar meke faruwa ,meke damun ki da har ya jefamin ke a tunani ?"
Nawara tace" dan Allah karki ɓoye min komai ,walahi wanan hirar da nake Miki bantaɓa yinta da kowa ba sai ke,yadda da ke da sanin ke wacece agurina yasa nake gaya Miki Abin farin ciki da ya sameni ,da na bakin ciki ne ma da zan Gaya Miki ba nasan ki da sa damuwa arai ,Amman inhar Kika Yi yinƙurin ɓoye min Abin da kike tunani wlh daga yau shaku da kokwanto zasu shiga tsakani na dake zasu Mana gatanga Mai kwarin da rugujeta sai ikon Allah"ta gama kalamanta tana nuna ma indo alamar fushi har tana suro baki.
Indo ta yi ajiyar zuciya ,Bata da hanyar gujema tambayar nawara.
Dan haka ta sanar Mata da Abin da take tunani cikin zuciyar ta .
Nawara tace "ƙawata karki damu ,na tabata Akwai Wanda suka taba Miki tayin soyaya kikaki Basu hadin Kai , Dan ba namijin da zai ganki beji kin kwanta Mai ba uwa uba Wanda ya sanki yasan d'abi'un ki da halayar ki da dadin zama da mu'amalar ki yaji beyi sha'awar ki zama Mata agare shi ba .
Komai lokaci ne , nasan tsarin ki nakin kula samari ada ,ayanzu ki dinga kulasu ko ba kowane Tom and Jerry ba , dan Allah Kinji daga yau duk Wanda ya Miki tayin soyaya ta sigar da ya Dace inhar kin yadda da nutsuwa hankalin shi ki fara kulashi Dan Allah karki ƙyin Amfani da magan ta".
Indo ta nisa tace "hmmm,naji Amman sai na tatara na dawo gidan inna Danni na gaji da aikin Nan ma".
Nawara tace" kun rabune da su? "
Indo tad'an saya Tayi Jim Kafin tace" aa matar gidan ce take aikin kwana a asibitin su shine muka koma gidan karkar su Noor maman dadyn su Noor din Kuma wallahi Basu da matsala inajin daɗin zaman gidan ko zasu rabu Dani sai ansha fama"
Nawara tace "to ki ƙara hakuri ki barsu zuwa wani lokaci wata rana sai labari"
"ki fara Aiki da maganar da na roƙeki ko agidan Nan Akwai wani hasashe da nakeyi nake so ya zama gaskiya kinji Dan Allah" nawwara ya faɗa da shigar rarashi.
Indo tace" a gidan mutanen? Zan bude musu kamfanin Hira d weni ƙato Ko ƙattai? "
Nawara tace" to meye? Su twins basa yi ne ?in kikayi korar ki zasuyi?"
Indo tace" aa sunayi ,Kuma banajin Akwai wani Abu da zai faru Sam Dan mutane ne masu karamci wlh ,kawai dai inajin tsoro da kunya idan dadyn su Noor yazo ya ganni tsaye da wani ne"
Nawwara tayi dariya Mai isarta ,lokacin Indo har ta ɓata Rai tana Mata wani kalo Jin haushi dan ita bata ga abin dariyar ba.
Nawara tace" yi hakuri kawata ,wlh bazaki gane bane , Anzo wajen da nakeso na baza komata Ne dan cafko min duk Abin da ya shiga Ni Kuma nayo waje dashi "
Indo tace" ohon Miki ke kikasan me kike nufi"
"eh nikam na sani kuka ki bini bashin wanan"
Nawara tace "ubangidan ki fa ba babanki bane , ko Akwai Yar tsama a tsakanin kune? Kamar matar sa Ko Yana nuna Miki tsana ko tsangwama ne ko zagi ko cin zarafi?"
Indo tace "ko ɗaya be taɓa nunamin ba ,kawai dai girmamawa da mutuntawa shine atsakani na dashi bama doguwar magana ma dashi bashi da matsala Kuma Kinga yanzu ma yadan sake jiki Dani kadan fa Amman ba kamar da ba ,kodan Ina tare da yaranshi Suma suna tare da Ni ne oho"
"kinsan ance Mai ɗa Wawa" inji nawwara Amman ahankali zamu Mai fatan sakowa gaba daya sai ma mun hadu da hidaya Naga ke sai ankawo Miki agajin gagawa.
Indo tace ku kuka sani keda itan kwaji da tashen balagar ku ƴan matan dole"
Nan dai nawara ta ba Indo shawarwari masu tsabta da inganci da cire Mata shak'ar duk Wanda zeci zarafin ta ko ya yagata a cikin jama'a.
Sunjima suna Hira kafin ta koma gidan inna.
Inna da Indo ma ranar ansha Hira sosai harda mafarkin da Indo ta taɓayi da wani datijon da yaro ya bige Saida taba Inna.
Inna ta jinjina Abun itama taba Indo labarin nata mafarkin kusan irin shi itama da wanna datijon da duk suka kasa fasalta surarshi ko kamanin shi azahiri.
Nan suka dinga Al'ajabin Abun da mamaki da son gano ma'anar mafarkin ,can Kuma Inna tace "komadai maye Addu'a na maganin komai sai gobe muyi sadaka Akan mafarkin insha Allahu"
Indo ya firta.
Haka sukayi kwanan farin ciki jika da Kaka .
************
Su Noor ko basuji daɗin rashin Indo ba ,Dan rigima suka dingayi wai akaisu wajen Indo ko amata waya ta dawo.
Twins nata Basu hakuri ,sai da ƙyar suka haƙura da dabara .
Huzna ko dama tun dawowar ta gidan ta dawo da ɓacin Rai matsanaici su twins na Lura da ita Bata gaya musu ba Basu tambaye ta ba , sai da ta gama fushin har ta sauka taje tayi baccin asarar ta sanan ta dawo falon ,ko rigimar da su Haneef sukeyi akan Indo shi ya ƙara kular da ita take ƙarajin tsanar Indo kamar sun had'a miji ga yarama wai sun iya kinibibi akanta ko wace ita agaresu oho ko kalon su batayi ba bare ta rarashe su .
dadyn su Noor ne ya Kira hassana yace" Ina su Noor ko suna tare da indo sun kwanta?"
Hassana tace" aa Yaya gasu Nan sunata rigima harda kuka wai akaisu wajen aunty Aishatu"
Dadyn su yace "to akaisu Mana , ko ba tare suke kwana ba?"
Hassana tace "tare suke kwana ,indon Ce Bata Nan Tana gidan Inna taje gaishe ta ɗazu"
Yace "haka kawai ta tafi kodai wani Abu akayi?"
Hassana tace "aa lafiya Lau sai da ta tambayi Ammy ma sanan ta tafi ,taje nee Tayi kwana biyu"
Dadyn su yace "har kwana nawa zatayi ?"
Hassana tace" wlh ban sani ba sadai munganta "
Yayi shiru badan ranshi yaso hakan ba Jin ance yaranshi nata rigima in Akwai Abin da yakeso a yanzu be wuce farin cikin yaranshi ba ,rabon da yaga kukan su har ya manta Amman yau harda kuka akan rashin Indo?.
Jin kukan Haneef yace" abashi Haneef din a waya"
Akaba Haneef waya ,dadyn shi ya fara aikin rarashi Yana tambayar dalilin kukan ,yadda hassana ta fad'a dai hakan ya faɗa shima ,Nan ya dinga rarashin shi da Mai wayo akan ze kirata gobe zata dawo sanan yayi shiru .
Yace aba Noor itama murya cikin shagwaba ,ya dinga rarashin ta Yana Bata hak'uri har saida tamai Alk'awarin ta daina kuka sanan ya kashe wayar zuciyar sa cike da tunanin ya zeyi da tafiyar Indo gidan Inna ,ga yaranshi sun shaƙu shi besan shaƙuwar tasu har takai haka ba sai yau .
Huzna ko ƙuluwa ta ƙara yi duk Abun da akeyi Tana Jin naji Tana kalon na kalo ,cikin ranta ta Fara tsanar yaran Tana cewa ai ko Auren safwan tayi sai tayi da gaske akan yaran inba hakaba tas zasu kashe Mata Auren da baban su Kuma da deal luv din su y faɗa ita da safwan, Indo sai tabar aiki agidan Dan zaman gidan sai ya gagareta Tama Bata Dace da zama ko Mai wanke toilet din gidan ba bare har tayi girki da gyara komai na gidan har suci suna Santi har a bar Mata ragamar yaran gida uwa uba gashi yanzu ta asirce kuruwar yaran har suna kuka Dan ta tafi gidan kasar d ta baro shegu kawai har ita ,tanata karatun jaridar jakuna.