PAGE 20
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 020.*
A ƙofar gidansu Safeera ya hange ta a tsaye ta harɗe hannu a ƙirji ta jingina da bango. Kana ganinta ka san a sama take, ƙiris take jira ta fara sauke faɗa da masifar da suke bayyane akan fuskarta.
Ya ƙarasa wajen yana kallon yadda fuskar ta take a ɗaure, ta kawar da kai gefe bata bari sun haɗa ido ba.
Ya ce, "Islaha meyasa za ki yi haka? Meyasa baza ki jure mu cigaba da lallaɓawa kafin Allah ya raba mu ba, meyasa za ki biyewa Hanan? Meyasa Islaha!?."
Ganin ya fara yi mata magana cikin faɗa, sai ta yi masa kallon kallon up and down ta ce, "ni fa ban biye mata ba, ta yi min magana yafi sau uku ban kulata ba, da kanta ta jawo ni. Ta ce min karuwa na yi shiru, ta ce mara tarbiyya na yi shiru na ƙyaleta, kawai sai ta jawo ni wai zata mare ni."
"Amma da kin sani baki kula ta ba, yanzu gashi Mama tace kin yi mata rashin kunya."
"Marina ta yi na rama, ta ce min mara tarbiyya na ce itace mara tarbiyya ba ni ba. Kuma na bawa Mama haƙuri ai."
"Yanzu ya ki ke so ayi? Ina ki ke so ki je?."
"Dan ni marainiya ce na tashi a orphanage, ba hakan yana nufin zan rasa inda zan je ba, dan suna ganin kamar gidansu ne kawai mafakata, shiyasa suke yi min abinda suka ga dama. Daman nima na gaji da zaman gidan, kafi kowa sanin haƙuri nake yi."
Ya ɗan yi tsaki ya ce, "kin ɓata komai Islaha, meyasa zaki biye mata don Allah?. Ran Mama ya ɓaci sosai, kuma bai kamata a gabanta ki dinga faɗar kalaman da ki ka faɗa ba. Sannan da kin bawa Hanan haƙurin da ba a wuce wajan ba?."
Ta ɗan buɗe tana kallonsa, ta girgiza kanta ta ce, "Wallahi bazan bawa Hanan haƙuri ba, dan ina cin arzuƙi a gidansu bazai yu ta taka ni na ƙyale ta ba. Mama kuma na bata haƙuri, ko babu kai bazan iya yiwa Mama rashin kunya ba, saboda ta haife ni, balle akwai ka a tsakani. Duk jurewar da nake yi baka gani ba? Dan yau kawai na tanka shine abin zai zama laifina Hamma?."
Kafin ya yi magana ta ce, "shikenan, ka ƙyale ni zan je na nemi wajan zama kawai, bazan sake zama a gidanku ba."
Ya dafe kai jin ya taɓo ta ya ce, "ba laifinki na gani ba Islaha..." ta katse sa cikin faɗa, tana kuka har ta manta waye a gabanta.
Ta ce, "to me ka ke nufi? Ka san irin abubuwna da ake yi min a gidan, duk bana ɗaga kai na kalla, ba dan an fi ƙarfina ba, sai dan alfarma nake ci a gidansu. Dan yau an kaini bango na rama shine sai ya zama laifina?. Shikenan mu da muka tashi a gidan marayu bamu da tarbiyya kenan, kowa kallon mu yake a matsayin waɗanda aka haifa aka cillar, wasu ne suka tsinta suka kai mu gidan maryu, ko kuma ni ce mara tarbiyyar a cikin gidan?. Dan a can na tashi hakan yana nufin iyayena suka yar dani, kenan ni ba ƴar halak ba ce?."
"Haka aka ce musu duk wanda ya girma a gidan marayu bata hanyar aure aka haifesa? Ko kuma duk wanda ya tashi a cikin gidan yar dashi aka yi?."
"Kullum sai sun ce min karuwa, me na aikata da yake nuna ni karuwa ce?. Haƙuri nake ina cigaba da zama a gidan saboda kai da Baffa, ba wai dan na rasa inda zan je bane. Ina da abokan arzuƙi da yawa, wanda zasu iya riƙe ni har abada, ina da wanda zasu jiɓanci lamarina babu gori balle cin fuska. Bazan sake komawa ba, nima na gaji da wulaƙancin dake yi min. Tunda Mama ta ce baza ka aure ni ba shikenan, zan je na cigaba da rayuwata yadda nake so!" Ta faɗa cikin kuka cike da tsiwa da fusata.
Saheer ya sauke numfashi yana kallon hanya, ya sassauta murya ya ce, "ki yi haƙuri, kin ga a akan hanya mu ke. Ki zo mu je na kaiki gidan Adda Sa'ida."
"Bazan je ba, zan je in kama hotel kafin na samu inda zani."
"Sai kin je Islaha. Ki jira in karɓo motar Sadik nazo na kai ki, kar ki motsa daga wajan nan, ki jira ni" ya faɗa yana juya ya bar mata wajan da sauri.
A lokacin Safeera ta fito daga gidan, fuskar ta babu walwala ko kaɗan.
Suka haɗa ido Islaha, islaha ta goge ido ta ce, "Safeera lafiya?."
Safeera ta sauke numfashi ta ce, "ba lafiya ba Islaha, ina cikin damuwa. Jiya ko bacci ban yi ba."
"Me ya faru? Kin ga yadda ki ka canja kuwa? Gabaɗaya kin koma wani iri kamar ba ke ba."
"Za ki raka ni Katsina?."
Da mamaki ta ce, "Katsina kuma, Wajan wa?."
"Dangin Umma, ƙarar Umma zan kai musu."
Islaha da mamaki ta ce, "kamar ya ƙarar Umma?."
Safeera zata yi magana suka ji horn ɗin mota, suka kalli wajan a tare.
Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "in kin shirya mu wuce."
Ta ɗaga kai ta ce, "mu je." Suka ƙarasa wajam motar suka shiga.
Ba yabo ba fallasa Safeera ta gaisa da Saheer, daga yadda suka gaisa ya san bata yanayi mai daɗi, bai tambaye ta ba suka cigaba da tafiya.
Islaha ta ce, "ka kaimu wajan aiki kawai, in mun dawo sai na wuce gidan Adda Sa'idan."
Ya bita da kallo ya ce, "baki da aiki yau ko?."
"Eh, zan je kawai"
"gwara mu je yanzun kawai."
"ba sai mun je ba, kawai mu wuce wajan aiki."
Ya sake kallonta, ganin fuskarta a ɗaure alamun tana cikin ɓacin rai, ya ɗan ɗauke ido bai ce komai ba ya cigaba da tafiya.
Sai da ya tsayar da motar sannan juyo yana kallonta, softly ya ce, "ki yi haƙuri, ɗazu na yi miki faɗa."
Ta sunkuyar da kai ƙasa, dan in akwai abinda yake saurin karya mata zuciya bai wuce ya bata haƙuri ba. Sai ta ga babba dashi yana bata haƙuri, yana matsayi mai girma a rayuwarta ya dinga cewa ta yi haƙuri, duk sai ta ji ta damu.
Bata ɗago ba ya ce, "ban yi miki faɗa dan na saka ki kuka ko dan ranki ya ɓaci ba, ina so ki dinga haƙuri da komai na rayuwa, zaman gidanmu ya kusa ƙarewa. Ba ina yin duk abinda nake yi dan baki da inda zaki zauna sai gidan namu ba, ke kin san waye ni, kin san zan iya sadaukar da komai saboda ke. Mama mahifiyata ce, yi mata biyayya dole ne a gare ni, duk abinda ta ce sai na bi koda bana so. In ta hau sama dole na bari ta sauka ƙasa saboda uwata ce, sai ta yi sanyi zan bata haƙuri. Ki yi haƙuri!."
Ta ɗago ta kalle sa ta ce, "ka daina bani haƙuri Hamma, komai ya wuce."
"Komai bai wuce ba Islaha, na san na ɓata miki rai sosai da sosai. Ku je wajan aikin, in kun gama ki kira ni, zan zo in kai ki gidan Addan ki zauna kafin Mama ta huce."
Ta ɗaga kai ya ce, "kin cin abinci kuwa?."
Ta girgiza kai ta ce, "bana jin yunwa."
"Kwana biyu bakya son cin abinci, ko baki da lafiya?."
"lafiya lau nake, kawai bana jin daɗi ne."
Ya ɗan kalle ta sai ya ɗauke kai dan ya gano abinda yake damunta, ya ce, "kin sha maganin da na baki jiya?."
Ta girgiza kai ta ce, "ba yanzu nake sha ba."
Ya ɗaga kai ya ce, "sannu. Ku je." A hankali suka buɗe suka fita duka shiga ciki.
Islaha kai tsaye office ɗin Chairman ta wuce, tunda ta shiga yake tafa mata, ita kuma da yake bata da walwala ko murmushi bata yi ba ta zauna.
Ya ce, "good job Islaha, ina ji dake sosai. Saleem ya bani labarin komai, na ji daɗi. Domin an tabbatar min indai ka haɗu da Mr Jafar kamar ka ga Mr Rahaan ne."
Ta yi murmushi ta ce, "na gode Chairman."
"Ni zan yi miki godiya, ina jin daɗin aiki dake sosai."
Ta yi murmushi bata ce komai ba. Ganin kamar bata cikin walwala sai ya ƙyale ta tafi.
Record office ta tafi wajan safeera, ta same ta ita kaɗai ta dafe kai cikin damuwa.
Islaha ta zauna ta ce, "Safeera faɗa min, meye ya faru?."
Ta ɗago ta kalle ta ta ce, "Islaha Umma ce take so na tafi ƙasar waje aiki, da Baba ya hanani sai ta ce ita zata je. Islaha Umma tana iƙirarin kashe aurenta ta tafi aiki ƙasar waje."
Islaha ta zaro ido waje ta ce, "Umman!."
Safeera ta ɗaga kai ta ce, "jiya faɗa suka dinga yi ita da Baba, yana faɗa tana faɗa. Tana cewa wallahi sai ta je sai dai ya sake ta, shi kuma ya ce indai ta tafi to babu aurensa a kanta."
Islaha ta cw, "innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Mun shiga uku."
"Islaha wallahi bacci kaɗan na yi, da tunanim wannan abun na kwanta na tashi. Ni na amince zan tafi aikin indai zata zauna a gida, amma Baba ya hana, ya ce wallahi baza ni ba. Islaha ta ya zan iya zuba ido Umma ta tafi ƙasar waje aikatau ina nigeria? Ni ce babba a gidan fa, ya take so na dinga tafiyar da al'amurana gabaɗaya?. Ban taɓa jin zafin rasa Hamma Muhammad ba sai yanzu, sai yanzu nake jin zafin rashin ɗan uwa babba."
Islaha ta yi bata ce komai ba, Safeera ta ce, "shiyasa zan je Katsina na kai ƙararta wajan ƴan uwanta, wataƙila in suka yi mata magana zata ji. Ina Umma ina tafiya aiki wata ƙasar don Allah? Abinda mu ke yaƙi dashi ni dake, gashi yazo mana har gida."
Islaha ta ce, "gaskiya tunda abin ya kai haka ya kamata a sanarwa da na gaba da Umma su ɗauki mataki. Kuma wallahi Mama ce take zugata, a gabana na ji suna maganar. Ke Mama ta wuce duk yadda ake tunani, ni kaina haka aka saka ni a gaba wai sai na tafi aiki. Kin san bazan iya shiru ba, na kalle ta nace wallahi bazan je ba."
Safeera ta ce, "Gaskiya Mama ta cuce ni, tana neman ruguza min rayuwa gabaɗaya."
Islaha ta ce, "ki yi haƙuri kawai, ki fara faɗa musu ta waya kafin ki je. In zuwan ya kama sai in raka ki."
Safeera ta ɗaga kai tana dafe da kanta kafin ta ce, "me ya faru, na ji Hamma Saheer yana cewa zaki je gidan Addarsa?."
Islaha ta taɓe baki ta ce, "to ni meye ma bai faru ba? Mamansa kin san ba ƙaunata take yi ba. Yarinyar nan Hanan ce ta ɗaga hannu ta mare ni, ai kuwa kafin ta sauke na mare ta har sau biyu. Shine fa Mama wai sai na duƙa na bata haƙuri, ke ma kin san sauran."
Safeera ta yi dariya ta ce, "Allah ya shirya min ke Islaha, ƙanwar mijin naki ki ka mara?."
"Ƙanwarsa ai Yayarsa ba ce, in ba dan Maman ba akwai wanda zan ɗagawa ƙafa a cikin gidan nan nasu ne? Wallahi babu wata halitta da zan saurarawa."
Safeera ta ce, "shine ki ka bar gida?."
"Cewa tayi na fita, har tana cewa indai tana da rai aurena da ɗanta bazai faru ba. Shine shima yazo yana cemin danasani na bada haƙurin waye waye, ban san na balbalesa da masifa ba, sai da naga yayi sanyi na fahimta."
"Kina wahalar da Hamma, dan kin ga yana da haƙuri da sanyi. Dan kuma kin san yana sonki ne. In ba shi ba, ba ko wanne namiji ne zai ɗauki wannan bala’in naki ba, da wuri za a yanke miki hukunci.”
"A'a fa, dan ina zaune a gidansu bazan ɗauki ko wanne wulaƙanci ba Bestie. Bani na ce ya karɓo ni daga orphange ba, shine ya dage ya takura sai da na bar gidan hankalinsa ya kwanta. Dan na dawo kuma bazan ɗauki raini ba wallahi."
Safeera ta yi murmushi ta ce, "ni so nake ayi auren a wuce wajan. Ko dan ya yi maganin wannan rashin kunyar nan ta ki."
"Ke ko ni na gaji, so nake nayi auren na huta da wannan tashin hankalin wallahi. Kin san me?."
Safeera ta girgiza kai ta ce, "ni fa zargina yana so ya tabbata akan gidan marayun da na tashi."
Safeera ta ce, "me ya faru?."
Ta miƙa mata wayarta, Safeera ta karɓa ta ce, "Islaha wannan ba Hafsa ba ce?."
"Itace, a hotel."
"Hotel kuma? To meye abin ɗaga hankali a nan? Kamar ni dake muna yaƙi akan ba iskanci ne kawai yake kai mace hotel ba. Kema jiya kin je ai ko?."
Islaha ta bata labarin duk abinda ya faru kafin ta ce, "so nake na haɗa hujja mai ƙarfi, so nake na tabbatar da zargina ya zama gaskiya. Wallahi sai mun shiga kotu, sai na san yadda na yi maganar nan ta je gaban gwamna, dan na san irin waɗannan badaƙalar bai san yana faruwa ba."
Safeera ta ce, "gaskiya ne wannan, in dai maganar ta tabbata wallahi kar ki bari."
"Sai ma kin ce, wallahi bazan barta ba. Shiyasa har na yi magana da Brr Suraj, na shigar da lauya cikin maganar, dan ba ƙaramin abu bane ba."
"Gaskiya ne wannan. Allah ya taimaka."
A lokacin Saleem ya shigo ya kalli Islaha ya ce, "islaha yau me yake damun masoyiyata ne? Gabaɗaya ko kallona bata yi ba."
Ta ɗan yi murmushi ta c, "bata jin daɗi ne shiyasa."
Ya kalli Safeera ya ce, "Sannu." Sai ya bata dariya ta ɗan sunkuya tana dariya kaɗan.
Muslim ne ya shigo yana faɗin, "Islaha wai an canja kati jiya?."
Islaha ta ɗauko katin ta ce, "Muslim in ba dan Allah ya kiyaye bai karɓa ba, da yanzu ina cell."
Sauka yi dariya gabaɗaya, ya karɓa yana dubawa ya ce, "ikon Allah, ko waye da wannan aikin oho."
"Koma waye dan kansa Muslim, ni aka so a tozarta Allah ya nuna musu basu isa ba. Tunda Allah ya kare ni ban damu na san waye ba, su suka sani" ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Saleem ya ce, "gaskiya ne, koma waye Allah ya mayar masa da muguntarsa kansa." Ta amsa da amin ta fita daga office ɗin. Da Ummi suka haɗu bata kula su ba ta wuce.
Ummi office ta shiga ta kira Muslim a waya, babu jimawa ya shiga wajanta ta ce, "kaga kallon rainin da yarinyar nan take yi min? Yanzu haka zamu zuba ido tana yin abinda taga dama a gidan nan muna gani?."
Ya kalle ta ya ce, "ta tsallake jiya, amma baza ta tsallake tarko na gaba ba wallahi."