PAGE 21
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 021.*
Islaha a kiɗime take bincika wayarta amma babu hotunan Hafsa babu alamarsu. Ta duba trash da duk inda take tunanin zata gansu amma babu.
Mamaki da al'ajabi ya kamata, ta riƙe baki zuciyarta tana bugawa cike da tsoro.
Da hanzari ta juya ta koma office ɗinsu Safeera, tana shiga ta ce, "Safeera kin goge hotunan da na nuna miki ne?."
Safeera da mamaki ta ce, "ban goge ba, ta ya zan goge waɗannan hotuna nan masu amfani?."
Islaha ta dafe kai ta ce, "Safeera daga fita ta daga office ɗin nan an goge hotunan nan, an goge su wallahi."
Safeera ta miƙe tsaye cike da tashin hankali, ta kalli Saleem da yake kallonsu, ta sake kallon Islaha. Cikin mamaki ta ce, "An goge kuma!."
"An goge su, babu inda ban duba ba, amma ban gansu ba."
Safeera ta ce, "Islaha wallahi ban goge ba, ni ban san ma kin bar wayar nan a office ɗin nan."
Saleem ya ce, "me yake faruwa? Wanne hotuna ne?."
Islaha bata kula shi ba ta ce, "da ki ka fita daga nan waye ya shigo?."
"Ban sani ba, da na san wayarki a nan bazan fita na barta a nan ba."
Ta dafe kai ta ce, "Daga ni sai ke, sai Hamma da Barr ne kaɗai muka san da hotunan nan, waye ya san dasu har ya biyo ni office ya goge?."
Safeera ta ce, "Wallahi nidai ban goge miki ba, akan me zan goge to?."
Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "dallah bana zarginki, ki daina yi min rantsuwa. Abin ne ya....."sai ta kasa ƙarasawa ta dafe kanta cikin yanayin da bata san meye ba.
Saleem ya ce, "kun barni a duhu, ku faɗa min abinda ya faru mana. Wanne hotunana aka goge?."
Islaha ta kalle sa ta ce, "ka yi haƙuri, bazan iya faɗa maka a yanzu ba, amma nan gaba kana daga cikin waɗanda zasu sani. Safeera in kin gama mu wuce kawai" ta faɗa tana fita daga offife ɗin cikin mamakin wanda ya san da hotunan har ya goge.
A wannan yanayi ta kira Saheer ya zo ya ɗauke su a mota suka tafi.
Tunda suka shiga bata ce komai ba, tana tunanin wanda ya goge hotunan nan, tana mamakin ya aka yi aka san dasu har aka biyo ta aka goge?. Kuma gashi a wajen aiki ne, kenan an san ta ɗauki hotunan?. Amma babu wanda ya ganta, ko an ganta ai ba a san ta yi hoto da video ba. Lallai akwai lauje cikin naɗi, dole ta dage sosai akan lamarin nan, dan taga ba abin wasa bane ba.
Saheer ya katse mata tunani, ya ce, "Baffa ya ce na mayar dake gida, ko gidan Addn kar ki je."
Ta ɗago ido ta kalle sa suka haɗa ido, ya ɗauke kai ya ce, "Ya kira ki ba ki ɗauka ba, ya ba da umarnin in mayar dake gida. Amma in baza ki koma ba ki kira sa ki faɗa masa, sai in kai ki inda ki ke so."
Shiru ta yi bata tanka ba dan bata san me zata ce ba, ta ya zata iya yi masa musu akan maganar Baffa? Ai ko bata so dole ta yi haƙuri.
Har suka je ƙofar gidan bata ce komai ba, sai da ya tsayar da motar Safeera ta ce, "Hamma sai anjima."
Ya yi murmushi ya ce, "To Safeera, a gaishe da Umma." Bata ce komai ba ta fita ta shiga gida.
Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ka san meye?."
Ya kalle ta ya ce, "ina jinki."
"Hotunan nan da na nuna maka na hafsa?" Ta faɗa da sigar tambaya.
Ya girgiza kai ya ce, "ina ji."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "wallahi an goge su Hamma."
Ya buɗe ido cike da mamaki ya ce, "kamar ya an goge? Waye ya goge su?."
Ta ɗan tafa hannunta ta ce, "wallahi ban sani ba Hamma, abinda na sani na gama nunawa Safeera kenan, sai na bar wayar a office ɗinsu na fita naje na dawo. Ashe itama ta fita bata san na bar wayar a wajan ba, wallahi dana dawo na duba babu su ko alama."
Saheer ya ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. Mu ga wayar."
Ba musu ta miƙa masa ya karɓa yana dubawa, kafin ya ɗago ya ce, "An goge su gabaɗaya."
Cike da damuwa ta ce, "ban san waye ya goge ba."
"Waye ya san dasu?."
"Daga kai sai safeera, sai....." sai bata ƙarasa ba tana kallonsa.
Ya bita da kallo ya ce, "Sai waye?."
Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "Barr Suraj. Na sanar dashi ne saboda shine lauyan da nake so ya yj handling case ɗin. Kuma na tura masa, amma view once."
Ya zuba mata ido yana kallon ta har ta kai ƙarshe, kafin ya ce, "waye ya saka ki tura masa?."
Ta kalle sa ta ce, "Saboda lauya ne, dole ina da buƙatar lauya."
"To yanzu amfanin me hakan zai yi miki?."
Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya yi tsaki ya ce, "Bakya jin magana Islaha, bakya jin magana kwata-kwata shiyasa bakya jin maganata. Sai da na faɗa miki kar kowa ya san maganar nan amma sai da ki ka zagaye ki ka faɗa masa. Dan kin faɗawa Safeera ba laifi bane, Safeera ƴar uwa ce a gare mu gabaɗaya. Amma shi fa?."
Ta rausayar da kai ta ce, "shima ɗan uwa ne a gare ni."
Ya harare ta ya ce, "yanzu me gari ya waya? Meye amfanin faɗa masa ɗin?."
Ta sauke numfashi ta ce, "Wallahi bana zargin Barr ko kaɗan, na san bazai aikata min haka ba."
Ya kalle ta yana harɗe hannu a ƙirji ya ce, "tunda shi bakya zarginsa, faɗa min ni ko Safeera waye abin zargi?."
Ganin yadda ya kafe ta da ido sai ya bata dariya, ta yi dariya dan ta san yana matuƙar kishi da Suraj, tunda Suraj ya furta yana sonta shikenan Hamma yake jin haushinsa.
Ta kalle sa ta ce, "ni na isa? Wace ni da ce haka?."
Bai ce komai ba ya ɗauke kai daga kallonta bai kula ta ba. Islaha ta ce, "duk wanda ya goge ma ya je dan kansa, sun yi a banza dan wallahi bazan bar maganar nan ba."
Ya kalle ta yana girgiza kai ya ce, "hakan alamu ne na ana bibiyar ki, hakan alamu ne da an san kina bincike akan lamarin nan."
"Hakan kuma shine alamar da take nuna min zargina gaskiya ne Hamma. Zamu haɗu dasu Hafsan, zan san duk abinda zan yi akan maganar nan."
Ya bita da kallo a sanyaye ya ce, "ki bi komai a hankali, kin ga gobe zan yi tafiya, don Allah ki nutsu."
Ta yi murmushi ta ce, "To Hamma."
Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "akwai abinci na siya miki" ya faɗa yana ɗauko ledar ya miƙa mata ya ce, "ki bawa Safeera sai ki riƙe sauran. Kayanki na kai miki ɗakinki na ajjiye."
Ta yi murmushi tana wasa da hannunta bata ce komai ba. Saheerya ce, "ya jikin, kin daina jin ciwon?."
"Na daina, daman yanayi ne kawai."
Ya ɗaga kai ya ce, "ki shiga ciki, zan shigo in anjima."
Ta ɗaga kai tana murmuahi yana kallon ta. Ya ce, "Debbo am."
Ta kalle sa ya ce, "da na dawo daga Niger za a yi auren mu in sha Allah, ina so na mallake ki nan kusa."
Ta yi dariya ta ce, "Allah ya dawo min da kai lafiya Hamma."
"Amin matar Hamma. Ki je ciki, ki fara shiga wajan Baffa yace yana son ganinki. Nima yanzu zan shigo." Ta amsa da to ta fita daga motar ta fara shiga gidansu Safeera.
Da ƙanwar Safeera suka haɗu, ta bata abincin ta koma dan bata son haɗuwa da Ummansu Safeera.
Kamar yadda ya ce wajen Baffa ta shiga, yana ganinta ya yi murmushi ya ce, "Islaha kin dawo?."
Ta yi murmushi itama, ta ƙarasa ta zauna ta ce, "na dawo Baffa. Ina yini?."
"Lafiya lau, ya aikin na ki?."
"Alhamdu lillah Baffa."
"To ma sha Allah. Saheer ya faɗa min duk abinda ya faru, ki cigaba da haƙuri kin ji? Ko wanne bawa akwai irin tasa jarabawar, ke taki ga a yadda tazo miki, ki yi ƙoƙari ki cinye sai ki dace. Kar komai ya dame ni, indai ina gidan nan baza ki wulaƙanta ba."
Ta yi murmushi ta ce, "In sha Allah Baffa. Amma Baffa sai na ga kamar baka da lafiya."
"Eh haka ne Islaha, kwana biyu bana jin daɗi. Ina fama da ciwon haƙarƙari, ga zazzaɓi. Kin san jikin tsufa, abin sai a hankali."
Islaha ta ce, "Allah ya ƙara lafiya."
"Amin."
"Ki cigaba da haƙuri, kar wani abu ya kuma faruwa ki ce zaki bar gidan nan, har abada nan gidanku ne, kin ji?." Ta yi murmushi bata ce komai ba.
Baffa ya ce, "Tashi ki je, Allah ya yi miki albarka." Ta amsa da amin ta miƙe ta fita daga ɗakin Baffan.
Da ta shiga ɓangaren Mama bata nan, ɓangaren shiru babu kowa. Hakan ya yi nata daɗi sosai, ta ci abincin da Saheer ya bata, ta gama duk abinda zata yi babu mai takura mata.
Islaha har ta yi bacci Mama bata dawo ba, hakan ya saka ta yi baccinta hankali kwance ba tare da wata damuwa ba.
Bayan sallar asuba Saheer ya shigo yiwa Mama sallama, ya shiga ɗakinta ya samu ta koma bacci.
Yana fitowa ya haɗu da Hanan, Saheer ya bita da kallo ya ce, "jiya a ina ki ka yini har dare?."
Hanan ta ce, "muna tare da Mama fa."
Ya girgiza kai ya ce, "ki yi yadda ki ka zaɓa Hanan, duniya dai ta ishe ki." Daga haka ya bata waje ya fita yana kiran Islaha a waya.
Tana zaune tana azkhar taga kiransa, ta miƙe ta fito ta gansa riƙe da jaka yana kallon ta.
Hawaye suka cika mata ido, haka kawai ta ji bata so ya tafi ya barta, duk da yana irin wannan tafiyar amma wannan karon sai ta ji ta damu.
Ta ƙaraso a sanyaye ya bita da kallo har ta zo inda yake, ya ce, "Matar Hamma zan tafi, ki yi min addu'a."
Hawaye ya sakko mata, ta ɗago ta kalle sa ta ce, "bana so ka tafi."
Saheer ya kalle ta, cikin damuwa da rauni ya ce, "meye na kukan? Kina so na fasa tafiyar ne?."
Ta ɗaga kai alamun eh, ya gyara tsayuwa yana gifanta da murmushi ya ce, "In na zauna da me zan aure ki? Kin manta kina da tsada, dole sai na dage na nemo sannan zan mallakeki?."
Ta kalle sa har tana ɗaga hannu sama, ta ce, "ni na yafe maka komai, kawai a ɗaura auren, ba sai ka bani komai ba."
Ya wara ido waje cikin tsokana ya ce, "duk wannan halittar a kyauta za a bani?."
Islaha ta ɗaga masa kai alamun eh, dan da gaske bata so ya tafi, da ya tafi gwara a aura masa ita ɗin ba tare da ya bata komai ba.
Ya yi murmushi ya ce, "Daɗin sai ya yi min yawa ai, sai na zama mai son kaina. Ina ni ina ɗaukar matar Hamma a kyauta? Daraja da matsayin matar Hamma ya wuce haka, dole na fita na nemo na aure ta. Dan tana da tsada sosai, dole sai na dage da neman kuɗi."
Cikin rauni ta ce, "Allah ni bana so ka tafi, indai akan neman kuɗin aurena zaka tafi gwara mu zauna a ɗaura auren, ni ko sadakin sai in yafe."
Saheer ya yi dariya mai sauti, ya bita da kallon ƙauna ya ce, "Har sadakin sai a yafe min matar Hamma?."
Cikin shagwaɓa ta ce, "i'm not joking, Allah so ka je ko ina. Haka kawai yau bana son tafiyar nan, ji nake kamar in ka tafi komai zai canja, don Allah ka zauna."
Ganin da gaske take ba shagwaɓar da ta saba yi masa bace sai ya nutsu ya ce, "Meyasa bakya so?."
"Ina ji kamar wani abun zai faru in ka tafi. Kamar...Kamar....ni dai ina jin kamar komai zai canja in baka nan."
"Babu abinda zai faru sai alkhairi, wani lokacin samuwar alkahiri tana zuwa a haka, kafin ya samu haka ake ji kamar abu mara kyau zai faru. Ki kwantar da hankalinki, zan dawo mu yi aure, ki haifa min kyawawa yara, masu irin fatarki, hancinki, girar ki, da bakin ki....."
Ta ɗan sunkuyar da kai tana murmushi, shima ya yi murmushi ya ce, "kin san abinda ya fi komai burge ni a fuskar ki?."
Islaha ta ɗago ta kalle sa, ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Bakin ki! Yana ɗaukar hankalina sosai, musamman a yanayi irin wannan."
Ta sunkuyar da kai tana wasa da hijjab ɗin jikinta bata ce komai ba.