BARRISTER SUHAIL

33

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----33

Na’ima ta tsaya tana kuka kamar ranta zai fita

Mami ta tashi ta bisu ganin yadda suhail ya shiga komai zai iya faruwa

tana shiga taga abinda Suhail yayi wa naima

Suhail! Ka haukace ne? Saboda wachan ƴar Malan din shine zaka mari ƙanwarka"

Suhail ya juya ya kalli Mami

“Mami idan ba zaki iya tsawatar mata akan iman ba ni zanyi mami ki tuna ko bakomai yarinyar Amana a wajen mu,but mami while the All hate duk kun bi kun tsaneta ba tare da wani dalili Iman is innocent kuma banda ta samu tarbiya mai kyau daga iyayen da sai rama duk abinda kuke yi mata"

"ke kadai zaki yi mata abu a gidan na kyale bayan ke duk wanda yayi mata wallahi sai na mishi ko wanene"

baki mami ta saki cike da mamaki  tana kallon sa bata taɓa ganin suhail a yanayin baccin rai irin haka ba 

cikin zafin rai ya bar ɗakin zuciyar har tafasa take sai huchi yake tamkar namijin zakayan

mami ta juwa wajen na'ima "next time ki kiyayye duk abinda zaki mata har kiyi a gaban idanun sa kinga dai an riga an asiri ce mana shi har an fara ƙoƙarin raba ku dashi"

share hawayen tayi ta ce"mami kullum kara tsanar yarinyar nake Suhail bai taɓa daura hannunsa a kaina ba sai sanadiyar Iman"

Iman na zaune gefe Guda tare da aunty Fauziya gaba ɗaya hankalin gaba jikin baya jikin ta 

bawai Abinda na'ima ta yi mata ya tsaye mata ba Tun da aka ɗaura auren nan take jin kamar rayuwarta ta tsaya cak 

Suhail ya nufo inda suke hannunta ya kama yaja ta suka bar wajen ƙoƙarin kwachewa take amman ta ƙasa cikin mota ya wurga ya shiga driver seat ya zauna

tsoron Suhail ya cika zuciyatar ganin bata saba ganin a yanayin irin wannan ba ganin duk ta tsorata dashi ya saisaita fushin sa kare mata kallo yayi 

ganin dan karamin veil din data yafa duk ya bayyana surar jikin ta ga dinkin ya dan kamata

"waya baki karamin gyalen nan"

"aunty Zarah ce" ta faɗa ciki wata siririyar murya da ko fita batayi 

bakin shago sayar da abaya yayi parking ya fito da leda ya miƙa mata "wear it" shine abinda ya faɗa

amsa tayi ta fara kokarin sakawa 

ba wanda ya sake magana duk zaton gida zai Kaita da mamakin sai ta taga yayi hanyar gidan malan  da ita haka kawai taji ta tsinci kanta cikin farin ciki 

ta jima tana son tazo taga Ammin ta Amman bata san taya zata fadawa Suhail ya kai taba

a halin da take ciki yanzu bata da Burin da ya wuce ta ganta gaban iyayyen ta wanda duk duniya basu hada kaunar ta da kowa 

bayan yayi parking ya juyo ya kalle ta "gobe zan dawo na dauke ki kuma ki fadawa malan jibi zamu koma Abuja"

"Abuja kuma" ta faɗa

kai ya daga mata "zan haɗe ku tare da Zeenah"

bata sake magana ta buɗe kofar motar ta fita 

a tsakar gida ta ishe ammi tana kwashe kayan wanki da gudu ta faɗa jikin ta rungume ta  Ammi ta saki kayan dan gaba daya tsoro taji bata tsammaci ganin Iman a wannan lokacin ba

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce"Kai iman wai yaushe zaki girma ne"

murmushi tayi ta ce"haba Ammi ai indai a wajen kine da Malan bazan taɓa girma ba"

Kayan da Ammi ta zubar ta fara kashewa suka shiga ciki 

Ammi sai kallon Iman take ta rame ta ƙara wani haske

"daga ina kike da yammar nan"

"yaya Suhail ne ya kawo ni ya ce sai gobe zai dawo ya dauke ni"

Ammi ta ce"lafiya dai ko Iman

Murmushi Iman tayi.

“Lafiya ƙalau Ammi.”

Sai dai murmushin nata bai kai zuciyarta ba a iya kan fuskar ta kawai ya tsaya

Ammi ta lura da hakan
Tun daga ranar da Iman ta shiga gidan Suhail, ta san duk lokacin da wani abu ya dame ta, idanunta ne suke fara tona asirin da ke zuciyarta

Abayar jikin ta cire ta shiga dakin ta,ta cire kayan jikin kin sun fara takura mata bata samu Ammi a falon hakan yasa tayi kwanciyar akan kujera 

daren ranar tare suka ci abinci da Ammi tuwan Masara ne miyar danyar kuɓewa taji man shanu sai Kamshi take 

Ammi na lura da yadda Iman bata cin abinci sosai sai wasa da take dashi ba Kamar da ba ta idan akwai wani abinci da tafi so ya biyo bayan wannan ne

Ammi ta kalleta gaba daya ta tafi duniyar tunani koda ta kira sunan ta bata ji ba sai da ta taɓo ta juyo a rude

Ammi ta zare hannun ta daga ƙwanan Abincin ta maida sa gefe 

Ta maida hankalin ta ga iman
"khadija Ashe kina da wata uwar data fini kina cikin damuwa amman ki kasa buɗe baki ki faɗamin idan baki gaya min ba kike dashi da zaki faɗa wa ina lura da ke tun zuwan da kikayi kwanaki akwai damuwar da kike boyewa"

Iman ta sunkuyar da kai.

Nan take idanunta suka cika da ƙwalla

Ta yi ƙoƙarin danne hawayen amma ta kasa

Ammi ta matsa kusa da ita.

“Iman, me ya faru?”

Shiru ta yi na ɗan lokaci.

Sai kuma ta fashe da kuka

Kukan da tun lokacin  da aka ɗaura auren Suhail da Zeenah take riƙe da shi a ƙirjinta

Ammi ta rungume ta

Cikin kuka ta ce

“Ammi… Yaya Suhail ya yi aure yau"

Jikin Ammi ya yi sanyi

Ta yi shiru na wasu dakiku

sai yanzu take gaskata mafarkin ta tun cikin satin nan mafarki Iman take kuma baya da nasaba da auren da mijin ta yayi a yau 

A hankali ta shafa bayanta cikin kulawa 

bata son ta nuna wa Iman damuwar ta a hankali ta ce"dan mijin ya kara aure ba wai yana nufin baya sanki bane Iman, kuma addinin sa ya yarje masa ya auri mace fiye da ɗaya matuƙar zaiyi adalci akan su"

"na sani Ammi"

"to miya sa kike damuwa kawai dan ya kara aure"

cikin kuka Iman ta ce"Ammi nima na rasa Na yi ƙoƙarin karɓa Ammi amman zuciyata ta ƙasa duk lokacin da na tuna sai naji zuciyata na min ciwo"


Ammi ta fahimci kishi ne kawai ke dawainiya da ƴar ta duk ka yaushe ma tayi auren da har tasan tayi kishin mijinta hakan ya tabbatar da tana son shi kenan tunda har take kishi a kansa

"ki cigaba da addu'a in sha Allah zakiji saukin abinda ke damun ki" 

nasiha mai ratsa jiki Ammi tayi mata har sai taji damuwar da take ciki ta soma raguwa ko ba komai ta samu wanda ta tattauna damuwar da shi 

a daren ranar bayan Ammi ta kaiwa Malan Abinci take faɗa masa Suhail yayi aure yayi mamakin yadda akayi ta sani ta ce"Ai iman ta faɗa mata yanzu haka ma tana daki"

Malan ya ce"ai shi baban Suhail da kansa yazo ya faɗa masa komai har ya sheda masa ma sun daɗe da Yarinyar ai tun kan Iman"

Ammi ta fahimta ta ce"Allah ya basu zaman lafiya"

Malan ya ce"Amin ya Allah"

hirar suka dan taɓa daga bisani Ammi ta koma dakin ta ta tarad da Iman har tayi bacci ta dade tana kallon ta cikin idanun tausayi hannu ta daga ta roki Allah ya sassauta yarinyarta kishi dake adabar zuciya 

daren Ranar  Ammi bata runtsa ba kwana tayi tana sallah Wada tayi sane musamman saboda iman 


sai da aka kira sallar Asuba ta tada Iman tare sukayi sallar bayan ta gama fita daura masu abincin safe iman kuma ta gyara musu gidany