34
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----34
Bayan Iman ta gama gyaran gidan ta shiga kitchen ta tarar da Ammi tana sauke kunun gyada daga wuta
Iman ta soya pancake bayan sun kammala taje tayi wanka ta saka wata doguwar riga mai mayafi
Ammi ta bata Abincin malan ta kai masa yana zaune a dakin yana jan charbi da sallama iman ta shiga
bayan ta ajiye abincin ta gaida shi cike da ladabi
malan ya ce"Iman kina lafiya ko ya mai gidan naki"
"Alhamdullilah Malan"
"dama ko kamar kinsan ina son magana da ke akan auren ya mijin ha kara"
dago idanunta tayi tana kallon sa bata yin mamakin yadda malan ya sani ba kila ko Ammi ce ta fada masa gyaran murya yayi ya ce"ai tun a baya mayafin sa ya sameni akan maganar zai kara auren nasan halin ki nasan wacece ki kiji tsoron Allah Akan abokiyar zaman ki Iman, ki sani kishi abu ne da Allah Ya halicci mata da shi, saboda haka ba laifi bane ki ji zafi Amma laifi shine ki bari kishin ya sa ki manta da Allah ko ya sa ki zalunci wani
Duk lokacin da kishi ya taso miki, maimakon ki zauna kina kuka, ki yi alwala ki yi raka’a biyu,Ki roƙi Allah Ya gyara zuciyarki,Domin yaƙin da yafi wahala ba wanda ake yi da mutane ba ne, yaƙin da ake yi da zuciya ne
ki taya mijinki wajen ganin ya sauke nauyin da allah ya daura masa ki zama mai haƙuri da juriya aduk halin da kika tsinci kanki a gaba kar ki zama mai yawon ƙorafi ko nuna fushi nan take wannan ba halin Mutanen kwarai bane ki zama mak yafiya ga duk wanda kike tare dasu domin Allah yasan mutune masu hakuri da tafiya
Kai Iman ta sunkuyar tana jin kalaman Malam suna sauka a zuciyarta ɗaya bayan ɗaya kamar ruwan sama a ƙasa mai ƙishirwa
maganganun sun shiga jikin ta kuma ta saka su cikin zuciyar zatayi amfani dasu duk wani haushin Suhail da ta jima tana ji a hankali ya soma raguwa hakan na nufin nasihar Malan ta soma aiki akanta
Cikin sanyin murya ta ce"in sha Allah malan zanyi ƙoƙarin haka"
“Allah Ya yi miki albarka Iman, Ya ba ki zuri’a ta gari masu biyayya fiye da yadda kika yi mana"
"Ameen"
tashi tayi sanyi qlau ta fita a baranda ta iske Ammi ra tisa kwanan abincin tana jiran ta ido ta zaro ganin bata fara cin abinci ba ta ce"Ammi wai ni kika tsaya jira ai da kinci kar yayi sanyi"
"sanyi na yaushe kuma,Imankinje kin zauna wajen malan sai surutu kuke "
hannu tasa ta fara cin abinci
karfe biyu na rana motar Suhail tayi parking kofar gidan Malan,ganin ba kowa kofar gidan Suhail ya samu yaro yayi masa iso koda ya fito yaga Suhail ya bashi izinin shigowa cikin gidan
Iman na zaune tsakar gida tana gyaran zogalen da ammi zatayi Dambu dashi Suhail ya shigo kamar an ta ce ta kalli kofa eye Contact suka haɗa da Suhail da sauri ta janye idanun ta daga kansa
dakin mala ya shiga bayan sun Gaisa malam yayi masa Allah sanya Alkhairi wani irin nauyi yaji wanda har yasa ya ƙasa amsa addu'ar da yake yi masu
Malan ya kalli Suhail cikin nutsuwa ya ce"Suhail, ka sani aure ba soyayya kawai bane, amanar Allah ne,Ka ji tsoron ranar da zaka tsaya gaban Allah Domin ba za a tambaye ka nawa ka kashe wa matanka ba, za a tambaye ka adalcin da kayi a tsakaninsu karka bari ɗaya ta ji kamar ka fifita ɗayar a kanta.”
Suhail ya sunkuyar da kai yana sauraro
Na san Iman yarinya ce mai haƙuri, amma kar ka kuskura ka ɗauki haƙurinta a matsayin rauni Mace mai haƙuri idan zuciyarta ta karye, wani lokacin ba ta sake komawa yadda take ba
kar ka dauka ina goyon bayan ƴa ta ina faɗa dan kasan da wa kake zaune
Kalmomin sun shiga zuciyar Suhail
"Allah baka ikon sauke nauyin da Allah ya dora maka"
sai lokacin Suhail yayi magana"Amin malan Nagode kuma zanyi ƙoƙarin sauke nauyin da Allah ya dora min"
kudi ya dauko a aljihun masu yawa ya ajiye a gaban Malan
malan ya ce"a'a shi bazai karɓa ba"
Suhail ya ce"malan idan baka amshi kudin nan ba zan dauka kana jin haushi nane saboda nawa iman kishiya"
Malan ya yi murmushi kawai ba tare da ya ƙara magana ba, Suhail kuma ya miƙe ya fita.”
Suhail na fita ya bude Boot din mota ya kira yara suka fara shiga da kayan Abinci masu tarin yawa sai da suka kusa cika taskar gidan malan
har suka kammala shigowa da kayan iman tafi su da kallo kayan abincin da Suhail kaw tamkar za'a bude shago
malan kansa sai da yayi Mamaki bare Ammi da fitowar kenan daga daki bama tasan da zuwan suhail ba. ganin kayan
ta ce"Malan wannan"
"Suhail ne ya kawo"
kai ta jinjina a ranta ta ce"kila kayan rufin baki ne ya kawo kar a ga laifin sa"
A fili ku ta ce"Angode"
juyawa tayi ta koma dakin malan ga kalli iman ya ce"ba jiran ki yake ba ki shiga ki hado kayan ki ku tafi"
daki ta kuma ta dauko jakar da tayi musu sallama suka wuce
lokaci zuwa lokaci take satar kallo Iman so take taje wani abu amman yaƙi bata fuska
"yaya Suhail"
juyowa yayi ya kalleta
"thank You so much for the food stuff"
Da mamaki ya kalleta
"did i ask you to thank me ko kinaso ki nuna min Malan ke kadai ya haifa banda ni"
kai ta girgiza suka cigaba da tafiya har suka kai gida a kofar gida yayi parking suka shiga
Har falo "ki shirya karfe biyar Flight din zai tashi zuwa Abuja"
kai ta daga masa
a falon ya zauna wayar ya dauko ya ga misscall zeeenah kusan biyar
wanda a yanzu ma ta soma bashi haushi tun ranar da akayi daurin aure yaso ta tare Saboda iman amman taƙi wai a bata kwana biyu
ya rasa wannan changin nata ko na miye gaba daya bata cikin hankalin ta
Iman na shiga daki wanka kawai tayi ta haɗa duk wani abu da tasan mai Amfani waje guda wanka tayi ta shirya cikin wata black egypian abaya
light make up tayi tayi wani irin masifar kyau tayi rolling da gyalen hill ta saka ta dauko Black hand bag din ta rike a falo ta sami Suhail agogon hannun sa ya duba karfe hudu da rabi trolley din hannun ta ya amsa ya saka a mota
tunda ta fito yake kallon idan kaga iman zaka rantse irin wayyayun matan nan ne da suka gaji da boko
a filin airport yayi parking suka fito
gaba daya hankalin mutane ya dawo kansu ya Allah"beautiful couples"
ba ƙaramin dacewa suka yi da juna tun da zasu Fara hawa jirgin Iman ta riƙe Suhail wannan shine karin Farko da ta taɓa hawa jirgi a rayuwar ta tsoro fal a zuciyar ta
ya lura da hakan shiyasa ya bata damar riƙe sa har zuwan kann kujeru bayan Mutanen sun gama shiga a hankali ya fara tashi har lokaci Iman na jikin sa
kallon ta yayi cike da kulawa"are You okay"
kaii ta daga masa kwanciya tayi a jikin sa
a haka har bacci ya dauke ta
sai da suka sauka ya tashe ta bolt ya kira ta dauke zuwa sabon gidan dake copa cabana estate dake cikin garin Abuja
end