Chapter 4
by @reza12
MATAR MAZA
Ganin yadda ya matso kusa da ita ne yasa ta fasa wani uban ihu Kamar wanda yayi mata wani abun. Ya tsaya yana ta kallonta kusan minti biyu kafin ya sake kiran sunanta hankali. Ta ce "Ni gida nake son zuwa gurin Hajiya, dan Allah ka barni na tafi, bana son zama anan ka rabu dani" Ta faɗa cikin kuka. "Ok tom shikenan zan kaiki, amma ina so kiyi shiru tukunna, kuma ga nama nazo miki da shi, idan kinci ni da kaina zan kaiki gurin Hajiya nayi alƙawari". Ɗago kai da sauri ta kalleshi ta kalli ledar da yake nuna mata. Ta ce "Ni na koshi ba zanci ba, kawai ka kaini yanzu". "No dole sai kinci zan iya kaiki, muddin baki ciba to banyi alƙawari ba". Jin haka yasa ta saki jiki ta ci kazar kaɗan, ya bata ayaba itama taci kaɗan. Kafin ya lallabata suka yi sallah, yayi musu addu'a. Suna shafawa ta miƙe tsaye ta ce "Muje" ya mike tsaye shima ya ce "Tom ina zuwa bari na kwashe kayan nan na kai kiching". Ya tattara kayan zai fita itama ta biyo shi, har cikin kiching ɗin tana binsa, ya ajiye ya fito ya koma ɗakin nan ma ta biyo shi. Ya ɗauki wayar hannunsa ya nuna mata ya ce "Karfe nawa yanzu?" Ta kalli agogon ganin sha ɗaya da arba'in. Ta faɗa masa da muryar kuka. Ya ce "To yanzu kinga dare yayi kawai..." Ai tana jin haka ta fashe masa da wani irin kuka mai lasisi, sosai take yi harda hawa da sauƙa, duk yadda ya so da tayi shiru taki, ihu sosai kamar ana bugunta. Haka ta cigaba da kuka duk ta hana su barci, har sai kusan ɗaya tayi shiru. Izuwa lokacin ya haƙura ya kwanta saidai ya kasa barci. Yana ji ta kwanta a ƙasa, ai kuwa bata dade ba barci yayi gaba da ita. Ya tashi ya dawo da ita kan gadon ya ƙura mata ido. Haka kawai Allah ya ɗora masa son yarinyar, tun ganinta na farko yaji ta tafi da imaninsa, duk yadda ake ta faɗin halinta na rashin kunya amma sai yaji kamar ma kara masa sonta ake yi, kuma dama shi da yake tafiye-tafiye yana son Mace irinta wacce bata da sakin fuska, kuma Mace doguwa fara siririya mai kyau, sannan ƴar gayu ta fita kunya. Kuma mai ilimin zamani, kuma duk Azima ta haɗa, kawai matsalar shine da bata sonsa, kuma ya shirya koya mata sonsa ko tana so ko bata so, muddin da gaske zuciya tana son mai kyautata mata to zuciyar Azima zata so shi ko ta yaya. Kiss yayi mata a goshi yana sake kallon kyakkyawar fuskarta yana godewa Allah da ya bashi ita, domin har ga Allah kyawunta na daga cikin abun da ya fara jan hankalin sa gareta. Kasancewar ana sanyi yasa ya lulluɓe ta da bargo ya koma gefe barci yayi gaba da shi.
Sosai Malam Musa ya ɗaura ɗamarar zama da halin Azima duk yadda tazo masa dashi, a cikin wata ɗaya da suka yi babu irin abun da baya mata, amma har lokacin baya gabanta, sannan bata bashi haɗin kai ba, ko kusa da ita ma bata yarda yazo. Girki shine zai mata, haka a cikin wata ɗayan nan taje gida sau kusan ashirin, domin kusan kullum sai taje, kuma duk shi yake kaita da kansa ya dawo da ita a motarsa. Hatta abinci wani lokacin sai ya gama tace bata son wannan, abubuwa dai iri-iri take masa. Sosai fa Azima ta samu guri, huta ya fara nunawa a jikinta, daga taci sai barci, gashi ya sakar mata bakin aljihu duk abun da take so shi takeyi. Har yan uwansa na mamakin yadda har wata ɗaya ba'a ji wata matsala a tsakanin suba, kuma kullum tana hanyar gida. Itama bangaren ta, ko kaɗan bata jin sonsa, kuma bata da burin kashe auran dalilin Baba da tasan muddin hakan ya tabbata to zai iya yanka ta a soya namanta a cinye. Sai dai ta sa a ranta idan ta gaji zai rabu da ita ko baya so. Dama hutun wata ɗaya aka bashi a gurin aiki, hakan yasa ya fara shirin komawa, koda ya faɗa mata cewar tare zasu tafi tayi tsalle ta dake akan sam ita ba zata iya binsa har wata ƙasar ba, to ina zata bar Hajiya da kannenta. Nan fa ya nuna mata nasa ɓacin ran amma ta ce ko sama da ƙasa zasu haɗe ba zata bishi ba. Sai lokacin Musa ya sake tabbatar da halin Azima na kafiya da rashin kuwa, domin bata ko jin shakkar sa zata kalli cikin idanunsa tace ba zata je ba, abun ya ɓata masa ko ba komai ya chanchanci girmamawa, ko maganar ce ma tayi masa cikin roƙo mana da girmamawa. Hakan yasa ya kasa haƙuri, yaje ya fadawa mahaifiyar sa, da yake matar tana son Azima itama sosai, sannan itama tana bata girmanta, dama ita matsalar ta kawai a rainata ko a shiga sabgarta, muddin ba haka ba to tana da kirki da kuma iya zama da mutane. Haka Mahaifiyar Musa da wata yayarsa da Suke cewa Anty suka zo har gidan domin lallaɓa Azima. Nan suka mata faɗa da nasiha, akan mai zai hana ba zata bi shi ba, ita bata tsoron ma yaje ya haɗu da wasu manta acen ne. Sai da suka gama ta fashe musu da kuka, ita dai wallahi ba zata iya tafiya ba, dama ita Anty ba son yarinyar take ba. Hakan yasa taja tsaki tana kallon Musa da ya fara bata hakuri ganin tana kuka. Haka a gabansu ya shiga lallashinta har itama mamar ta buɗe baki da mamaki tana kallon ikon Allah. Haka suka tafi ba tare da ta yarda ba. Shima dole ya haƙura domin baya son ya kaita gurin Baba, dan wallahi har cikin gidan zaizo yayi mata duka, shi kuma baya son haka, yafi so ya tafi da ita ta daɗin rai. Haka dole ya hada kaya ya bar Nigeria zuwa Ƙasar Maroco inda yake aiki ba tare da matarsa ba.
Tun da ya tafi kuma kaninsa mai suna Mudam ya saka mata ido, haka zai zo gidan tun safe har dare, daga yaci wannan ya yasa ta dafa masa wannan, sannan ɗan yawon ma da take sanyi duk yasa dole ta rage. Sannan danginsa ma gaba ɗaya sun sauya mata, kusan kullum sai wasu sun zo, kuma tsaf ta kula neman magana da gulma ke kawo su. Shi kansa Mudam ɗin gane turosa akayi domin ya sa mata ido, yaga abubuwan da take yi. Kusan wata ɗaya da tafiyarsa shima Mudan ɗin ya rage zuwa gidan, amma kullum zai zo daddare yaci abinci, wani lokacin ma sai ta fara barci zai tashe ta yace ta dafa masa. Da taga abun nasa bana ƙare bane, domin shi dama tun kafin auran ta san shi ya santa, gasu dai yan uwa ne amma san baya shiga gonar ta itama haka, sau ɗaya Abu ya taɓa haɗa ta da shi, nan ma bai musu dad'i ba, hakan yasa basa ko ga maciji da shi da ita. Ganin dai so yake ya maisheta yar aiki yasa duk lokacin da ya zo zata ce ba zata dafa ba, idan yana so ya shiga ya dafa, a ranar ma har faɗa suka yi yana cewa idan ya ga dama zai mata duka ta bar gidan, jin haka yasa tace idan ya isa ko sau ɗaya ya taɓa ta, faɗa dai sosai harda zage-zage da zagin Iyaye. Washegari ya kai ƙarar ta gurin Mamarsu, ai kuwa aka turo Anty tazo tai mata tatas, amma hakan dai bata sauya ba, suka kira Musa akan tsara masa karya da gaskiya nan ma dai sai ya goyi da bayan matarsa akan to me yake kai shi Mudam ɗin gidan nasa, shi ai bai aike shi ba. Wannan dalilin ya ƙara tada wutar bala'i aka ce wai Hajiya ce ta bata asiri taiwa Musa, dama ai Itama shi tayi ta mallake Baba. Maganganu dai ya dinga yawo a cikin dangi ta ko ina.
Wata biyar yayi ya dawo, izuwa lokacin Azima ta sake girma sosai tayi tsayi, sannan ta ƙara cika saboda ta samu hutu sosai, ba abun da ta nema ta rasa. Lokacin da ya ganta kamar ya haɗiye ta tsabar so da kewa da kuma sha'awar ta. Nan ma duk yadda yaso ta bashi haɗin kai taƙi, duk yadda yayi ta ki yarda, yayi riƙon da magiyar amma sai ta fashe da kuka akan ita tsoro take ji ba zata iya ba. Haka aka cigaba da irin zaman baya. Babu irin kulawa da tarairaya da baya mata amma dai abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, izuwa lokacin duk ƴan uwansa sun fahimci irin son da yake mata, hakan yasa gaba ɗaya suka tsaneta. A wannan karan da hutunsa ya ƙare ya mata maganar tafiya nan ma tace ba zata je ba, kar ma ya ɓata bakinsa. Ai kuwa baiyi wata-wata ba ya haɗa ta da Baba domin wannan karan ba zai iya jurewa ba, tabbas yana bukatar matarsa a kusa da shi. Magana ɗaya baba yayi mata ta, akan idan bata bisa ba zai zo gidan nan sai ya karyata, ai kuwa tuni ta isa gida da kuka tana fadawa Hajiya, itama ta ce to da mai take nufi, dole ta haɗa kaya ta bi mijinta, haka dole ta fara shiri ran nan a ɓace, sati ɗaya suka ƙara jirgin su ya tashi zuwa Maroco.
Sosai tayi kuka harda zazzaɓi, ko magana taƙi tai masa, duk ta ɗora masa laifin Komai. Sati ɗaya da zuwa ta warware, sai dai kewar gida. Idan ya tafi aiki ya barta ita ɗaya haka za tai ta tsoro domin bata ko fita waje, wannan dalin yasa wani lokaci yake tafiya da ita gurin aikin. A wannan tsakanin yayi sa'a ta bashi haɗin kai a dalilin kusan ko yaushe suna tare, ba tare da tursasawa ba ya mayar da ita cikakkiyar matar aure. Ba ƙaramin dad'i yaji ba da ya sameta yadda yayi zato, sai dai fa ya shafe sati yana lallashi da jinyarta, sosai ta samu nayi, tun daga lokacin kuma wata sabuwar soyayya da kulawa ta fara. Itama dai duk da bata fara sonsa ba, amma ta rage wasu abubuwan da take masa, ta ɗauki auran nasa a matsayin Ƙaddarar ta, kuma zata zauna. Sosai yake bata kuɗaɗe masu yawa, kuma idan za su koma Nigeria haka zasu je tare yasa ta sayi duk abun da take so. Ita kuwa zata jidi kaya na Hajiya da kannenta harda Baba. Haka suka kwashe shekara biyu tare, izuwa lokacin ta sake girma ta zama babbar Mace domin ta buɗe sosai, duk masu yi mata fatan mutuwar aure tuni san haƙura, sai aka koma cewa ta mallake shi da asiri. A wannan tsakanin ne Sadiya ta fara ciwon ido, da yake suna Nigeria da zama yasa kusan kullum tana hanyar gida. Kakarsu mahaifiyar Hajiya, itace ta faɗa musu cewar a kwai asibitin da suke aikin ido mai kyau anan Niger inda take, hakan ne yasa Azima ta shiga fafutukan neman kudin da za ai mata aikin. Kaman yadda kowa ya santa Mace ce ita mai kamar Maza ta fannin tsayawa da kanta, ko Baba bata iya tambayar Abu, dan dama-dama ma Hajiya lokacin tana ƙarama. Bata so faɗa masa ba amma shi da kansa ya gano kamar tana cikin damuwa, bayan ta sanar masa da abun da take son yi ne kuma bata da kuɗi, ai kuwa nan ya bata kuɗin masu yasa, take kuwa aka tafi da Sadiya gurin magani a Niger. Tai masa godiya domin taji daɗin abun da yayi mata. A lokacin yana Maroco, sai aka kai masa maganar cewar Azima tana fita babu hijjabi, kuma kullum tana kan hanya, wanda shi kansa ya santa, bata son saka hijjabi, idan har yaga tasa hijjabi to sai dai ko gidan Hajiya zasu je, zai ce idan bata sa ba sun fasa, shine zata saka, shima hakan tun farkon auransu ne. Ana wannan halin ciki ya baiyana a jikin Azima. Waiyoo Allah murna kashe bayin Allah. Sosai daga shi har ita kowa yake murna, amma kamar dai ya fita son cikin. A dalilin wannan cikin ta dawo zaman Nigeria, yanzu ko zai tafi shi ɗaya ne yake tafiya, Yusra ta dawo gidan da zama domin ta taimaka mata. Kullum kuwa Musa na kiranta yaji lafiyar ta da ta ɗan nasu. Bangaren Sadiya ma tana cen ana mata aiki, itama tayi murna jin Azima ta samu ciki. Haka taci gaba da rainon cikinta har ya kai lokacin aihuwa ta haifi ƴa mace. Mai kama da ubanta sosai kamar an tsaga kara. Ranar suna taci sunan Fadila. Har zuwa lokacin Azima tana jin kawai zama da Musa ya zamar mata kaman dole ne, domin ko kaɗan bata jin sonsa, wannan aihuwar da tayi kuma sai ya zama kamar wani girma da cika ta ƙara, ga kyau da aihuwar tayi mata. Shekarar Fadila biyu da aihuwa Sadiya ta dawo gida cikin sa'a idanunta sun warke. Sai dai ba'a fi sati ɗaya ba ta fara ganin dishi-dishi hakan yasa dole ta sake komawa. Shima dai komawar Azima ce ta tsaya mata. Da yake yanzu ta fara kasuwanci tsakanin Maroco da Nigeria, Musa ya bata jari tana sayan kaya tana turowa nan. Sosai kuma Allah ya dafa mata, Fadila kuwa dama cen gurin mahaifiyar sa suke barinta domin tayi wayo sosai. Ranar tana gida take jin gabanta nata faɗuwa, hakan yasa ta kasa natsuwa ta kira shi ko yana lafiya, yace mata lafiya lau yake gashi nan ma zai je shigo gida. Sai dai har lokacin bata daina jin faduwar gaba ba. Ai kuwa misalin ƙarfe bakwai taga kira daga number Yusra, take gabanta ya faɗi, wani irin tsoro ya kamata saboda abun da ya darsa mata. Daga jin muryar Yusra cikin kuka yasa kawai Itama ta fashe da kuka tana aiyanawa Hajiya ta mutu. Cikin kuka ta ce "Anty Azima Baba ya mutu". Ta faɗa tana sake fashewa da wani sabon kukan. Daidai lokacin shima Musa ake faɗa masa ta kiran da ya shigo masa waya. Salati kawai yake yi yana kallon yadda ta tsayar da kukan ta kasa ko motsi. Ta ce "Waye ya mutu, Baba ne da gaske? Baba na ne, da gaske ya mutu?" Ta shiga tashin hankali da fargaba. Washegari kuwa suka dawo Nigeria izuwa lokacin an binne shi ana zaman makoki. Tana shiga gidan ta nufi ɗakin Hajiya suka dasa sabon kuka gaba dayansu. Sosai wannan mutuwar ta taɓa duk wani dan ahalin wannan gidan daga marayun da yake riko har masu iyayen. Har sadakar bakwai Azima bata bar gida ba, sai da a kayi kwana goma.
(Wannan mutuwar ce tayi sanadiyar komai da zai faru a wannan labarin. Daga yanzu hargitsin rayuwar Azima zai fara)
Wata huɗu da rasuwar Baba gida ya tarwatse. Gidan da suke ciki dama ance ba za'a raba ba, kowacce ta zauna a sashen da take, sauran abubuwa kuma aka raba, dama su gaba ɗaya bangaren su mata ne, yasa babu abun kirkin da suka tsira da shi. Ya zama Azima ce ke daukar ɗawainiyar yan uwanta. Wannan dalilin yasa ƴan Musa sukayi chaa a kansa akan ta yaya za'a bari komai ita keyi da dukiyarsa. Farko yana goyan bayan ta, duk abun da suka ce yace matar sa ce ta isa tayi komai da dukiyarsa. Kusan kullum zaka ganta a gida tazo tayi musu girki, ga jikin Hajiya da kusan kullum sai ya tashi, gashi Sadiya ma tana cen gurin magani har yanzu. Wasa-wasa fa zuga ya fara shigarsa, ya fara fito mata da wasu sabbin halaye wanda bata taɓa tunanin zai iya ba. Da yake ya dawo hutu, sai ya ce ta daina fita akai-akai, kuma dole ta koma saka hijjabi idan zata fita, sannan wannan almabazarancin da take yi dole ta rage. Jin haka yasa ran Azima ɓaci, domin ita Mace ce da ta tsani gori da wulaƙanci. Hakan yasa ta daina amfani da komai nasa, sai dai nata, sai dai ba'a kai ko ina ba ta cinye uwar kuɗi da ribar kasuwancin nata. A lokacin shi kuma Musa ya shirya ya horar da ita, ganin dai yanzu ko bata so dole ta zauna da shi, saboda ko taje gidan ba komai, zaman gidan nasa ne dai dole. Idan zata fita ya ce bai barta ba, komai tayi faɗa, abu kaɗan zai bata laifi, duk ta kasa gane masa, a gida kuma Hajiya na bukatar ta, domin ciwo dai kusan kullum sai ya tashi, kuma Sadiya da ta ke da ɗan wayo bata nan. A daidai wannan lokacin ta shirya biye masa duk abun da yake nema, domin yanzu Baba baya nan kuma bata shirya tsayawa shan wulaƙancin ɗa namiji ba, koda zai sake ta wallahi sai ta je gida domin taimakawa yan uwanta.
Da ƙyar ta haɗa kuɗin da Sadiya zata dawo daga gurin magani ta tura mata. Hakan yasa ta kirata akan karfe goma na safe zata sauƙa tazo ta taryota domin jirgi ta biya mata Niger to Nigeria. Shine fa tun shida ta shirya zata je gida tayi mata girki kafin tazo, ko kayan abincin ma a cikin nata na gida ta ɗiba kamar dai yadda ta saba. Amma Musa yace babu inda zata je, saboda yanzu dole ne ya nuna mata cewar shine gatanta, kaman yadda yan uwansa suka zuga shi, cewar ya daina bari tana yin abun da taga dama, dole ya kwaci yancin ya, ya dawo namiji a gidan sa. Sosai take mamakin sa, dama haka yake, kenan dama saboda Baba ne yasa ya zauna da ita a baya, har yake haƙuri da ita. Shekara shida kenan da auransu, basu taɓa yin faɗa mai girma irin wannan ba, domin ita dai bata jin akwai wanda ya isa ya hana ta zuwa tarɓar yar uwar ta. Shi kuma domin ya nuna mata cewar bata da wani gata sai nasa yasa shi faɗin idan ta fita a bakin auranta. Yasan ba zata iya yarda ta rabu da auran nasa ba, saboda bata da gurin zuwa, domin ko gidan nasu ma dai taje iya abinci ma ya ishe su bare sauran abubuwan rayuwa. Sosai kalmar ta ɗan bata tsoro da farko, domin dai ta gane saki yake nufi idan ta fita, duk da bata taɓa jin sonsa ba, amma kalmar tazo mata a bazata, take wani irin ƙwarin guiwa yazo mata najin kenan dai idan ta fita ta rabu da auran Musa kenan. Ai kuwa take tayi waje abunta. Da yake lokacin har goma ɗin ma ta yi yasa ta wuce filin jirgi abunta. Bata fadawa kowa ba har ta kawo Sadiya gida. Sai dai kallo ɗaya za kai mata ka gane tana cikin damuwa da rudani domin sai take ganin kamar tayi wawta, a wannan lokacin da basu da kowa tana bukatar zaman gidan miji ko ba komai zata taimaki yan uwanta. Ta kalli Fadila da take ta wasa a jikin Hajiya da yake tare suka taho da ita, sai kawai ta kawar da kai tana tunanin mafita. Wani irin rauni ne ke son kamata idan ta kalli yadda Hajiya ta rame ga sauran kannenta suma duk babu ta fara nunawa a jikinsu. Saƙo ta ji ya shigo mata cikin wayarta, tana dubawa taga shine ya turo mata message ya sake jaddada mata sakin kuma yace kar ta dawo masa gida tunda bata da hankali bata jin magana. Sauke ajiyar zuciya kawai tayi bata cewa kowa komai ba har lokacin. Ganin zata kwana a gidan ne yasa Hajiya tambayar ta ba zata tafi gidanta bane, sai tace mata shine yace ta kwana. A cikin daren kuwa taje gidan Musa da yake tana da ɗan maƙulli ta kwaso kayanta wanda take so, wanda bata so kuwa ta bar masa a gidan, anan ta hado sauran kuɗaɗen da basu da yawa. A cikin daren ta bawa Sadiya gaba ɗaya sauran kuɗin, tace duk abun da suke bukata su saya ita zata je Niger ne gurin kakarsu domin ta huta, kuma karta faɗawa Hajiya dan Allah. Sadiya ta fashe da kuka jin wai auran ta ya mutu, tana girgiza mata kai amma ina Azima a kwai abun da take tunani a ranta. Ai kuwa washegari ta kama hanyar Niger domin bata so Hajiya tasan da batun mutuwar auran tana gabanta, dan komai zai iya faruwa. Ai kuwa washegari da safe Sadiya ta kasa ɓoye wannan maganar ta sanar wa da Hajiya cewar auran Azima ya mutu...📝
Wata Ƙaddarar tana da wahalar jurewa. Shin yaya rayuwar Azima zata kasance bayan mutuwar auren? Gashi basu da komai, Baba ya rasu, kuma gashi itama ta bar Nigeria ta tafi Niger.