Sawun Giwa

05

by @ammimalami99


~~


Karar gudun da El Yakoub yakeyi akan treadmill ne kadai sautin dake fita a cikin gym din. Bai bar office ba a ranar sai wajen karfe shida dab da maghrib shiyasa saida ya tsaya wajen masu siyar da abincin nan ya siya abinci tukunna ya wuce gida. Yana isowa kuwa ana kiran maghrib dan haka bai ma shiga cikin gidan ba yaje masallacin yayi sallah tukunna ya dawo. 


Yayi wanka da ruwa masu dumi suna narkar mai da duk wata gajiya da yakeji a cikin jikinsa. Saida ya gama cin abincin nan tukunna yana zaune akan kujerar parlour da plate din abincin a gabansa da bai dauke ba ya kira wayar mahaifiyarsa Hajiya Firdausi. Mai aikinta Shema'u ce ta dauki wayar kamar koh yaushe suka gaisa tukunna ta kaiwa Hajiyar wayar. Ya tambayeta idan an mata gashin kafarta na yau bayan sun gaisa nan fa ta fara mai bayanin yanda sam wannan sabuwar nurse din da aka kawo mata bata iya aikinta ba dan ruwan zafin da take amfani dasu har tiriri sukeyi toh kuma idan ba kona mata kafa takeso tayi ba ya za'ayi ta ringa mata gashi da ruwa masu zafi haka. 


El Yakoub ya ringa mata bayanin cewa ai Nurse din daga babbar asibiti ya dakko mata ita tayi hakuri kar a chanja wata amma tace bata san zancen ba dama tun jiya take cewa Shema'u ta kira mata shi a chanja mata ita amma Shema'un taki. El Yakoub ya bata hakuri yace za'a chanja shikenan kuma sai ta kwantar da hankalinta har akalar zancen tasu ta chanja zuwa tambayar yaya aikin nasa yake tafiya da yi mai addu'ar Allah ya bada sa'a kafin suka kashe wayar. 


Ya kira Mahmoud ( babban yaronsa na Abuja kuma secretary dinsa na office ) yace mai Hajiya tace a chanja mata nurse dinnan. Dama tun farko wata Nurse Falmata ce take kula da Hajiyar wacca ta kusan shekara daya tana musu aiki amma sai aka mata transfer daga Abuja zuwa wata asibiti dake Lagos shikenan fa Hajiyar bata sake wata Nurse data kwanta mata ba. Kowacce aka kawo sai ta samu wani abu guda daya da zata kushe ta dashi shikuwa El Yakoub baya taba gajiya da bauta mata dan Allah ya sanya masa tausayin mahaifiyarsa a ransa duk kuwa da irin rayuwar data jefa shi a ciki a baya na kaddarar auren Muneera. 


Yana yin sallahr Isha ya shirya cikin kayan gym dinsa dogon wando sweat pants da kuma wata bakar riga mai dogon hannu sai takalmansa da katuwar gorarsa ta ruwa. Gym din farkon da yaje sam bai masa ba dan mutane ne da yawa ke shige da fice kamar kiyashi daga mata har maza shiyasa ya sake duba wani a map ya nufe sa duk nisan sa kuwa. Da yaje kuwa ya samu abunda yakeso dan yanada kyau gym din kuma ba wasu mutane bane da yawa dan har ya gama abunda zaiyi ya hau treadmill din dai daikoun mutane ne da suka gama ma suka barsa shi kadai a gym din. 


Ya kai hannunsa ya danna saman fuskar treadmill din daya bada d'an karamin sauti gudunsa na karuwa. Ya cigaba da gudun dukda yanda yakejin zuciyarsa na hauhawa wannan zafin na kokarin fara zagaye kirjinsa. Likitansa dama ya masa gargadi kan gudun treadmill dinnan shikuwa a rayuwa bashida escape kamar gudun nan. Shi kadai ne wani abu guda daya da yake mantar dashi duniyar da yake ciki ta yanxu, ya tube mai sunan da duniya ta sanshi dashi as YK Ventures, ya yaye mai wannan nauyin da sunan ke dauke dashi. Ya maidashi mutum, d'a da kuma uba. Wannan d'an da yayi kokarin nunawa mahaifiyarsa hanya, d'anda yayi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya nunawa mahaifiyarsa cewa hanyar da take ganin mai bullewa ce ba zata kaisu ga komai ba sai duhu. D'a ga mahaifinsa da kasa ta rufewa ido tun kafin ya girma ya zama wani abun da zaiyi alfahari dashi. Sannan kuma uba, uba ga d'ansa da Muneera ta raba shi dashi ta karfi da yaji. Uban ga d'anda baya tunanin koh fuskar sa zai iya tunawa yanxu. 


Ya cigaba da gudun nan fuskar Muneera na fitowa cikin ganinsa yayinda wannan igiyar ke cigaba da tamke zuciyarsa wannan zafin yana zagaye kirjinsa. Wayarsa dake cikin d'an karamin console dinda akayi jikin treadmill din ta dauki karamin sauti alamar shigowar sakon daya saka ba shiri ya danna stop jikin treadmill din lokaci daya gudunsa na ragewa har saida ya tsaya. El Yakoub ya kama gefe da gefen treadmill din yana sauke jerin numfashi saboda yanda zuciyarsa keta tsere a kirjinsa kamar zata buge allon kirjin ne ta fito. 

Ya cigaba da sauke numfashi har zuwa lokacinda yaji numfashinsa na kokarin daidaita saidai wannan zafin da kirjinsa yakeyi koh kadan bai daina ba. Ya ciro wayarsa daga cikin console din ya kalla layin sakon da Mahmoud ya turo masa 


'An tura kudin watan nan y'allabai'


Sai kawai ya rufe wayar ya sakata cikin aljihunsa kafin ya dakko gorarsa yana sauka daga treadmill din. Locker room din gym din ya wuce direct yana jin wannan zafin yana cigaba da kara yawa har yana haddasa masa sakin huci akai akai. Saida ya dakko y'ar karamar jakarsa da abubuwan bukatarsa na gym din suke ciki tukunna ya fice daga wajen. Kafafuwansa na takowa wajen harabar sassanyar iskar dake busawa ta dake sa sabannin iskar cikin gym din dake a gume. Ya shaki iskar mai yawa har yana lumshe idanuwansa yanaji dama iskar zata bi ta fatarsa ta shige har cikin kirjinsa ta tafiyar mai da wannan zafin. Ya bude motarsa ya shiga ya ajiye jakar a dayan seat din tareda gorar kafin ya bude console dinnan ya ciro maganinsa ya ballo daya yana dora sa kasan harshensa. Ya lumshe idanuwansa ahankali yana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa a kirjinsa. 


A kace kowani mutum da tasa kaddarar, yasani cewa bazai taba iya gujewa kaddararsa ba koh ya bijirewa Allah saboda kawai yana jarabtarsa dan bayan Muneera da kuma d'ansa babban jarabawarsa shine wannan ciwon. Ciwon da bakin cikin Muneera da rashin d'ansa ne ya haddasa masa shi. 


"Ka hakura Saraki, ka hakura kawai mutane nan sunfi karfin mu yanxu


Ya tuna kalaman Habeeb na wannan lokacin. 


"Ya za'ayi kace na hakura da d'ana? taya?


Tasa muryar dake fitowa tareda kuncin da zuciyarsa take ciki a wannan lokacin ta dawo masa a kai. 


"Right now Muneera tanada hujjar da zata iya kaika prison ka fahimce ni. Mubi abun nan a hankali"


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel


Ya furta kalmomin da yanzu ma su ya kama a bakinsa kafin ya shiga jero addu'oin da a duk lokacinda ya shiga wani hali irin wannan yake karantowa Allah su. 



~~~


Muneera Ibrahim Indimi y'a ce ga wani babban d'an kasuwa wanda sunansa yayi fice a kasar Nigeria. Ita kadai ce y'ar da Allah ya azurtasa da ita wadda bayan ita matarsa bata sake haihuwa ba har Allah yayi mata rasuwa wannan ne dalilin da ya saka ya kara aure. Ya auri kanwar Hajiya Firdausi mai suna Umaima. Itama kuma Allah bai azurta da koh da barin ciki ba bare haihuwa wanda hakan sosai ya tada hankalinta da na maigidanta.


Sunje asibitoci da dama ana duba ta amma babu sa'a har sai da suka fita kasar waje tukunna aka musu gwaji duk su biyu wanda result ya fito Ibrahim din shine yakeda matsalar rashin haihuwa. Magani kuwa ba wanda ba'ayi ba, manyan manyan asibitoci na duniya duka anje ba'a samu sa'a ba har suka hakura suka mika lamarin su ga Allah. Wannan dalilin ne ya saka Ibrahim Indimi ya dauki soyayyar duniya ya dora akan y'arsa Muneera babu abunda ta nema ta rasa. Shagwabata da ririta ta yakeyi kamar y'ar gwal. Duniya ta sheda sannan kowa ya sheda gabaki daya dukkan dukiyar da Indimi ya mallaka toh a sunan Muneera take. Dukkanin kamfanoninsa da wasu gidajen mai duk mallakin Muneera ne wannan ne dalilin da ya saka kowane saurayi ke kokarin gwada sa'arsa a wajenta dukda kankantar shekarunta dan bata wuce shekaru ashirin ba a wannan lokacin. 


Lokacinda Hajiya Firdausi ta sanarwa da El Yakoub mafitar data samo musu na dawo da dukiyar da suka rasa ta hanyar auren Muneera ki yayi. Ya nuna mata cewa babu wata riba da wannan auren zai kawo musu sannan kuma shi da bai wuci shekaru ashirin da daya ba ma taya za'ayi yayi aure. Yayi kokarin nuna mata cewa makaranta yake har wannan lokacin aure ba shine a gabansa ba amma ina a wannan lokacin Hajiyar tareda kanwarta Umaima sun riga da sun shafawa idanuwansu bakar tokar da taki basu damar ganin abunda El Yakoub din ke nuna musu. 

Duk yanda yabi dasu kuwa nuna masa sukeyi sun isa dashi kuma abunda sukeso shi zaiyi dan Umaima har rantsuwa tayi bazai yiwu ta zauna da Indimi ba shekara nawa sannan tazo tayi biyu babu. Ba haihuwar ba dukiyar, dan koh lokacinda akayi gwajin nan aka gano shine da matsala sai da ya bata zabin zama koh rabuwa dashi taje tayi aurenta amma sanin cewa idan ta fita ta bar dukiya da daula ya saka ta yarda ta zauna dashi din. 


Tun daga wannan lokacin kuwa El Yakoub bazai ce ga takaimai man abunda ya faru ba dan watanni biyar cif basu rufa ba aka daura mai aure da Muneera. Watannin biyar dinda da za'a bude kwakwalwarsa a binciko su a duba za'a gansu ne tamkar wucewar iska dan duk lokacinda yayi kokarin tuna su ba abunda yake iya hangowa a cikinsu sai duhu. 


Aurensu da Muneera da y'an watanni ba tareda sun shirya koh sun tsara da hakan ba ta wayi gari da jaririn ciki a cikinta. 



~~~


Da safe ne karfe bakwai da kusan rabi sassanyar iskar safiyar tana kadawa cikin tsakiyar gidan Mallam Bappah. Karar haduwar karfen tukunya da simintin dake shafe a filin gidan da Juwaira ke wankewa daga inda take zaune wajen wanke wankensu ya hade da kukan ragunan Mallam dake bayan gidan tareda karar dakan turmin da suke jiyowa daga gidan Hajiya Zulai makociyarsu. 


Labulen kofar dakin Inna ya dage Khausar na tako kafarta waje cikin shigarta ta uniform din makaranta da jakarta data rataya a kafada daya batareda ta sakala dayan hannun ba. Aisha ce biye a bayanta tana amsa Allah ya tsaren da Inna ke musu ta tako kafarta waje inda Khausar ke dakko sandals din makaranta da ke ajiye jikin tagar kofar dakin baccinsu Aishar ta sanya. Itama Aishar ta dakko nata flat shoes din ta ajiye a kasa kafin ta saka. 


"Karbi" ta fada tana mikawa Khausar basket din abincinta data dafa musu bayan ta gama sallahr asuba itama ta zubawa kanta cikin wata tsohuwar kular makarantar Khausar din irin mai rike zafin nan ta saka cikin wata jakar souvenier din bikin kawartar nan dataje inda Mu'azzam ya ganta wanda tunda ta nade jakar ta soka cikin wata akwatin sababbin kayanta bata sake waiwayenta ba sai yau. 


Khausar ta karba "Yaaya na dauki zobon?" 


Aisha ta gyada kanta tana mika mata darin data dakko daga cikin purse dinta tun dazu zata baiwa Khausar din dan tunda ta tashi take damunta kan tanaso ta tafi da zobon maman nana makaranta. 


"Jeki bata kudin tukunna"


Khausar ta karba kuwa ta nufi kitchen inda Maman Naanan take. Dai dai nan kuma Nana ta bude kofar bandakinsu ta fito da karamar buta a hannunta da brush da toothpaste dinda ta gama amfani dasu jikinta jike da ruwan wankan da ta gamayi. Dama cewa tayi tana da exams yau acewarta kenan ba, doguwar kalabar kanta na lilo gaban fuskarta lokacinda ta duka tana ajiye butar bakin kofar bandakin. 

Ta kai idonta kan Khausar da ta iso bakin kofar kitchen din tana mikawa Maman Naanan kudin zobon kafin ta sake juyowa tana saukesu akan Aisha da tayi wani sihirtaccen kyau cikin shigar datayi ranar cikin wata doguwar rigar atamfa mai ratsin ja da ya haska fatarta sosai dukda ba kwalliya tayi ba amma kalar ta karbeta matuka. Rigar atamfar wani ankon kawarsu ce ta Islamiyya da akayi bikinta shekarar da ta wuce. Nana ta tabe baki wani abu na ratsa zuciyarta mai kamada kishi, kishin yadda Aishar ta fi ta da kusan komai dan Allah ya gani ta tsani ma kallon Aishar idan tayi wata shigar. Ranar da akayi bikin nan sun dawo gida alokacin Nanar tanada wani saurayi Khaleed da yazo wajenta suna cikin mota suna hira tana nuna mai hotunan da tayi ranar bikin amma lokacinda Aishar tazo wucewa cikin gida ya bita da kallon da sai da Nana taji kamar ya soka mata mashi ne a tsakiyar ranta. 


Mesa ita datayi wani arnen dinkin da ya fitoda shape dinta kuma yayi mata kyau bazai kalleta ba sai Aishar da doguwar riga tayi da ba ka ma iya tantance yaya jikinta yake a cikin rigar? Me Aisha tafita dashi har da hankalinsa zai dauku daga zafafan hotunanta datake nuna masa? Yanxun ma ta sake jin wannan abun yana ratsa zuciyarta dan akowani lokaci idan tagan Aishar sai taji kanta kamar y'ar karamar tauraruwa a gefen wata wannan shine abunda yake cigaba da rura wutar tsanar Aisha a zuciyarta. Allah ya gani bazata taba iya sonta ba a zuciyarta har abada kuwa. 


"Ke kuma ina zakije na ganki da katuwar jaka haka" 


Nanan ta fada ga Aisha bayan ta ajiye butar hannunta tana kallon jakar souvenir dinnan. Aisha ta dago ta kalleta kuma tana kokarin bata amsa ne Juwaira data gama wanken wanken ta taje daukar tsintsiya dan ta share wajen da ruwan suka malalo tace 


"Office zataje"


Nanan ta tattare girarta waje daya 


"Office kamar ya" 


Juwaira tayi y'ar karamar dariya, y'ar karamar dariyar da ta huda wani katon huje a zuciyar Maman Naana da ke kitchen tana jiyosu. Taji kamar Juwairar da ita take. Dariya take mata kenan koh na cewar Aisha tayi gaba ta bar y'arta. 


"Ta samu aiki a kamfani ai yarinya" 


Juwairar ta fada tana bubbuga bakin tsintsiyar kwakwar data dakko. 

Nana taji wani abu ya soke ta a kirji da bata san ma shin ta wani bangaren yazo. Shin daga saitin inda Juwaira tayi maganar ne koh kuwa daga saitin inda Aisha take tsaye ne tana jira Khausar ta dauki zobon su wuce. 


"Lallai, har Aisha ta samu aiki a kamfani a gidan nan kuma ba'a samu wanda ya fada mun ba" 


Ta sake fada tana yiwa Aisha wani shegen kallon da ita Aishar bata ma san tanayi ba dan ita Allah Allah ma take ta fita dan a duk lokacinda Nana take nan batason abunda zai hadata da ita saboda tana ganin girma da mutuncin Maman Nana sosai. Bata taba so tayi wani abun da zai nuna bata girmama ta koh wani abu da zai janyo wa Inna matsala a wajenta shiyasa a duk lokacinda Nana zata tsiri fada da ita na babu gaira koh dalili shareta kawai takeyi duk kuwa da yanda abun yake tafarfasa mata zuciya. 


"Kin ajiyemu ai dole mu ringa kawo miki rahoton abunda yake faruwa a gidan da ba zamansa kikeyi ba" 


Juwaira ta bata amsa dan dama Nanar a wuyanta take. 


"Eh din ai nima ba ajiye ni kikayi a gidan ba da zan zauna muna kallon juna dake, Zaman gidan me zai tsinana mun. Idan kuma akwai wanda ya ajiye ni sai yazo ya daure mun kafa ya hanani fita" 


Aisha ta kama hannun Khausar suka fice daga gidan zuciyarta na mata zafin yadda Nana ke budar baki tana gayawa Juwairar data girmeta magana. Tana jin ciwon kuma yadda ita bazata iya tanka Nanar ba koh ta ramawa Juwaira. 

Lokaci daya chachar baki ta kaure tsakaninsu. Inna tana zaune a daki tana jan charbinta ahankali tana jinsu har izuwa lokacinda fadan nasu ya gangaro izuwa mutuwar auren Juwaira da kuma rashin aurenta har yanxu wanda Nana bata taba gajiya da ambatonsa a duk lokacinda suke fada. A irin wannan lokacin ne ya kamata ace Maman Naana ta dakatar da Nana tunda Mallam dakinsa na can hanyar waje ba jiyosu zaiyi ba. Ta fara mata fada akan idan ta sake jin bakin nan nata saita mata dukan da koh motsi bazata iyayi ba a gidan amma sai Inna taji shiru. Maman Naanan ta cigaba da harkokinta batareda tace komai ba. 

Inna ta girgiza kanta ahankali tana kokarin kawar da sabon tunanin dake kokarin dasa kansa a zuciyarta game da Maman Naanan. 



~~


Tana sauke Khausar a makaranta ta wuce kamfani. Suka gaisa da Ayo kafin ta shigewarta office dinta kuma koh mintina shida batayi kwakkwara da zama a wajen ba tana duba ayyukan da take dasu a gabanta Habeeb ya fito daga cikin office din El Yakoub. Suka gaisa dashi ya mata sannu da zuwa kafin ya mata bayanin yanda zata ringa hadawa El Yakoub schedules dinsa dan yanxu ma zai tura mata dukkan wasu abubuwan da suka tsara dashi zaiyi sati mai shigowa kasancewar yau jumu'a sannan a duk lokacinda ta shigo office zata je wajensa ne ta sanar dashi schedule dinshi na ranar. 


Tace mishi toh kafin ta fara aikin kuma ba karamin wahala tasha ba dan wasu abubuwan computern ma Allah yagani ita duk ta manta yanda akeyin su. Wasu abubuwan ma sai ta shiga youtube ta duba yanda akeyi tukunna. Tana aikin taji karar shigowar waya a Telephone dinda ke ajiye a gefenta. Kai tsaye kuma ta dauki wayar ta dora a kunnenta da tsammanin cewa Ayo ce kamar jiya saidai tausashiyar muryarsa mai cike da wannan amon ta daki kunnenta lokaci daya wanda ya saka ba shiri ta lumshe idanuwanta tana sake waresu. 


"Aisha" Ya kira sunanta. 


"Good morning sir" Ta samu zarafin gaishe sa bayan sakan daya da ya wuce da fadan sunan, dan saida ta jira yanda ya fadi sunan ya fada cikin kokon kwanyarta tukunna. 


"Morning" Ya amsata ta cikin wayar 


"Kabir nakeso ki kiramin ya sameni a office dina yanxu" Ya sake fada. 


"Sir?" Ta furta kalmar sir din cikin yanayi na tambaya dan bata san waye Kabir ba. Dududu ma mutane nawa ta san sunansu a kamfanin, daga Habeeb sai Ayo fa. 


Muryarsa ta fito cikin wayar cikin wani irin tone da ya taba zuciyar Aisha 


"Read your staff directory Aisha". 


Yana fada kuma ya sauke wayar. Ta kara sakan daya kafin ta ajiye wayar tana maimaita staff directory. Ita ba'a bata wani staff directory ba bare tasan waye Kabir. And why is he being strict to her. Gaskiyar kalaman y'an matan nan kenan, ashe dai bazata ji dadin aiki dashi ba. Ashe dai fatan Allah ya karbi addu'an Inna ne dagaske akan cewa duk tsaurin sa Allah ya dorata akansa. Ta fara bincikar na'urar sai gashi kuwa ashe akwai wani file a cikin File Explorer na staff directory din dake dauke da sunan kowa da yakeda office a kamfanin da kuma matsayinsa da kuma number ofiice dinsa da zata kira. Ta runtse idanuwanta ahankali, ita ai Habeeb bai fada mata wannan ba. Shi yanxu Sarakin kamar yanda taji ya kirasa zai ga kamar tana wasa da aikin koh? 

Kawai ta danna number Kabir din wanda ta gan ashe operations manager ne ta kira sa ta fada masa daga office din Ceo ne yana bukatar ganinsa kafin ta katse wayar. Ba jimawa Kabir din yazo tace mai ya shiga, shigar da bayan wani lokaci ya sake fitowa kafin kuma sha daya tayi mayawar Kabir office din ta kai uku. 

Karfe sha dayan da tun kafin tayi take kallon lokaci dan bata manta yanda ta tsaya a gabansa ba tana kallon yadda ya hada matchar nan da yadda ya juyo yana fada mata haka yakeso ta ringa hada mai shi kullum karfe sha daya. 


Ta tashi daga kan kujerarta ta nufi wajen ta fara hada matchar kaman yanda taga yayi. Saida ta hada komai ta zare straw din kamar yanda yayi shima jiya ta ajiye kafin ta bude fridge ta dakko robar fruit salad mai sanyi wanda mangon cikinsa yafi yawa da Habeeb ya shigo dasu dazu yace ta hada da matcha din ta kaimai. Ta nufi kofar ta kwankwasa sau biyu ta tura ta shiga tana rike da kofin matchar nan a hannunta da kuma bowl din a d'ayan hannun. 


Wani dogon bayani Kabir ke masa akan abunda ya tambayesa dan wani aikin ne ya basa ya mai kuma yaga kamar ya masa shirme a ciki. Shine ya kirasa ya mai bayanin yanda aka samu matsalar da sai yanxu Kabir din yake sanar mai da ita dan har komawa shi Kabir din yayi office dinsa kusan sau biyu yana tattaro wasu takardun. Kuma zai rantse yana gane duk abunda yake fada masa daki daki dalla dalla kafin Aisha ta kwankwasa kofar nan ta shigo yayi mistake din daga kai ya kalleta. Yaji sanda Kabir din ya tsayar da maganarsa na d'an sakanni kamar ya lura yanxu ba jin nasa yakeyi ba kafin ya cigaba. 


Ya samu nasarar yakice idanuwansa daga kanta. Aishar ce wai koh an chanja ta ne an kawo mai wata? Kawai itace tambayar da tazo ransa a wannan lokacin saboda yanda yaga ta chanja mai gabaki daya cikin wannan shigar tata ta atamfa, ga ratsin jan da atamfar ke da shi da ma jan gyalen data dora saman simple daurin datayi ya karbeta sosai yana sake dallaro mai hasken fatarta. 


Ya cigaba da kallon Kabir kuma tsakani da Allah bakinsa kawai yake kallo yana fata ya iya karantar me yake cewan dan kunnuwansa sun rufe kansu, kai kwakwalwar ce gabaki daya ma ta rufe kanta. Abunda bai sani ba a wannan lokacin ita kanta Aishar yabar shigarsa ta manyan kaya takeyi a ranta. Yanda launin shudin ya sake jaddada kyawu da haduwarsa, ga wani girma da ya kara mata a ido. Tayi saurin dauke idanuwanta daga kansa lokacinda ta karaso.


"Sir" ya jiyo muryarta a kusa dashi lokacinda take ajiye kofi kan teburinsa cikin wani dan karamin console da akayi na ajiye kofi sai bowl din a kusa da shi. Ashe kunnuwansa suna aiki har yanxu, Kabirun ne dai kawai baya jin me yake cewa. 


Ya gyada kansa kawai batareda ya sake kallon sashenta ba har lokacinda ta juya ta fice daga ofishin nasa. Ta cigaba da aikinta bayan ta dawo har izuwa lokacinda Kabir ya fice, El Yakoub ya turo mata wasu files da yace ta duba mai. Lokacin sallahr azahar Habeeb ya shigo office din nasu shima yau shigar manyan kayan yayi tunda Jumu'a ne. Tare suka fito Habeeb na dariyar wata maganar da El Yakoub ya fada 


"Haba Saraki ai kaima kasan wannan bazai ma yiwu ba" 


Yake fada cikin dariyar tasa data karade iskar office dinta. Daga inda take zaune ta dago idanuwanta ta dora kansa yana tafiya bayan Habeeb din d'an karamin murmushi a fuskarsa. Fuskarsa da kyawunta ya sake fitowa, ya fito asalin bahaushensa zagayayen sajensa na sake kawatar fuskar tareda murmushin, ga kuma hular da ya dora saman kansa. Hannunsa daya dardumarsa ce da ya riko baka kuma sai data gan yana kokarin dago idonsa ne ta sauke nata. 


Suka fice zuwa masallaci itama tayi sallarta dan dama tazo da wata dardumar ta da aka basu kyautar ta lokacinda sukayi walima a Islamiyya, irin marar nauyin nan masu jakarsu wadda idan ka gama saika nade ka mayar aciki. sukaje lunch break taci abincinta bayan ta gayawa Ayo bazataje wajen siyan abinci ba tazo da nata.


Tana gama cin abinci Mu'azzam na kiranta a waya kuma tana wayar ne El Yakoub ya turo kofar ya shigo.  


"Kinci abinci toh?"


Ta jiyo muryar Mu'azzam ta cikin wayar da muryarsa data kara kauri saboda daga bacci yace mata ya tashi. Da ta tambayesa bai je masallaci ba kenan kawai sai ya fara mata kame kamen ai kansa ne yaketa ciwo tun safe shine ya sha magani ya d'an kwanta har sallahr ta wucesa. Ta girgiza kanta kawai tana jin wani takaici yana mamaye mata zuciya dan ba wannan ne karo na farko ba. A yanda ta fahimta ma ba wani ciwon kan da yakeyi tun safe yake baccin bai tashi ba kuma sai yanxu.


"Babe?" 


Ta sake jiyo muryar Mu'azzam yana kiranta tunda bata amsa tambayar ba saboda yanda tagan El Yakoub din yana nufo teburinta kuma Allah yagani kasa ko motsi tayi dan kafinma hankalinta ya gama tantance wani abu ya sunkoya dai dai gefenta.



~~


Ehm ehmm🤭