PAGE 22
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 022.*
Islaha ko bacci bata iya komawa ba, tana zaune kawai tana kewar Hamma. Har Saheer ya yi mata waya yace motarsu ta tashi, ta sake yi masa fatan alkhairi kafin ta kashe.
A sanyaye ta tashi ta gyara ɗakin da take ciki, ta fita ta damawa Baffa kunun kanwa da yake yawan sha, ta dafa tea ta juye a flask sannan ta ɗauko doya ta fara gyarawa dan ta soya.
Har ta kammala ta yi wanka babu wanda ya tashi, ta fito ta sha tea ɗinta dan zata je su haɗu Zainab a inda ta ce su haɗu.
Ta gama kenan Mama ta fito tana amsa waya, Islaha ta tsaya cak har ta ƙaraso, sannan ta ajjiye wayar tana bin Islaha da banzan kallo.
Islaha ta ce, "Mama ina kwana? Hamma ya ce in faɗa miki ya wuce, ya shigo kina bacci" ta faɗa lokaci ɗaya, dan kar Mama ta ɓata mata rai ta manta bata faɗi saƙon Hamman ba.
"Uwar iyayi, dashi nake waya ai. Ɗanki ne ko ɗana?."
"Ɗanki ne Mama, ki yi haƙuri" ta faɗa a sanyaye dan haka kawai take jin kanta babu daɗi.
Mama ta bita da harara tana ƙwafa ya wuce bata ce komai ba.
Islaha ta yi ajiyar zuciya ta ɗauki handbag ɗinta ta fita daga gidan. Sai da ta fita sannan ta saka facemask, ta kawo cotton ta toshe kunnenta saboda iska, bayan ta saka hijjab har ƙasa.
Lokacin ƙarfe tara na safe, ta hau napep ta nufi makarantarsu Zainab dan a nan suka yi zasu haɗu.
Tana sauka ta yiwa Zainab waya bata ɗauka, ta ajjiye wayar tana jiran Zainab. Babu jimawa ta ƙaraso ta saka niƙab, dan Islaha bata gane ta ba sai da ta ƙaraso. Zainab ta zauna a kusa da ita ta ce, "Adda ina kwana."
"Lafiya lau Zainab, na fito dake da sassafe ko?."
"Babu komai Adda. Ki yi sauri kafin a farga bana nan, yau sun san bana zuwa lecture kuma ban sanar zan je yin kitso ba."
"Hafsa ta dawo gida ne?."
"Ta dawo, amma jiya da daddare an sake fita da ita. Hafsa gabaɗaya ta canja Adda, kashe kuɗi take yi yadda take so. Haka su Sauda suke yi suma, to itama ta shiga sahun su."
Islaha ta ce, "ba ki ga wata alama a tare da ita na rashin gaskiya ba?."
Ta girgiza kai ta ce, "yanzu sun daina hira dani, ko yaushe warewa suke yi ita da Fadwa."
Islaha ta ɗan yi shiru tana tunani, Zainab ta ce, "ranar da mu ka haɗu dake sai da aka kai ni wajan Mama, ta ce in dai ta sake ganina tare dake wallahi sai ta yi maganina."
Ta kalli Zainab ɗin ta ce, "ke ba a taɓa neman fita dake ba?."
"Na faɗa miki lokacin da aka kira mu office ɗin nida Hafsa cewa aka yi ni na je waje, daga ranar Hafsa ta canja. Dan yanzu ma ance babbar makarantar kuɗi zata koma da karatu."
Islaha ta dafata ta ce, "Zainab don Allah kar a kira ki ki aikata wani abun mara kyau, ki taimaki maraicinki, ki cigaba da sana'arki, har ki yi aure."
Ta ɗaga kai ta ce, "in sha Allah Adda bazan yi komai ba."
Islaha ta ce, "Yauwa, na san ke rainona ce, baza ki yi wani abu mara kyau ba. Na gode sosai, zaki iya komawa" ta faɗa tana buɗe jaka ta ɗauko dubu goma ta bata.
Islaha ta ce, "ki yi kuɗin mota, sannan ki siyi abinda ki ke so. Ko da za a ce ina ki ka je, ki nuna kuɗin kice kin je kin yiwa wata kitso ne ta baki.”
Zainab ta girgiza kai tana ji kamar ta faɗa mata matsalar da take damunta amma bakinta ya yi nauyi ta kasa. Daga nan suka yi sallama suka rabu kowa ya kama hanyarsa.
Islaha gida ta koma dan bata da inda zata je, bata da aiki kuma baza ta wahalar da kuɗinta ta je babu abinda zata yi ba.
Tana shiga ta ga Mama ta fito daga ɗakin Baffa hankali a tashe tana faɗin, "Islaha Baffa ba ya motsi!."
Gaban Islaha ya faɗi, bata taɓa jin kalmar da ta soki zuciyarta lokaci guda ba sai wannan, ta ji wani iri yarr a jikinta, kanta ya sara, naman jikinta ya fara rawa. Da hanzari ta bi Mama, ta shiga ɗakin taga Baffa kwance ya kumbura kamar wanda aka hura. Hankalinta ya tashi ta gigice, ta fito jikinta yana rawa ta rasa ya zata yi.
Waya ta ɗauka hannu yana rawa ta kira Sadik, yana ɗauka ta ce, "Hamma Sadik! Ka zo gidanmu, kazo gida, Baffa ba yamotsi, ka zo don Allah!."
Tsabar ruɗewa bata tsaya ta ji me yake faɗa ba ta kashe wayar tana kai kawo, suna tsaye ita da Mama da Labiba da Hanan, Islaha ta fi ce da gudu.
A lokacin Sadik ya shigo a ruɗe, ganin halin da Baffa yake ciki ya saka ya fita da hanzari nemo maza biyu a ƙofar gida, suka ɗauki Baffa aka saka mota.
Islaha ta shiga gaban motar, Mama da Labiba suka shiga kusa da Baffa aka ja motar suka tafi.
Babban asibiti suka tafi ɓangaren emergency, aka karɓi Baffa da gaggawa dan yanayin nasa abin tsoro ne, yana buƙatar kulawa da gaggawa.
Sun kasa tsayawa sai kai kawo suke yi ciki kiɗima da tashin hankali, Islaha kamar ta shiga ta ga abinda yake faruwa haka take ji. A lokacin take ji ina ma karatun likita ta yi, da yanzu ta san me ake yi a ciki, da tana ciki ana duba lafiyarsa tare da ita. Mintina ashirin da shigarsu, sannan nurse ɗin ya fito, ya kalli Sadik ya ce, "a je a siyo wannan maganin yanzun nan."
Sadik ya karɓa ya fita, ba jimawa ya dawo ya shiga ciki ya kai musu ya dawo ya zauna.
Har azahar ta yi suna wajan a tsaye, a wajan suka yi sallah suna jira su ji abinda za a faɗa musu akan Baffa amma shiru.
Sai ƙarfe biyu na rana sannan Sadik ya koma yake tambayarsu jikin Baffa. Likitan ya kalle sa ya ce, "yauwa daman ina neman ka, kai ɗansa ne?."
Sadik ya ce, "ni abokin ɗansa ne."
"Okay, ina iyalansa?."
"Suna waje."
"Kira su."
Sadik ya fita ba jimawa suka dawo dasu Mama suka zauna.
Likita ya ce, "majinyacin ku shine Mustapha Maddibo ko?."
Suka ɗaga kai alamun eh, ya sauke numfashi yana kallonsu ya ce, "ya taɓa fama da ciwon ƙoda ne?."
A tare gabansu ya faɗi a tare, kowa ya zaro ido jin ana maganar ƙoda. Mama ta ce, "bai taɓa ba."
Ya girgiza kai ya ce, "Jininsa ya hau sosai, sannan kuma sugar sa ma ya hau fiye da ƙa'ida."
Cikin ruɗewa Mama ta ce, "daman yana da hawan jini da sugar ne?."
Likita ya ɗaga kai, ganin hankalinsu ya tashi sosai sai ya ce, "ku shiga ciki ku ga yanayinsa."
Sadik ya miƙe zai fita sai Dr ya ce, "ban da kai abokina, akwai maganin da zaka siyo. Ku je" ya faɗa tana kallonsu Islaha.
Islaha ta ƙi fita, dan a yanayinsa ta fahimci ba lafiya ba, yana ɓoyewa ne saboda ya ga sun tayar da hankalinsu daga cewa ciwon ƙoda.
Har ta fita ta dawo, likitan ya kalle ta ya kalli Sadik ya ce, "Baban ku yana fama da matsalar ƙoda, daga ganin yanayinsa da komai na sa ciwon ya bayyana sosai. Yana buƙatar kulawa ta musamman gaskiya, yana buƙatar ganin likitan da ya ƙware a wannan fannin."
Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!Likita amma bai taɓa ciwon ƙoda ba, ko Islaha?."
Islaha ta ce, "nidai iya zamana a gidan ban san ya yi ba, ban taɓa ji an bada labarin ya taɓa yi ba."
Likitan ya kalle ta ya ce, "ina ta so in tuna inda na sanki, yana cewa Islaha na fahimci wacece ke. Ashe presenter mu ce a gabana." Ta ɗan yi murmushi kaɗan kafin ta ce, "yanzu ya za a yi dr?."
Dr ya ɗauko takarda ya yi rubutu ya ce, "Zan tura ku wajan likitan da ya ƙware a wannan fanni, shi gabaɗaya aikinsa akan ƙoda ne, akan haka ya ƙware kuma yake da sani a kai. Su mu ke kira nephrologist."
"Ana iya ganinsa a nan, amma gaskiya a kan sha wahala sosai, amma in ku ka je asibitin da yake aiki za ku samu ganinsa sosai, zai yi muku bayani yadda ya kamata. Amma asibitin kuɗi, asibitin kuɗi bana wasa ba, sai dai za ku samu biyan buƙata in sha Allah."
Sadik ya ce, "to zamu gwada."
Dr ya miƙa masa takardar ya karɓa ya ce, "ku je, in kun gansa ku ce Dr Habib ne ya turo ku daga nan babban asibiti, zai yi muku komai yadda ya kamata. Amma ina sake maimaita mu ku, asibitin kuɗi ne, iya kwanciya da duba mara lafiya za a yi za a chajin ku kuɗi mai yawa."
A lokacin Mama da Labiba suka dawo, a lokacin Sadik ya ce, "zamu gwada mu ji, mun gode sosai likita."
Dr ya ce, "Allah ya ƙara sauƙi." Suka amsa da amin. Dr ya kalli Islsha ya ce, "na ji daɗin haɗuwa dake." Ta ɗan yi murmushi bata ce komai ba, dan rashin lafiyar Baffa ya tsaya mata a rai sosai.
Sai bayan sun fito suke faɗawa su Mama za a canja asibiti ne, aka basu ambulance suka tafi asibitin da aka faɗa musu.
Haka kawai ƙirjin Islaha yake bugawa ba tare da ta san dalili ba, tunda suka ɗauki hanyar asibitin gabaɗaya yanayinta ya canja take ji kamar ba ita ba. Da suka hau kan titin asibitin sai take kallon titi, tana jin kamar akwai wani abun da zai faru, amma ta rasa meye shi.
Tun daga farkon layin da zai kai ka asibitin za a ka san asibitin ba da wasa bane, an zuba masa titi mai kyau, hanyar ta yi kyau kamar kar ka daina tafiya.
Tun daga wajen asibitin take ƙare masa kallo, an yi masa wani irin gini da bata taɓa gani ba, ga shi tsaho kamar hotel, floor by floor. Babban asibiti ne, kai daga ganinsa ka san an kashe kuɗi wajan samar dashi, yana da girma mai ban mamaki tun daga waje, ga kyau da ɗaukar ido.
NADIRA HOSPOTAL shine abinda yake a rubuce da wani irin front mai kyau, da design mai ɗaukar hankali. Parking space ɗin asibitin ma abin kallo ne, yana da matuƙar girma, gashi an samar da duk wani abu da ya kamata a wajen.
Labiba da ta gama ƙare masa kallo ta ce, "Hamma Sadik wai wannan asibitin? Anya zamu iya biya?."
Ya kalli Ambulance ɗin da tuni har ta shiga, ma'aikata sun fito an shiga da Baffa ciki.
Mama ta ce, "abinda zan ce kenan, naji ana zancen asibintin nan, ba dai kashe kuɗi ba."
Sadik ya ce, "zamu gwada Mama, in zamu iya to, in baza mu iya ba sai mu canja waje" ya faɗa yana shiga da motar, suna sake kallon asibitin dan wajan ajjiye motar ma wani waje ne mai zaman kansa da kansa.
Suka fito a sanyaye suna takawa a hankali zuwa ƙofar da zata shigar dasu.
Ƙofar automatic slide glass door ce, kana zuwa kusa da ita zata buɗe, tama buɗewa zaka ka ji ƙaramin sauti ana cewa welcome to Nadira Hopital. Sanyi da wani shegen ƙhamshi ya ratsasu, Islaha ta yu saurin saka facemask ɗinta, dan sanyin zai iya yi mata yawa.
Babban reception ne mai kyau, ga kujeru lafiyayyu an tanada, ga tv da duk abinda ya kamata a wajan.
Table ɗin ma'aikatan suka ƙarasa ita da Sadik. Islaha ta ce, "barkan ku da aiki."
Baturiya ta ɗago ta ce, "you are welcome Ma'am, hausa kaɗan kaɗan."
Islaha ta yi murmushi, ta canja yare zuwa turanci ta ce, "akwai mara lafiyan da aka kawo yanzu, ko zamu iya sanin inda aka kai sa?."
"Yana emergency, kafin ku je zaku cike form, sannan za ku cike file da payment."
Islaha ta cike komai da sunan Baffa da duk abinda za a yi. Bayan ta gama ta miƙa mata, Sadik ya miƙa Atm ɗinsa dan a cire kuɗin file ɗin da aka cike.
Bayan ta saka ta miƙo masa ya saka pin yace ya ji wayarsa ta yi ƙara, ya zaro ido ganin uban kuɗin da aka cire masa kawai na kuɗin file.
Ya kalli Islaha ya ce, "Matar Hamma anya asibitin nan zai zaunu a wajen mu? Kalli fa."
Ta kalli alert ɗin ta zaro ido ta ce, "kai! Iya wannan kuɗin file ne ko harda ganin likita?."
Kafin ya bata amsa ta juya tana tambayar matar dan ta tabbatar, ta bata amsa da na file ne da ganin Dr a emergancy.
A sanyaye Islaha ta ce, "ina son haɗuwa da Dr...." Sai ta kalli takardar da Sadik ya bata ta ce, "Dr Esma'il."
Matar ta ce, "A nephrologist?."
"Yeah."
"Office ɗinsa yana sama, floor 2, office number 4." Suka yi mata godiya suka fara zuwa inda Baaffa yake ko zasu ganshi. Basu samu damar ganinsa ba, hakan ya saka Islaha da Sadik suka wuce wajan Dr.
Suna zuwa inda aka faɗa musu suka gansa ya fito daga office ɗin. Sadik ya ce, “Dr barka da aiki.”ya bashi hannu suka gaisa, Islaha ta ce, "mun zo daga general hosptal ne" ta faɗa tana miƙa masa takardar.
Ya karɓa ya karanta ya kalle ta ya ce, "Dr Habib?."
"Shine."
"Ina mara lafiyan?."
"Yana emergency."
Ya girgiza kai ya ce, "zan je in gan shiyanzu." Daga haka ya bar wajan su kuma suka biyo bayansa.
Ta wani section suka zo wucewa daidai inda zaka hau elevator ka koma floor 1, ta gasecurity guard a wajan a tsaye alamun akwai babban mutum da yake a kwance a wajen, ta girgiza kai tana cewa, "Maybe gwamna ne a kwance" ta faɗa tana wuce wajan.
Rehaan yana zaune kusa da Mamy, ya kwantar da kansa a kafaɗarta ita kuma tana shafa kansa a hankali. Mamy ta shagwaɓa Rehaan, musamman in bashi da lafiya komai yi masa take yi, hatta wanka da zai tsaya Mamy zata iya yi masa saboda kar ya wahala.
…