RAGAYAR DUTSE

PAGE 23

by @nanahaleema11

 *RAGAYAR DUTSE.*


                ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 023.*



Ko da aka buɗe ƙofar bai buɗe ido ba dan ya yi tunanin Jafar ne, idanunsa suna a lumshe bai fahimci wutar asibitin ta ɗauke ba dan idanunsa a rufe suke. 


Jin shiru Jazy bai ce masa komai ba sai ya fara buɗe ido a hankali, kafin ya kai idanunsa wajan ƙofa da ya gawaye, sai ya fara jin sautin fitar numfashi daƙyar, alamun ko numfashin waye yana barazarar ƙwacewa. Ya kalli wajan da yake jin sautin, ya hango ta a zaune a jikin ƙofar sai jan numfashi take yi, ta gigice ta fita daga hankalinta.


Ya miƙe zaune a hankali dan har lokacin yana jin ciwo a cikinsa sosai, ya bita da kallo ganin wannan dai ba Janan bace, kuma ba Riyya ba ce. 


Da mamaki yake kallon ɗakin ganin babu haske sai kaɗan, duk da ba ya hango ta yadda ya kamata, amma ya tabbatar mace ce dan yana ganin hijjab ɗin jikinta. 


A hankali ya tashi tsaye ya ƙarasa ya buɗe window yana kallon compound ɗin asibitin, sai ya ga gabaɗaya asibitin babu wuta ta ɗauke. Ya dawo da kallon sa gare ta, har lokacin jan numfashi take yi tana neman ɗauki.


Ya ɗan matsa tana kallon ta, a yadda take fitar da numfashin ya tabbatar masa da asthmatic patient ce, tana buƙatar inhaler, tana buƙatar iska, tana buƙatar kwantar da hankali. Asibitin babu iska tunda babu wuta, sannan bai sani ba ko tana da inhaler, gashi babu wuta balle ya saka a kira wani a taimaka mata.


A hankali yake takawa kamar ba ya so, ya dawo inda gadon yake, ya sake juyawa ya kalli Islaha yana tunanin taimakon da ya kamata ya bata, tunda numfashin nata bai ɗauke ba. Ya buɗe drawer ya ɗauko hand oxgyen yana juyata a hannunsa, yana tunanin zata iya taimaka mata na ɗan lokaci kafin wutar ta dawo. 


Ya juyo ya kalli Islaha, kamar kar ya ƙarasa sai kuma ya tuna shi Dr ne, taimakon mara lafiya aikinsa ne, hakan ya tako a hankali ya tsaya a inda take. 


Ya zuba mata ido na wani lokaci ganin yadda yake jan numfashi da alamun ta samu attack ne, sannan ga facemask a fuskarta. 


A hankali ya tsunguna a gabanta, kamar mai jin tsoron wani abun ya kai hannunsa ya zare facemask ɗin fuskarta, hawaye suka sakko daga idanunta da suke a kulle.


Ya saka mata oxgyen ɗin a hancinta ya matsa, yana taimakawa numfashinta dan ya ɗan daidaita kafin hasken ya dawo. Ya zubawa fuskarta ido yana kallo, kuma ba ya ganin fuskarta yadda ya kamata, dan babu hasken da zai wadacesa har ya ga fuskarta sosai.


Idanunta yana kulle bata san waye a kusa da ita ba, neman ɗauki take yi, numfashinta gab yake da tsayawa. A daidai lokacin hasken asibitin ya dawo, har lokacin yana tsugune a gabanta, duk da yadda yake jin ya takura kansa saboda ciwon cikin da yake yi, amma hakan bai saka ya miƙe ba. 


Ya ɗaga ido ya kalli fuskar ta, duk da idanunta a rufe suke amma tsaf ya gane fuskarta, dan itace fuskar mace ta farko a duniya da ta taɓa tsaya masa a rai har yake so ya sake ganinta.


Y janye ido daga kanta, a lokacin ta zame a hankali ta kwanta a wajan tana mayar da numfashi, har lokacin bata dawo normal ba, kawai ta ɗan samu nutsuwa kaɗan.


Ya miƙe daƙyar, yana ja baya ba tare da ya juya ya kalli gabansa ba, yana tafiya yana kallon ta, ya girgiza kai yana mamakin abinda ya kawo ta asibitin har ta samu ta shigo ɗakin da yake kwance.


A lokacin aka turo ƙofar aka shigo, suka haɗa ido da Dr Abdul, wanda ya kasance manager na asibitin gabaɗaya. Dr Abdul cikin girmamawa ya ce, "Sir, i'm sorry." 


Rehaan ya koma ya zauna, ya mayar da abinda ya ɗauko sannan ya ce, "me ya faru?."


"An samu fashe gas ne, sai wuta ta ɗauke." 


Ya girgiza kai kamar bazai yi magana ba, kafin kalle sa ya ce, "call a meeating, now." 


Dr Abdul ya kalle sa, gabansa ya faɗi sosai, dan ya san babu kyau tunda ya ce a haɗa meeting a lokacin, daƙyar bai kori wanda ya yi sakaci har aka samu wannan kuskuren ba. 


Dr Abdul da girmamawa ya ce, "Okay Sir." 


Har ya juya zai fita Rehaan ya ce, "wait." 


Ya juyo yana kallonsa, ya nuna masa Islaha ya ce, "she had attack." 


Dr ya juya kalle ta, tana kwance tana jan numfashi a hankali. Dr ya fita ya kira nurses aka ɗauki Islaha suka fita da ita, ya bisu da kallo har suka ɓace. 


Amon muryar Jazy yake jiyowa yana zazzagawa securities masifa a waje, ya yi murmushi tare da lumshe ido, ya girgiza kai ya ce, "an taɓa sarkin faɗa da masifa."


Ya shafa kansa yana murmushi har lokacin, im aka cire iyayensa babu mai ƙaunarsa kamar Jafar, ko su Riyya sai dai su biyo bayan Jafar. Ko yaushe yana tare dashi, ba dan neman wani abu ba, sai dan ƙauna da shaƙuwa mai tsanani. Duk da suna faɗa, har su daina yiwa juna magana, amma haka zasu shirya su dawo a cigaba daga inda aka tsaya.


A lokacin Jazy ya shigo ɗakin fuskarsa a ɗaure ya ce, "ta ya za a samu fashewa gas a nan? Ta ya zasu yi sakaci wuta ta ɗauke?. Su kuma waɗanan security guards ɗin na baki ƙofa, sun tafi sun bar wajan babu kowa, in plan aka haɗa fa? In da gangan aka aikata fa?."


Ray buɗe ido ya kalle sa bai ce komai ba, dan bai san me zai ce masa ba.  Jazy ya ja tsaki ya ce, "shirme!" Ya faɗa yana zama. 


Sai kuma ya kalli Ray ya ce, "kai kuma ka zuba min ido, i hope lafiya ka ke?." 


Sai ya bawa Rehaan dariya, ya yi murmushi mai sauti yana kallonsa, dan yadda ya yi maganar da fusata ya ba shi dariya sosai. Sai hakan ya tuna masa wani lokaci da suke yara, in ya ɓata masa rai haka yake fusata ya yi ta masifa kamar zai ci babu. Shi Rehaan bai cika faɗa kamar Jafar ba, amma shine mai takalarsa har ya yi faɗan. In ka ga ran Rehaan ya ɓaci to babban abu ne, ƙaramin abu baya ɓata masa rai kamae Jafar. 


Ray ya ɗan shafa kansa yana ɗan girgiza kai kafin ya ce, "i've called for a meeting, let's go" ya faɗa yana miƙewa tsaye daƙyar. 


Jazy ya bi shi da harara ya ce, "baka da lafiyar zaka iya wani meeting, Kai wai baka da hankali ne?." 


Ray ya sake yin murmushi yana kallon sa ya ce, "bani dashi Jazy. Let's go."


"Wait! An ce wata yarinya ta shigo nan, ka ganta?." Ray ya kalli Inda ta kwanta, yana hango yadda hawaye yake sakkowa daga idanunta saboda attack ɗin da ta samu.


Jazy ya ja tsaki ya ce, "ban ga amfanin mutanen nan ba, har su bar wata mace, wacce bamu san wacece ba ta shigo nan. Wai sun tafi bada taimako inda gas ɗin ya fashe, ko waye ya aike su oho." 


Shi dai bai ce komai ba, ya yi shiru yana kallon inda Islaha ta tashi, yana sake tuna fuskarta a hotel da fuskarta ta yau.


Jazy ya taɓa shi ganin ya zubawa waje ɗaya ido ya ce, "Mr man ina magana ka yi min shiru, baka jina ne?." 


Ray ya kalle shi ya ce, "sai masifa ka ke yi, me ka ke so in ce?."


"Sai ka ƙyale ni cigaba da yi, da yake mahaukaci ko?." 


Ya sake bashi dariya, ya sake murmusawa sannan ya ce, "Mu je." 


Har zasu fita Ray ya dawo, ya ɗauki jacket ɗinsa ya ɗora akan kayan jikinsa, hular da take baya ya saka ta a kansa sannan suka fita.


     Islaha kuwa ana fita daga ita daga ɗakin, aka kai ta aka bata taimakon da ya kamata har ta dawo nutsuwar ta.


Islaha ta miƙe zaune ta kalli Nurse ɗin ta ce, "Don Allah ina Dr Isma'il yake?." 


Nurse ɗin ya ce, "Sun shiga meeting, amma baza su jima ba. Ki kwanta ki huta."


Ta miƙe tsaye, ta ɗauki hijjab ɗinta da aka cire mata ta saka, ta saka takalmanta da ta gansu a wajan a ajjiye ta ce, "i'm okay, thank you." Tana faɗa tana fitowa ta koma inda su Mama suke ta gansu a zaune harda Sadik.


Suna hango ta Sadik ya miƙe ya ce, "Ina kika shiga?." 


Ta ɗan sauke numfashi a sanyaye ta ce, "hayaƙin nan na ɗazu ne ya saka na ɗan samu attack, ni kaina bazan ce ga yanayin da na kasance ba. Ina Baffa? Ka haɗu da Dr?."


"An ce sun shiga meeting" ya faɗa yana miƙa mata wata leda ya ce, "da yake asibitin na masu kuɗi, akwai lafiyayyen entry da ake siyar da abinci, kuma na ji ance ga wanda zai zauna jinyar mara lafiya, da mara lafiyar abinci kyauta ne. Karɓi ki ci, ke ce baki ci komai ba duk mun ci."


Ta miƙa hannu ta karɓa tana jin jiri yana ɗaukar ta ta ce, "wallahi bana jin yunwar, so nake mu san yanayin da Baffa yake ciki." 


Labiba ta ce, "gwara dai, dan wallahi na gaji gida nake so naje na kwanta na huta. Ita waccen sagalalliyar har yanzu bata zo ba." 


Islaha zata yi magana Adda Sa'ida ta ƙaraso wajan, ta ce, "Islaha tunda nazo ban ganki ba." 


Islaha da fara'a ta ce, "Yaushe ki ka zo Adda?."


"Ban wani jima sosai ba, na je nayi sallar i'sha ne."


"Lah nima ban yi sallah ba, bara na je na yi na dawo" ta faɗa tana juyawa a sanyaye tana jan numfashi a hankali. Sai da ta shiga restroom ɗin asibitin ta ga yanayin fuskarta, hijjab ɗinta duk ya jiƙe da gumi. Ta ɗan gyara fuskarta, ta mayar da facemask ɗinta  sannan ta fito. 


Tana shiga masallacin lafiyayyen ƙhamshi ya yi mata sallama, bata tsaya ƙare masa kallo bata ƙarasa ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta tayar da shafa'i da wutir. 


Tana cikin yin sallah wata mata da take gefenta, wacce turaren ta ya cika masallacin da ƙhamshi ta miƙe ta fita, sai wata daga gefe ta ma ta fita alamun tare suke. 


Islaha ta kalli inda ta tashi, sai ta ga ta bar atm card ɗinta da key ɗin mota. Islaha ta miƙe ta ɗauka ta zata fito, sai ga wacce ta fita daga baya ta dawo. 


Ta kalli hannun Islaha, ta kalli fuskar ta ta ce, "asibitin nan dai ba a sata, daga fitar mu har kin ɗauki abinda muka bari zaki gudu?."


Islaha ta kalli matar, babba ce dan ta haifi wanda suka girme mata ba ita ba. A lokacin Mamy ta dawo ta ce, "ba ki ɗauko ba?." 


Islaha ta kalli Mamy, dan ita da ta ganta a cikin masallacin bata yi tunanin tana jin hausa ba, tunda asibitin akwai fararen fata kala-kala, ta ɗauka Mamy tana daga cikin wanda basa jin yaren nigeria. Gashi ta saka baƙar a abaya, sai ta tashi kamar balarabiya.


Ƙawar Mamy ta nuna Islaha ta ce, "har ta ɗauke, ba ban dawo ba da baza mu ganta ba" ta faɗa tana sake kallon Islaha. Ta yi tsaki ta ce, "a haka kamar yarinyar kirki, ɓarauniya kawai."


Islaha ta ɗan lumshe ido, bata jin daɗin yanayinta ko kaɗan, haka ta buɗe ta ce, "ni ba ɓarauniya bace, na ɗauko dan na biyo ku na kawo muku, ba wai dan in sace ba" ta faɗa tana miƙawa ƙawar Mamy atm card ɗin da key ɗin motar.


Ta karɓa tana kallon Islaha ta ce, "ɓarauniya ce mana."


"In duniya zaki ajjiye, ban ga abin sacewa ba."


"rashin kunya za ki yi min? Kin san su waye a gabanki?."


"Ko su waye ku ɗin ina ruwana? Title ɗinku ne ba nawa ba, dan na taimaka na ɗauko zan miƙo muku sai ya zama laifi?. In sace miki atm card da key ɗin mota in yi me dasu? Na yi miki kama da ɓarauniya ne?."


Islaha ba da faɗa take maganar ba, a hankali take magana, dan yanayin da take jin numfashinta bazai barta faɗa ba, kuma dan taji haushin kalaman matar ne da baza ta saurare su ba. 


Ƙawar Mamy ta ce, "ni ki ke faɗawa haka?."


Islaha ta ce, "in babba bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki bazai ji nauyi kayar dashi ba."


Mamy kallon Islaha take yi, duk da ba faɗa take yi amma mamaki take bata. Bata ce komai ba ta gaji da tsayawa, ta karɓi atm ɗin ta ce, "na tafi" ta faɗa tana shiga asibitin ta bar ta wajen.


Islaha bata ce komai ba ta raɓa ta zata wuce, ta hana Islaha wucewa ta ce, "kin san wacece ni?."


A ƙufule Islaha ta ce, "wacece ke?."


Ƙawar Mamy mamaki ya hanata magana, Islaha ta ce, "don Allah ki ja girmanki, bana son yi miki abinda baza ki ji daɗi ba. Kowa wacece ke wannan ke ya dama bani ba" ta faɗa tana fita ta barta a wajen a tsaye tana kallonta.


        Babban meeting room ne mai girma sosai, ya tsaru, ya yi kyau sosai. Ga babban table a tsakiya da kujeru, wanda zasu kai guda hamsin ko wanne da abar magana a gaban ko wacce kujera. 


Ga tv mai girma da take kallon kowa, sannan ga dispenser da ruwa a kanta. 


Gabaɗaya kujerun babu wanda babu wani a kai, suna zaune sun yi shiru ana jiran shigowarsa. Kowa ya san baza a tashi lafiya ba, dan ba ya ɗaukar kuskure, ba ya son kuskure ko kaɗan. Gashi dai ba yawan zuwa asibitin yake yi ba, amma duk ranar da ya zo sai ya tafi hankalin kowa yake kwanciya saboda gudun kuskure.


Lokacin da ya buɗe ƙofar ya shigo da sallama, duk sai da suka miƙe tsaye ana amsawa. 


Sababbin staffs waɗanda basu taɓa ganinsa ido da ido ba ranar sun ganshi, kowa ya yi tsit ana jira ya ƙaraso. 


Rehaan ya taka a hankali zuwa tsakiyar room ɗim, sai ya tsaya ya jingina da bango yana kallonsu, kafin ya yi musu alamu da su zauna. 


Duk suka zauna suka yi shiru, ya taka ya je inda kujerar zamansa take, ya zube hannayensa akan table ɗin ya ɗan sunkuya kaɗan yana bin kowa da ido. Gabaɗayansu sun nutsu, kowa da inda yake zaune, dan meeting ne ba iya na Dr's ba, har waɗanda aka samu matsala ta ɓangarensu. 


Ray ta cikin loudspeker ya ce, "What caused the gas cylinder to explode?."


Suka yi shiru basu amsa ba, ya bisu da kallo one by one kafin ya ce, "Who is in charge of that section?


 Ta miƙe a sanyaye ta ce, "ni ce Sir." 


Ya bita da kallo kafin ya ce, "Explain to me, ya aka yi hakan ya faru?."


 Ta ɗan gyara tsayuwa ta ce, "Sir it's a mistake." 


Ya ɗan ɗage gira sama ya ce, "mistake!." 


Ta ɗan girgiza kai ta ce, "yes Sir."


"Who told you akwai mistake a ɓangaren lafiya?."


Ta yi shiru tana sunkuyar da kai bata ce komai ba, ya girgiza kai ya ce, "yaushe ki ka fara aiki a nan?." 


Jikinta sai rawa yake yi ta ce, "last month." 


<…