GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar giwa

by @auntyindo

Tuni Hamdan ya daɗe yana ambaton sunan Allah don samun temako da Ƙwarin gwiwa daga gareshi, hakan ya sa  ya yi nasarar danne Sirrin zuciyarsa wato tsananin Ƙaunar Hibba da ta yi wa rayuwarsa Ƙanwanya!.

 Ɗan gyara zama ya yi gami da cewa "My Dad! ba wani abun tayar da hankali ban....."  "Wannan maganar banzar ce ba abun tayar da hankali ba??  me za ka yi da wannan Yarinyar in ka Aure ta?, Yarinyar da Ubanta ko cikakken Asali ba shi da shi?"  a Fusace Daddy ke jefo masa tambayoyin,  ya ɗan yi shiru yana tunanin ta yadda Daddyn nasa ke iya fusata a daidai lokacin da yake nishaɗi da walwala.

  "Wai kana nufin ka ce min Son yarinyar ma kake yi?, wai ko dai ka fara Hauka ne?"          "A'ah!   Ba sonta nake ba, ko kusa da hakan ma babu, kawai ta Burge ni ne,   sai nake ga kamar za ta dinga temaka min wajen Kasuwancina, kuma ka ga Ƴar Uwa ce ai ba laifi don na Aureta!" 

  "To na tayaka Murna da ba sonta kake ba, don ko zaka Haɗiyi Harshen Wuta ba za ka Auri mara Asali mara tushe irin Yarinyar nan ba!,  idan Auren Zumuncin kake so ai ga Ƴaƴa nan a wajen ƙawayen Mahaifiyarka, kuma ga Ƴaƴa nan masu Asali a wajen su Mukhtar, da Muhammad!,  ko Ƴar wajen  Nafisa ka nema ai ita tana da Asali tana da abun da za a yi alfahari da shi  ba wai ka ɗauko Ƴar Matsiyata ka Aura ba,        Ƴar  da ba a gaji Arziƙi  Gidansu ba ita kake tunanin za ta temaka ma wajen Kasuwanci??,  kana hayyacinka kuwa?!!"   

 Tamkar an ɗora Ƙaton Dutse an danne Zuciyarsa haka ya ji  ta yi masa wani bala'in nauyi,  a yanzu kam duk yadda ya so saka fara'a akan fuskarsa ya kasa,  cikin wata kalar murya  ya ce "Kenan Kuɗi da Dukiya su ne Asali Daddy?"    "Oh! magana kake so ka faɗa min?!"  Daddy ya faɗa a fusace,  girgiza kai ya yi ya ce "No kawai tambaya na yi don samun ƙarin haske akai,  gaskiya kam na gane me kake nufi Daddy, abar maganar  na fasa gaskiya ba za ta iya ba ma,   don ba huruminta ba ne!"
  cikin hargagi Daddy ya ce  "To kuma! ,  ina amfanin ma ka Auri wadda ba ka sonta?, in da za ta iya taya maka ɗin ne ma da sauƙi  amma ba za ta yi maka komai ba in banda ta ci Moriyarka ta Yada kwauren,   shi ya sa ma ashe Aminar ta yi kyakkyawan Shiri ta kai Ƴaƴanta Family a wannan Sallar ashe da biyu ta je  dan ta samu wanda za ta Mora ta jefar!"

   Shiru Hamdan ya yi don in ya buɗe baki bai san  me zai furta ba.

  "Lallai ma Yaron nan ka ba ni Kunya da Mamaki wallahi!"  muryar Ammynsa ce ta karaɗe kunnuwansa, gabansa ya faɗi ras! amma sai ya maze ko motsi bai yi ba.

 Ƙarasowa ta yi ta zauna tana zuba masa idanunta wanda suka ƙawatu da Kwalli suka ƙara mata Kyau da Kwarjini,     "Kamata ya yi ka zamo Yaro me sanin Darajar kansa, kamar dai ni ko Mahaifinka  amma sai ka zama wani iri daban!,     to ka tabbata in ma son nata kake yi ka dena don ba za ka taɓa Aurenta ba, na riga na yi maka Mata!"  
Murmushi ya yi ya ce "Wai ke ma Fusata kika yi Ammy?, kin san dai ba zan yi abun da zai zubar da kimarki ba,  ba ma zai yuwu in fara sonta ba ai,  kawai dama na ga yanayinta ne ta ɗan burgeni to kawai se na ji ina so in Aureta,    ba wai don ta zama Matata Da'iman ba fa! kawai dai....!" shiru ya yi yana ɗan murmushi.

    Ammy ta sauke numfashi, yanzu ta samu nutsuwa da ta kalli ƙwayar idonsa, ba ga ga alamar son Hibba a cikinsu ba, sannan alamun maganar da ya faɗa kawai don cimma manufarsa ne ta burge shi,   ɗan murmushi ta yi cikin salonta na kissa ta ce "Haba ni fa na dan ka haifu daga cikina Hamdan, Yaron kirki, ba sai ka wahalar da kanka wajen Auren wadda ba ta cancanta ba,     idan wani abun kake buƙata a gurinta ai kana da damar da za ka yi komai,  a taƙaice ma ba Ƙaramar ƴa ce a Ƙasar nan zata zamo me tsada gareka ba Hamdan,  ka dena irin wannan tunanin, ni Mahaifiyarka na riƙe maka kan Macijin ka je ka yi wasa da Bindinsa!, ka yi sharafinka Ɗana!"      Godiya ya yi mata cikin sakin fuska  don kar ta gane halin da yake ciki.

  Cigaba suka yi da yi masa Nasiha irin wadda suke ganin ta dace da shi,   shi kuwa sai ya nuna musu ya ɗauki komai ya riƙe,  ya yi namijin ƙoƙari wajen kawar da tunaninsu kan zargin yana son Hibba.
 Sai da Ammy ta tabbatar ta zuge shi tatas sannan ta gabatar masa da Matar da ta yi masa wato Farida,  bai amsa ba kuma bai ƙi amsawa ba sai ya ce zai cigaba da Nazari akanta, amma yanzu ba ya son Auren soyayya saboda ba shi da cikakken lokacin bawa Matar kulawa a yanzu,   cikin sa'a  Ammy ta yarda da hakan har da farincikinta don a tunaninta ya yi hakan ne don tanadar wa Farida tsantsar Ƙauna.

     Sun daɗe suna  hira kafin ya yi musu sallama ya gudu Bedroom ɗinsa.
Yana shiga ya kulle ƙofa ya jingina a jikinta yana cigaba da maimaita addu'o'i   "Tabbas so ya zamo bala'i gareni!, wanda yake shirin lalata min farincikina, yanzu kenan ajiye Ƙaunar iyayena zan yi in nuna musu ba su isa da ni ba kokuwa haƙura zan yi da Hibba?"   "Ba zai yuwu ba, babu ɗayan da zan iya yi!"   ya furta hakan a sarari!...


   Tunanin kalaman iyayen nasa ne ya fara dawo masa, ya saki wani malalacin murmushi me taɓa Zuciya,  "Ya za a yi na canja wannan Bahagon tunanin nasu??"   ya jefawa kansa tambayar da ba shi da amsarta.

     Ismail
Hajja Halima ta yi matuƙar mayar da hankalinta kansa tana duk bakin ƙoƙarinta don gusar masa da damuwarsa,   ba laifi ta yi nasarar zubar da kaso me yawa a ciki.
Shi ma da kansa yana ƙoƙari wajen kore damuwar ta hanyar maye gurbinta da Nishaɗi. 

Kabeer  Shi kaɗai ya yi ƙuncinsa ya gama ko Muhsin bai gayawa ba bare iyayensa dan ya san ba sa bayansa akan hakan,  da kuwa ya san abin da za a shige masa gaba ne da ya gayawa Daddynsa,  ko dan Hibba da Maama su ga Bambancin Ɗan Talaka da na me Kuɗi.
  Ya gama Ƙufular ya dena sai dai fushin abun na maƙale a ransa har yau, sometimes yakan yi tunanin yadda ze rama wulaƙancin da aka yi masa, sai ya yi tunanin keta haddin Hibba sai ya ji hakan bai kwanta masa ba, ya yi shawarwari kala-kala shi da Zuciyarsa  amma ya kasa samun ɗaya ƙwaƙƙwara wadda zai aiwatar don haka ya yi kwanton ɓauna ya cigaba da sabgoginsa.

     Hamdan, Hibba,  suna zaune kan Kujeru a harabar Gidan su Hibba sun yi jigum-jigum kamar an aiko musu da saƙon Mutuwa.
Hibba ce ta fara ankara da zaman shirun nasu ya yi Yawa, ta yanke hukuncin katse hakan da cewa "Hibban! ko dai yunwa kake ji ne?"    ya ɗan zaro ido yana murmushi ya ce "Acici kika mayar da ni kenan?"       "To ai na ga shirun ya yi yawa ne!"  ta faɗa gami da kawar da kai gefe.

    Shiru ne ya ɗan ƙara shiga tsakaninsu kafin Hamdan ya katse tunaninta ta hanyar faɗa mata abun da ba ta yi tsammanin ji a wannan lokacin ba....

   "Na yi magana da su Daddy, amma ban samu goyon bayan su ba, don ko sha'awar alaƙar tamu ba sa yi ko da sunan wasa!"   cikin sauri ta runtse idanunta da ƙarfi a ranta ta furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"......