GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
Gadar giwa
by @auntyindo
"Hibbah!" ya furta sunanta cikin matuƙar kaɗuwa. Da sauri ya kai hannunsa zai riƙo nata hannun wanda yake wata irin karkarwa.... ta yi saurin ɗaga masa hannu, ido ya cigaba da zuba mata yana jin raɗaɗi da ƙunar halin da ya ga ta faɗa nan take.
ware masa idanunta da suka fara gane mata dishi-dishi ta yi cikin rawar baki ta ce
"Hamdan! kenan har rabuwar tamu ta zo cikin Sauƙi haka?, kuma da wuri?"
tsare ta ya yi da narkakkun idanunsa kafin ya ce "Haka wasu suke tunani, amma a nawa ɓangaren ba hakan take ba!"
"Me za ka yi kenan?, cigaba za ka yi da bibiyata kana cutar kanka, ni ma kana cutar da ni? ko kana nufin za ka bujire wa Umarninsu ne?"
"Abin da ya dace da rayuwata shi nake son yi, amma bisa yardarki da yardar Danginki , ku kaɗai ne ƙwarin gwiwata a yanzu, ba na buƙatar sa hannun wani daga cikin Dangin Mahaifi ko na Mahaifiyata, iya Albarkar Ƙanwar Mahaifina guda ɗaya ta isheni in Aure ki!"
ta ƙara buɗe idanunta da suke ta ɓulɓular da hawaye akansa cike da son tantance da wa take magana, shin Hamdan ɗin ne ko wani ne daban?. Kuma Shi ɗin ne dai ba wani ba.
Katse mata tunanin ya yi ta hanyar kiran sunanta cikin raunin murya, "To ai na kasa gane wane yare kake min ne, ban fahimta ba!"
gwauron numfashi ya sauke ya ja kujerarsa ya ƙara matsawa daf da ita sannan ya dube ta a tsanake ya ce "Sai iyayena sun san batun Aurenmu sannan ransu zai ɓaci, don haka ni a nawa ɓangaren na yanke hukuncin zan Aure ki ba tare da sanin kowa daga cikinsu ba, a sirrince za mu rayu tare!"
"Kenan, irin Auren da ake kira Auren Sirri?, Aure ba tare da sanin kowa ba?"
Ya bata amsa da cewa "Ni fa na shirya rayuwa da ke Hibbah! a ɓangaren Danginki za ki zamo Matata , a ɓangaren nawa Dangin kuma zan cigaba da zama da su a matsayin wanda ba shi da Mata, hakan ne kawai zai sa mu rayu tare cikin farinciki ba tare da kin fuskanci takurawarsu ba, idan kin amince ki shirya don ni a shirye nake, kar ki yanke hukunci yanzu ki fara yin nazari da Shawara!"
rasa amsar da za ta ba shi ta yi sai idanu da take rarraba masa.
Tashin hankali ba a sa masa rana, wannan shi ake kira RINTSIN SO (Littafin Anti Indo) kokuma SIHIRIN ƘAUNA .... (Littafin Anti Indo)
Tabbas ba son wasa take yi wa Hamdan ba, za ta so zama Matarsa, sai dai wannan babban Ƙalubale ne , kuma cusa kai a cikinsa tamkar Tarar Yaƙi ne da wanda ya fi Ƙarfinka!".....
"Na hango wasu Tantabaru suna Soyewa!, da ina gda Danƙo da na harbi Ɗaya". Khalil ne ya yi maganar yana dariya tare da nufar hanyar fita, suka yi saurin zuba masa na Mujiya don ko shakka babu da su yake.
Ƴar dariya Hamdan ya yi gami da cewa "Khalil zo nan, shakiyyi!" zuwan ya yi yana ɗan yin ƙasa da kai, Hamdan ya riƙo hannunsa yana cewa "Wato kana da son wasa ko?, to yanzu wa za ka harba kenan ni ko?"
Girgiza kai ya yi gami da cewa "A'a O'o! idan na harbe Matar ai da kanka za ka rataye kanka, ka ga na huta asarar dutse biyu"
"Ɗan Duniya ai kuwa kana harbo dutsen naka zan shiga tsakani in kareta!" Hamdan ya faɗa yana dariya
Hibba da take ɗan murmushi ta ce "Kuma sai ka biyewa Khalil ko? zai sa maka ciwon kai yanzun nan" "To ai sai in sha Magani ko Ƙanina?"
"Ƙwarai da gaske, ni dai yanzu bari in tafi inda zan je, ku cigaba da Yaƙar Ƙauna kawai" Khalil ya yi maganar yana zame hannunsa daga na Hamdan.
"Ka gaishe su " Faɗar Hibba tare da binsa da harara.
"Hibba ki shiga gida ko?, kina buƙatar nutsuwa sosai kafin yanke hukunci!" gyaɗa kai ta yi alamar ta gamsu da hakan, cikin sanyin jiki ta miƙe ta nufi hanyar shiga ciki, da ido ya bi ta yayin da yake jin kamar ya haɗiyeta saboda tsantsan Sonta da ke ƙara azabtar da zuciyarsa.
"Hibba!" juyo wa ta yi don sauraren abun da zai faɗa, tashi yayi ya taka zuwa inda take har lokacin ya kasa dena kallonta, idanunsa sun cika taf! da zazzafar ƙwalla, "Wallahi ina Matuƙar sonki Hibba!, ina cike da tsoron in rasa ki, don gani nake kamar ba zan samu wata ba bayan ke!" ya yi maganar cikin murya irin ta me shirin fashewa da kuka.
Zazzafan Numfashi ta furzar tare da ƙaƙalo murmushi ta ɗora akan fuskarta, cikin sassanyar murya ta ce "Kar ka damu, abin da Allah ya hukunta mana shi ne mafi daidai da mu, kawai mu yi tawakkali gareshi!" ya ɗan gyaɗa kai yana ƙoƙarin goge hawayensa da suka fara zirara.
"oh! Tabbas in kana min kuka zan dinga kafa Camera ina yaɗawa Duniya ga Ragon Maza!" ta yi maganar cikin sigar zolaya tana yi masa wani ƙifil-ƙifil da ido......
Aunty Indo