GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar giwa

by @auntyindo

Ƴar dariya ce ta kufce masa tare da faɗin "Kai?!" ta ɗage masa gira ɗaya ta ce "Eh mana!" "To aikuwa zan dena, don na fi so in zamo Gwarzon Masoyi a wajen Ƙawayenki, don wannan me surutun idan ta fara tsatstsage ni ba zan iya ƙwatar Kaina ba!" "Kuma ita zan fara turawa!" "A'a na dena ai!" ya faɗa yana dariya gami da share ƙwalla, ajiyar Zuciya ta sauke yayin da tausayinsa ke ƙara mamayar zuciyarta, "Anya kuwa ba zaka shiga Gaida Maama ba?!" "Zan shiga yanzu ma kuwa" ya ba ta amsa cikin sauri.
   Gaba tayi ya bi bayanta suka rankaya ciki.

      Daddare....
Hamdan yana kwance magashiyan kan Doguwar Kujera ɗaya daga cikin waɗanda aka ƙawata Ɗan Lambun da su, sama yake kalla ya yi matashin kai da tafukan hannunsa, ko Motsi ba ya yi sai wanda ya zama dole, duk hankalinsa na kan Taurari da Wata yayin da ya yi nitso wajen tunane-tunane.

    Ji ya yi an taɓa ƙafarsa ya yi saurin zabura ya tashi zaune yana wararo ido, Sabran ya gani tsaye ya riƙe Ƙugu yana zuba masa kallo wanda Allah ne kaɗai yansan manufarsa.
    Kallon-kallo suka cigaba da yi na ɗan wucin gadi kafin Hamdan ya doka tsaki ya juya ƙeya.

   Sabran ya murmusa gami da yi wa kansa Masauki a kusa da Hamdan, cikin ƴar zolaya ya ce "Tsorata ka yi ko?" "In ji wa?" Hamdan ya faɗa fuska a haɗe kamar gaske.

   "Ai dole ma ka firgita tun da ka zo ka kwanta a wannan sararin Allah kana kallon Taurari da Wata, ina ga zata za ka yi Aliens ne suke neman yin sama da kai!" "Ka fiya kawo sokana a cikin rayuwa, do Allah bar ni in sha iska ba na son Hayaniya"  
    "Hmm ! duk iskar Fanka da Ac da ke cikin gida bai isa ba sai ka sha iska a nan?" 
  "Sabran!" Hamdan ya kira sunansa cikin marairaicewa. Sabran ya ɗan gyara zama gami da saita nutsuwarsa ya ce "Yanzu dai a bar maganar wasa, ni ina ganin kamar kana cikin damuwa amma kuma ka ƙi faɗa wa kowa ka ƙi bari kowa ya gane, amma dai ni ina ganewa gaskiya sai dai ban tabbatar ba" "Ba ni da wata damuwa kawai dai hasashen zuciyarka ne" jim! Sabran ya ɗan yi kafin yace "Anya kuwa? amma dai idan ka tabbatar hakan ne shi ke nan, kawai dai ba na so ka zauna da damuwa kai kaɗai bayan muna da yawa!" Hamdan ya ɗan murmusa tare da ɗora hannunsa kan na ƙanin nasa, cikin hikima da taushi ya ce "Lallai kuna da yawan da za ku tayani Ɗaukar damuwata, amma ka sani ba kowace damuwa ba ce Ƴan Uwa suke da kafaɗun Ɗaukar wa Mutum!, ba wai don ba za su iya ba ne, kawai lamuran ne sukan bambanta!" ba komai Sabran ya gane a cikin maganar ba kuma ba shi da niyyar tsawaita bincike don haka yace "Eh to haka ne, yanzu za ka shiga ciki ne ko in bar ka, amma dai dare ya yi" "Mu je kawai, nima na gaji da zaman!" Hamdan ya faɗa tare da miƙewa.

     Gidan su Hibba...
Maama, Khalil, Hibba suna zaune a ɗan madaidaicin Falonsu wanda ya sha ado daidai na me ƙaramin ƙarfi, Khalil da Maama ne suke ɗan hira yayin da Hibba ta doka tagumi ta tsura wa Maama ido....

 Wani irin Alhini take ji har cikin ƙoƙon ranta, ta rasa gane ina ne bakin zaren, sai ta ji tamkar ana shirin nesanta ta da Ahalinta, nisan da iyakarsa ba za ta misaltu ba, a wani sashin kuma takan ji tamkar ana shirin jefa ta cikin wata uƙuba da ba ta san yaya zata misalta ta ba.

   "Ke Hibba wai lafiya kike ta kallona?" Maama da ta gaji da sa idon na Hibba tayi tambayar cike da son jin damuwarta.

 Murmushi ta ƙaƙalo ta ce "Ba komai kawai dai tambaya nake son yi kuma na rasa ta inda zan fara" "To meye amfanin kallon tun da ba ki san me za ki faɗa ba?, ai wata maganar da sassarfa ake fara ta in ta ɗore sai ki ga an miƙe da gudu"

       " Bai wuce akan soyayya za a yi Tambayar nan ba daga gani" Khalil ya faɗa tare da komawa kan kujera ya kwanta.

    Shiru ne ya ɗan ratsa tsakani har lokacin da Hibba ta jefo tambayar ba tare da ta sani ba "Wai yin Auren Sirri yana da wani alfanu kuwa ?" ...... suman zaune Maama ta yi tana kallonta cike da firgici, sai da ta numfasa sannan ta iya cewa "Kar dai ki ce min abin da zuciyata ta daɗe tana ayyana min shi ne yake shirin faruwa da ke??" ƙasa Hibba ta yi da kai cikin tsinkewar zuciya.

 Cikin tsantsar tausayawa Maama ta ce "Ba shiru za ki yi ba amsa za ki ba ni!, Auren sirri kuke ƙoƙarin yi ke da Hamdan ko?"   

     Amsar Tambayar Maama tana da matuƙar wahala gareta, sai dai fayyace gaskiyar shi ne mafi alkairi.

  Lumshe ido ta yi gami da haɗiye yawu me cike da ƙunci da ɗaci, cikin son danne tsananin damuwar da ke cin ranta ta gyaɗa kai tare da ƙarin bayani "Haka ne! amma a nasa ɓangaren!, ya shawarce ni da yin hakan amma bi sa Amincewar ku, saɓanin yardar ku kuma alaƙarmu za ta rushe a yanzu!" duk yadda ta kai ga nuna Jarumta sai da hawayen da take ɓoyewa suka shiga ƙwarara.

    Tasbihi Maama ke jerawa a cikin Zuciyarta har na tsayin mintuna kafin ta iya kallon Ɗiyar tata da idon nutsuwa....
    "Hibba! kina nufin idan mun yarda kin yarda?" cikin hanzari ta bar kukan ta ɗago ido tana kallon Maama sai kuma ta yi saurin sadda kai ƙasa tare da rushewa da kuka me
ai tsuma zuciyar duk wani me Imani...

     "Tab ikon Allah! abu ba zato ba tsammani sai gashi yana faruwa" Khalil ne ya yi maganar cike da jimami da mamaki.

     Shiru Falon ya ƙara ɗauka kowa ya tafi nasa tunanin.
Maama ce ta katse shirun da cewa "Tabbas ina so ki cika muradinki da farincikinki!, amma ina tsoron Son Zuciyarmu na son ba ki farinciki ya jefa ki cikin Wani Mummunan hali, kin ga mu kanmu ba za mu yafe wa kanmu ba, ke yanzu idonki ya rufe mu ya kamata mu yi hange sosai akan Goben rayuwarki!"   
   "Kawai zan ce masa A'a , nima bana son in bar ku!" Hibba ta faɗa cikin tsananin kuka...
 
   Maama ta yi murmushi tana cewa " Uhm! ai rabuwa da iyaye ga kowane Ɗa ya zama dole, sai dai ba rabuwa ce ta har abada ba, rabuwa domin Aure ta zama dole, ko a Sirri ko a sarari indai da rabo wataran za mu raba Muhalli" ɗan tsayawa ta yi kafin ta cigaba "Na karance ki sosai, na lura kina matuƙar son Hamdan, kuma shi ma yana Sonki, ko domin shi ina ganin idan na zamo silar Rabuwarku na yi rashin Adalci, don na san zai shiga damuwa fiye da yanzu, ba ni da ƙwarin gwiwar da zan iya zama Katanga a tsakaninku , don haka zan kai maganar wajen Abbanki, sai ki shirya buɗe baki ki ba shi amsa, ba wai ki yi shiru ba" 
    Tana kaiwa nan ba ta jira amsarta ba ta fice daga ɗakin ta nufi ɗakin Abba.

      Wata sabuwar Bugawa zuciyarta ta shiga yi, tunanin yadda za ta iya kallon tsabar Idon Abba ta ba shi wannan amsa me tsauri take yi, ga shi a gefe guda tana jin cewa zaɓar Hamdan a matsayin wanda ta yarda da shi tamkar Babban kuskure ne da ka iya Tarwatsa rayuwar farinciki a Ahalinta......

   "Ya zan yi?!! anya kuwa ban yi Babban Ganganci ba in na amsa da E,? idan na ce A'a ya zan yi da Son Hamdan da yake neman Kashe ni??, Yaya Hamdan zai rayu idan ya rasa ni?, wa zan Aura da zai Mantar da ni wannan Ƙaunar da ta danne Zuciyata?!, idan na Zaɓi Hamdan kuma wace irin rayuwa zan yi da shi?, da ya zamu yi Rayuwar Aure ba tare da Sanin Mahaifansa da suke Kula da duk lamuransa a matsayin Mara Aure ba?!!...." 

   Wannan Tambayoyin su ke Gasar Fidda Gwani a cikin Ƙwaƙwalwa da Zuciyarta.
Babban rikicin da ya haifar mata da juyawar kai gami da ƙarancin shigar tunani Ƙwaƙwalwa da faɗaɗa shi a zuciya, har da jiri da gani dishi-dishi.......


Aunty Indo ✍️