GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
Gadar Giwa
by @auntyindo
***
........GABA.......
"Wata banzar magana na ji a gurin Ammy, wai kana son wannan Yarinyar Agola!" Marwan ne ya yi maganar cikin sigar rainin hankali.
Ji ya yi kamar ya dirka masa ashar, amma sai ya maze ya kawar da kai gefe sannan ya ce "Gyara zancen!, don na ce zan Aure ta ba wai ina sonta ba ne!, ko ba ka san ana Aure ba don So ba?" Marwan ya saki Murmushin gefen baki gami da cewa "Kenan Sha'awarta kawai kake yi?"
a zafafe Hamdan ya zuba masa ƙartin idanunsa, kafin ya ce "Yes! Sha'awarta nake, ai na Balaga! kuma ina da dama da Lafiyar da zan yi Sha'awar kowace Mace, ba sai Ƴar Masu Kuɗi ba!" Marwan ya jinjina kai yana wani taƙadirin murmushi, "Lallai ka balaga don na ga alama, ni kake gaya wa duk maganar da ta zo bakinka ko?" "Na nuna Sha'awata akan abu, kuma kamar yadda aka saba na janye saboda Iyayena ba sa so, maganar ta wuce!, idan ba ka so in gaya maka ba suga kar ka ƙara dawo min da abunda baya gabana, ka san ni ba mutum ne me kwana da damuwar wani ba, bana so ka dinga mayar dani baya!"
yana kaiwa nan ya ratsa ta gefensa zai wuce, Marwan ya yi saurin riƙo hannunsa, ya tsaya cak! ba tare da ya juyo ba, Marwan ya ɗan numfasa kafin ya ce "Alamomin balaga sun ƙara tabbata!, amma ba laifinka ba ne, laifin wanda suka nuna maka Yayanka ba shi da daraja a idanunka ne, sai dai kasan Sama ta fi ƙarfin Zungura da Kara, mu zuba mu gani!"
Duk yadda Hamdan ya so danne Zuciyarsa ya kasa, sam ba Mutum ne shi me son hayaniya ba, sai dai yana da zuciya idan aka kai shi ƙarshe. Fizge hannunsa ya yi tare da juyowa yana fuskantar Yayan nasa , cike da ɓacin rai da takaici ya ce " Marwan! kasan dai ko dambe za mu yi ban yi Lalacewar da zan daku a gurinka ba! dan haka ka bar ni in yi rayuwata daidai da yadda na tsara!, ni bana cikin masu ra'ayi irin naku, Gasa, Adawa, ko wani abu duk baya gabana, ku je kuyi da wanda yake son yi!"
"Good Action!" Hairaan ya faɗa yana sakin nasa murmushi irin na Miskilan Yara masu ji da Shu'umanci.
Wani mugun dafi ne ya soki zuciyar Hamdan, ya zuba wa Hairaan ido yana jin wani abu a ransa wanda ya kasa fassara shi.
"Kun gani ai, kuna yi wasu na muku dariya, haka kuke so dama Ko?" Sabran ne ya yi maganar cikin takaici da baƙin cikin abun da suka yi ɗin.
Hairan ya watsa wa Sabran wani banzan kallo kafin ya juya ya yi kamar bai san da su a wajen ba, cikin nutsuwa Hamdan ya matsa inda yake , cikin raunin murya ya furta sunansa,,, kallon ko in kula ya yi masa ya kawar da kai, bai gaza ba ya ɗan murmusa gami da cewa "Kenan abun daɗi ne abunda muka yi ko?, ba ka ji takaicin ganin Yayyenka suna Sa'insa ba?" "Ana jin hakan, amma ba akan kowa ba, kuma ba koda yaushe ba!" ya ba shi amsa a taƙaice.
Marwan da ke ta zuba musu harara su duka ya yi ƙwafa gami da girgiza kai, da sauri Sabran ya ce "Don Allah Yaya meye na biye masa kuna wannan kuma?, kai ne sama...." katse shi ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce "Ya isa!, ka dinga tauna magana kafin ka faɗeta, ka dinga tunawa mu Yayyenka ne ba wai Ƙannenka kamar wancan Mara kunyan ba!" ya ƙarashe maganar yana kallon Hairan shi kuwa ko a jikinsa ransa fari tas!.
Kafin Sabran ya yi magana tuni Marwan ya bar wajen, Hairaan ma saɓewa ya yi ya bar Hamdan yana famar bin sa da kallo.
Allah ya sani yana matuƙar Ƙaunar Ƴan Uwansa!, bambancin Ƙauna da Iyayensu suke nunawa bai sa ya ji akwai Bambanci tsakanin shi da su ba, sai dai a wannan Gaɓar ya lura Tarihi ne ke shirin maimaita kansa, abunda ya faru da Zumuncin iyayensu shi yake shirin faruwa tsakaninsa da Ƙannensa, Laifin Waye??? shakka babu laifin Iyaye ne da masu faɗa a ji, dama an ce GAƊAR GIWA Toro ne ke Buga Ganga, wanda bai kai ba to fa bai isa yayi wannan gagarumar Ɓarnar ba.
Riƙo hannunsa da Sabran ya yi ne yasa shi dawowa hayyacinsa, ya sauke nannauyar ajiyar Zuciya kafin ya zame ya nufi cikin Gida....
........BAYA.......
tunda Maama ta bar ɗakin shiru kawai ke aiki,,, Khalil yana zaune kamar wanda aka dasa a gurin, Hibba kuwa yamutsin da ƙwaƙwalwarta ke yi yasa kukan nata ma ya ɗauke gabaki ɗaya ta rasa inda kanta yake.
sun ɗau tsawon lokaci a haka kafin Khalil ya numfasa ya ce " Yaya Hibba!, Ni fa da na ga bakya saurarar kowane Saurayi na ɗauka ma ba zakiyi Aure ba sai dai in mun gaji dake mu samo wani ƙaton Tuzurun Mu Aura miki, sai gashi yau an wayi gari kin Faɗa Rijiyar SO me tsanani wanda fitowarki sai dai Allah kawai!"
Yin maganarsa a daidai wannan datsin ya temaka sosai wajen dawo da Hibba inda take zaune saɓanin yadda Ruhinta yayi fitar burgu zuwa Birnin ruɗani...
Ta zuba masa ido tare da sakar masa wani wahaltaccen murmushi da ke ƙara bayyanar da saƙon Zuciyarta.
Cigaba ya yi da cewa "Kuma Son wanda sam bai dace da Salihar Mace irinki ba, ni fa ko Mace ne ni ban ga abun so Ajikin Yaya Hamdan ba saboda Kwata-kwata tun daga Iyayensa har Ƙanne da Yayyensa ba wata Ɗabi'ar ƙwarai ce da su ba!" "Uhm! Khalil kenan, Ita Ƙauna ta gaskiya babu ruwanta da Kyawun fuska bare kuma Halin wasu na kusa; Tabbas ina cikin Jarrabawa mai tsanani! kawai ka tayani addu'a Allah ya ba ni ikon tsallakewa, ina matuƙar Ƙaunar Hamdan, yadda nake ji a raina,, zan iya Fuskantar kowane Ƙalubale dominsa, ba na son ganin Rauni ko damuwa akan Fuskarsa, ina son zama Haske ga rayuwarsa, a taƙaice dai idan na rabu dashi ba haka zuciyata ta so ba, don ba yadda zan yi ne!" Matse ƙwalla Khalil yayi gami da zuba tagumi, yanzu kam bai san me zai ce ba, don Ƙwaƙwalwarsa ba ta yi girman da za ta iya Ɗaukar wannan Babban lamarin ba.
Maama ce tayi sallama a ɗakin, ba ta jira amsa ba ta ce "Abba na kiranki!" "Yasalam! Maamata!....." Hibba ta faɗa gami da rushewa da wani azababben kuka.
Aunty Indo ✍️