GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar Giwa

by @auntyindo

   "Mene ne kuma Hibba?" Maama ta tambaya cikin matuƙar damuwa,
"Don Allah ki yanke hukunci a madadina!,,, ina Cikin ruɗani, ina cike da tsoro Maama, don Allah ki yanke hukuncin da ya dace da ni"     
 "Ba ni da damar yin hakan, rayuwarki ce Hibba dole Abba ze so jin ta bakinki, ki sani ni zan iya yi miki dole amma Shi ba ze iya hakan ba, sabosa ke AMANA CE GARE SHI"    

   "Kawai ni ba na son shi!,, ba zan iya zuwa gurin Abba ba, don Allah kawai ki ce masa bana so"
   Cikin Muryar kuka Khalil ya ce "Wallahi Maama Ƙarya take, tana son shi ni Shaida ne, kuma yanzu ta gama gaya min ba ta son rabuwa dashi, kawai Maama ku yanke hukuncin da kuke ganin yafi"

   Ƴar harara Maama ta yi masa tana cewa "Yayar taka ce take Ƙarya?, yi min shiru anan wajibinta ne ta je ta amsa da bakinta ba da nawa ba"
 "To ki koma zan rako ta" Khalil ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa.

  Ficewa Maama ta yi , Khalil kuma ya ɗauko Hijab din Hibba ya damƙa mata gami da cewa "Ki lallaɓa ki je, ki cire duk wannan tsoron naki da rarraba ra'ayi, ki yanke hukunci daidai raunin zuciyarki" cigaba ta yi da kukan ba tare da ba shi amsa ba.
Ya karɓe Hijab ɗin ya ƙaƙaba mata sannan ya riƙo hannunta yana cewa "Tashi mu je!" a yanzu kam ba ta samu ƙwarin guiwar yi masa jayayya ba, tashi tayi ta bi bayansa shi kuwa sai janta yake kamar shine sama da ita .

       Ɗan gyaran murya Abba yayi , ya kalleta cikin sakin fuska ya ce "Kukan na meye kuma?, ki share hawayenki kin ji? ba a son yawan kukan nan Addu'a zakiyi" "Toh!" ta amsa cikin shashshekar kuka.

    "Na ji bayanin da Maama ta zo min da shi, kuma zan yi na'am dashi ne bayan jin ta bakinki, duk da akwai rikici acikin hakan, amma tunda ya kasance da alaƙa ta jini ina ganin haɗarin bai kai yadda muke zato ba" jim! ya ɗan yi kafin ya ƙara maida hankali kanta ya ce "Kina son Hamdan duk da wannan Uzurin da ya zo dashi?" ƙasa ta ƙara yi da kai tana ƙoƙarin danne kukan da take shirin rushewa, maimaita tambyar Abba ya ƙara yi cikin tausasawa, ta runtse idonta da ƙarfi daidai lokacin da Sunan Hamdan ya sake fitowa a bakin Abba.

  "Ina Matuƙar Tsoron in rasa ki Hibbah!" wannan Kalma ɗaya da take yawan ji a bakinsa itace fitilar da tafi haska tunaninta a daidai wannan lokacin.

    ba ta san lokacin da ta gyaɗa kai ba, tare da ƙarin bayani a gaba "Don Allah ku yafe min Abba!, zan iya haƙura da shi idan bakwa goyon baya zaɓinku kawai shi nake so!" Abba ya sauke wani zazzafan numfashi, zuciyarsa ta yi wani bala'in nauyi, ya gama tsunduma cikin matuƙar Tausayin Marainiyar da Amanar ta ke rataye a wuyansa.  
Ko shakka babu shi ma a gurinsa wannan tsananin Ƙaunar da Hibba ta kamu tamkar Wasan Makaho a bakin Rijiya ne, idan yayi wani motsin yana iya jefa kansa cikinta.
   Yau dai yana kan wani Siririn layi wanda ya raba tsakanin cika Alƙawarinsa da kuma rusa farincikin Amanarsa, tabbas idan ya barta ta Auri Hamdan kuma ta rozarta daga baya shima yana da Alhaki akai kuma hakan na nufin ya karya Alƙawari , idan kuma ya hana ta tamkar rusa Farincikinta ne wanda ba ya fatan hakan.

     Sai da ya ƙara sauke ajiyar zuciya kafin yayi magana cikin sanyi "Zaɓin Allah shi muke nema gabaki ɗaya, ki tashi ki je , kuma ki cigaba da Addu'a ki miƙa dukkan lamuran ga Allah, shine ze kawo mana hasken da za mu gane inda ya kamata mu dosa, Hamdan ɗin kuma zan yi magana da shi a ce masa ina son ganinsa!" ya rufe maganar gami da kallon Maama.

   amsawa ta yi gami da gyara zamanta ta doka tagumi.
Bayan su Hibba sun fita Abba ya dubi Maama ya ce "Me zai hana wai mu nemi iyayen Yaron mu yi magana a junanmu?, ni zan samu Alhaji Ahmad ɗin da kaina sai mu daidaita"  
   Tunda ya fara magana Maama ta tsura masa ido har ya kai ƙarshe kafin ta sauke idon, hakan ya yi daidai da zubar zafafan hawayen da suka jima suna shirin zubowa.

   "Ka manta waye Yaya Ahmad?!, ko a yanzu aka zuba ƙuri'ar raba Aurenmu, ka san shi ne sawun farko wajen zaɓar Rabuwarmu, a hakan kake ganin zai yarda Ɗansa da ya fi Ƙauna ya Auri Hibba? wadda ba komai ba ce face Marainiya Ƴar wanda......" katse ta yayi cikin haɗe fuska , "Kar in sake jin surutan nan!, wannan abun da ya faru a baya ne kike faɗe, wannan kuma akan Yara ne zan same shi kawai" cikin muryar kuka ta ce "Idan kayi haka ka tarwatsa sauran alaƙar da ke tsakaninmu da Yaron nan!, kawai ka yanke Hukunci a matsayin Mahaifinsu duka su biyun , da ni da Hibba mun shirya kuma mun ɗauka ko Amincewarka ko akasinta, amma kar ka manta shi ma Hamdan Ɗanmu ne, yana buƙatar taimakonmu!"   

   Shiru yayi yana nazari kafin yace "To shikenan, idan na yi magana da Yaron zan ƙara nazartar abun sai in yanke hukunci, wannan kukan kuma na gaji da ganinsa!"
  ya ƙarasa maganar yana sauke rumfar Ido, share hawayen ta shiga yi tare da dannar zuciyarta don gudun cigaba.

      Hamdan ...
Yana kwance kan makeken Gadonsa yayi lakato yana tunanin rayuwa, wayarsa ce ta fara ƙara ya tashi a firgice ya rarumo ta, haka kawai gabansa ya faɗi daga jin ƙarar wayar.
 Gani lambar Hibba yasa shi saurin ɗagawa tare da furta sunanta cikin rawar baki.
    
  ta sauke ɓoyayyar ajiyar Zuciya kafin ta ce "Ba ka yi bacci ba?" "11:00pm fa kodai bacci kikai kika tashi ne?" 
  "A'a !" "To ya akai na ji muryarki haka a sanyaye, kamar ma kuka kike yi" shiru tayi gami da cije gefen leɓenta, "Hibbah! faɗa min me yake faruwa please!" "Babu komai fa, kawai Abba yana son ganinka" "To gani nan zuwa yanzun nan!" ya faɗa tare da tashi cikin rawar jiki.

  Dariya ya ba ta don haka ta ɗan dara tana cewa "Ba yanzu ba fa!, ka bari sai da safe dare yayi" "Ba wani dare ne ya yi sosai ba, ki bari in zo kawai don Allah" "Ba zan barka ka fito yanzu ba, unguwar Masu kuɗi fa da tazara tsakaninta da ta talakawa" "Ke unguwar kike dubawa, ni kuma ina duba alaƙa ne, babu tazara tsakanina da ke Hibbana, goben nan fa da nisa, yanzu sai in ga kamar Gari ba zai waye ba" "To yanzu dai Abba yana buƙatar hutawa bacci zai yi, yi Alwala ka yi Nafila sai ka yi mana Addu'a" "To shikenan, zan yi yanzu" "To sai da safe ko? saura kuma ka shiga damuwa har in ga ka rame kafin gobe"
  "In sha Allah ba zan rame ba, ke ma kar kiyi kuka don Allah!" "Yanzu fa in na biye maka za ka kwana kana surutu ne don haka sai Allah ya kaimu" kafin ya amsa ta katse wayar.

 ajiyar Zuciya ta sauke tana tuno yadda ta ji duk ya ruɗe, wai wannan ma kenan ina ga sun yiwa Juna tazarar da babu iyaka?.....

       Washegari....

   Tun sassafe Hamdan yake yunƙurin fita sai kuma ya fasa in ya tuna zai iya zuwa ba su tashi ba.
Ƙarfe Takwas na yi kuwa ya fito da shirinsa tun na sassafe, Mamy da Hairaan ne kaɗai a Fal.

 Tun da ya doso suke binsa da wani Kallo me alamun manufa, ya ɗan zauna ya gaisar da Mamy, amsawa ta yi ba yabo ba fallasa.
Hairan kuwa wani shegen kallo na kar ta san kar yake binsa da shi, ɗan murmusawa ya yi ya ce "Hairan yau da wuri haka?"  
  "Kai ma da wuri haka?" Hairan ya faɗa yana tsare shi da ido, ɗan jinjina kai ya yi ya ce "Ina da wani ɗan Uzuri ne" "Oh!" kawai Hairan yace gami da kawar da kai gefe.

   Wannan babban lamari ne da ke damun Hamdan sai dai a yanzu damuwarsa ta wuce wannan, "Mammy sai na dawo" ya ce tare da nufar hanyar fita, yana jin tsakin da Hairan ya zuƙa amma hakan ba ya gabansa.

       Hibba na zaune ta doka tagumi Khalil ya shigo yana dariya gami da cewa "Ga Tauraron can fa ya bayyana!" "Wai da gaske?" "Fita ki gani" "To ai Abban bacci yake" "Shi ina ruwansa, ai ba a Bori da Sanyin jiki, yanzu dai kam na ƙara tabbatarwa so yake ya rabani da ke ya zama ganinki sai na cike form" "Kai fa gandun shirme ne, an ce maka don nayi Aure rabuwa ne?, ai za ka dinga zuwa ni ma duk sati zan dinga zuwa".

    "Saboda ke ce Daɗi Gida ko?" Maama da ta ɗage labulen ɗakin ta leƙo, ta faɗa tana ɗan murmushi , ƙarawa tayi da cewa "Ka je ka ce masa ya shigo, ke kuma ki koma Ɗakin Gado ki ba su nan ɗin" Duk suka amsa gami da ƙoƙarin aiwatar da abunda ta ce.


Aunty Indo