GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar Giwa

by @auntyindo

Tun da ta fice daga ɗakin ba ta ƙara bibiyar abin da ya faru ba.
 Tun daga kan Abban har Maama da Hamdan ɗin babu wanda ya ce mata ga matsaya, sosai zuciyarta ta yi rauni ta shiga matuƙar damuwa don da alama dai Alaƙarsu ta gama tsinkewa , gashi ta kasa fahimtar komai daga motsin Maama, Hamdan kuwa ko Flashing ɗinsa ba ta gani ba bare kira.

    Washegari...
 Tana zaune ta tasa Abincin karin kumallonta a gaba tana ɗan tsikara da kaɗan-kaɗan Maama ta ɗan dube ta da murmushi ta ce "Ba ki tambayeni ƙarshen Tattaunar Abbanku da Hamdan ba!" ƙasa ta yi da kai kawai sai wani ɗan murmushi da ya suɓuce mata.
 "Da alama dai Abba ya amince don yanzu abunda ya rage kawai zuwa ga Iyayenki ne Dangin Babanki!" wata kyakkyawar bugawa zuciyarta ta yi, cikin kaɗuwa ta ce "Kenan,......" sai kuma ta yi shiru.

 "Kin daɗe ba ki je gaishe su ba ma, ban san me ya hanaki zuwa ba"  
  "Kawai na gaji ne, yadda na ɗauke su da muhimmanci su ba haka suke ɗaukata ba, in na je sai in ji na Muzanta shiyasa kawai na dena zuwa" "To yanzu zuwa ya kama ki kuwa, Bayan Abban ya je sai ku je ke da Hamdan ku gaishe su" gyaɗa kai ta yi don bakinta ba zai iya furta komai ba, tabbas ta san ba su damu da damuwarta ba hakan kuwa ze iya zamo mata matsala a wannan lokacin, da akwai mafita bayan haka da ta hana aje musu da maganar nan, tunanin da take kenan sai dai sanin ba me ɓullewa ba ne yasa ba ta yi wani yunƙuri ba.

    Kamar yadda Abba ya ce ya samu Baba Habib da Umma Zaliha da Zancen Auren Hibba.

Baba Habib Yaya ne ga Mahaifinta uwa ɗaya uba ɗaya.
Umma Zaliha kuma Ƙanwar Mahaifinta ce uwa Ɗaya uba ɗaya.
 Su uku ne a wajen Iyayensu, kuma za a iya cewa su Biyun nan ne kaɗai suka rage mata a dangin Mahaifinta sai Ƴaƴan da suka Haifa.

   Tun da Babanta ya rasu kuwa babu ruwansu da ita, sai ita ke nemansu kamar yadda Abba ya ɗora ta akai, amma hakan bai sa sun ja ta a jiki ba, musamman da yake suna jin haushin Abba ya riƙeta bai ba su ita ba, sai ya zama sun cireta daga cikin Dangi, ita kuwa da ta girma ta gane hakan sai ta ɗauke ƙafarta ta cigaba da sabgoginta.

     Sun kawo inkari sosai akan Auren musamman da suka ji cewar ba Aure ne irin wanda aka saba ji ba, za a yi shi ne ba tare da sanin iyayen Ɗa ba, a gefe guda kuma sun faɗi maganganu iya ƙoƙarinsu kan cewar an raba su da Ƴa an fi su iko da ita sai yanzu da Aure ya taso ake nemansu.

  Shi dai Abba banda haƙuri da lallami ba abunda yake musu har ya samu nasarar Shawo kansu da Ƙyar. 

   Hamdan .....
Gabakiɗaya ya rasa inda ze tsoma ransa , yadda tattaunawarsa da Abba ta kasance shi ne abun da ya fi damunsa a duk ƴan Kwanakin nan, ya kasa A
amsa duk wata Tambaya me tsauri da Sharaɗoɗin da ake son cikawa na Auren Hibba, tambayarsa ɗaya a yanzu ya akai hakan take faruwa duk da irin son da yake Mata?, Ismail, Maama, da shi kansa Abba, duk sun yi masa tambayar da ya kasa buɗe baki ya amsa ta...

   Cikin wannan Tunanin me cike da ruɗani gami da sanyaya jiki Hamdan ya dosa kai cikin Babban Falon Gidansu, gangar jikinsa ce kawai a wajen, hankalinsa kuwa yayi nisan kiwo...

 Ba zato ba tsammani ya ji an bugi ƙirjinsa tare da hankaɗa shi baya yayi sauri ɗago ido don ganin waye, durum!! Zuciyarsa ta buga ya ƙara tsirawa Marwan ido har ya ƙaraso inda yake.

  Wani shu'umin murmushi ya saki me cike da ma'anoni kafin yace "Wata banzar magana naji a gurin Ammy wai kana Son wannan Yarinyar Agola!"....................

     Cigaban Labari.......

     "Wai ke bakya tashi Faɗawa Mutum ana nemansa sai dare ya tsala kuma ki hana ni fitowa" Hamdan yayi maganar cikin wata shagwaɓaɓɓiyar murya, cikin murmushi ta ce "To ai se da daddaren aka neme ka, ka ga kuwa gwara in bari sai dare yayi sosai don nasan idan ƙarfe 8:00 ne sai ka fito a wannan Daren" "Gaskiya kar ki kuma, in ba haka ba kuma zan dinga fitowa ko ƙarfe biyun dare ne" "To shikenan zan dena" "To ki kwanta kiyi bacci don gobe da wuri zan tashe ki" "To" ta faɗa tana ɗan murmushi.
Da haka suka yi sallama kafin kowa ya ɗora tunaninsa daga inda ya tsaya.

       Tun Ƙarfe Bakwai ya gama shiryawa tsaf! sai kuma ya nemi guri ya zauna yana jiran lokaci ya ɗan ƙara ja ya wuce Gidan su Hibba.
Cikin sa'a sai ga Kiran Daddy ya shigo cikin rantsatstsiyar Wayarsa.

 Sai da gabansa ya faɗi ya bi wayar da kallo cike da tunanin abun da Daddy ya zo masa dashi a wannan Safiyar.
da ƙyar ya amsa kiran yasa handsfree "Good Morning my Son!" Daddy ya faɗa cikin murya da ke nuna farinciki da tsantsar Ƙauna . 

Hamdan ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, cikin muryar da taso fito da damuwarsa ya ce "Ina Kwana Daddy!" Daddy yayi wani dum!! a ransa yana faɗin "Ji wani sabon Salo, yaron da gaisawar Aboki da Aboki muke dashi yau kuma shi ne yake wani ce min Ina Kwana?" bai zurfafa tunanin ba sai ya amsa ya ɗora da cewa "Na ga yanzu da wuri kake fita, kuma Aiki na tafiya daidai, sai dai mun daɗe ba mu yi zaman Lissafi ba, shi yasa na kiraka yanzu duk abun da kake ka bari ka zo ina nemanka, yau sai mun yi lissafi za ka bar Gidan nan, tun da naga yanzu zaman waje ya fi maka daɗi fiye da na cikin Gida" Hamdan kamar zai fashe da kuka ya ce "A bari sai gobe...." kafin ya ƙarasa Daddy ya katse shi "A'a fa, maza ka zo yanzu, yau ba fashi don ina da lokaci yanzu, Ko ka manta zan bar Ƙasa nan da Kwana uku?" "Uhm Daddy da Kuɗi.... Ban manta ba!" Hamdan ya faɗa cikin salon Zolaya.
Dariya Daddyn yayi ya ce "Daddy da Kuɗi Abokin Hamdan!"     
murmushi me sauti kawai Hamdan ya yi ya katse wayar cike da takaici.



aunty Indo