GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar Giwa

by @auntyindo

tashi yayi ya canja shirinsa ya saka Jallabiya ruwan Toka (ash color) ya zabari takalmi Slipper, ya san in yaje da shirinsa na fita sai an tambaye shi inda ya nufa.

    Sai 11:00am har da ƴan Mintoci sannan ya samu damar Fita zuciyarsa a dugunzume!.... ko tsayawa sake shiri bai yi ba, da Jallabiyarsa tun ta safe ya fice.

   Cikin fatan Allah yasa Abba be fita ba ya ƙarasa Ƙofar Gidan sai dai abun da idonsa ya gane masa yasa shi tsayawa cak! tare da zuba maganansa, zuciyarsa ta shiga wani mugun tsalle.

   Ismail ya gani tare da Hibba , yadda suka bawa juna dukkan nutsuwa ya tabbatar masa magana ce me muhimmanci suke yi, "Kar dai tsuntsun SO ya tashi daga kaina ya koma kan Ismail?" ya jefa wa kansa tambayar cikin tashin hankali da matsanancin kishin da ke turnuƙo masa!...

    Har ya ɗaga ƙafarsa da niyar komawa sai kuma wata Zuciyar ta tsawatar masa.
   Cikin wani irin yanayi da ya kasa bambance shi ya ƙarasa inda suke gami da ƙaƙalo murmushin dole, Ismail yana murmushi ya miƙo masa hannu tare da faɗin "Barka da Asbah Ƙanina" Da ƙyar ya ɗaga nasa hannun ya miƙa sukai musabaha, kafin ya ce "Bari in shiga wajen Maama" "Ok ya yi kyau, gaishe min da ita don Allah" kai kawai Hamdan ya iya gyaɗawa, shakka babu Ismail Babban mutum ne gareshi, hakan yasa zuciyarsa ta ƙara yin nauyi tausayin kansa ya kama shi.

   "Yanzu yaushe za ki dawo bakin aiki?" Ismail ya tambaye ta yana tsare ta da haɗaɗɗun idanunsa, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce "Bana son yin komai ne a yanzu, hankalina ba a jikina yake ba kwata-kwata" "Ai kuwa Gidauniya tana buƙatarki Hibba!, kin san ke Tauraruwa ce me Haskaka Al'umma, ita kanta Ummina tana Bikon ki, su Anti Rahma kuwa sun damu sosai!" "Zan dawo amma sai dai ayi haƙuri da yanayin aikin nawa, ba zan iya yi kamar Da ba, tunanina akan abu ɗaya yake yanzu"  
  "Ki cigaba da Addu'a, komai ya yi farko yana da ƙarshensa, idan kin shiga Gida ki cewa Hamdan ya ɗan leƙo mu ƙara gaisawa" gyaɗa kai tayi, ta ce "Ka cewa Anti Rahma zan dawo aiki cikin satin nan in sha Allah, ina bada haƙuri" "Zan faɗa mata" da haka suka yi sallama ta wuce cikin gida.

A tsaye ta samu Hamdan kamar wanda ya haɗiyi Taɓarya ya yi lamo a jikin bango fuskar nan a cukune irin ta me jiran ƙiris ya fashe da kuka.
     Tun da suka haɗa ido tayi ƙas da kai ta zagaya kusa da Maama ta zauna, Maama ta ce "Kun gaisa da Hamdan ɗin?, yau dai ya ƙi zama kin ganshi nan inda yake"
 Ƴar dariya ta yi tace "Yau dai da alama Bacci yayi maka daɗi da safen nan, sai gashi wanda zai tashi jama'a tun sassafe sai ranar Allah ya tashi" "Ya Allah! ba zaki gane ba ne Hibba " yayi maganar a shagwaɓe.
   "Yaya Ismail ya ce ka ɗan leƙa ku ƙara gaisawa" Maama ta ce "Gashi kuma da daddare ma ba ze daɗe anan ba Abban, saboda yau yana Ɗaya Gidansa ne, sai dai in can za ka je da daddaren " "Kai! wai ba ke kaɗai ba ce dama?" ya yi tambayar cike da mamaki.
 
Murmushi ta yi ta ce "Eh mana, ina da Anti, ka ga sai ka gaisheta ma in ka je" "Ikon Allah, to shi ke nan zan je can ɗin, sai in zo Khalil ya raka ni ko?" "Yaya Ismail yana jiranka" Hibba ta katse musu maganar , "To na ji!" ya faɗa tare da nufar hanyar fita.

      "Hamdan !" Ismail ya kira sunansa cikin taushi da nutsuwa, sai da ya sauke wata zazzafar ajiyar zuciya sannan ya amsa, Ismail ya cigaba da cewa "Hibba tayi min bayani akan abun da yake faruwa, ina fatan dai babu matsala a cikin hakan?, ina nufin idan ka riga ka Aureta to fa kaine bango gareta, koda duk Duniya za ta juya mata baya a wannan lokacin indai har kana tare da ita to fa raɗaɗin zai zo mata da Sauƙi" ya jinjina kai ya ce "In sha Allah ina tare da ita ba......" sai kuma ya yi shiru saboda baƙin mashin da ya saba sukar zuciyarsa a duk lokacin da ya zo yin furci makamancin wannan.

    Ismail yayi murmushi me taɓa zuciya, cikin raunin murya ya ce "Wallahi na yarda da kai ɗari bisa ɗari Hamdan! hakan yasa na iya janye kaina na bar ka ka Aureta"  

  "Yanzu ni ba wancan Ismail ɗin ba ne, wannan da Yayanta ne kake magana, na san kasan akwai bambanci tsakanin Auren Ƴar da take da Iyaye a raye da kuma Marainiya!, ina so ka yi min alƙawarin za ka kula min da Ƙanwata fiye da yadda kake kula da Dukiyarka!, ka yi min Alƙawarin ba za ka bari ta wulaƙanta, ba za ka juya mata baya, ba zaka bari ta yi Nadamar Aurenka ba!" 


*Aunty INDO*