GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar Giwa

by @auntyindo


Runtse idanunsa ya yi da ƙarfi gami da haɗiye ƙululun da ya kafe a maƙoshinsa.
  Sai da ya yi namijin ƙoƙari sannan ya iya tarkato kalmomi ya aza akan harshen "Indai ina raye!, ba zan gaza ba, zan cika alƙawari da dukkan Sharuɗan da kuka saka min akan ta" sai lokacin ya buɗe idanunsa ya zuba wa Ismail kafin ya ƙara da cewa "Ina matuƙar sonta sosai fa! ban san me zan ce a yarda da hakan ba, amma ni na san ba Ƙarya nake ba Yaya!" daidai lokacin wasu zafafan hawaye suka fara aiki sintiri akan kumatunsa....
 
  Shi ma Ismail matse nashi hawayen ya yi tare da aro juriya da jarumta, ya dafa kafaɗarsa cikin tausasawa ya ce "Karka damu, indai haka ne ni ma zan nuna maka na kai Yaya na Ƙwarai!, kuma ina so ka yi tawakkali ga Allah in ka yi hakan ze kawo maka sauƙin komai" gyaɗa kai kawai ya yi yana jan wani dogon numfashi... "Ni zan wuce, anjima da daddare sai ka dawo wajen Abba da wuri tun da yanzu ka makara!" ya ƙarasa maganar yana murmushi.
   "Na gode" kawai Hamdan ya iya faɗe.
  Ismail ya amsa kana ya shige Motarsa.

  .........Duk wunin yau hankalinsa bai kwanta ba har saida ya dangana da Abba , anan ne kuma Lokacin farincikinsa ya fara tafiya.
Bai tashi daga wurin ba sai da ya tabbatarwa Abba shi fa a wannan Watan yake son a Ɗ
ɗaura Auren, kawai Abba ya ce ga lokaci kokuma shi a ba shi dama ya saka...
  Sai da Abba ya yi da gaske sannan ya shawo kansa akan a bari sai Sabon wata ya kama.

   
 12:00Am.... Kira ya ƙara turawa Hibba a karo na ba adadi, cikin sa'a ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama, "Bacci ma kika yi abun ki, bayan kin bar Bawan Allah ya kasa zaune ya kasa tsaye" "Ta ya ka san na yi bacci?" "Ai daga jin muryarki , don sallamar taki ma bata kammala ba, kuma sai kira nake shiru, ina kika shiga ne tun bayan Isha kaɗan fa" "Yi haƙuri don Allah, da farko dai ban bi takan wayar ba ne kuma tana silent, daga baya kuma na yi bacci, yanzu ma Maama ce ta ga kiran ta ba ni wayar, na gaji ne sosai na daɗe bana iya bacci me daɗi" "Oh! yana da kyau kiyi baccinki kuwa, amma fa sai kin gama rarrashina!" "To fa! rigima ce ta motsa da tsohon daren nan?" "Tun kafin daren yayi ai nake ji da rigimar kuma ban samu me rarrashina ba" "Me ya faru to" tayi maganar cikin shagwaɓa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da murmushi ya ce "Kin san Abba ya amince da Aurenmu shine ba ki gaya min ba ko?, kika barni ina tafiya ina karo da gini" "Ayya yi haƙuri!" ta faɗa tana ƙoƙarin danne dariyarta, "Dariya ma kike min ko?, idan na yiwa bango wani kyakkyawan Karo goshina ya kumbura ya ƙara tsini ke kika jiyo, ke za a dinga Kira Matar Goshi!" yanzu kam sai da tayi dariyar sosai sannan ta ce "Tab! ai kuwa ba da ni ba, sai a ɗaga Auren sai ka warke" "Wallahi baki isa ba, a ranar ma za a ɗaura shi kuwa, ke zaki yi jinyata !" "Har na hango ka kana tafiya Goshi ya fara sallama kafin gangar jiki!" ta faɗa tana ƙyaƙyata dariya, da sauri ya ce "Kam bala'i! ni ɗin? lallai kuwa da zan ƙarawa naki goshin tudu kinga se mu zama ɗaya, sai mun fi matching" ɗan shafa goshin nasa yayi yana dariya ya ce "Wai!.... ni kuwa ya za a gan ni da ƙaton goshi, rangyal! kenan" Hibba ta ƙara fashewa da dariya "Allah ya gani zaka ƙara zama haɗaɗɗen Saurayi a wurin Hibba kawai!, na huta cecekuce da Ƴan Mata don ni kaɗai zan dinga ganin Kyaun ka" "Lallai ma! wato kin samu bakin magana yau ko?, ni fa ban san ma kina dariya har haka ba!" "Tunda ba ka nema na sai da WUTAR SO ta koro ka dama ai ba za ka san ina dariya ba!" Tsam! ya ɗan yi don maganar tata ta taso masa da tsohon miki, ya ɗan numfasa sannan ya ce "Haka ne fa!" jim ya ɗan yi kafin ya ɗora da cewa "Na gode Hibba!, Allah ya ba ni ikon Faranta miki fiye da yadda kika yi min adalci a rayuwata!, da kin guje ni saboda wannan Dalilin da ban san Yaya rayuwata zata ƙare ba Hibbah!, Da ke, da Ismail, da Su Maama Ku ne Fitila Mafi Haske a Rayuwar Hamdan!" "Ina cikin nishaɗi kake son saka ni Kuka !" yadda tayi maganar cikin shagwaɓa yasa yayi saurin gimtse bakinsa ba don ya gaji ba, cikin raunin murya ya ce "Dole ma in yi shiru duk da kuwa gaskiya nake faɗe, ki cigaba da Farinciki Hibban Hamdan!" "To shi ke nan amma ka yi min alƙawarin ba zaka yi tunanin wani abun damuwa ba a wannan Daren" ya ɗan murmusa gami da rausayar da kai, " Gaskiya ba zan iya yi miki wannan Alƙawarin ba, don kuwa yadda Ƙwai yake a lulluɓe da bawonsa haka nima nake lulluɓe da Damuwa, ko ba komai ina jin ciwon zaki zama Matata amma ba ni da Ƴancin Amsa Matsayin Mijinki a duk inda na so!" ''Uhum! uhum! Ni Bacci nake ji ka bar ni nayi baccina!" tayi maganar cike da shagwaɓa tamkar Yarinya Ƴar Yaye.

  "Hamdah na!" ya faɗa cikin salon tashi Shagwaɓar, cigaba yayi da cewa "Na lura dai ba kya son jin kukan da zuciyata take rerewa a yanzu, na barki kiyi baccinki, Allah ya tashemu lafiya, gobe in sha Allah zan zo bayan azhar haka, anan zan ci Abinci sauran ki haɗa ki cinye da rabona" "Allah yasa Maama ta yi Tuwon Dawa, kuma ba zan ce mata zaka zo ba" "To ai ko me kika ci nima zan ci da murna ma ku....." katse shi tayi kamar zata yi kuka ta ce "Wai ba ka de ka dena magana ba in yi baccina'' "Ke kam akwai rigima!, to kiyi addu'a kafin baccin, Allah ya tsare min ke ..." kafin ya ƙarasa ta ce "Amin, kai ma haka, sai da safenka sauran ka yi mafarkina kuma" ba ta jira amsar shi ba ta katse kiran, ya bi wayar da kallo yana murmushi, zamewa yayi ya kwanta yana kallon sama tare da tafiya nahiyar tunani, Wataran dai tare zamu kwana kina baccinki ina kallon kyakkyawar fuskarki... 


   Hibbah... 
Tun Safe tana gama karin kumallo ta ɗauki waya ta kira Raihana ta sanar mata ba zata fito yau ba. Sai da Raihana tai ta ƴan gunguni kafin ta yadda ta amsa.

 Murmushi kawai Hibba ke saki bayan ta ajiye wayar a gefe .
Khalil ne ya katse mata tunanin da cewa "Yaya, Wai duk wannan fallin na meye ne?, har da ƙin zuwa aiki" "Kai dalla, kai fa wani lokacin sai Addu'a, Yaya Hamdan ne fa zai zo, kuma anan zai ci Abincin rana" "To fa Allah gwanin hikima, shi ne bakinki ya ƙi rufuwa tun asuba?" "Wai kai ina ruwanka ne?, kai fa Yaro ne ka dinga yin shiru da bakinka" 
 "To na yi shirun, ido ne nawa, abun da ya fi ƙarfin waiwaye ai sai in sa gaba in ta kallo"
  
 Ɗan harararsa tayi ta kawar da kai, ɗan jim! kaɗan kuma ta ce "Yawwa me ya kamata in dafa masa ne?, duk kaina ya kulle" "Aaaa! abu ɗunɗumi gyambo da Laya!" Khalil ya faɗa gami da riƙe haɓa" "Innalillahi!, ai fa yanzu sai mun gwabza sannan zaka dawo hayyacinka" "Allah ya ba ki haƙuri, ina ganin ki tambaye shi kawai abunda yake so , kar kiyi masa Abincin talakawa ya kasa ci" Ta saki baki tana kallonsa cike da takaici, "Aikin banza" ta ce tare da gyara zama ta koma fuskantar ƙofar shigowa Ɗan madaidaicin Falon.

    Ɗan murmusawa ya yi ya ce "To tunda shawarar tawa ba tayi ba yanzu ga wata, kawai kiyi masa ko Taliya ce" a ɗan hasale ta ce "Khalil na gaji da shawarar nan taka ba na so, kawai kayi shiru!" "To ai ba sai kinyi faɗa ba, kawai ki ce batai ba, bari in yi tunani"
Banza tayi masa, shi ma yayi shiru tare da kashingiɗa.

   Bayan minti ɗaya ya ce "Yawwa to kawai kiyi masa Dambu!" da sauri ta juyo tare da washe baki tana faɗin "Allah ko?" "Ƙwarai kuwa, na san duk Gidansu ba za a samu wadda ta kai ki iya Dambu ba" Tana dariya ta ce "Wallahi ka zo da shawara me kyau, Yaron kirki lallai za a je da kai Garin Gabas" Shi ma dariyar yayi gami da cewa "Yaya Hibba Ƴar Soyayya, to idan kinyi Dambun kawai sai kiyi Soɓo da Kunun Aya me sanyi kawai" yana rufe baki ta ce "Kai Jama'a Lallai zan baka tukuici, gaskiya ka kawo haske a wannan sabgar, to yanzu wa ze gayawa Maama?" "Yo ai ke zaki faɗa, ni ai nayi iya nawa ƙoƙarin" Khalil ya faɗa tare da miƙewa tsaye, "To ai naji ma, Hamdan ne zai zo ko?" Maama ce tayi maganar tare da ƙarasowa ciki ta yiwa kanta masauki kan Kujera 1str........

Aunty Indo