GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar Giwa

by @auntyindo

Khalil ne yac ce "Eh mana, shiyasa kika ga ta tashi tana washewa mutane baki" Maama ta ɗan murmusa ta ce "To yanzu wace Shawarar kuka tsayar?" Khalil ya ba ta amsa, "Za ta yi masa Dambu da Soɓo da Kunun Aya, nasan ma sai ta ƙara da wani ƙalabusan"
  "To hakan yayi, sai ki tashi ki fara shirye-shirye don kin san Dambu yana da ɗan ɓata lokaci, don ma ke na ga be fiya baki matsala ba" Amsawa tayi da "To" sannan suka cigaba da Hira.

    Sai da Maama ta ga rana ta falle sosai ta ce "Ki tashi kiyi abunda zakiyi fa, don yanzu lokaci gudu yake" Ta amsa tare da miƙewa ta nufi Ɗakin Ajiyar Kayan Masarufi, don fara aikin Ka'in da na'in.

 .......

  Hamdan da ya gama ƙure Basirarsa wajen zaɓen kayan da zai saka, duk ya burkita kayan nasa sannan ya samu da ƙyar.
   Wani tsadadden Yadi ne wanda ya sha Aikin hannu me ɗauke da Kyawawan zane Tamkar na Sarakai, shakka babu an sha wahala wajen yin Aikin, domin kuwa komai ya ji banda tsiya in ji Maroƙa. Hula ya ɗauka wadda don Kayan aka yita ya ɗora ta, kana ya cigaba da ƙarewa kansa kallo a Madubi.

Yayi Masifar kyau komai ya bi jikinsa lif-lif ga ƙawatattun Idanunsa masu ɗauke da dogayen gargasa sai sheƙi suke a cikin Adon, ga wani tsabar Kwarjini da ya ƙara .

Shi kaɗai yake zabga murmushi musamman in ya tuno Kyakkyawar Sarauniyarsa wato Hibba.

Sai da yaga ya fara dena ganin Kyaunsa sannan ya matsa daga wajen Madubi ya kwashe wayoyinsa, har zai fita sai kuma ya dawo wajen Madubin ya ƙara Feshe jikinsa da Turaruka tsadaddu masu taushim Ƙamshi.

  Ɗan riƙe haɓa ya yi tare da Tambayar kansa "Ya ma ake Kalaman Soyayya?" wata Zuciyar ta bashi amsa "Ya kamata ka tsara su kafin ka tafi" a sarari ya ce kuma fa haka ne, ya ɗan yi gyaran Murya kafin yace "Am!.. uhum..!" dariya ya saki tare da rufe fuskarsa da tafukan hannayensa yana faɗin "Ni wallahi ma kunya nake ji!" Wayoyinsa ya ƙara kwasa ya ce "Idan na je ma da kansu zasu zo, ai ba ma dole ba ne, ita Ƙauna a cikin jini take ba a cikin kalami ba!" har ya zo ƙofa ya ƙara tsayawa yana cewa "Bari dai in kashe kaina da Camera ko sau ɗaya ne" zuba sauran wayar guda biyu yayi a aljihu ɗayar kuma ya matsa ta ya fara laluben camera.
    Bai tsaya wani duba kyau ko tsayawar hoton ba kawai dai ya ɗauka,,,, ya jefa wayar a aljihu gami da ficewa daga Bedroom ɗin nasa.

 Kai tsaye Babban Falo ya nufa wanda acan ne zai samu Hanyar zuwa waje.

   Yana ƙarasowa Ammy ta saka wata dariya me kama da shewa, kafin ta miƙe ta nufi inda yake tana magana cikin kalamanta masu ɗauke da zallar Yaudara da ɗaukar hankali. "Allah sarki Ɗana abun Alfaharina!, gaskiya kayi kyau, Na ji daɗi da ka bani goyon Baya haka!, tawo ka zauna kusa dani in ji Ɗuminka kafin wasu su gama gane Kwalliyar nan taka!" ta ƙarasa maganar tana janyo hannunsa zuwa kan kujerar da take zaune.

  Kamar wani soko haka ya zauna yana rarraba ido tsakanin Ammy, Mamy, Hairana, wanda su kaɗai ya gani a Falon.
  Cike da fargaba ya motsa laɓɓansa da suka yi masa nauyi lokaci guda ta hanyar cewa "I don't understand, Ammy!" Tallafo haɓarsa ta yi kamar zata sumbaci bakin nasa,, cikin ƴar shagwaɓa ta ce "Kar kayi kamar baka sani ba mana!" Dum! Zuciyarsa ta ƙara bugawa da ƙarfi, kallon Hairana kawai ya koma yi ko zai samu wata alama, amma sai ya ga tana basarwa kamar ba ta gane me yake nufi ba.

   Mamy kam da takaici ya isheta sai ta tashi ta bar musu gurin.
 
 Muryar Ammynsa ce ta dawo dashi hayyacinsa, cikin wata firirita take magana kamar wata ƙaramar yarinya "Gaskiya Farida ta yi sa'ar samun ɗan Kyakkyawan Yaro!, duk wannan Kwalliyar don ita kaɗai, ni har ma Kishi nake ji!" "Farida!" ya maimaita sunan cikin cunkushewar murya, yana shirin ƙara magana Farida ta ƙaraso ta zauna tana fuskantarsu, sai wani yauƙi da kwainane take tana sakar masa wani Malalacin murmushinta wanda yake matuƙar fizgar mafi yawan Maza zuwa gareta.

  Kallonta yai cike da takaici ya ce "Wai ta zo kenan?" Ammy ya yiwa tambayar don haka ta bashi amsa, "Gata nan ma kuwa, ai ka yi daidai da ka shirya yanzu, yau sai ka bata lokacinta, ina so ku fahimci juna sosai, na sa ma tayi maka Girki" "Wai duk ni ɗin kuma?" ya ƙara tambaya.

 Murmushi ta yi tare da miƙewa tana zubawa Hairana wani shu'umin Kallo, cikin salonta na gadara ta ce "A tashi a bawa Yaya guri, zai gana da Matarsa!" Hairana ta tsame ɗan jikinta ta bi bayan Mamynta.

Ammy ta kalli Farida ta ce "Ki kula min dashi fa Ƴata!" Farida tayi ƙasa da kai tana cewa "Kar ki damu Ammyna!" "Ni fa ina da ɗan gurin zuwa, ina ganin idan na dawo sai mu yi maganar" Hamdan ne ya katsewa Ammy hanzarinta na barin gurin...

   Tayi saurin juyowa tana zuba masa Mazajen idanunta kafin ta ce "Ba ka da wani uzuri a yau wanda ya wuce wannan!, don haka ka kwantar da hankalinka ko me kake son ayi maka zan sa ayi, Ki kawo masa Abincin da kika haɗa masa" ta ƙarasa maganar idonta akan Farida.

  Bata jira amsarsu ba tayi gaba tana taku ɗaya bayan ɗaya.
 
Wani irin zafi da zugi Zuciyar Hamdan take ta ko'ina, har wani duhu-duhu yake gani saboda ɓacin rai, Farida kuwa idan ya kalleta sai dai yayi saurin runtse ido don ganinta yake tamkar wata Halitta mafi muni a faɗin Duniya, ga tarin haushinta da yake ji don shakka babu ita ce silar tarwatsa farincikinsa na yau wanda ya daɗe yana yi masa Tanadi.

   Ido Farida ta zuba masa ita ma tana tata Saƙar a cikin ranta, babu abunda tafi hangowa irin ranar da za a wayi gari ya zama Mijinta, daga nan kuwa ai tafi Matar Gwamna a ganinta, nan take ta fara tsaro yadda zata dinga Sarrafa shi cike da salon Ƙauna da kuma nuna iko, shakka babu lokacin takunta kansa sai ya canja.

   Tuno Huɗubar Mahaifiyarta yasa ta saki wani murmushin alfahari da Uwar tata.
Cikin tattausar murya me ɗauke da salon jan hankali sirki da shagwaɓa ta ce "Honey! ka ƙi kallona ka ga irin kwalliyar da nayi maka!" "Auzubillah!" ya furta acan ƙasan zuciyarsa, wani lokacin yadda Yarinyar take iya yaudararsa shakka babu tana yi masa kama da Shaiɗaniya.

   "Wallahi kayi kyau sosai kamar in sace ka fa!, don Allah kayi min kyakkyawan murmushin nan naka mana!" cikin shagwaɓa ta ƙarashe maganar kamar zatayi kukan gaske.
  Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa wanda zuwa yanzu sun fara canja launi ya zuba mata tare da ƙoƙarin danne raɗaɗin da Zuciyarsa takeyi.
Murmushin wanda be wuce kan laɓɓa ba yayi mata ba tare da ya ce komai ba.

  Cikin salo ta tashi ta dawo kujera mafi kusa dashi ta zauna sannan ta cigaba da zuba masa Yaudarar tata. Tun bai saki jiki ba har ya saki, ya fara amsa mata in tayi magana.
Da yake tasan irin hirar da yafi so ta san kan kayanta, shi yasa duk ƙuncin da yake ciki take iya ji dashi, bata wuce gona da iri akan abunda baya so, sai dai takan zurfafa a fannin da tasan yana burge shi.

   Koda la'asar tayi Ammy bata barshi ya fita ba, haka ta sa shi gaba yayi sallar a gida sannan ta tisa kansa akan Abincin Farida wanda gabakiɗaya be kwanta masa a rai ba.
Sai da ta ƙara jaddada masa yau fa shi da fita sai Farida ta bar gidan, ya san ta zauna don haka ya kwantar da hankalinsa, yayi zaune a Falon yana jin Sokiburutsun su Faridan da ƙannensa kamar yadda Ammy ta bashi umarni.

 Kafin yamma ta ƙarasa yi tuni ya gama Galabaita, jikinsa yayi wani mugun laushi, idanunsa banda zugi da yaji ba abunda suke yi, a gefe guda kuwa rauni da Karyewar zuciya sun sako shi gaba, ji yake ina ma yana da hali da ya ɗora hannu a ka ya fasa ihu...
  Haka yayi zaune dandazai a cikin Yara a cewar Ammy da haka ne zasu ƙara shaƙuwa.
Duk Ƴan Mazan ƙannensa da suka shigo banda dariya ba abunda suke masa. shi dai sai yayi shiru ya miƙawa Allah lamarin.


*Aunty INDO*