SAWUN KEKE
by @auntyindo
Misalin ƙarfe 03:00 na dare ya shigo ɗakin cikin tafiyarsa me kama da sanɗa, wajen Drower ya wuce ya ajiye duk wasu tarkacen makamai na jikinsa sannan ya buɗe sif ɗinsa, kamar kullum sabuwar riga fil ya ɗakko don kuwa ba ya saka kaya kuma ya maimaita su, da ya yi sawa ɗaya sai dai ya bayar ko ya jefar, sai dai in ya na son irinsu ma ya kuma yi.
Doguwa ce har ƙasa maɓallanta guda uku ne a jiki kacal a iya tsakiyarta, sama da ƙasanta a buɗe yake, sai ɗan ƙaramin wandonta iya guiwa.
A gefen gado ya ajiyeta sannan ya shiga toilet, bayan ya fito ya zura rigar sannan ya nufi kan Gado.
A gefenta ya zauna ya zubawa fuskarta da take a cukurkuɗe idanu tamkar don ita kaɗai aka halitta masa idanun ko son ƙiftawa ba ya yi, daga yanayinta ya fuskanci a cikin damuwa da takura take yin baccin da alamu ma ba jin daɗinsa take yi ba, gashi ta duƙunƙune cikin lafkeken Hijab wanda ko likafani za a yi mata da shi zai isa.
Cikin nutsuwa ya ɗora tattausan hannun akan fuskarta ya na shafata a hankali a hankali, "Asma'u!! ji nake tamkar tamkar garkuwa ce ke gareni, zan so na kasance me sanya ki farin ciki a koda yaushe, sai dai ba zan iya ba rayuwata cike taf da abubuwa iri-iri, a memakon ki yi farin ciki sai dai ki kasance cikin zubda Hawaye Asma'u" a zahiri yake maganar ya na yi ya na kewaye hancinta da kan idanunta da babban yatsansa, har zuwa lokacin kallonta yake yi tamkar wata sabuwar halitta ba mutum ba.
Ya ɗebi ɗan lokaci cikin wannan yanayin kafin ya janyota jikinsa ya rungumeta a cikin ƙrijinsa ya fara ƙoƙarin cire mata hijabin a hankali ta yadda ba za ta farka ba, har ya cire ya ajiye shi can gefe ba ta farka ba sai ma numfashi dogaye da take ja ta na ƙara linƙaya a cikin baccin, ga dukkan alamu ta samu sauyin yanayi wanda ya sa Zuciyarta ta samu sakewa, har ila i yau bai dena kallon fuskarta ba kai ka ce haɗiyeta yake shirin yi, idanunsa sai wani irin sheƙi da ƙyalli suke yi su na ƙara canja kala.
Hannunta ya riƙo ya zuba masa ido, ganin zobensa ya na nan a jikinta ya sa shi sauke wata sirrintacciyar ajiyar Zuciya, "Asma'u ina buƙatarki a rayuwata, ki kasance tare da ni ."
Ya faɗa cikin wani irin yanayi wanda ya na da nasaba da shaukin sonta, wanda shi kansa bai san da hakan ba.
Har 04:00am daidai ya na rungume da ita sannan ya zameta daga jikinsa ya kwantar da ita, sai da ya ƙara ɗibar lokaci me tsayi ya na kallonta sannan ya sauka daga kan gadon, Alwala ya ɗauro sannan ya canja rigar jikinsa ya zura wata sabuwar jallabiya Brown ya sanya hula ƴar ƙarama taɓani ka ji hadisi sannan ya fara Sallar nafila.
Sai lokacin da aka kira Sallar farko sannan ya tashi daga kan dardumar ya fice daga gidan bakiɗaya.
Sai bayan an idar da sallah a masallatai Allah ya bata ikon farkawa firgigit kamar wadda aradu ke shirin faɗowa a ka.
Zazzare ido ta shiga yi ta na duba ko'ina ko za ta ga Akhiee amma fayau ko ƙyallin rigarsa ba ta gani ba, wayarta ta jawo ta duba agogo ganin lokacin salla na neman ƙure mata ya sa ta yi saurin direwa ta fito daga ɗaki ta na dube-dube ko za ta ga banɗaki, ɗaki biyu ne a wajen daga wanda ta fito daga ciki sai wani da alamu dai ba banɗaki, gashi ko ina a bushe yake ba alamun akwai ruwa.
Komawa ta yi ɗaki da zummar ɗaukar waya ta kira Rislan don jin inda za ta samu ruwan ta na komawa idonta ya sauka akan ƙofar toilet na cikin ɗakin, duk da ba ta da tabbas amma ta na kyautata zaton shi ne don haka ta nufi wajen domin ganewa idanunta.
Sai da ta sauke ƴar ajiyar Zuciya ta jin daɗi sannan ta ɗauro Alwala ta fito, ta na idar da sallar ta yi addu'a ta zame ta kwanta akan dardumar daga haka bacci ya sake surarta.
Yazeed kwana biyun nan sam ba ya iya baccin kirki sabida tunanin Ma'u, har ƙagara yake a kira Asbah da ya fita masallaci ya dawo ko ɗakinsa ya ba ya komawa sai dai ya zauna a harabar gidan don kuwa in ya koma ma ba shi da abin yi sai damuwa anan kuwa ko shuke-shuke ya kalla zai rage zafi.
Yau ma kamar kullum ya na zaune ya buga tagumi kamar a mafarki ya ga gilmin Ma'u da ƴan ƙullin kayanta a hannu ta nufi wajen get.
Zundum!!! Zuciyarsa ta yi wata mummunar bugawa wadda ta yi daidai da tashinsa tsaye, razanar da ya yi gami da bugun Zuciyarsa suka bada gudun mawa wajen juyawar kansa hakan ya haifar masa da jiri idanunsa su ka fara ganin duhu kansa na wata irin majaujawa tamkar ana girgizar ƙasa a cikinsa.
Cikin wata wahaltacciyar murya ya shiga kiran sunanta duk da ba shi da tabbacin za ta ji shi kuma ta saurare shi, da yake suna linzami ne kamar gizo haka ta ji an kira sunanta, gabanta ya yanke ya faɗi har ƙasa, kasa juyowa ta yi don kuwa ba ta san me kiran nata ba, a wannan lokacin kuwa ba ta son kowa ya ganta don so take ta gudu, in ma ba inda za ta je gwara ta dinga tafiya ko ba ta da wurin zuwa, a tunaninta Allah zai haɗata da waɗanda za su temaketa, Ta ɗauki ƴan sakanni a tsaye ba ta ƙara jin an kirata ba don haka ta ci gaba da tafiya cikin sanɗa har ta isa bakin get, sai dai abinda ba ta sani ba ko kuma ta manta da shi, me gadi ya na sa mukullai a ƙofar kuma ba wanda zai bata su sai shi ko Haj Laure, turus ta tsaya Zuciyarta ta karaya tamkar za ta fashe da kuka.
Juyawa ta yi ta na kallon ɗakin me gadi tare da tunanin ko zuwa za ta yi ta roƙi alfarmarsa?
Kamar saukar aradu haka ta ji lokacin da muryar Yazeed ta karaɗe Fadar cikin Masarautar Kunnuwanta, sabida firgici sai da Zuciyarta ta ɗan tsaya na wucin gadi yayin da numfashinta ya sarƙe kamar me shirin sumewa.
Da rarrafe ya ƙaraso inda take don kuwa ya na miƙewa zai iya faɗuwa, sai da ya dangana da inda take sannan ya tsaya durƙeshi akan gwiwoyinsa, idanunsa da ke gani dishi-dishi ya ɗago ya na kallonta kafin ya fara magana cikin sarƙaƙƙiyar murya tamkar an shaƙare shi, "Ma'u kar ki gudu ki barni, don Allah ki tafi da ni duk inda za ki je zan biki, kuma akanki zan iya jurewa kowace irin rayuwa wallahi!!"
Yadda yake maganar tamkar zautacce ya sa Ma'u ta ƙara tsorata da shi, salon bugun zuciyarta ya ƙara canjawa daga sauri zuwa gudu, kai kawai take girgizawa don kuwa yadda numfashinta da Zuciyarta suka burkice ba za ta iya furta ko uffan ba.
"Ma'u zan mutu idan ki ka gujewa rayuwata, wallahi zan iya makancewa idan idanuna suka dena ganinki, iya tashin hankalin nan da suka gani har sun fara dena nuna mini daidai, duhu nake gani, ƙwaƙwalwata ta na juyawa alamar hauka ta fara tabbata a gareni, wallahi Ma'u ina sonki so me tsanani, irin azababben son nan da yake tarwatsa rayuwar ɗan adam, ki jiƙaina ki tafi da ni ko zan samu sassauci.
Abin nasa haushi yake bawa Ma'u a gefe guda mummunar tsanar da ta yi masa na ƙara zigata akan ta ci mutuncinsa ko zai gane da gaske ba za ta taɓa ƙaunarsa ba, cikin sassarƙewar murya gami da ƙarfin hali ta ce "Ni ba zan taɓa son watsatstse irinka ba, mazinaci ƙazami mashayin giya wanda bai san daraja da kimar kansa ba bare ta wani, ka fita daga rayuwata in ba haka ba kashe kaina zan yi wallahi, ni na tsaneku bakiɗayanku kuma Allah sai ya saka min."
Wasu zafafan hawaye ne suka yiwa fuskarsa mugun wanka, ya girgiza kai gami da dafe ƙirjinsa daidai saitin Zuciyarsa, "Ma'u Zuciyata shirim fashewa take yi, don Allah kar ki hukuntani akan laifin da ba ni na aikata ba, idan wani ne ya yi miki laifi don Allah ki ƴantani daga ɓangarensa, ni ban kasance irinsu ba, kuma wallahi tallahi ba na iya zama na sha giya tin daga ranar da na furta miki kalmar so kika jefani cikin tashin hankali, a da na ɗauka abinda nake yi shi ke kawo nishaɗi na ɗauka tarayya da matan banza shine more rayuwa, amma tinda na kamu da sonki na gane martabar mace, na gane duk abinda nake yi ba shine ke sanya farin ciki ba, na dena ba zan ƙara ba na tuba ki yafe min; yanzu rayuwata da mutuwata sun rataya a wuyanki Ma'u!! ina fatan ki yi mini kyakkyawan zaɓi."
Ya ƙarasa maganar gami da rushewa da wani susutaccen kuka tamkar ƙaramin yaron da ke neman Mahaifiyarsa.
Dogon tsaki Ma'u tafka me cike fa ɓacin rai da tsantsar ƙiyayya, ba tare da ta sake kallon inda yake ba ta ja ƴan ƙullin kayanta ta koma cikin gida cike da baƙin ciki da takaicin yi mata silar rashin guduwar da ta yi niyya.
A take a wajen wani mugun azababben tari ya sarƙe shi wanda ya haifar masa da shiɗewa daga haka bai ƙara sanin inda kansa yake ba.
Tin da safe da Baba Sa'idu ya je gaisawa da Abee ya gyara zama ya tankwashe ƙafa kamar me shirin kwasar taushe, ya karya harshe ya rattabawa Abee maganganun son rai akan Auren Rislan da Husnee, Abee ya gama saurara sannan ya jinjina kai ya ce "Duk ina ƴan uwan nasa?, a zo min da su don in ji menene aibun da suke gani a cikin hakan?" Baba Sa'idu ya ce "To Yaya" tashi ya yi ya fita don nemosu, da Adamu ya fara karo don haka ya ce masa ya je ya tarkato sauran.
Da yake duk jiran kaɗan suke yi da wane gayawa wane dandanan suka cika tafkeken Ɗakin Abee ɗin, ciki kuwa harda Umma, Innajo, Umma Azima, Umma Uwani, matan Abee, sai Matan Baba Sa'idu su biyu, Inna Huwaila da Inna Kulu, sai iyalinsu cunkus amma banda Sheikh Auwal da Zara da Sauran waɗanda ba sa kusa.
Aunty Indo