Sawun Keke
by @auntyindo
Jiki na rawa Zara ta fara zaro kayan, danƙara-danƙaran Ababen Ado ne dangin su Sarƙa, Awarwaro, Ɗan Kunne, Zobe. daga yanayin kyawunsu da ɗaukar ido ko ba a faɗa ba za ka gane na zallar Lu'u-lu'u da Zinare ne, wato Gold da Diamond, gasu nan kala-kala kowanne da nashi style ɗin.
Ita kanta Zara lokacin da ta kammala fito da su sai da ta kasa jurewa ba tare da ta shiryawa kuka bata fara yinsa.
Daidai lokacin Ruƙayya ta yi sallama a ɗakin tare da shigowa gadan-gadan "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!!!!" ta faɗa cikin kaɗuwa gami da firgici, cike da rashin sanin abun yi ta ƙarasa kan kayan ta durƙusa, har lokacin bakinta a buɗe kamar ƙofar gari sai jinjina kai take yi ta ma rasa abin furtawa.
Zara ce ta fara ƙoƙarin mayar da kayan cikin sauri don kuwa ba za ta so mutan gida su san irin abinda ke cikin Akwatinan ba, sai a lokacin Ruƙayya ta ƙara samun ƙwarin guiwar cewa "Zara! anya kuwa Akhiee ba ɗan Mafiya ba ne???" ta yi maganar cikin tsananin mamaki da fitar hayyaci.
Cikin shashshekar kuka Zara ta ce "Haba Ruƙayya! kamar ba ɗan uwanki ba? ko a titi kika gamu da mutum bai dace ki dinga jifansa da irin wannan kalamin ba, Allah shi ya barwa kansa sanin inda ya same su, ban ga amfanin ku zauna kuna faɗen mugayen kalamai akansa ba."
Ruƙayya ta taɓe baki gami da cewa "Tab!!! Allah ya sittiri buƙui in ji kishiyar me doro, gaskiya ce dai ba kwa so kuma dole a faɗa, don in ba ɗan mafiya ba banga a inda zai samo waɗannan gwala-gwalai da kayan ba, dama indai shan jini ne ai ya saba, ƙila in ya kashe mutum tsafi yake yi da shi."
a fusace Zara ta ce "Tashi ki bar ɗakin nan Ruƙayya!! ba na son ƙara ganinki anan don Allah ki ƙyalemu!!, abinda ya shafemu ne ba buƙatar ki ƙara sa baki a ciki, kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce ka faɗi Alkairi ko ka yi shiru."
"To Alawadaran naka ya lalace, jakin dawa ya ga na gida." ta faɗa tare da tashi jikinta har ɓari yake tsabar zaƙuwa da son ta je ta bada labari.
Tana komawa ɓangaren nasu ta fara ƙwalla kira, "Innajo! Umma! Inna Kulu! Inna Huwaila! Umma Azima! Yaya! Yaya Lantana! duk wadda ta ji ni in bata tsakar gida ta fito."
Inna Huwaila dama itace ta aikata don ta gano abinda Zara da kuma Husnee ɗin suke yi kuma ta yi sa'ar shiga, da yake abin boni na iya ne tamkar kiran Allah haka suka gaggauta bayyanowa, Innajo da Umma Azima da sauran yara dama suna tsakar gida.
Nan fa suka yi rukuni Ruƙayya ta zayyana musu abinda ta gani, har da ƙara zuzutawa abinda yake ƙarami ta kumbura shi ya zamo babba.
Nan fa suka fara magana kowacce ta na gwaɓo tata sobaɗanar, haka suka dinga luliya zancen har wasu daga cikin mazan gidan suka dinga shigowa suna iskar labarin su ma sai a zauna a Zana musu abinda ya faru. Duk wannan abin da ake yi Inna Huwaila ba ta iya cewa komai ba sabida wani miki da ya maƙale a cikin Zuciyarta, ba komai take tunawa ba sai Kisan da Rislan ya yiwa ɗanta, da ya bar shi a raye da tuni ya na nan yana rayuwa amma shi ya kashe shi sannan ya zo ya na tashi rayuwar ba abinda ya sha masa kai. Da wannan tunanin ta gama ƙuluwa ta fara mugayen saƙe-saƙe a ranta.
a Ɓangaren Yaya Fiddausi Matar Yaya Aminu, abin ya fi ƙarfin ta yi magana don kuwa wani mugun kishi ta ji ya tokare mata maƙogoro, ji take ina ma itace ta samu irin wannan hamshaƙan kayan daga mijinta?, Da a kaf gidan Mijinta ya fi kowa bajinta, ta fi duk sauran mata sanya tufafi masu kyau da ɗaukar ado, duk itace tauraruwa, amma yanzu gashi wata Yarinya ƙarama kuma Matar wani Banza mara galihu ta zarceta, sai ta ji kamar ta sokawa Zuciyarta wuƙa kawai ta mutu, "Ta yaya ma zan bari wata Faccala ta fini komai? ya zama dole in san abin yi domin duk gidan nan ni ce Tauraruwa domin Iyayena ma masu kuɗi ne, bai kamata wata kucaka ta zo ta nuna mini iyakata ba, gwara ko kasheta ne na yi na kwashi abinda zan kwasa a cikin kayan nata."
Wannan tunanin kawai take maimaitawa a cikin Zuciyarta wadda take ɗaci da raɗaɗi. Fuuuu!! ta tashi ta koma ɗakinta don ta gaji da jin maimaicin labarin kayan.
Inna Huwaila ta na ankare da ita, duk ta lura da yanayinta don haka ta saki wani shu'umun murmushi don kuwa alamu sun nuna mata ta samu makamin da za ta yaƙi Rislan ta hanyar Cutar da Matarsa, Kakkaɓe zaninta ta yi ta miƙe ta na cewa "Uhm!! mun dai godewa Allah da muka samu haihuwa me rana ba mu haifi annoba ba, Ita dai Hadiza ba ta yi sa'ar zuwanta Duniya ba."
A ɓangaren Zara da Husnee kuwa har yanzu Husnee kuka kawai take yi ko motsawa daga inda take a zaune ta kasa yi, Zara ce ta yi ƙarfin halin mayar da kayan ta na yi ta na sharce ƙwalla don kuwa ita ma abin ya taɓa Zuciyarta matuƙa gaya, kowane ɗan-adam idan ya ga waɗannan kaya kuma a ce sun samu ne daga wurin Akhiee sai ya dasa alamar tambayoyi ba ma tambaya ba. Bayan ta kammala Mayarwa ta koma kusada Husnee ta zauna, kafin ta yi magana a sanyaye "Anti Husnee ki yi haƙuri don Allah ki dena kukan nan, shi dama Akhiee haka yake, ko a karan kansa idan ya saka kaya sau ɗaya ba ya ƙara saka su, idan aka lissafa kayan da yake sawa yau da gobe kinga waɗannan ma ba komai ba ne, Ba sata yake yi ba don ban ga alamar shi ɓarawo ba ne, kuma ya na da sana'a sai dai sana'ar ta shi ba me kyau ba ce tinda Dilan Wiwi ne, yanzu ki kwantar da hankalinki idan ya dawo ki ce masa ya rage kayan ko ajiyewa ne ya yi a wani wurin in ya so in wasu suka tsufa sai ya kawo miki sauran kin ji?" ta ƙarasa maganar cikin sigar rarrashi, gyaɗa kai Husnee ta yi alamar ta gamsu da hakan, Zara ta ƙara da cewa ''Yawan kukan nan zai kawo miki wata larurar, don Allah ki rangwanta, kuma kar ki ce ba za ki yi amfani da kayanki ba don ransa zai iya ɓaci, kuma sai kin dinga lura don za a iya a dinga ɗaukar miki abubuwanki, Ni yanzu zan tafi in kwanta sai Allah ya kaimu" ta ƙarasa maganar tare da tashi ta nufi hanyar fita.
Haɗe kai da gwiwa ta yi ta na sauke Ajiyar Zuciya akai-akai, a haka wani yamutsatstsen bacci ya yi tafiyar ruwa da ita.......
Aunty Indo