35
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----35
Motar ta tsaya a gaban wani katafaren duplex mai cike da kyawun gani da tsari na zamani
remote ya dan na dandanan katafaren gate din ya buɗe kansa
ya kama hannun ta zuwa ciki
Iman ta zuba ido tana kallon gidan cikin mamaki
kallon gidan tamkar wacce aka kawo wata sabuwar duniya, domin ko a mafarkinta bata taɓa tunanin zata zauna a irin wannan gida ba.
idan ka kalli Suhail kwata-kwata bai yi kama da wanda ya mallaki wannan babban gidan ba ,amman a zahiri ba abinda mamaki bake kasancewar matashin Barrister kuma ɗa ne ga Alhaji munnir Mahmud
a hankali suka soma shiga ciki babban gidana mai dauke da part biyu sai boys quarters da kuma dakin mai gadi
A tsakiyar harabar gidan akwai wani ƙaramin lambu mai cike da furanni kala-kala da ciyayi masu kyau da daukar ido kamshin mai sanyi ke tashi daga wajen su Gefe guda kuma akwai parking space mai ɗaukar motoci sama da biyar
Babbar ƙofar shiga palorn an yi ta da glass mai kauri da aka kawata da golden design Da zarar ka shiga falon, idanuwanka za su fara sauka kan katafaren chandelier mai sheƙi da ke rataye daga saman rufin gidan dakin
a hankali ya ajiye trolley ɗin hannunsa a gefen ƙofar ɗakin
Iman kuwa har yanzu kallon ɗakin take yi cikin mamaki.
Duk da cewa tun shigowarta gidan take mamakin tsari da ƙawun wajen, wannan ɗakin ya fi komai ɗaukar hankalinta Fiye da wanda ta gani a baya"
Fararen leather sofas ne masu tsada suka kawata ƙaramin falon ɗakin, yayin da wani katafaren plasma TV ke manne a bango.
Labulayen ɗakin masu launin ash da fari sun ƙara fito da ƙawunsa, yayin da ƙamshin turare mai sanyaya zuciya ke tashi a ko’ina.
A hankali ta tura ƙofar bedroom ɗin.
Nan ma wani sabon mamakin ya tarbe ta.
Katafaren Italian bed ne a tsakiya, an shimfiɗa farin bedsheet mai laushi tare da pillows kala-kala da aka tsara cikin tsari mai kyau.
A gefe akwai dressing mirror mai girma, da wardrobe da ya kusan mamaye rabin bangon ɗakin
Iman ta lumshe ido na ɗan lokaci
A ranta tana tuna ƙaramin ɗakinta na gidan Malam
Ba don ta raina rayuwar da ta taso a ciki ba, amma bambancin ya yi yawa
duk sanda ta tuna cewar ba ita kadai zata zauna a gidan sai taji gara suyi zaman su a karamin gidan su na kaduna su rayu su biyu kadai
Da ƙyar ta dawo hayyacinta lokacin da ta ji muryar Suhail
"ki duba duk abinda bai maki a chanza idan kuma akwai abinda kike so let me know"
kai ta girgiza alamar babu
fita yayi ya masu order abinci ya kawo mata mata
washe gari da yamma jirgin su zeenah ya sauka a airport wanda ta samu rakiya daga dangin ta da kuma na Suhail Aunty Zarah ce Aunty Aisha
Motoci ukku suka raka zeenah gidan ta ,ta Suhail sai kuma biyu da aunty Zarah ta saka a kawo daga gidan ta
iman na zaune a bedroom taji hayani da sauri ta daga labule ta leƙa ta window
sai taji faduwar gaba ganin an nufo ciki da zeenah bata samu gadamar ganin fuskar taɓa sakamakon a rufe take
har bakin gado suka shiga da ita dagin mahaifinta dana mummy suka mata rakiya aunty Zarah ta ce"masha Allah gida yayi kyau zeenah Allah ya tabbatar da Alkhairi ya baku zaman lafiya"
kanwar Alhaji ibrahim ta bude baki ta ce"da yake ma gidan ba bakon ta bane ta tashi cikin arziki ba wai hayen sa tayi a gidan miji ba"
Aunty Zarah tayi murmushi ta kalli aunty Aisha ta ce"mu basu waje ko"
"da dai yafi" maku
wata dattijuwa daga cikin su ta ce"Farida miyasa baki da mutunci ke ko ina sai kin nuna hali ne addu'a fa kawai tayi amman sai da kika maida mata baƙar magana"
tabe fuska tayi ta ce"baba gaje kenan ai wallahi ba'a dagawa dangin miji Kafa dan hakan ba abinda yake kawo wa sai raini ki barni dasu dan ma ita kanta zeenah ba kanwar lasa bace shiyasa koda aka ce tana kishiya banji komai ba dan irin hali na gare ta kingani nan baba gaje har uwar miji bana ragawa bare wata kishiya ko kannen miji"
baba gaje ta ce"naga alama ai shiyasa naga auren ki nata mutuwa gaki nan yarinyar ki karama kinyi aure ya fi sha tun ana lissafi har an soma ɓata"
bata rai tayi ta ce"baba dije miya kawo gori kuma daga magana aure ai kaddara ce idan aure dari nayi wannan ƙaddara ta ce"
"ƙaddara da kuma hali ba,ba shegen mijin da zai iya zama dake da wannan mugun halin naki tirr dashi wallahi"
"tsaki Farida taja" ko kunyar shekarun baba dije bata ji ba
iman dake tsaye bakin kofa ta koma ciki duk hirar da suke babu abinda bata ji ba kalaman farida ke mata yawo a rai"zeenah ba kanwar lasa bace"
jin an turo kofar ta saki labulen aunty Zarah ta gani da sauri ta rungume aunty Zarah ta kamato ta kawo ta bakin gado
ta jima tana karewa Iman kallo haka kawai Allah ya dora mata san ta da kaunar jin take kamar kanwarta da suka fito ciki daya ko ba'afaɗa ba tasan iman taji duk maganar da dangin zeenah sukayi
ƙasa tayi da murya ta ce"nasan kinji duk abinda ake faɗa a bangaren zeenah"
Aunty Zarah ta kamo hannunta
"iman kina da zuciya mai tsabta kar ki bari Mutane su chanza ki"
ki zauna da zeenah a matsayin yar uwa ba kishiya ba kar kiyi la'akari da ke Suhail ya fara aure koba komai ki ba ta girmanta a matsayin babba a gare ki, amma kar ki taɓa raina kanki ko ki manta darajarki"
sai da aunty Zarah ta gama mata nasiha ta tashi zasu tafi dan a daren zasu koma kaduna kuma by road zasu bi shine dalilin da yasa tabar junaid da Amatullah gidan mami
har falo ta raƙo ta wajen aunty Aisha bayan sun gaisa ta ce"Zarah ta shiga ta kirawo su baba dije su wuce"
aunty Zarah ta ce"sai dai iman ba abinda zai kara shigar dani dakin chan"
dakin ta ,ta koma ta dauko hijabi gaban ta na dukan uku uku ta shiga dakin dasu zeenah suke da sallama ta shiga baba dije kadai ta amsa farida ta nuna Iman da yatsa ta ce"zeenah dama wannan yar fiririyar ce matar Suhail din" ta fashe da dariya Wannan ai renon ta kawai yake yanzu yayi aure"
"a hakan ma fa wai ta kile an ci jar miya da kaji"
sai lokacin zeenah ta dago ido ta kalli iman tun daga har ƙasa wani tsaki taja "lalle ai ita bata ga ma abin kishi jikin iman ba Yarinyar da ko yan aikin gidan sufi ta wayewa"
iman tama kasa fadar abinda ya kawo ta ,ta juya zata fita aunty Aisha ta biyo bayan ta jin ta shiru bata fito ba
duk abinda suka faɗa kan kunnen aunty bata sha wahalar tambaya ba
"baba gaje ku tashi mu tafi kar dare yayi" cewa aunty Aisha data haɗe girar sama da ƙasa
Farida ta ce"a rasa wanda za'a turo yayi kiran mu sai Wannan abin wannan ai cin fuska ne idan ta shigo muna sirri fa"
Aunty Aisha bata ce"uffan ba gudun kar ta fadi abinda zai sa Farida tayi mata rashin kunya dan baza ta dauka ba idan ya kama sai tayi ƙasa ƙasa da ita kuma ba Abinda zai faru
kuyi manage da Wannan