FARASHIN IZZAH

Chapter 29

by @hauwajaywrites

Chapter 29


Fitar Abbah da Ya Umar ke da wuya daga parlorn, Mami ta miƙe tsaye.


Tun kafin Mummy ta yi wata magana, ta gyara mayafinta.


“Zan haura sama.” Ta faɗa a taƙaice


Mummy ta haɗe gira

“Ni kam meke faruwa ne?”

Ta tambaya cikin son jin abin da ke gudana 


Mami ko kallonta bata yi ba.


“Babu komai” Kawai ta faɗa, daga haka ta juya ta nufi staircase.


Zahra ma ta miƙe a hankali


“Bari na sha maganina.” Ta faɗa, sannan ta bi bayan Mami


Batoul ta kalli Mummy, Mummy ma ta kalleta sai dukansu suka yi dariya


“Wallahi akwai wani abu Mummy” Batoul ta faɗa


Mummy ta gyada kai

“Ni ma haka na gani, amma idan tayi tsami zamu ji”


Da suka shiga ɗakin Mami. Mami ta zauna a gefen gado sannan ta kalli Zahra


“Zo nan.”


Zahra ta ƙarasa kusa da ita. Mami ta kama hannunta


“Ki kwanta Zahra.” Ta faɗa cikin taushi.


“Amma dan Allah ki cire duk wani damuwa daga ranki.”


Zahra ta yi shiru tana kallonta.


Mami ta ci gaba.

“Kar ki sa wa kanki hawan jini. Abin da ya faru ya riga ya faru, haka taki kaddarar ta zo sai ki karɓa ki ci gaba da rayuwa kamar yadda kika saba”


Murmushi Zahra ta yi

Ba ta da ƙarfin magana sosai a halin yanzu


 ɗaya daga cikin masu aikinsu ta shigo da bowl ɗin fruits, ta ajiye a kan side table


Mami ta kalleta

“Dan Allah ku haɗu ku gyara ɗakin Zahra, tunda yanzu ta dawo gida”


“Toh Hajiya.” Ta amsa, daga haka ta fita


Wani dattijo mai shekaru ne ya zo gidansu Ibrahim, baƙin cikinsa a bayyane yake


Mai gadi ya shigar da shi ciki bayan ya bayyana dalilinsa na zuwa


Yana tsaye ne a bakin parlorn, bai jima ba Ibrahim ya fito


Suka gaisa.


Sai dattijon ya gyara tsayuwarsa 


“Kai ne Ibrahim?”


“Eh.” Ibrahim ya amsa


Dattijon ya gyada kai.

“Nine uban Saudat ne.”


Nan take Ibrahim ya ɗago kai.


Dattijon ya ci gaba.

“Na zo ne dan na shaida maka.”


Ibrahim ya yi shiru.

“Ina neman magabatan ka dan zan aura maka Saudat”


Fuskar Ibrahim ta canza ya koma na mamaki


Dattijon ya ɗora

“Ka gama cutarta, yanzu babu wanda zai yi sha’awar aurenta don haka yadda kuka fara haka zaku karasa, manyan ka nake son gani dan aura maka ita”


Ibrahim ya sauke kansa ƙasa, kafin ya samu damar magana


Sai suka ji takun sawu, Mama ce ta fito, tun daga ƙofar parlorn ta ji ƙarshen maganar.


“Ai Malam.” Ta faɗa tana ƙaraso wa


“Yana da mata, sannan bai daɗe da yin aure ba, taya zai auri wata yanzu?”


Dattijon ya juya ya kalleta.


“Ko mata uku yake da su.” Ya faɗa cikin fushi


“Ko jiya ya aure su, sai ya aureta.”


Mama ta haɗe hannu tana masa wani kallo ta ce “A bisa wani dalili?”


Dattijon ya kalleta

“A dalilin abin da ya bata min ɗiyata.”


Mama ta yi wata dariya mai cike da raini

“Toh dama yarinya naka tana da tarbiya ne?”


Nan take fuskar dattijon ta canza


“Ke ki iya bakin ki” Ya faɗa da ƙarfi yana nuna ta da yatsa 


Mama ta matso gaba

“An ƙi har talaka da kai zaka zo kana mana ihu a gida?”


Dattijon ya kalleta sosai, sai ya gyada kai


“Haka kika ce ko?”


Mama ta ɗaga kafaɗa.


Dattijon yayi wani murmushi yace


“Ki jira” 

Ya faɗa cikin sanyin murya


“Za ki gani.”


Daga haka ya juya ya fice.


Ibrahim ya daɗe tsaye a wajen kansa a sunkuye, ba shi da ƙarfin wata magana.


Daga ƙarshe kai tsaye BQ ya nufa.


Ba ya son jin wata magana daga kowa a wannan lokacin...


Abbah da Ya Umar suna fitowa daga wani chamber

Barristers uku ne suka rakosu har bakin mota.


Suna godiya saboda ba kadan ba abbah ya jikasu da kudi


“Mun gode sosai sir” Ɗaya daga cikinsu ya faɗa


“Ai irin wannan case din muke so Sir, ya bashi da bakin magana daga shi har Wanda zasu tsaya masa”


Abbah ya yi murmushi

“Ku tabbatar kun yi aikinku yadda ya kamata.”


“In sha Allah sir.” Suka amsa gaba ɗaya.


Abbah ya gyara agogon hannunsa.


Sannan ya ce,

“Make sure ku kai masa yau.”


Dukkansu suka gyada kai.

“Ai dole ne sir, yau ɗin nan za a kai.”


Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa, daga haka suka yi sallama


Ya Umar ya shiga seat ɗin direba.

Abbah ya shiga dayan site din, daga haka suka bar wajen


Firdausi ce ke sallama a bakin parlorn.

Da alama yanzu ta iso.


Farida ta leƙo daga kitchen

“Laaa Anty Firdausi!” Ta faɗa cikin fara’a.


“Shigo mana.”


Firdausi ta yi dariya, sannan ta shiga


Bayan sun gaisa, Firdausi ta tambaya


“Ina Zahra?”


Farida ta nuna sama

“Tana bangaren Mami.”


Firdausi ta gyada kai.

“Toh.”


Daga haka ta juya ta nufi staircase

Kai tsaye zuwa bangaren Mami.


Domin tun da ta ji an sallamo Zahra daga asibiti, zuciyarta ta kasa haƙuri har sai ta gan ta da idanunta


A parlorn Mami suka fara haɗuwa.

Mami na zaune tana duba wasu takardu lokacin da Firdausi ta shigo


Da sauri ta durƙusa ta gaishe ta

Mami ta amsa cikin fara’a.


“Firdausi, sannu da zuwa.”


“Yauwa Mami.” Ta amsa.


Mami ta nuna mata ƙofar ɗakin

“Ki shiga ciki, tana can.”


Firdausi ta gyada kai.


“Toh Mami.”


Daga haka ta miƙe ta nufi ɗakin.


A hankali ta tura ƙofar.


Zahra na kwance kan gado tana duba wayarta. Da ta ji an shigo ta ɗago kai, Idanunsu suna haɗuwa Zahra ta dan bata rai


Nan take Firdausi ta lura akwai wani yanayi a fuskar Zahra, ba irin fara’ar da ta saba yi mata ba


Duk da haka ta ƙarasa cikin murmushi, ta rungume ta a hankali.


“Sorry my friend” Ta faɗa.


“Ya jikin naki?”


Zahra ta rungumeta back amma babu walwala.


“Da sauƙi” Ta faɗa a taƙaice. Sai kuma ta ɗan ja baya ta zauna, Idanunta na kan Firdausi


“Firdausi… “Ta kira.


“Na’am?” Firdausi ta amsa


Zahra ta yi shiru na ɗan lokaci kafin tace


“Meya sa za ki yi posting hotunan Ibrahim da Saudat?”


Firdausi ta haɗe gira “Ban gane ba.”


Ta faɗa

“Wane hoto kike nufi?”


Zahra ta ce,

“Wanda yake trending mana”