HADIN KADDARA

Chapter 30

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                     By

         
           AyshaNalado


Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍


BOOK 1


Page  30



Damƙe kuɗin a  hannuta ta yi da karfi,  gabanta na faduwa. A hankali ta dinga takawa,  ƙafafuwanta na hardewa kamar na me koyan tafiya, saboda tasirin idanuwansa da take ji suna yawo a bayanta. Sai da ta yi taku goma sha  kafin ta ji sautin rives da tashin motarsa. Dakatawa ta yi, ta lumshe ido tare da sakin  wani wawan ajiyar zuciya, ta kai hannu ta dafe ƙirjinta da ke bugawa, “Ya Salam!  Me ke shirin faruwa? Ya Ammar why?”  A hankali ta yi maganar da raunatacciyar murya.

“Salmah Mu'az!”  Muryar Zahra ya katse mata tunani, da sauri ta ware idanunta, akan Zahra dake nufota da sassarfa. Hannunta ta damƙa, cike zaƙuwa da ɗokin ganinta ta ce, “Mutuniyar tun ɗazu nake ta zuba idon ganinki, na kira wayarki ya fi a kirga ta ƙi shiga.”  Ido kawai ta zuba mata tana kallo,saboda yanayin da take ciki. Zahra ba ta kula da sanyin da ke tattare da ita ta ci gaba da cewa, “Jiya kun yamutsa hazo a cikin Campus fe ke da mutuminki, kun bar baya da ƙura, hmmm ko kin san bidiyon marin nan ya fita?”  Tamkar dukan wuta, batun  ya daki zuciyarta,  amma a zahiri ko gezau,  yamutsa fuska ta yi ta taɓe baki  “And so what?”  Kallon ba ki da hankali, Zahra ta watsa mata, sai kuma ta girgiza, “Ina ga baki fahimci abinda nake nufi ba ko?” “Look Zahrah. Go straight to the point, ki gaya min abinda ke faruwa.”  “Ai ni kin wuce tunani Salmah  Ɗan tsaki ta saki, “Ki na da matsala wallahi.”  Ta bata amsa  tare da fara tafiya cike da kwarin gwiwa, yayinda daga cikin ƙirjinta, zuciyarta ke dakan uku uku. Zahra bata kara ce mata komai ba sai  biyota da ta yi suka jero zuwa cikin school ɗin.

Tun daga yanayin yanda idanun suka yo  kanta yuuuuh! ana binta da kallo kamar za a cinyarta ɗanya,  ta fahimci da wata a ƙasa. Duk da school ɗin bai kai jiya cika ba, ya fi jiya daukar zafi. Duk in da ta gifta kuskus, da hayaniya ke tashi ƙasa ƙasa, wasu tana jin abinda ake faɗa wasu kuma bata iya tantancewa me suke nufi, take  ta samo shinshino abinda Zahra ke son nusar da ita. Siririn tsaki ta ja, ta san dai ba zai wuce akan abinda ya faru jiya ba,  mutane sam  ba su raina abin gulma. Sake ɗaure fuska ta yi tamau, ta ci gaba da tafiyarta a tsanake, sam babu wani alamar ruɗani a yanayinta na zahiri.

Kai tsaye corridor ɗin da zai sada su da department ɗinsu suka nufa.  

 “Ah, my celeb friend… seems like you’re the talk of the whole campus today, ko kin lura?” Cewar Zahra ta faɗa tana ɗan murmushin tsokana.

Salmah ta ɗan kalleta da gefen ido ta ɗan ja numfashi kadan sannan ta kawar da kai ta ce.
“Hakan ba sabon abu bane ai.”  Girgiza kai kawai Zahra ta yi tana ci gaba murmushi, a haka suna suka isa bakin department ɗinsu. 

Kamar inda suka baro, nan din ma dai bata sauya zani ba, zance ɗaya ake yi kamar cin kwan makauniya.
 
Bullowarsu ya ja hankalin dukkan jama'ar wajen, dake tsattsaye kamar abinda da suke jira kenan dama. 

“Ita ce yarinyar?”

 “Yaran nan fa suna cikin alheri, wato shi trending na Allah ne, kalli yadda dan karamin abun nan ya jawo musu suna a duniya, kaga yadda suke zagayawa a media kuwa?” 

“Ni na rasa wanda ya yi bidiyon marin nan ya fitar.”

“Shege kamar yasan abin da zai faru kenan, tun daga shigowar wajen ya fara dauƙa.” 

“Wow Salmah ta zo, yanzu wasan zai fara.”

“Ni haduwarsu ta yau kawai nake son gani.” 

“Kai dai bari, akwai show fa,  don ina da tabbacin sai ya rama marin nan.” 

“Dama shi ɗan iska ne da zai bari ta sha shi sillah.”

“Ni kuma bana tunanin zai iya rama.”

“Allah yasa dai ya zo ɗin, kasan jiya kunya bai bari ya sake dawowa cikin school ba.” 

“Gaskiya dakyar ya iya zuwa.” 

Ire iren hirarrakin da ke tashi kenan a tsakanin matansa, kuma da yawa daga cikin zantukan  sun sauka a kunnen Salmah, amma ta dake kamar ba ta ji komai ba,  sai ma murmushin da ta ara ta yafa, ta shiga ɗan jan Zahra da hira.

Ba su shiga lecture hall ɗin ba, kamar yadda suka tarar da sauran daliban da yawa a waje, suma wajen zamansu na yau da kullum suka nufa, wani  ɗan bench na karfe dake kafe  daga gefen corridor. 

Suna zama sai ga Sofiyyah da Azizah, nan take hira ta barke suka shiga mayar da zancen a tsakaninsu kamar dai sauran dalibai, a nan ne Salmah ke samun labarin sahihanin abinda ke faruwa.

Jiya bayan ta bar school  an samu wani clips na dai dai wajen da ta mari  Suraj da irin zafafan maganganun da ta yaɓa masa, yana ta yawo a group group na school ɗin, wadanda ba su ga zahiri abinda ya faru ba, da wandan da ma ba su san an yi duk suka gani. Wannan shine asalin abinda ya kara hura wutar zancen.  Bugu da ƙari kuma a cikin daren aka samu wani matashi shima ɗan school ɗin ne, kuma tictoker ne sosai, ya kafe bidiyon Salmah wanda Suraj ya fitar,  da kuma na abin da ya biyo baya, wato marin da ta yi masa a bainar nasi, ya yi sharhi akai, ya faɗi maganganu son ransa akan Salmah, ya kuma ce idan har Suraj bai zo ya rama marin da Salmah ta yi masa a gaban kowa ba, su kungiyar matasan Royal Crest University (RCU) Kaduna suna Allah wadai da shi. Nan da nan gayen nan ya yamutsa hazo, kasancewar dama already mutane sun riga sun san abinda ya faru. Kafin kace kwabo take comments section dinsa ya zama filin cece-kuce.  Salmah Mu'az  term Vs Suraj Al-Hikima term. Nan da nan duniyar yanar gizo ta san da zaman Suraj da Salmah.

A daidai wannan lokaci, Suraj ne zaune cikin motar AA bangaren me zaman banza. Idanunsa dake ɓoye cikin baƙin glass akan faskekiyar wayar Ya B dake hannunsa, ba komai yake kallo ba sai yadda duniya ke juyin waina da labarin soyayyarsa,  wani comment wanda ya samu over 2000 reply a karkashinsa ya tsurawa ido yana kallo babu ko keftawa.  Kallonsa AA dake driving ya yi, ɗan murmushi ya yi ya girgiza kai,  “Suraj!” Ya kira sunansa a tausahe, a hankali ya juyo ya kallesa “Me ka ke kallo haka? Ko zantukan mutane sun fara rinjayar zuciyarka ne? Ko kana jin tsoron su yi maka dariya su raina ka su kira ka da lusari, bayan sun yi Allah wadai da kasancewar ka jinsin su?”  Murmushi ya yi mai ciwo,  “Ya B, ban fara son Salmah domin su sani ba, kuma maganar su ba ta isa ta canza ni ba.” 

“Very Good!” AA ya furta tare da gyaɗa kai, a daidai lokacin da yake daidaita parking a kofar shiga RCU.

“Je ka ƙanina. Ka fuskanci kowa da dukkan kwarin gwiwa da jarumtarka, kada ka bari su kai ka ƙasa, ka tuna cewa har abada ina tare da kai.” 

Gyaɗa kai ya yi, yana jin tamkar zuciyarsa na rikiɗewa daga zallar tsoka mai bugawa, zuwa namijin dutse. Da sauri ya bude kofar motar ya fito, tsayawa ya yi, yana karewa kansa kallo ta tinted glass ɗin motar Ya B.

Suraj kyakkyawan matashi ne dogo mai cikakkiyar siffar mazantaka,  jikinsa a gine, kirjinsa a buɗe, diri na isassun mazan da za a yiwa kallo ɗaya a kira maza. Fuskarsa mai ɗan tsayi mai dauke da  wasu shanyayyun idanu masu bala'in kyau da daukar hankali, hancinsa mai tsayi da kauri, labbansa sirara masu ɗan fadi da suka baiwa bakin wani irin shape mai kayatarwa, suman kansa mai taushi da sheki  baƙiƙirin, da ya yi mata wani irin aski irinta matasan zamani yan kwalisa masu ji da gayu, gemu da sajensa irinta matasa sababbin jini masu shekaru irin tasa. Duk da shigarsa ta yau da kullum, amma yau ta musamman ce. Sanye yake da, fitted black jeans da plain white T-shirt ya ɗora slim black jacket mai sauƙin nauyi. A ƙafarsa sneaker ne fari fes irinta gayu, hannunsa daure da wata tsaddiyar a agogo mai shegen kyau,  Baƙin glass ɗin da ya toshe idanunsa da shi,  ya ƙara masa wani irin kwarjini da mysterious presence.

Sai da ya gyara zaman glass dinsa, kafin ya juya ya tunkari get ɗin RCU cike da wani irin confidence.