GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 12

by @nusybee143

Page 12




Kai tsaye Amra ta ce"noted!

Me za'a biya ni?"hassy cikin zaƙuwa ta ce"5m, yanzu ma zan tura miki ita ta account ɗinki"murmushi Amra ta yi ta ce"kuma bayan nan kafin ki yi komai ni zan fara gaskiya,don na juma sosai ina kwaɗayinta tana raina min hankali,don dai ƙarya take ta ce ita ba yar bariki ba ce"

Hassy ta ce shikenan babu damuwa,ga ni nan zuwa,ki tabbatar da cewa komai ya hau kan saiti kafin na ƙaraso "

Amra ta jinjina kai ta ce"babu matsala uwar ɗaki"

Ƙwayar maganin da suka saba sakawa mutum a drink,su bugar da shi don biyan wata buƙata tasu,ko dai su yi masa sata,ko su aikata mugun ƙudurinsu ta ɗauko,ƙananan ƙwayoyi ne sosai,ta ɓoye su sannan ta fita zuwa ɗakin da shishar tata take 

Yadda ta bar Roxy haka ta koma ta same ta,kanta akan wayarta tana dannawa,ta yi murmushi ta ajiye mata shishar a gabanta ta kama haɗawa tana faɗin "Barka dai Madam!

Ga mutuniyar tana yi miki sannu da zuwa"Roxy ta ɗago ba tare da ta yi magana ba ta kama pipe ɗin shishar ta fara zuƙa yadda ta saba tana cigaba da danna wayarta 

Amra ta fice daga parlourn tana leƙen Roxy, tunani take yi ta inda zata fara ɗauke mata hankali 






*MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*


*MUYASSAR RESIDENT*


Shiru Hajiya Ruƙayya ta yi tana duban Arfa da mamaki bayan ta gama tsara mata ƙarya da gaskiya,mamaki ƙarara ya bayyana a fuskarta,don ya rasa yadda aka yi aka samu matsala, saboda ƙarfin aikin nasu da aka yi musu bata yi tsammani zai salamce da wuri haka ba 

Zuwa can ta ja ajiyar zuciya ta sauke,ta ce"shikenan babu matsala,da Ni yake zancen,zan ɗauki tsatstsauran mataki akan shi, wannan alƙawarina ne"

Daga nan suka fara tsare-tsaren yadda za su tafiyar da gidajensu ba tare da wata matsala ba, Arfa cikin ɓacin rai ta ce"ni abin da yake ba ni mamaki aunty me ya haɗa Abban Zuhra da son waccan kilakin?

Sun rabu fa!ya haƙura haka mana,da me na rage shi don Allah?"

Murmushi Hajiya Ruƙayya ta yi ta ce"ke ba ki san halin namiji ba,ko me kike yi masa,ko yaya kike da kyau da kulawa sai ya leƙa ya ga wata,don haka ke dai ki san yadda za kiyi ki mallake shi kawai,amma shi namiji ɗan kunama ne,ba shi da halacci"ƙugin motar Muyassar da suka ji ne ya sa suka yi shiru suna kallon ƙofar da zai shigo

Babu jumawa Muyassar ya shigo da sallama,babu wadda ta yi yunƙurin amsawa a cikinsu, bai damu ba,ya dubi Hajiya Ruƙayya, cikin girmamawa ya ce"sannu da zuwa Mamie!"

"Sannu Muyassar!ai kai ne da sannu,kai ka fi cancanta da sannu"

Shiru ya yi bai yi magana ba, Hajiya Ruƙayya ta ja tsaki ta ce"na ji abin da ka yi,ka tabbata butulu,wanda bai san halacci ba

Amma ka sani ba ka isa ka zalunci ƙanwata ba wallahi,abin haushi ma,akan wata kucaka can,ko na ce karuwa!

Ita uwar taka ita ce ta saka ka ka rinƙa kallon hotunan ta a gidan ƴar'uwata har kana cewa kana sonta wa ya je wa ya dawo?

To ka so ta ɗin!amma muddin ka auro ta wallahi sai dai ka zaɓa ita ko ƙanwata, mutumin banza kawai!"tana kai wa nan ta ja tsaki ta miƙe ta nufi hanyar fita,ta fice daga parlourn, ƙanwarta ta miƙe ta raka ta

Muyassar ya bi su da kallo kawai,a duk maganganun da Hajiya Ruƙayya ta faffaɗa babu wadda ta fi yi masa zafi da ciwo kamar kiran Shaheeda da karuwa da Hajiya Ruƙayya ta yi,karuwa!karuwa dai!!

Shaheeda bugun numfashinsa ita take kira karuwa,bata san ƙanwarta ce karuwar bane da har take da zarrar kiran wata da karuwa?ya yi ƙwafa yana girgiza kai,sai kuma ya yi murmushin takaici da ya tuna maganarta da take cewa sai dai ya zaɓa ko Arfa ko Shaheeda,shi kuwa Allah ya bayyana masa Shaheeda,ya aure ta ya ga ubanda za su yi

Wacece Arfa ma? wadda tunda ya aure ta ba zai iya ɗorar da wani abu na jin daɗin aure a tare da ita ba?

Bata san cinsa ba,bata san shanshi ba,komai sai dai ya nema da kanshi,bata girki,ko ta yi ma ba daɗin girkin yake ji ba,shara, wanke-wanke,da sauran ayyukan gida babu ruwanta da su,ya ɗauko mata ƴan aiki ba sau ɗaya ba,ba sau biyu ba,amma saboda mugun halinta da baƙin kishinta bata taɓa barinsu,a watanni kaɗan zata kore su

Dama babu batun ruwan wanka, wannan sai dai ya haɗa da kanshi,batun hira kuwa babu wata kalma mai daɗi,ga masifar zargi 

A fili ya furta "Allah sarki Shaheeda na!

Ko a ina kike Allah ya dawo min da ke lafiya,ina kewarki,na san da ke na aura da hakan ba ta kasance da ni ba"ya ƙarasa magana yana shigewa ɗakinsa, ranshi a matuƙar ɓace






*HAISAM*


A hankali motarshi take gangarawa zuwa tsukukun layin,wanda yake cike da kwatoci da shara,ga ƙananan gine-gine marasa fasali da kyan gani,don wasu ma sun fara zubewa 

Daidaita parking ɗin motarshi ya yi,yana ƙarewa wajen kallo,ya kai mintuna biyar yana kallon masu wucewa ta bakin glass ɗin motarshi,wasu yaran ma har hannu suke sakawa suna shafa motar,bai yi mamakin hakan ba,don ya san irin motarshi baƙuwa ce a irin wannan yankin 

Ya kai a ƙalla mintuna goma a cikin motar kafin ya buɗe murfin motar ya fita yana ƙarewa ko'ina kallo, tunani yake yi wa zai tambaya a wannan wajen don ya nuna masa gidan da yake nema?

Da ƙyar dai ya yi shahada ya tambayi wani matashin yaro mai tahowa"Am.....abokina...don Allah tambaya nake yi"

Yaron ya kalle shi ya ce"Allah ya sa na sani"Haisam ya ce

"Don Allah gidan malam Tajo nake nema,marigayi malam Tajo"shiru matashin ya yi na ɗan lokaci, kafin ya ce"gida dai gashi can,ka ganshi can? wanda yake kulle da kwaɗo?

To nan ne,amma yau kwana biyu sun tashi,kuma ba mu san inda suka koma ba

Amma ka tambayi maƙwabtansu,za su iya sanin inda suke"

Shiru Haisam ya yi,a ranshi yana jinjina makirci da taku irin na Roxy,wato ta san zai nemi iyalan shiyasa ta canja musu location ko?

Ya yi ɗan murmushi ya dafa kafaɗarshi ya ce"babu damuwa,na gode,sai anjuma"bai sake sauraren saurayin ba ya faɗa motarshi,ya tayar ya yi reverse ya bar unguwar, fuskarshi a ɗaure cikin ɓacin rai,amma ko me zai faru sai ya kama yarinyar nan





*SULEJA*


Roxy tana zaune riƙe da shisha tana zuƙa Kamar yadda ya zamar mata jiki Amra ta shigo ɗakin riƙe da kofunan lemo mai sanyi a hannayenta 

Tana shiga parlourn ta miƙawa Roxy ɗaya Glass cup ɗin da ta riƙo,ta janye pipe ɗin shishar gabanta tana faɗin"aikin kenan Madam!

Ko hutawa da bankawa cikinki hayaƙi ba kya yi!

Let's chill girl!"

Ba tare da Roxy ta kalle ta ba ta ce"but kin san i don't normally take alcoholic drinks "

"Madam da hankalina fa!

Ta yaya zan ba ki alcoholic, wallahi non alcoholic drink ne"ba tare da Roxy ta sake magana ba ta gyara zamanta tana kallon cup ɗin na ɗan lokaci,amra ta samu waje ta zauna tana kallonta 

Hannu Roxy ta miƙawa Amra, Amra ta zaro idanu tana faɗin "me zan ba ki?"kai tsaye Roxy ta ce"lemon hannunki za ki ba ni, I want to switch it"

Ɗan murmushi Amra ta yi tana faɗin "Roxy kenan!

Har ya zuwa ba yanzu ki yarda da ni ba?kina tunani zan iya cutar da ke?

Haba Roxy!ko don halaccin da kika yi min ai ..."Roxy ta ɗaga mata hannu fuska a ɗaure tana sake miƙa mata hannu, alamun ta ba ta kofin 

Babu musu Amra ta miƙa mata,ta ɗauki na gabanta ta miƙawa Amra, Amra ta karɓa ta fara sha, itama ta mayar da kai ga na hannunta,tana sha tana danna wayarta 

Sai da ta sha kusan rabi sannan Amra ta miƙe tana murmushi,ta dubi Roxy tana faɗin "welcome to our world Madam Roxy! Hermosa!!!"tana kai wa nan ta fice daga parlourn tana ƴar dariya 

Roxy ta ɗan bi ta da kallo ba tare da ta yi magana ba, lokaci guda kuma ta fara jin kanta yana juyawa sosai,bata iya ganin komai sai duru-duru,hakan ya sa ta saki kofin ba tare da ta sani ba,ta dafa bango tana sauke numfashi 

Amra da hassy ne suka dawo ɗakin a tare,suka tsaya a kanta suna dariya 

Amra tana dariya ta ce"dama na san yadda kike akan rashin yarda,na san yadda kike da wulaƙanci, shiyasa na yi miki haka, kofin farko lafiyayyen drink ne,kika ce sai an yi switching,gashi nan ƙwayoyin da na zuba miki sun fara aiki,yau dole na more wannan jikin naki Roxy,ba ni kadai ba,har da ƙawata ma"ta karasa faɗin haka tana ƙokarin cire riga 

Kai tsaye ta nufo Roxy wadda take zaune kanta yana juyawa,tana zuwa bata yi wata-wata ba ta cafke ƙirjin Roxy,duk da cewa tana cikin hali na maye da gushewar hankali amma sai da ta ji zafi,ta runtse idanu tana tuno mutum na karshe da ya kama mata breast,take ta ji wani ƙarfi ya maye gurbin dukkan wasu gurabu da mayen nan ya cinye, cikin tsananin zafin nama ta hankaɗe Amra sannan ta kama buga kanta a jikin gini 

Kafin wani dogon lokaci kokawa ta sarƙe tsakanin su Amra da Roxy,ita dai Roxy Allah ne yake ba ta Sa'a take kare kanta kawai,amma taron su biyun ya wuce ƙarfinta,ga abin da ta sha da ya bugar da ita ya taimaka sosai wajen guduwar karfin nata 

Allah ya ba ta Sa'a ta janyo wata ƙaramar tukunyar shayi da Amra ta siya,ta bugawa kan hassy, wadda ta fi dagewa dole sai ta raba ta da kayan jikinta 

Ai kuwa ta yi sa'a,tuni jini ya wanke kan Hassy,ya zuba ya wanke fuskarta,cikin gigita da tashin hankali Amra ta ja baya tana kallon Roxy wadda har yanzu take tangaɗi,amma ta ƙi yarda ta faɗi,sai buga kanta da bango da take yi lokaci zuwa lokaci 

Amra ta yi kukan kura ta yi kan Roxy, cikin wata iriyar fusata ta hau dukanta ta ko'ina,don ta san babu abin da zata iya yi mata,ba ma zata iya gane ta ba a cikin wannan halin,sai da ta yi mata duka sannan ta jefar da ita, ta kama jan Hassy don ficewa daga ɗakin,don ta kai ta asibiti a duba lafiyarta,ta bar Roxy a kwance tana sauke numfashi 

Abin da ya sa ta yi haka kuwa shine,ta san Roxy bai zama lallai ta iya gane cewa ita ta yi mata wannan dukan ba, sannan kuma tana samun kuɗaɗe daga wajen Hassy,ya zama dole ta yi wani abu wanda Hassy ɗin zata ji cewar ba bakinsu ɗaya a wannan wulaƙancin da Roxy ta yi musu ba,suna fita Roxy ta dafa bango,ta ciro wata ƴar ƙaramar allura daga jikinta ta yiwa kanta, sannan ta koma kan kujerar yaraf ta zauna,ta kwashi a ƙalla mintuna biyar kafin ta buɗe idanunta da suka kaɗa suka yi ja,har yanzu bata gama dawowa daidai ba, ta miƙe tsaye tana gyara kayan jikinta, sannan ta ɗauki wayarta ta fice daga gidan 






*ROCKY ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*

"Daddy please ka zo mu yi game ɗin tare ka ji Daddy!"

Muryar Amna ta katse masa hanzari, cikin shagwaɓarta da ta zamar mata jiki

"Amna just do your work alone, nima kin ga aiki nake yi,don Allah ki daina interrupting ɗina"

Shura ƙafa ta fara yi, Haisam ya lumshe idanu ya buɗe ya furzar da huci,ya ce"okay finally!

Kawo mu yi game ɗin,amma idan na yi winning ɗin ki kar ki ce za ki yi min kuka"

"Okay thanks Daddy"ta faɗa da murna, kafin ta ƙaraso wajen riƙe da tab ɗinta 

Ba'a juma da fara game ɗin ba Haisam ya cinye ta,ta kama kuka har da shura ƙafa tana faɗin sai an sake,ai bata shirya ba, Haisam yana murmushi ya ce"babu abin da za'a sake,ai ke kika ce a yi, leave me alone Madam!"ta faɗa jikinsa tana kukan shagwaɓa 

Nimra ce ta shigo sashen nashi da sallama,ya ɗaga kai yana kallonta gami da amsawa 

Nimra ƙanwar Hajiya Mariya ce,wato matar babansa,kamar yadda ta saba yau ma sanye take da kayan da suka ɗame ɗan siririn jikin nata,sai ƴar light make up da ta yi wa fuskarta,da mayafin da ta saƙala a kafaɗarta 







#Nusy_bee