Chapter 5
by @reza12
MATAR MAZA
5
Da yake a lokacin Hajiya bata da waya, itama Sadiya ɗin lokacin tafiyarta Niger ɗin ne Azima ta saya mata ƙarama wacce suke waya da ita. Nan fa aka naimi number Azima a kashe, sosai hankalin Hajiya ya tashi. Babu irin kiran da basu mata ba kullum wayarta a kashe. Gashi kuma ko a cen Niger ɗin kakar tasu ba waya ce da ita ba, kuma babu number wani da za'a iya samu aji ko tana cen ko bata je ba. Sati ɗaya da tafiyar Azima Musa yazo gidan domin a tunaninsa ai yanzu ta horu zata dawo hankalinta, sai ya kafa mata sharuɗa ya mayar da ita. A wannan zuwan ne kowa ya san da maganar sakin domin Hajiya da Sadiya ɓoyewa sukayi, daga ƴan gidan su Musa ɗin zuwa nan gidan ɗin. Gashi kuma ba'a san ina ita Azima ɗin ta tafi ba, domin Sadiya da Hajiya sunki faɗin Komai. Wasa-wasa har wata ɗaya babu Azima babu labarinta, gashi kuma su Hajiya sun shiga wani irin hali na rashin ci da sha. Domin wani lokaci sau ɗaya suke iya samu suci abinci a rana. Yan gidan kam sun samu abun faɗa cewar Azima duniya ta shiga. Bangaren Musa kuwa sosai soyayyar Azima ke ƙara hargitsa shi, mahaifiyar sa da Anty dai suna nuna masa cewar ai rabuwa da ita ɗin shine alkairi, ba gashi ta gudu ta bar uwar tata ba, nan suka ɗauke Fadila ta koma hannunsu, a cewarsu kar ma ta tashi irin halin uwarta. Har ta kai ta kawo Sadiya ta sayar da wayar hannunta sunci abinci, ga ciwon Hajiya da yanzu ya sake hauhawa sosai. A daidai lokacin ne kuma wani ɗan unguwar su mai suna Mansur yaga Sadiya ya ce yana so, a lokacin gaba ɗaya basa zuwa go ina daga Sadiya ɗin har Yusra da Ummi. Ba islamiyya babu Boko, babu aikin fari, kullum cikin tsangwamar yan uba da kishiyoyin uwa, abun da ba dad'i, sun dawo kamar wasu bare, ko almajirai a gidan, dama Azima ce ke tsaya musu. Haduwarsu da Mansur ya zamar musu wata ƙofa ta rahama daga Allah, domin da gaske yake son Sadiya, hakan yasa ya dinga ƙoƙarin ganin ya taimaka musu daidai ikonsa, duk da yake shima a lokacin ba wani sana'ar kirki yake da ita ba. Haka suka cigaba da rayuwa har wata biyu. Hajiya tayi kuka har ta gaji akan abun da Azima tayi. A wannan lokacin kuwa Musa yazo domin a mayar da auran nasu aka ce ai dole sai tana nan.
A bangaren Azima kuwa lokacin da ta isa Niger a wahale, domin sai da kuɗi ya yanke mata a hanya. Nan ta sanarwa da Kakar tasu komai da ya faru da mijin nata, da yake itama kakar ba son auran take ba, sai ta bata goyan baya akan sai ta kammala idda zata koma domin kar ma ace za'ayi mata dole ta koma gidan Musa. Kaman yadda ta tsarawa kanta zatayi hakuri har na wata biyu zuwa uku ba tare da taga Hajiya da ƴan uwanta ba, duk saboda samun mafita, daga lokacin kuma zata koma Nigeria ta fara neman na kanta, babu kuma maganar aure har a bada a rayuwarta, zata zauna da yar mahaifiyar ta da yan uwanta har karshen rayuwarsu.
Sosai ta ɗan samu natsuwa a wannan lokacin. Kuma ko sau ɗaya bata manta da lissafin ta ba, hakan yasa lokacin kammala iddar ta nayi tasa ranar komawa gida. Ta sayar da wayar hannunta tayi sallama da kakarta ta kamo hanyar Nigeria a Mota.
Azima ta iso gida lafiya, sai dai ta samu gidan nasu a rikice domin yafi da lalacewa. Lokacin da ta haɗa ido da Hajiya kawai kuka ta fashe mata da shi. Ita kanta Hajiya ɗin duk yadda take ji ɓacin rai amma ganinta ɗin yasa taji sanyi domin tabbas Azima garkuwa ce a rayuwarsu, tabbas idan babu ita suna cikin masifa a rayuwa. Azima ta karaso gaban Hajiya ta durƙusa tana kuka tana bata haƙuri akan ta yafe mata, dan Allah kar tayi mata faɗa, ita tasan mai take yi. Kafin kace me har kowa yaji labarin dawowar Azima, har shigowa ake anan kallonta kamar wata halitta dabam. Musa da yake Maroco sai gashi ya iso a washegari. Bai sauka a ko ina ba sai gidan su Azima. Yazo gashi ga Hajiya ga Azima ga kuma kawun su gaba ɗaya wanda shine ya daura musu aure. Nan Musa ya ce ya zo ne domin ya koma da ita dakinta. Amma ta miƙe tsaye ta ce ba zata koma ba, ita ta gama ma yin aure a rayuwarta gaba ɗaya. Wani daga cikin yayyenta ya daka mata tsawa harda zagi wai to dan ubanta idan an mayar da ita karta koma tunda ta raina mutane. Ko kwallonsa batayi ba, ta cigaba da faɗa musu cewar bama Musa ba, ko wani yazo ta hakura da Aure. Duk yadda aka yi da Azima ta ce ba zata sake yin aure ba, da abun ya kaita bango ma ta ce dama ita bata taɓa sonsa ba, ta zauna da shi ne kawai saboda Baba, kuma saboda yana sonta, amma tunda har ya iya sakinta to wallahi ta gama auran. Sosai ran Musa ya ɓaci, hakan yasa ya bar gidan cike da burin da kanta zata neme shi idan har taji uwar bari, sannan kuma ai zata so ganin yarta ko, zai yi amfani da Fadila ya wahalar da ita, ba dai haka ta zaba ba, muje zuwa. Koda suka dawo daki babu yadda Hajiya batayi da ita ba akan ta koma ta ce ita fa ba zata koma ba. Hajiya ta zuba mata ido tana kallonta ta rasa mai zata ce. Sai cen ta ce "Azima me yake damun ki, kina da hankali kuwa, taya zakiyi rayuwa babu aure, ko dai a kwai matsala ne?" Ta faɗa tana jin tausayin yar tata. Azima ta ce "Hajiya, ko yanzu nayi aure, kuma na haifa, dan haka alhamdu lila, kawai ki cigaba da min addu'a akan rayuwar da zan fara ta neman na kai, wannan shine kawai abun da nake bukata a tare da ke. Wannan maganar tasa Hajiya yin shiru.
Nan fa aka fara wata rayuwa ta tsananin wahala da ƙunci. Ga baƙaƙen maganganu a wajen ƴan gida, ga rashin zuwa school, ga rashin abinci da sutura. Duk da Mansur na taimaka musu amma shima watarana bashi da wanda zai ci ma bare ya basu. Rayuwa tayi tsanani har Azima ta fara tunanin bin wata hanya domin ganin ta ciyar da ƴan uwanta, babu mai taimako sai Allah, duk abun da tayi niyyar farawa babu jari, ga zuciyoyin ta da suke tai mata huɗubar baƙar hanya, ga ciwon Hajiya da ya sake cin jikinta. Sannan bangare ɗaya ga zawarawa ta ko ta ina da suke kawo mata hari, masu hankali da kuma masu son jikinta, sai dai ita bata jin yin auran ne gaba ɗaya. A haka ta shekara a gida babu wani abun ci gaba sai ma komawa baya, haka take fita ta zage kamar namiji duk da ƙananan shekarunta, tana nemawa kanta mafita. Izuwa lokacin Hajiya bata da magana sai dai tace ta fitar da Miji kawai tayi aure shine rufin asirinta, sai kawai ta yi murmushi domin ta lura Hajiya ba zata gane ba. Ganin dai abun nata kamar akwai rashin hankali a ciki yasa Hajiya ta tashi mata da gaske, domin yi tai kamar zata mata duka Kafin ta fara fita. Sai dai fara fitan nata ne ya sake sauya mata rayuwa, sannan itama idanunta suka sake budewa akan wasu abubuwa da bata san da su ba.
Ranar da ta fara tsayawa da wani mutum mai mata ɗaya, bayan sun gama hira taga ya ɗauki kuɗi masu yawa ya bata. Farko ma taji tsoro domin batayi tunanin haka ba, kuma ba wai kuɗin ne sukai mata yawa ba, domin lokacin da take gidan Musa ta riƙe fiye da su sosai, kawai tayi mamakin yadda daga zuwa hira sai ɗaya kawai zai bata kuɗi haka ne. Tun daga lokacin kuma sabuwar duniya ta buɗewa Azima, domin a rana sai tayi zawarawa huɗu, kuma babu shegen da ya isa yazo ya koma hannu rabbana, ko baka bata bama zata tuna maka. Cikin kasa da wata ɗaya rayuwar su ta sake sauyawa, nan ta mayar da kannenta makaranta, haka zata zaɓi ɗaya daga cikin zawaran nata ya sayo musu kayan abinci, kuma mutum cikin murna zai kawo. Har wannan lokacin kuma bata ƙara haduwa da Fadila yarta ba, domin tana gurin yayar Musa Anty. Ita taje da nufin ganinta ace tana makaranta. Da yake a lokacin bata da wani iko, sai bata matsa ba, yanzu kuwa da take jin ta fara riƙe kuɗi kuma a cikin samarin ta a kwai masu daurin mazaunai a ƙasar sai ta fara kokarin haduwa da ita. Sosai yanzu take daukar wanka, wanda bai santaba ba zai taɓa cewa tayi aure harda ƴa ba. Kuma har lokacin Musa bai daina zaman jiran ta dawo gareshi ba. Ta tsaya ta lura da cewar wannan wata dama ce Allah ya bata da zata ci kuɗin samari da zawarawa dan ubansu, dole ne ma ta fara gayu da kuma gyara.
Yamma kamar kullum ta ci uban kwaliyar atamfa doguwar riga, ta riƙo hannun Ummi zata kawota bakin titi ta tare mata mashin da zai kaita makaranta. Tana tsaye a bakin titi, minti kusan uku da yake safiya ce bata ga mai mashin ba, ta ɗan gara gaba kasancewar akwai jakshon a gaba. Ta gefen ido taga wata fallaleyar Mota fara tana yin ribas tana dawowa gurin da take. Haka ta kawar da kai taci gaba da tafiya har ta samu mai mashin ta ɗora Ummi, ta bata Naira ɗari kudin break. Ta na juyowa taga motar daf da ita kamar za'a taka ta da ita. Tayi kamar bata kula da motar Ba tayi gaba . Haka suka ta binta a baya a hankali. Hakan yasa ta tsaya sai taga suma sun tsaya. Ta samu gefen hanya ta tsaya tana jira su wuce amma dai ta ga sun sake tsayawa. Hakan yasa taci gaba da tafiya, nan ma taga suna binta. Hakan yasa ta sake tsayawa tajuyo ta nufo cikin motar rannan nata a ɓace, yan zuciyar sun zo kusa. Ta na zuwa ta daki glas ɗin motar tana faɗin "Kai Malam meye haka ne, ko kayi hauka ne, baka ga na baka hanya bane"? Ta faɗa a fusace tana kuma kallon baƙar galas ɗin motar da bata iya ganin na ciki. Shi kuwa sarai ita yake kallo daga sama har ƙasa, Tashi ɗaya yarinyar ta wawashe masa sauran imaninsa tun daga kallo ɗaya. Tafiyarta, jikinta, da yadda take magana, harda wannan haɗe ran duk sun sake kiɗima shi. A hankali ya sauke glass ɗin yana sakar mata murmushin sa mai girma a gurin al'umma. Lokaci ɗaya maganar da tayi niyya furtawa ta koma mata ciki harda wani haɗiya tayi kamar wacce tayi gamo. Kallon sa tayi a karo na dayawa gabanta na faɗuwa. Ya buɗe motar ya fito yana ƙara maƙureta da mamakin da ya kusa fasa mata ƙirji. Hannu tasa ta murtsike idanunta da kyau domin tabbatar da abun da take gani. Maganar da yayi ce ta sake dawowa da ita tuniyarta. Bata ma ji mai yace ba sai dai taga yana miƙa mata hannu alamar su gaisa. Wallahi bata san lokacin da murmushi ya kufce mata ba tsabar mamaki da kallon ikon Allah.
Ya sake faɗin "Sunana Alhaji Audu, ni ba ƙaramin mutum bane, na samu labarin Komai akan ki, kinyi aure harda yarinya ɗaya, ni kuma ina da mata biyu, yara sha uku, maganar aure ne ya kawo ni gurinki ba wasa ba, wannan katina ne, keje kiyi shawara, duk abun da kika yanke ki sanar dani" Ya ƙarasa yana miƙa mata katin sa. Sai a lokacin ma ta gane ashe tun ɗazun ma kati yake miƙe mata tana ce ko gaisawa zasuyi. Ta sake kallonsa da kyau domin ko rantsuwa tayi ba zata yi kaffara ba zai iya Girman Baba, abun da ya bata dariya kuma shine... furfura ce cike dam a kansa da gemunsa (salamu alaikum ƙabari kenan) amma yake batun wai ita zai aura. Tana tsaye tana dariya ya dauko daurin Uku na dubu-dubu Ya miƙa mata. Ai da sauri ta amshe tana sake kallonsa. Yayi mata sai an jima akan sai ya jita ya shige mota, ya tafi. Tabi motar da kallo yadda take tafiya da baya har ta fita. Ai kuwa ta buɗe gyalan da ke kafadarta ta zuba kuɗin ta tattare doguwar rigar tayi gida da gudun tsiya kamar wata ɓarauniya.
Dama tun da ta fara tsayawa da zawarawa to Sadiya ce abokiyar shawarar ta, ganin bata nan yasa ta boye kuɗin har sai ta dawo daga school domin susan yadda zasuyi da wannan baba tsohon. Dan ya kamata ko kuɗin sa suci Kafin su saita masa hanya. Koda Sadiya ta dawo taga kuɗin sai da ta buɗe baki itama jin wai mutum ɗaya ne ya bayar. Suka yanke shawarar bayan kwana uku su kira shi da yake yanzu tana da waya. Haka suka shiga kasuwa da wannan kuɗin suka sayo duk abun da suke bukata. Ita dai Hajiya kullum gurinta Allah ya kawo mata miji na gari tayi Aure. A cikin kuɗin suka bawa Mansur dubu talatin akan ya kara a kasuwancinsa saboda ba zasu taɓa mantawa da shi ba, yayi musu halacci a rayuwa, amma yaƙi amsa, nan take kuwa Azima ta ce ta bashi Sadiya har a bada, duk lokacin da ya shirya kawai yayi magana ya turo iyayen sa. Suka yi dariya duk su ukun ya ce "Kai Anty Azima sai kace kece mai aurar da ita.
Bayan kwana uku suka kira Alhaji Audu. Ai kuwa washegari sai gashi a ƙofar gidan su. Yace mata mahaifinta zai gani domin shi aure ne ya kawo shi ba wasa ba. Sosai taji tsoro domin a lokacin tana da Samari da zawarawa sun kai goma, kowa da alƙawarin aure. Nan ta faɗa masa cewar ita ba yanzu zatayi aure ba, so take sai ta kammala karatu, domin tana so ta cigaba da karatu. Ta faɗa masa haka domin dai ya hakura domin ta fahimci ba zasu shirya da shi ba, dan bata son maganar aure kusa, ta ɗaura ɗamarar cin kuɗin Rijalu kafin ta san mai zatayi. Ya ce mata wannan ba damuwa bane, koda karatun ne sai tayi a gidan sa ya yarda. Ta zaro ido ta ce ita da bata son haɗa aure da karatu ne shi yasa. Ya ce mata to yanzu yaya take so ayi. A tsorace ta ce masa, dama dai zata gama karatun ne da sai ayi auran. Ya yi murmushi na manya ya ce mata karatun na shekara nawa ne ta ce masa shekara huɗu. Cike da madarar mamaki taji ya ce "Ba damuwa, shi zai ɗauki nauyin karatun nata, daga farko har ta gama, amma da sharadin tana gamawa zata aure shi. Sosai Azima ta faɗa kokin zumar rudani da mamaki da kuma kokwanto. Kanta ya cika ta rasa wani tunani zatayi, nauyin karatun jami'a fa, kuma har sai shekara huɗu. Babu wata-wata tace ta yarda. Bai bar ƙofar gidan ba sai da ya shigo suka gaisa da Hajiya ya sake faɗa mata yadda sukayi, ita kanta Hajiya ta jinjinawa daga shi har ita ɗin wannan haukan, tama rasa mai zata ce, to shi da ita waye za'a cewa mara hankali, amma dai tayi godiya. Haka ya ajiye wa Hajiya rafa ɗaya yace ta sayi gora. Koda Azima ta rako shi waje, ya kawo mata siyayya sannan ya haɗa mata da kuɗi yauma guda Uku. A cikin kasa da sati ɗaya yayi mata komai na irin makarantar da take so da yake dan siyasa ne, sannan ya ware mata Mota guda da dreba wanda zai dinga kaita school kullum. Sannan duk sati ɗaya yana zuwa su gaisa, idan zai zo zai kawo mata tsaraba da kuma kuɗi. Sosai fa hidimar tasa take bawa Kowa tsoro a gidan nasu. Wannan sauyin rayuwar ne ya sake fito da salin kyawun Azima. Tana shiga sutura mai tsada, ga yanzu kanta ya sake budewa saboda kawaye da tayi a makaanta. Gefe guda ga Samari da zawarawa da suke karuwa, nan fa ta fara saka samari a kwali, komai take so sai ta zaɓi wanda zai kawo mata. Nan sirikanta kuma ƴan uwanta suka fara mata fassara akan bin Maza take, hatta Yan gidansu abun da suke ce mata kenan. Ita kuwa ada ma da bata da komai bata raga wa kowa bare yanzu. Tsaf zata zage su buɗa da mace har yanzu idan tayi a gabanta. Cikin kasa da shekara da haɗuwar ta da Alhaji Audu ta mallaki abubuwa da yawa, ciki kuwa harda dawo da kasuwancinta na da wanda take yi daga Maroco zuwa Nigeria. Saboda shi da kansa yayi mata maganar sana'a tace ai da tana yi jari ne ya ƙare. Take kuwa ya bata taci gaba da nata kasuwar. Yanzu harda abubuwan da bata sayowa ma ta koma kawowa. Bayan motar da ya bata wacce ake kaita school, itama ta mallaki tata, ga ƙaton shago na kaya ga kuma kuɗi a account, ga samari, sannan yanzu tana zuwa har gida taga Fadila, sai dai bata tafiya da ita, sai dai kawai taje ta ganta su gaisa . A wannan lokacin ne Musa ya sake dawowa wannan karan da roko, amma ta nuna masa tayi masa nisa wallahi. A lokacin da ta cika shekaru biyu a school, kuma tana samun nasara a karatu sosai saboda tana mayar da hankali domin dai tasan karatun shine gatanta. Daga lokacin Alhaji ya fara Mata maganar aure. Abun da bai sani ba kuwa, gaba ɗaya babu maganar auransa a lissafinta, sai dai yadda zata rabu da shi ɗin ne bata sani ba, to amma ko dai ta aure shi ta bashi sati ɗaya sai ta tasar masa da hankali ya sake ta. Sosai dai take ta tunani domin dai dole fa tasan sai ta auri wannan mutumin ko bata so, kuma ita ba zata iya auran tsoho ba, kuma ma ai sai Musa yayi mata dariya yace ta auri tsoho, to ma ina zata kai shi, idan ma ta kalli kanta a yanzu sai taga ina wallahi tafi ƙarfin sa. Sosai a wannan tsakanin ta shiga tunanin mafita. Kaiwa ta yanke ta aure shi, sati ɗaya kawai ta fito domin dai abun da yayi mata ba zata iya kallon idonsa tace ba zata aure da ba...📝
Hahaha auran sati ɗaya dai.