PAGE 24
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 024.*
Abba yana zaune a falonsa yana amsa waya, Umma ta fara shigowa da sallama, kafin ta zauna Mama ta shigo fuskarta a ɗaure ta nemi waje ta zauna tana cin magani.
Abba sai da ya gama wayar sannan ya kallesu ya ce, "na kira ku ne dan na ji dalilin ku na ƙin zuwa asibiti duba Rehaan. Dukkanku kun san guba ya sha, da ace akwai ƙarar kwana da yanzu ya jima da barin duniya. Yau kwanansa biyu a asibiti, amma ace babu wacce ta je ta ga ya jikinsa yake. Ƙaramar cikin ku ta je, amma ku da ku ke manya ba ku je ba. Meyasa?."
Umma ta ɗan kawar da kai ta ce, "a yi haƙuri, bana jin daɗi ne kawai. Amma yanzu na shirya zan je na dawo."
Abba ya ce, "sai yanzu, sai da dare ya yi sannan za ki je? Tun safe me ki ke yi da baza ki je ki duba sa ba?."
Ta yi shiru bata ce komai ba. Abba ya kalli Mama da take ɗaure fuska ya ce, "ke kuma fa?."
Mama ranta ya ɓaci matuƙa, ta tsani ya dinga yi mata irin haka a gaban kishiyoyinta, bata so a dinga yi mata irin wannan wulaƙancin a gaban na ƙasa da ita. Ai ko faɗan ne sai ya yi mata nata personal tunda itace gaba dasu, ta wuce ya haɗa ta waje ɗaya da ɗaya daga cikin matansa ya yi musu faɗa tare, ta jima da wuce wajan amma ba ya fahimta.
Mama ta ce, "babu komai" ta faɗa a cushe cikin ɓacin rai.
Ya girgiza kai ya ce, "kawai saboda bakwa son mahaifiyarsa sai ƙiyayya ta shafesa?. Ban ga amfanin keeping malice ɗin nan da ku ke yi da Rehaan ba, ban ga amfanin wannan ɗaure ɗauren fuskar da ku ke yi a kansa ba. Ko bakwa so Rehaan jinina ne kamar ƴaƴanku, abinda ku ka saka a zuciyarku, kuke wani tunani a kansa wannan duk ku ku ka sani, abinda ya shafe ku ne, ku ya dama tunda har ku ka ɗorawa zuciyarku. Wallahi inda ɗaya daga cikin ƴaƴanku ne aka kwantar a asibiti, na tabbatar kullum Nadira sai ta je ta dubasa, saboda ita tana zaune daku cikin ruwan sanyi ba kamar ku ba."
Umma ta gaji da maganar, jin sai yabon ƴar gwal yake yi ta ce, "ai na ce zan je na duba sa. In ka yi min izini na tashi in je na shirya." Da hannu ya nuna mata ƙofa ta je, ta miƙe ta fita.
Mama ta kalle sa ta ce, "Abba."
Ya ɗaga kai ya kalle ta ta ce, "Gaskiya ban jin daɗin abinda ka ke yi min. Bana son abinda ka ke yi min a gaban kishiyoyina ko kaɗan."
Bai tambaya ba ta ce, "ta ya zaka dinga zaunar dani kana yi min faɗa a kan ɗaya daga cikinsu? In faɗan ne ban wuce shi wajenka ba, amma me zai hana baza ka kira ni ni kaɗai ka yi min ba? Meyasa zaka dinga haɗa ni dasu kamar wasu sa'annina, kana mantawa da matsayina ne?."
Abba ya ce, "tare ku ka yi laifin ai, dan an yi muku faɗa a tare ai ba komai bane."
"Komai ne wallahi, zubar min da mutunci ka ke yi a gaban na ƙasa dani. Ai na wuce a zaunar dani a cikinsu ayi min faɗa, ni sai dai a yi min nawa personal ba a haɗa ni dasu ba. Ai inda kara ni zaka yiwa faɗan, ni kuma sai in je in yi musu a madadinka. Haka kwanaki ka zauna dani da ƙaramar yarinyar nan amaryarka, yarinyar da na haife ta, amma ka haɗa ni da ita ka zaunar wai kana yi mana faɗa. Raini ka ke jawo min wallahi."
Abba ya murmusa yana girgiza kai ya ce, "ke kuma gaki shugabar masu son girma ko?."
Ta kalle sa ta ce, "ai girman ya kama ni ne, dukkansu a bayana suka tare, babu wacce ta riga ni aurenka, to akan me zaka dinga yi min haka?."
Abba ya ɗan taɓe baki ya ce, "ni ba wannan na kira ki na ji ba, ki je ki duba Rehaan kawai."
Mama ta ce, "ai zan je. Amma don Allah ka daina yi min haka, uwargida ce ni fa, uwar gida mai capacity."
Sai ta bawa Abba dariya, ya yi murmushi ya ce, "an gaishe ki, uwar gida. Ki je ki dawo zamu yi maganar."
Mama ta ce, "yauwa. Maganar kayan abincin nan da muka yi da kai, na bayar fa, kar ka tambaya ace babu."
"Ikon Allah! Dan na ce zan yi tunani har kin bayar?."
"Kuma kamar kaine ka bayar ba, ko na yi laifi ne?."
Abba ya ce, "Ya zan yi miki tunda kin bayar? Shikenan kawai."
Ta yi murmushi ta tashi ta fita, tana jin daɗin yadda take da zuciyar Abba har lokacin a hannunta, soyayyar ƙuruciya bata gushe ba tana nan, dan ko baƙo ne yazo ya kwana biyu sai ya san itace take mulki a cikin gidan. Haka take son yaranrta su kasance, ko tsuntsuwa ce ta zo wucewa ta saman gidan, tana so ta zama shaidar ƴaƴanta sune suke juya gidan. Ita a son ranta, Abban ma ya talauce, ya zama ƴaƴanta ne suke siyan komai a gidan. Hakan shine girma a gare ta.
Da safe Islaha da wuri ta tashi ta yi wanka ta shirya don komawa asibiti. Tana tsaye a kitchen sai ta kira Mama a waya, Mama ta ɗauka bayan sun gaisa ta ce, "Mama akwai abinda za a kawo miki?."
Mama ta ce, "ki taho min da kaya Islaha. Hanan ta dawo gida kuwa?."
Islaha ta ce, "eh ta dawo Mama."
"ƙarfe nawa ta dawo?."
"Wallahi ban sani ba, na ganta yanzu dana tashi
"shikenan, ki kawo min kayan sakawa."
"Abinci fa?."
"An bani abincin karyawa a nan Islaha, kaya kawai nake so."
Islaha ta amsa tana kashe wayar ta dafa tea ta sha ta fito falo ta shiga ɗakinsu dan ɗaya ta ɗauko mata kayan Mama.
Islaha ta tarar dukkansu basu tashi ba, ta yi ajiyar zuciya dan ba shiga ɗakin Mama take yi sosai ba, bata son ta shiga aga babu wani abun ace itace.
Daƙyar ta daure ta shiga, ta buɗe wajan kayan Mama ta ɗaukar mata doguwar riga da hijjab ta fito daga ɗakin. A daidai lokacin wayarta ta ɗauki ƙara, a tunaninta Sadik ne sai ta ga Zainab ce.
Ta ɗauka ta saka a kunne ta ce, "Zainab ya aka yi?."
"Adda jiya naje office ɗin Mama na ji tana waya tana cewa kawai a yi maganinki, in ba haka za ki zamar musu matsala. Adda ki dage da addu'a, inda dama ki daina bibiyarsu kar su cutar mana dake, don Allah."
"Yaushe ki ka ji suna wannan maganar?."
"Jiya ne."
"Ita da waye?."
"Waya take yi, ban sani ba. Tun jiyan nake kiran ki wayar ki a kashe."
"Shikenan, ki kwnatar da hankalin ki, duk abinda ya sake faruwa ki faɗa min. In kuma kin samu dama, in kin ji ana maganar ki shiga number ta ta whatsapp, ki danna voicenote ki tura min."
"To Adda zan yi."
"Amma fa in baza ki iya ba kar ki yi, kawai ki ji sai ki faɗa min."
Zainab ta ce, "Adda ga Fadwa nan, zan kashe" ta faɗa tana kashe wayar.
Islaha ta ɗan yi shiru ta ce, "har abin ya kai haka kenan? Lallai akwai aiki a gabana, dole a san abinda za a yi."
Kiran Saheer ne yake shigowa ta wahatsapp, ta yi murmushi ta ɗauka ta ce, "Hammana."
Daga can ɓangaren ya ce, "Matar Hamma."
Ta yi murmushi ta ce, "Ina ta jiran kiran."
"Ba wani nan, bayan ko message ɗin ki ban gami ba."
"Wallahi abubuwa ne suka yi yawa Hamma, amma kana raina."
"Meye suka yi miki yawan?."
"Aiki ne. Ka je lafiya?."
"Lafiya lau matar Hamma, kina nan lafiya?."
"Lafiya lau Hammana."
"Mama bata tashi ba? Na kira bata ɗauka ba."
"Ina jin bacci take yi."
"Baffa ma bai ɗauka ba. Kar na tare ki da surutu, ki je ki ci abinci." Ta amsa dan itama so take ta kashe tana jin kiran Sadik yana zuwa.
Tana kashewa ta kirasa, Sadik yake sanar da ita yana ƙofar gida yana jiranta.
Bata tsaya jiran komai ba, ta yafa chatelity veil a kanta, sannan ta ɗauko kayan Mama ta fito.
Sai da ta shiga motar ta kalle sa ta ce, "ina kwana Hamma Sadik."
Ya yi murmushi ya ce, "an tashi lafiya matar Hamma?."
"Lafiya lau. Ya gajiya?."
"Alhamdu lillah Islaha. Ke kaɗai ce?."
"uhum, bacci suke yi."
Ya ja motar suka fara tafiya ta ce, "ɗazu kana kirana muna waya da Hamma ne."
Ya yi dariya ya ce, "tunda na ji call waiting na san shine. Amma baki faɗa masa ba ko?."
"Ban faɗa masa ba, yana ta tambayar ina Baffa kuma."
"Za a faɗa masa, sai mun ji abinda yake damunsa tukunna."
Bata ce komai ba ta sauke numfashi suka cigaba da tafiya har suka ƙaraso asibitin. Suna tsayawa ta saka facemask dan ac reception ɗin nan zata iya cutar da ita.
Sadik ya kalle ta ganin ta gama sakawa ya ce, "anya ba asthama ce dake ba, Matar Hamma?."
"To Hamma Sadik an yi gwaji ance babu, babu irin gwajin da ba a yi min ba amma ance ba ita bace. Amma duk wani alamunta ya bayyana a gare ni."
"Gaskiya ya kwmata a faɗaɗa bincike. Dan ni nasan itace kawai." Ta yi murmushi ta fita suka shiga asibitin.A nan suka tarar da Mama a zaune, suka ƙarasa suka gaishe ta amsa.
Mama ta kalli Islaha ta ce, "ina Labiba ko Hanan?."
Islaha ta ce, "bacci suke yi dana fito." Mama ta girgiza kai ta ce, "bacci!" Ta maimaita cike da mamaki. Mahaifinsu yana asibiti cikin wannan yanayin amma su bacci ma suke yi."
Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Mama ta ce, "ai shikenan, mu je wajan likitan ko?."
Sadik ya ce, "Ki fara shiryawar Mama." Mama ta ce, "mu je dai Sadik" ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Islaha dai kallon Mama take yi tana mamakinta, ashe duk kafsa faɗan da suke yi da Baffa tana son kayanta, ita wallahi bata ɗauka zata damu ba, ta ɗauka murna zata yi dan Baffa babu lafiya zata samu damar yin abinda take so. Amma sai ta ga akasin haka, sai ta ga ta fi ƴaƴansa damuwa, kana ganinta kasan ta damu da rashin lafiyarsa sosai.
Islaha ce ta yi knocking ƙofar, ya amsa daga ciki suja shiga da sallama. Dr ya amsa yana kallon su ya ce, "Mustapha Maddibo ko?."
Islaha ta ce, "mu ne."
Ya nuna musu wajan zama ya ce, "bismillah ku zauna."
Sai da suka zauna sannan ya ce, "kamar yadda na faɗa muku jiya mun yi duk gwaje gwajen da ya kamata. Kuma alhamdu lillah mun kamo bakin zaren."
Dr ya ce, "ya taɓa yin ciwon ƙoda ne ko sau ɗaya?."
Mama ta ce, "eh ya taɓa yi, amma an fi shekera goma gaskiya."
Ya girgiza kai ya ce, "kuma ya san yana da cutar hawan jini da sugar?." Mama ta girgiza kai ta ce, "hawan jini dai an taɓa faɗa masa yana dashi, amma sikari gaskiya bai sani ba."
"Yana shan maganin hawan jinin?."
"Gaskiya ba ya sha."
"Kuma yana cin gishiri, kanwa, baya samun isashshen bacci?."
Mama ta girgiza kai ta ce, "gaskiya yana shan kanwa sosai, dan kullum sai an dama masa kunun kanwa."
Dr ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ciwon ƙoda ne ya kama shi mai ƙarfi Mama, dan har ya kai mataki na ƙarshe, mataki na biyar a cikin matakan ciwon. Wanda mu ke kira end stage kidney disease (Eskd)."
Islaha ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma Dr ya daɗe da yin ciwon fa."
Dr ya kalle ta ya ce, "Ko da bai taɓa yi ba, hawan jini da sukarin da suka yi masa yawa zasu iya taɓa masa ƙoda. Ƙoda bata kamuwa da ciwo haka kawai dole sai da dalili. Ciwon ya bayyana a yanayin da mu ke yiwa take da silent disease, ma'ana yana jin alamomin ciwon amma bai ɗauki mataki, su kuma ciwukan da suka haifar masa da kamuwar ciwon ƙodar bai san dasu ba, balle ya sha magani ko ya dinga dubawa akai akai."
"Ko yawan shan magani ba tare da umarnin likita ba yana lalata ƙoda, kamar haka kawai ka dinga shan maganin ciwon kai, ko na kashe raɗaɗi ba tare da dalili ba, ko magangunan hausa wanda basu da dose, haka kawai mutum ya dinga zubawa cikinsa. Yawanci alamun ciwon ƙoda yana bayyana ne in ya yi nisa sosai."
"Ba haka kawai ake kamuwa da ciwon ba, ana jin alamomin ta sai dai in an raina alamomin, dan ba wani abu bane mai ƙarfi da in mutum ya ji zai ce ai wannan babban ciwo bane. Ƙananun alamomin ta ana gane su ta raguwar fitsari, yawan yin fitsarin mutum ya ragu, kamar in yana yin fitsari sau goma a rana, sai ya koma yi sau uku wannan ɗaya ne daga cikin alamominta. Kun san ƙoda itace take tace fitsari, shiyasa ba a son yawan riƙe fitsari da mutane suke yi."
"Ka ji mutum yana cewa ai ni sai in yini ban yi fisari ba, hakan ba burgewa ba ce ba, a ƙalla ana so mutum ya yi fitsari duk bayan awa uku. Ya zama a rana, mutum yana fitsari sau huɗu zuwa takwas. Dan ruwan da ka sha mara kyau ƙoda take tacewa kai kuma fitar dashi. Rag…