RAGAYAR DUTSE

PAGE 25

by @nanahaleema11

 *RAGAYAR DUTSE.*


                ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 025.*


Daada tun tana jiran dawowar Islaha har ta gaji, mai kula da ita ta ƙaraso suka tafi ɗakin da Rehaan yake. 


Yana zaune shi da Mamy da Riyya Daada ta shiga da sallama, suka amsa ta ƙarasa tana ƙare masa kallo ganinsa dagashi sai three quater da ƙaramar riga, gabaɗaya guiwarsa zuwa ƙasa a bayyane yake, sai riga mai gajeren hannu, sai hular sanyi a kansa, ya harɗe hannu a ƙirji yana kaɗa ƙafa a hankali.


Ya buɗe baki zai gaishe ta Daada ta ce, "kai kuma meye haka? Ya zaka yi tsirara a gaban al'ummar annabi?." 


Ya kalli kansa jin wai ya yi tsirara, ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba ta zauna ta ce, "yanzu da na taho da wacce zaka aura haka zata ganka? Kai ko kunya baka ji, kalle ka fa."


Maimakon ya bata amsa sai ya ce, "sannu da zuwa, ina kwana." 


Daada ta ce, "lafiya lau. Yanzu mu ka haɗu da yarinyar a masallaci, har ta faɗa min sunan unguwarsu. Na ce ta zo mu je ta ganka amma ta gudu." Shi dai bai ce komai ba, suka gaisa da Mamy da Riyya. 


Riyya ta ce, "Daada ya sunanta?."


"Sunan nata ne wahalar faɗa yake yi min, amma sunanta ishlaya." 


Riyya ta yi dariya ta ce, "Ishlaya kuma? Wanne irin sunan ne wannan?." 


Daada ta taɓe baki ta ce, "ke ni ban iya faɗa ba, zan zo na san abinda za a yi a kai. Tunda na san sunan babanta da unguwarsu magana ta ƙare."


Shi dai kanzil bai ce mata ba yana zaune ya lumshe ido ya jinginar da kai yana tunani kala-kala a zuciyarsa. 


Miƙewa tsaye ya yi ya saka takalmi zai fita, Mamy ta bishi da kallo ta ce, "ina zaka je kuma?." 


Kafin ya bata amsa Daada ta ce, "to meye naki na tambaya? Yaro bazai je ya ɗan motsa jiki ya taka ƙafarsa ba, daga ya tashi sai a fara tambayarsa, ke lallai ga mai ɗa ko?. Sam baku da kunya, baku san kara ba. Ɗan farin ki ke yiwa wannan rawar kan, mtswww me ake yi da jinin da ba na fulani ba?."


Daada ta kalli Rehaan ta ce, "jeka inda zaka je. Amma ka je ka saka doguwar riga sai ka fita, haramun ne fita a haka." Ray ya koma ya zauna yana haɗe rai, fuska babu walwala  ya ce, "na fasa fitar, tunda bata so."


Daada ta saki baki tana kallonsa ta ce, "Saboda uwarka bata so dole ka koma ka zauna, dole ka nuna min itace ta haife ka bani ba. Amma ko ka ƙi ko kaso ni na haifi AbdulAziz, ina da iko da kai fiye sa kowa." Shi dai bai kula ta ba, ya rufe ido ya buɗe,  ya ɗauki wayarsa yana dunnawa dan yana buƙatar tafiya Jedda a cikin satin da za a shiga.


     Islaha kuwa tuni ta manta da wata Daada, tunda ta fita ta shigo da Saleem da Safeera, suka shiga suka duba Baffa daga nan suka zauna ana tattaunawa akan halin da ake ciki.


Safeera ta ce, "a.c wajan nan bata damun ki? Na san ki bakya son sanyi." 


Islaha ta gyara facemask ta ce, "ina manage ne kawai, amma a takura nake wallahi. Jiya ma attack na samu."


Saleem ya ce, "Islaha ni fa ina zargin Asthama ce dake." 


Safeera ta ce, "itace ma wallahi, duk wani alamominta ya gama bayyana a tare da ita." 


Islaha ta ce, "to ya zan yi? An yi gwaje-gwaje masu yawa an tabbatar da babu." 


Safeera ta ce, "kawai ki zo asibitin nan, dan ance indai ka zo asibitin nan kamar ka je asibitin turai ne. Duk wani ciwo da yakr maƙale a jikinka zai bayyana zasu gansa."


Saleem ya ce, "yanzu ya maganar Baffa?." 


Islaha ta ce, "ku faɗawa Chairman gobe bazan samu damar zuwa ba gaskiya, zan je bank zan nemi loan in zasu bani. Dashe za a yiwa Baffa, kuma ana zancen miliyan sha biyu." 


Safeera da mamakita ce, "miliyan sha biyun za ki ara!?."


"Ta ya zasu bani miliyan sha biyu ni da ba babbar ma'aikataciya ba? Zan dai nemi yadda zasu bani kawai." 


Saleem ya ce, "ke da ba ma'aikaciyar gwamnati ba ta ya zasu ɗauki loan su ba ki? A wanne kuɗi zasu dinga cirewa?."


Islaha ta sauke numfashi tana ɗan runtse ido, dan ciwon mara take yi kaɗan-kaɗan. A sanyaye ta ce, "bana ce ba Hamma Saleem, kawai a jikima nake jin zan warware matsalar nan in sha Allah." 


Safeera ta ce, "kar ki yi abinda zaki cutar da kanki, ki yi iya ƙoƙarinki, kar ki yi abinda zai lalata miki aiki ko sunanki. Ki bi komai a sannu, na sanki da gaggawa. Wani abun sai kin yi ki ke danasani mara amfani."


Ta ɗan runtse ido tana sake ƙanƙame jikinta, Safeera ta ce, "kema dai kina da matsala, maimakon ki saka hijjab sai ki ɗauko wannan mayafin ki yafa? Gashi nan sai ƙanƙame jiki ki ke yi saboda sanyi." 


Islaha ta ce, "yanzu meye abin yi?." 


Safeera ta ce, "Hamman ki ya sani?."


"Sadik ya ce zai faɗa masa."


"Gaskiya Sadik aboki ne na gari wallahi, ya tsaya a kan harkokin abokinsa kamar yana wajan."


"Gaskiya yana da ƙoƙari wallahi."


Safeera ta ce, "ni kuɗin nake ganin sun yi yawa, bayan na aiki ga na ƙananun abubuwa da zasu zo. Abinda zasu karɓa a hannunku Allah ne ya sani." 



Islaha ta ce, "nan ne maganin damuwarmu Safeera, babu wanda ya faɗi wani abu mara kyau akan asibitin nan. Amma ni kaina na san mun kawo kan mu gidan mutuwa, dan iya kuɗin da aka cire na file kuɗine masu yawa, balle yau ya kwana biyu, kuma ba a karɓi komai a hannunmu ba. Haka zamu daure ko kadara ce za a siyar don a ceto lafiyar Baffa."


Saleem ya ce, "gaskiya Baffa ya cancanci ayi masa komai Islaha, amma ya kamata a dinga tunani. Wallahi in ba a biya kuɗin asibitin nan ba tsaf zasu kama mutum su kulle. Asibiti ne babba fa, kuma asibitin babban mutum ne."


Islaha ta ce, "asbitin waye wai?." 


Saleem ya ce, "Mr Ray, wanda mu ka je nema har hotel. Wannan asibitin mallakinsa ne." 


Islaha ta wara ido ta ce, "da gaske?." 


Safeera ta ce, "ke da baki sani ba?."


"Wallahi ban sani ba, kuma naga sunan mace ne, ba Ray kamar yadda aka saba gani a abubuwansa ba."


Saleem ya ce, "ance sunan Mamansa ya saka. Wannan asibitin shine asibiti na farko mai tsarin turawa da aka fara yi a kaf Nigera, shiyasa ko yaushe a cike yake da ƴan gayu da masu kuɗi. Duk iyayin ƴan Abuja, nan suke shigowa ana duba su, dan asibitin ba dai kyau da tsari ba. Komai irin na turawa, hatta mai kula da mara lafiya nurses ne, masu jinya akwai ɗaki na musamman da aka tanada dan su. Abinci da komai a nan ake bayarwa. Gashi kamar hotel, gininsa ya yi kyau da tsari."


Islaha ta girgiza kai cikin mamaki ta ce, "tabɗi, lallai wannan Ray ɗin yana da matuƙar kuɗi, ko iya incomes ɗin da yake samu a iya asibitin nan ai ya ishesa rayuwar duniya."


Saleem ya ce, "kuɗi ba kaɗan kenan Islaha, yana da kuɗi kam sosai." 


Ta ɗan girgiza kai ta ce, "Allah ya fitar damu lafiya daga nan kawai." 


Suka amsa da amin kafin ta ce, "Don Allah ku faɗawa Chairamn kwana biyu bazan dinga zuwa ba, duk da zan yi masa massage, amma ku faɗa masa dai."


Saleem ya ce, "lallai gobe akwai ƙunci, kar ki manta gobe kina da talkshow."


"Ai sai dai yayi haƙuri kam, dan gaskiya bani da nutsuwar da zan iya yin komai" ta faɗa tana shafa goshinta dan mararta ta fara damunta da ciwo, duk da ta sha magani amma ciwo take yi mata sosai. 


Safeera ta kalli Mama da take gefe ita da yaranta, ta kalli Islaha ta ce, "matar nan bata ƙaunarki, amma kina ta faɗi tashi akan nemawa mijinta lafiya." Islaha jin ciwon ya matsa mata sai ta miƙe da sauri ta ce, "ina zuwa" ta faɗa tana barin wajan da sauri. 


Safeera ta tashi ta bi bayanta amma har ta shiga elevator ta bar floor ɗin. 


Tana shiga ta ga ta kalli madannan da suke cikin elevator ɗin. Numbers ne, sai R, sai G, sai P. Kawai sai ta danna P ɗin, ba tare da ta san ina zai kai ta ba. Yana buɗewa ta ga car park ne, tana fitowa ta ji ɗumi da wucin motoci. Ta tako a hankali tana kallon wajen, yana da girma sosai, tana ganin irin wajen a Kdrama da india.


Ɗumin wajen ya ratsa ta sosai, ta ja numfashi da ƙarfi ta sauke, ta samu waje ta tsaya yana runtse idanunta.


Mararta ta ɗaure matuƙa, a duk ranar da zata fara preiod haka take fama, in zata yi kamar zata mutu saboda azaba, duk da sai ta sha magani amma kafin fitar farko tana wahala. Ta je asibiti sau babu adadi amma babu wani amfani, dole ta haƙura ta rungumi ƙaddara. Wani lokacin in ciwon ya dame ta, sai ta nemi waje ta fashe da kuka mai ƙarfi ko zata ji daɗi.



Bayan wata mota ta samu ta zauna, ta haɗa kai da guiwa ta fashe da kuka mai sauti, tana jan numfashi daƙyar tana juya kanta cikin azaba.  Ta jima a haka, tana kuka tana addu'a har ta ɗan fara jin daɗi.


Ta fara ji tana flowing kaɗan, ta dafe kanta da duka hannayenta, tana ji ciwon yana ɗan raguwa kaɗan. Ido ta lumshe tana jin yadda zazzaɓi yake ratsa jikinta. 


Wayar ta ce tayi ƙara, ta ɗago daƙyar ta kalla ta ga hamma ne yake kira ta Whatsapp call, saboda shi bata kashe data. 


Ta jawo wayar ta ɗauka ta saka a speaker ta ce, "Hamma." 


A gigice ya ce, "Matar Hamma lafiya, Me ya same ki?."


"Babu komai, mura ce kawai."


"Kamar ya mura ce? Ga maganar ki tana nuna min baki da lafiya?."


"asibitin da mu ke zuwa ne akwai sanyi sosai, shiyasa nake mura."


Ya ɗan ja numfashi ya ce, "meyasa ki ka ɓoye min batun rashin lafiyar Baffa?." 


Bata ce komai ba dan bata cikin yanayin maganar, ya ce, "irin wannan ba a ɓoyewa kin ji?." 


Bata amsa ba ya ce, "Abu ne da ya zama dole na sani. Yanzu na turawa Sadik kuɗin da yake hannuna, kuɗin kayan lefenki ne da Adda take siyowa, su nake ta so na gama haɗawa kafin in dawo, amma Allah bai rubuta hakan ba. In sha Allah komai zai warware, kuma za a samu ƙodar da zata yi daidai in sha Allah."


Islaha ta ce, "Hamma in na faɗa maka rashin lafiyar Baffa daga zuwan ka, hankalinka bazai kwanta ba, shiyasa ban faɗa maka ba."


"Ina kwanciyar hankali mahaifina yana kwance a asibiti? Ai babu kwanciyar hankali Islaha. Haka Allah ya tsara, kuɗin da ake ta haɗawa dan a gama gini zasu tafi a neman lafiya."


"Neman lafiyar shine gaba da komai Hamma."


"Hmm auren naki ma samun lafiya ne. Sadik ya faɗa min likitan da ku ka fara gani a babban asibiti ya same sa wai yana sonki. A wannan asibitin da ku ke ciki ma baza a rasa wanda yake sonki ba. Ko ina aka je sai an ce ana sonki, ba dole na yi gaggawa na aure ki a huta ba."


Ta yi dariya tana sauke numfashi, ciwon yana lafa mata a hankali. Cikin dauriya ta ce, "Amma ai ni ban ce ina sonsu ba."


"in na killace ki a gidana mai faɗar ma baza a samu ba, in kuwa aka samu wanda ya yi wannan gangancin, alƙali ne zai raba mu. Shiyasa nake so ayi auren nan a huta. In shekara ta zagayo ki haifa min kyakyawan baby mai irin skin ɗinki." 


Ta yi murmushi bata amsa ba tana jin zazzaɓi yana ratsa ƙasusuwan jikinta


Islaha ta ce, "ina zuwa Hamma" ta faɗa tana kashe wayar tana ji mararta na cigaba da ƙullewa. 


Ta gaji da zama a wajen, ta miƙe daƙyar tana dafe kanta saboda nauyin da ya yi mata, ta ɗan sauke numfashi tana jin fitar abin kaɗan a jikinta, dan tasan farkon zuwa baya yi mata flowing sai kaɗan shiyasa take shan wahala har sai ya zuba sosai take jin daɗi.


A hankali take tafiya tana ji kamar zata kifa, bata ganin gabanta ko kaɗan, idanunta a lumshe suke, rana takawa kamar mara jini.


Babu zato ta ji an bangaji mutum, wayar hannunta ta faɗi ta yi ƙara mai nuni da ta fashe, dan ta daku a ƙasa. 


Islaha ta ɗago a hankali suka haɗa ido dashi, ta sauke facemask ɗinta dan wajan babu sanyi sai ɗumi, hakan ya yi daidai da yanayinta, bazai cutar da ita ba.


Tana kallonsa suka haɗa ido, ta ɗan yi siririn tsaki tana kallonsa, tana tuna haka ya yi mata a hotel ya zuba mata shayi, yau kuma ya yar mata da waya. Ta ja ta tsaya, tana jira ya bata haƙuri, sannan ya kuma sunkuya ya ɗauki wayarta ya bata.


Rehaan tsaf ya gane ta, dan shima ita yake nema dan ya saka ta san shi waye. Sai kuma ta bashi mamaki, yana tunanin ita ko ina tana nan?. Ya ganta a hotel, ya ganta a lokacin ta samu attack, yanzu kuma gata a car Park. 


Cikin seconds ya gama kallonta, ya ɗauke ido daga kanta, ga raɓa ta gefenta zai wuce dan bai yi niyar magana ba.


 Islaha ganin haka sai ta ce, "wait mr man." 


Ya ɗan tsaya kaɗan ta, ta dawo gaba ta tsaya tana kallon idanunsa. Idanun da suke yiwa duban jama'a wahalar gani, idanun da ko ka samu damar ganinsu kwarjini baya bari ka kalli cikinsu, idanun da suke da kaifi, in ya juya su a kan mace sai ta zauce.


Amma Islaha ko ɗar bata ji ba, ta ce, "kai wai wanne irin mutum ne, Ka buge mace baza ka iya cewa ta yi haƙuri ba?." 


Ta sunkuya ta ɗauki wayarta, ta ga screen ɗin ya zama fari alamun ya samu matsala, ta juya masa fuskar wayar ta ce, "ranar da na ganka a hotel ka zuba min tea a jikina, yau gashi ka fasa min waya. Kai baka san darajar mace bane ko kuma darajar ɗan adam ne baka sani ba gabaɗaya?."


Cikin faɗa take yi masa maganar kamar yaron ta, ko Mamy da ta kawo sa duniya bata taɓa yi masa faɗa haka ba. Shiyasa ya tsaya yana kallon ikon Allah, yana mamakin ƙarfin hali da ƙarfin zuciyar yarinyar, dan ko a haka ta yi nasara a kansa a karo na farko.


Islaha ta kuma fusata ta ce, "wulaƙanta ɗan adam ba abu ne mai kyau ba, kuma indai zaka dinga yiwa irinmu wulaƙanci wata ran ai an samu wata ta zabga maka mari wallahi. Nima kawai dan ina da tarbiyya ne, amma wallahi da sai na mare ka. Ba a yi mana mu ƙyale, akan gaskiyarmu sai dai a kaimu a kulle."


Rehaan ya ɗan cize bakinsa, bai ce mata komai ba dan bai nuna nata alamun ya ji yarenta ba. Walking slowly ya wuce ta yana ayyana abubuwa da yawa a ransa akan yarinyar.


Islaha ta ɗaga murya ta ce, "aikin banza, kuma wayarta da ka fasa min Allah ya isa." 


Ya tsaya cak jin kalmar ta daki zuciyarsa, ya ɗan rutse ido ya buɗe, kamar zai juyo sai ya fasa kawai ya danna key ɗin motar ya shiga ya ja ya bar wajan da sauri.


A lokacin Safeera ta