NADAMA page 8
by @mrsomar
NADAMAR DA NA YI🙆🏼
Fatima Isa
Edit.....2026
Love story 2015🥰
PAGE 8
************
Major Bilal ne ya turo ƙofa a hankali.
Kayan jikinshi mofti ne watau ( kayan gida ) daidai bakin gadon da Faruok ke ƙwance Major Bilal ya ƙarasa da sauri ya kai hannunshi jikin Col Faruok yaji kamar ana hura wuta a jikin nashi."
"Ya salam. Col what is wrong?"
Cikin muryar can ƙasa-ƙasa Col Faruok ya samu ya furta.
“Bilal marana zan mut..”
Bai ida magana ba ya koma rike cikinshi yana juyi.
Kai Major Bilal ya girgiza sannan ya dawo daidai kansa ya zauna, ya ɗaura kan Col Faruok saman ƙafarshi ya kura mashi manyan idanunshi cikin sanyin murya ya ce.
"Ina kaje har wannan matsala ta sake faruwa and you know ur problem but baka kiyayyewa kasan kana da yawan sha'awa Col amma baka kiyaye lafiyarka why?"
Da ƙyar Col Faruok ya iya ɗago kai ya kalli Major Bilal ya ce.
"Please major Bilal just forget about this, we will talk about everything later,
Please yanzu ka samu ka taimaka min ciwon nan ya lafa, wallahi ni ka ɗai nasan wahalar da nakeji yanzu Hafsat k.."
"What? Hafsat me ta yi maka ba dai ita ta sakaka cikin wannan matsalar ba?"
Shiru Col Faruok ya yi ya kasa ƙara magana. Major Bilal ya koma girgizawa kai sannan ya iya firta.
"Alright ina ka aje alluranka?"
Hannu ya ɗaga a hankali ya nuna mashi locker gefan gado da sauri Major Bilal ya nufa wajan ya ɗauko kwalin alluran bai wani ɓata lokaci ba ya haɗa duk wadda ta kamata ya yi mashi take guda biyu Major Bilal ya yi mashi.
Shi dama a cikin aikin soja a ɓangaran medical yake, kusan cikin soja za'a samu electrician kafinta da dai sauransu...
★★★
Ƙwance take akan ƙafarsa yayin da yake shafa gashin kanta mai santsi idanunta a rufe suke da alama tana jin daɗin yanda yake shafa kan nata cikin muryarta mai daɗin sauraro kamar sarewa ta ɗago kanta ta kama fuskarshi, ta fara magana kamar tana cikin wani hali.
“Ya kai kyakkyawan basaraken dake mulkin fadar zuciyata
nazo da littafin ƙauna dake rubuce da kalaman soyayyar ka, ka buɗe babin farko tare da haskawa dake haske zuciyata domin bin kalaman cike mai ɗauke da kaunarka,
kasani a fadar zuciyata kaine kake mulkinta ba ni da kamarka ina maka son da bana yiwa kaina saboda kaunar da nake maka yasa nasa maka suna da larabci Noor ql'bi hakika a baya naso na tafka babban kuskure dana rasaka da bansan inda zan saka rayuwata ba ashe kaine masoyina na gaskiya i love u Ya Faruok.”
Ji ya yi kawai ta jawoshi jikinta tana kiss nashi da sauri shima ya fincikota ya ci gaba da aika mata saƙoninshi iri-irin yana faɗin.
"Fatima are u sure yanzu kin amince dani wayyo Allah nagode maka fat.."
Dukan da Major Bilal ya kai mashi ne ya farkar dashi daga mafarkin da yake ga pillow nan rike a hannunshi ya rikeshi kam.
Kai major Bilal ya girgiza yana mai cike da bakin ciki halin da abokin shi ke son saka kan shi.
“Haba, Col what's wrong with you.
A kan mace kana so ka haukata kanka haba Faruok kaifa namijin duniya ne.”
A hankali Faruok ya tashi zaune ya lumshe idonshi ya buɗe su ya sake murmushin takaici ya fara magana cikin muryar mararsa lafiya.
”Major Bilal, hmm you will never understand me.
Ina tunanin dakai ka faɗa cikin halin da nake ciki tabbas da yanzu ka shiga wani ya na yi, wallahi tunda ka yi min allurar nan na samu barci nake mafarkin Fatima. Faruok wallahi idan ban mallaki Fatima ba rayuwa ta na dab da salwant..."
"Ya salam Col what are you saying haba mazaje kada ka bada maza mana.
Amma Faruok me zai hana ka amince ka aure Hafsat."
"What? Hafsat? never! I would never marry a useless woman like her. Major Hafsat? No"
"Why?."
Kai Major Faruok ya girgiza ya cije lips ɗinshi ya ce.
"Tarbiyar Hafsat Bilal sanin kanka ne bata dace dani ba a kullum ina addu'a Allah ya bani mata ta gari.
Bilal komin na yi tunanin na cire Fatima a raina sai naji na kasa, kullum ƙara sonta nake, na tabbata Fatima ita ce zaɓin da nake ta fatan Allah ya yi min."
A hankali Major Bilal ya ɗaga hannunshi ya dafa kafaɗar Faruok ya ce.
"Na yarda dakai Major Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Ameen."
Major Bilal har ya tashi sai kuma ya ce.
"Au Col wai kana nufin haka za'ayi hidimar bikin ba komi."
Murmushi ya yi ya shafa sumar kanshi ya ce.
"Hmm Bilal kenan ai hidimar biki ana yinta ne idan ma'auratan na cikin farin ciki da junansu.
Ni kam kaga namu auran za'ayi shine kawai."
Take fuskar Faruok ta sauya duk da dama fuskar tashi yau sai a slow.
Bilal yaga yanayin abokin nashi ya sauya dan haka sukayi ban ƙwana ya fita da sauri ya barshi..
«««««««««««««
Washe gari
Duk wata hanya da Fatima zata bi dan su haɗu da rabin ranta Musaddik ta kasa samu Dad ya hana ko nan da bakin get a barta ta fita.
Zaune take ta rasa mafita Mom ta turo ƙofa tana tare da wata mata mai ƙyau baza ta wuce shekarun Mom ba.
A hankali ta ɗaga kai tana kallonsu cikin girmamawa ta duƙa har ƙasa tana cewa matar.
"Pendo Ummi jamɓan duna."
"Jam Fatima noi shomri?"
"Jam Pendo."
Mom duk tana jinsu bata saka baki ba Pendo Ummi ta samu gefan Fatima ta zauna tasa hannu ta kama na Fatima ta ce.
"Fatima duk Adda Shamsiya ta faɗa min komi har zuwa yanzu ta ce kina nan a kan bakanki na kin amincewa da auran Faruok anya idan kika bijire wa iyayenki kin yi masu adalci?"
Shiru Fatima tayi tana wasa da yatsanta.
"Fatima magana nake maki."
A hankali Fatima ta ɗago kai tana kallon Pendo Ummi take idanunta suka cika da kwalla.
"Kinga Fatima ba kuka na ce kiyi min ba.
Amma ya kamata kiyi tunani sosai ki gani inda iyayenki suka dosa."
"Ummi ai bazata taɓa fahimtarki ba saboda yarinyar nan yanda kika san ba Fulani suka haifeta ba."
Ɗan murmushi Pendo Ummi ta yi cike da girmamawa ta dubi 'yar uwartata ta ce.
"A'a Adda kada ki faɗi haka ki dan bamu waje insha Allah zata fahimta."
Mom bata tsaya bata amsa ba ta yi waje abinta.
Pendo Ummi ta ɗago kan Fatima suna kallon juna ido cikin ido ta fara magana duk da Hausa.
"Fatima ki tausayawa mahaifiyarki kada kisa ta shiga cikin wani hali.
Wallahi Fatima Faruok shine mijin da ko wace mace ke fata ta mallaka, ya kike son wasa da damar da Allah ya baki ban ce maki Musaddik shima ba alkhairi bane amma ya kamata ki amshi zaɓin iyayenki dan kada daga baya kiyi dana sani."
Cikin muryar kuka Fatima ta ce.
"Pendo Ummi wallahi na yi duk yanda zanyi dan na cire soyayyar Musaddik a zuciyata amma na kasa.
Na tabbata ina dab da rasa rayuwat.."
Bata ida ba pendo Ummi ta yi saurin rufe mata baki da hannu tana faɗin.
"Don't say so please."
Hawayen da Fatima ke makakewa ne suka zubo da sauri Pendo Ummi tasa hannu tana goge mata.
Ta daɗe tana bata baki kafin daga baya ta ciro wasu abubuwa a cikin handbag ɗinta ta kama hannunta suka nufi toilet.
Bata ɓata lokaci ba ta shiga haɗa kayakin cikin ruwa iri daban-daban masu kamshin gaske ga garin lalle duk ta haɗa a ciki.
Sannan ta ce Fatima ta shiga cikin bathtub ta ƙwanta na wani lokaci bayan ta cire hayan jikinta Fatima na jin kunya Pendo Ummi babu yanda za ta yi haka ta amince da abinda ta faɗa mata ta yi..
Kuyi hakuri naso page ɗin yafi haka, amma ina..
#Love
#yaudara
#Cin amana
#Kiyayya
#Fatima
#Farouq
#Musadiq
#Hafsat
#bilal
#Aunty zee