GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 13

by @nusybee143

Page 13


Sau ɗaya ya kalle ta ya ɗauke kai yana ɗan taɓe baki, yarinyar sam bata burge shi saboda yadda bata da kamun kai sam,shi kuma a duniya ya tsani mace mara kamun kai 

"Hi!"ta faɗa tana murmushi sosai,ba ta ba shi damar magana ba ta cigaba da magana tana kallon Amna

"Amna babu magana ko?"Amna ta kalle ta ta ce"good morning aunty!"tana murmushi ta ce"No I'm your Mummy,not aunty,kin ji?"ita dai Amna bata yi magana ba sai kallonta take yi 

Ɗan murmushi ta sake yi,ta dubi Amna da ta sake lafewa a jikin mahaifinta ta ce"ki je wajen Hajiya Mamie kin ji?ko wajen Nanny,za muyi hira da Daddy"babu musu Amna ta miƙe daga jikin mahaifinta ta fice daga sashen tana waigen ubanta 

"Good morning love!"ɗaga kai ya yi yana kallonta,tsawon shekaru biyu kenan,tunda suka rabu da mahaifiyar Amna take bin shi da sunan neman soyayyarshi,sai dai sam yarinyar bata burge shi ko kaɗan, saboda bata da kamun kai,bata da wadatacciyar tarbiyya 

"Aiki nake yi, can you please excuse me zuwa anjuma??"

Kwaɓe fuska ta yi,a shagwaɓe ta ce"kai my baby boy!

Aren't you happy of seeing me?"

Ɗauke kai ya yi yanayin fuskarsa yana canjawa,ya ce"aiki nake yi ne,bana son a rinƙa interrupting ɗina "

"Amma na ga kuna hira da Amna time ɗin da na shigo"

Wani banzan kallo ya watsa mata ya ce"kishi kike yi da ita?"ɗan murmushi ta yi ta ce"no ba haka nake nufi ba,ya uwa zata yi kishi da ƴarta?

Kawai dai ina son ka ba Ni time ne,ka ga don kai kawai na zo gidan nan"bai amsa ta ba,ya cigaba da danna system ɗin shi 

Ganin ya yi banza da ita ya ƙi saurarenta sai kawai ta fashe da kukan kissa,ya ɗaga kai yana kallonta gami da sassauta fuskarsa,a hankali ya ce

"I'm sorry please,amma me ya faru da za ki yi kuka?me na yi miki?"

Goge hawayenta ta yi ta ce"ba ka yi min ba,ka ƙi yi min dai"

Ya sake dubanta sosai ya ce"me na ƙi yi miki?"

Ta karyar da kai ta ce"ka ƙi ka kula ni,ka share ni,bayan na shafe tafiya na zo don na ganka kai kaɗai,amma ba za ka iya ba ni time ɗinka ba?even a little?

Nima na ji ina da matsayi ko yaya ne a wajenka?"

Cikin kwantar da murya ya ce"okay na fahimce ki

Yanzu don Allah ki ba ni wasu ƴan mintuna na gama da wannan file ɗin da nake dubawa,idan ya so sai mu tattauna"

Kwantar da kanta ta yi a jikin kujerar da take zaune ta ce"alright!

I'm waiting"ya sake dubanta,ranshi ya fara ɓaci ya ce "I need space Nimra,idan kuma ba haka ba sai na bar miki gidan"

Cikin sanyin murya ta ce"But na ce zan jira ka ai, ka gama sai mu yi magana "cikin ƙosawa ya ce"okay!

To tunda ba za ki tafi ba ni bari na ba ki waje, I told you since bana son musu"ganin yana ƙoƙarin miƙewa ya sa ta miƙe ba a son ranta ba tana murmushi ta ce"I will wait sweetheart!bye!"ta fice daga sashen 

Tana fita ya miƙe da sauri,tuni ya ɗauki key din motarshi,ya fice daga gidan,don a rayuwarsa ya tsani a matsa masa






*ROXY*


A hankali take tafiya a gefen hanya,tana lumshe idanu tana buɗewa,da alamu har yanzu abin da ta sha bai gama sakinta ba, idanunta sun yi jawur, fuskarta a ɗaure tamau,alamun ranta a tsananin ɓace yake

Wayarta ta zaro,ta fara yunƙurin aika kira,bayan ya sakanni ta fara magana yanayin muryarta tamkar wadda take cikin maye

"Kana ina ne?"daga can ɓangaren Oga boss ya ce"ga ni a gida uwar ɗakina"

Kai tsaye ta ce"ka zo bayan gidan Amra,ina buƙatar ganinka"tana kai wa nan ta kashe wayar

Bata juma tana tafiya ba ta ji ana faɗin "wannan kamar wannan criminal ɗin da ake nema!"

Ji ta yi ɗayan ya ce"a haba!

Ta yaya zata yarda ta fito ita kaɗai a wannan lokacin?"

Ɗayan ya yi shiru yana duba hotonta da yake wayarta, kafin ya ce"wallahi ita ce fa,ka ga hoton"ita dai ko kallon su bata yi ba,ta cigaba da tafiya abinta 

Ji ta yi sun biyo ta suna faɗin "ke!tsaya!tsaya!!bari mu tabbatar,kar ki motsa,tsaya a inda kike"

Cigaba da tafiya ta yi a hankali har suka kusa cim mata,dayan ya ce "ki tsaya ko na yi harbi"

Cak ta tsaya a inda take,suka nufo inda take da gudu,amma kafin su ƙaraso ta shammace su ta saka gudu da tsananin ƙarfinta,suka rufa mata baya

Tsawon kusan awa guda tana ba wa yan sandan wahala,duk yadda za su kamo ta sun yi,amma ta ƙware wajen zilliya da rainawa yan sanda hankali,hakan ya fusata ɗaya daga cikinsu ya saita tsakiyar bayanta ya yi harbi,amma sai bai same ta sosai ba,ya same ta a kafaɗarta 

Sai dai a maimakon ta tsaya sai shigewa wani lungu ta yi ta ɓuya,duban duniya suka rasa ta, babu yadda suka iya haka suka juya suka tafi 

Ita kuwa Roxy bayan ta tabbatar sun tafi miƙewa ta yi ta cigaba da tafiya tana tangaɗi,ga mayen ɗazu har yanzu bai gama sakinta ba, saboda ƙwayoyin da su Amra suka zuba mata ba ƙaramin ƙarfi ne da su ba,ga jini da ya fara ɗibarta, saboda zubar jinin da take ta yi tunda aka harbe ta

Tun tana ganin gari yadda ya kamata har ta fara gani dishi-dishi,ga ƙarfin jikinta da yake ta ƙarewa,a hankali duhu ya rufe ƙwayar idanunta,duk da haka bata karaya ta tsaya ba sai da ƙarfinta ya ƙare duka,ita dai bata san lokacin da ta yanke jiki ta faɗi ba ma







*MALIYA ESTATE*

*UMMEEY*

Sauri sauri take yi don fita zata yi zuwa bikin ƴar ƙawarta Hajiya Jamila, Salma,amaryar ƙawa ce wajen ƴarta Shaheeda,sau tari idan ta ga yarinyar tana tunawa da ƴarta Shaheeda, saboda yadda halayyarsu ta zamo ɗaya,kuma manyan ƙawayen juna ne sosai 

Ko lokacin da aka aiko mata da katin gayyatar bikin Salma ta yi kuka sosai,don ta tuna Shaheeda, wadda a halin yanzu bata da tabbacin tana raye ko ta bar duniya 

Ƙoƙarin fitowa take yi daga ɗakinta sai ga Hajiya Sa'adatu ta danno kai cikin parlourn ta kamar wadda aka wurgo,sai huci take yi,da alamu ranta a ɓace yake, Ummeey ta kalle ta cikin faɗuwar gaba,ta daure ta ƙaƙalo murmushi ta ɗora akan fuskarta tana faɗin 

"A'a!

Hajiya Sa'adatu yau ke ce tafe?

Maraba da zuwa"Hajiya Sa'adatu ta watsa mata wani mugun kallo ta ce "ai ke ce da sannu Hajiya Zainab!

Wai me yake faruwa ne? meyasa ba za ki bar ni haka na huta bane? meyasa kika zamar min masifa da bala'i a rayuwata ne?"Ummeey da ke tsaye tana kallonta ta safe ƙirji tana faɗin "subhanallahi!me ya kawo wannan maganar kuma?

Don Allah ki yi haƙuri ki zauna mu yi magana ta fahimta,me yake faruwa ne?"

Kai tsaye Hajiya Sa'adatu ta ce"ba zama ne ya kawo ni ba,dama na zo ne na gaya miki ki yi wa yarki gargaɗi akan ɗana,ta hana shi zaman lafiya da matarshi,an kawo min ƙararta,bana son hakan ya kuma faruwa 

Haka kawai yanzu ta haddasa gaba tsakanin Muyassar da matarsa,ba zai yiwu na ɗauki ƴar mutane na ba shi sannan yarki ta hana su zaman aure ba,kar hakan ya kuma faruwa, bana buƙatar matsala a gidan ɗana

Ba sai an faɗa ba kowa ya san yarki masifa ce,kuma annoba ce,to bana buƙatar wani tashin tashina a kusa da ni"ta juya da zummar ficewa daga parlourn 

Cikin karyewar murya Hajiya Zainab ta ce"Hajiya Sa'adatu ki fahimtar da ni,wacce ƴar tawa kike nufi?

Dama ina da wata yar ne ban sani ba?"

Kallon banza Hajiya Sa'adatu ta yi mata ta ce"wacce ya kuwa banda wadda ta janyo mana abin faɗa a family, ƴarki Shaheeda?

Bana son abin nan ya kai mu gaban Alhaji, shiyasa na zo na gaya miki don ki ja mata kunne,ta fita harkar ɗana da gidansa, idan ba haka ba kuma komai zai iya faruwa,sai anjuma Hajiya "ta juya ta fice daga sashen zuciyarta cike da hassadar ganin Hajiya Zainab ta sake gogewa ta yi kyau kamar ba wadda take cikin damuwa ba

Zama Hajiya Zainab ta yi a hankali a gefen kujera cikin wani irin yanayi da ta kasa fassarawa, Shaheeda?ina suka ga Shaheeda?tana a wanne halin?

Ita a yanzu da zata ganta da bata san wanne irin farin ciki zata tsinci kanta ba,wai me yasa abubuwa suke ta faruwa da ita ne akan Shaheeda?

Ta goge hawayenta tana faɗin "ya Allah ga yata nan, Allah idan da rabo ina roƙonka ka dawo da ita gare ni, ya Allah kaine masani kuma mafi hikima, Allah ka yi min daga taskarka"

Kamar babu Abin da ya faru ta ƙarasa shiryawa ta fice don zuwa taron bikin yar su Salma,tana kallon su Hajiya Ruƙayya da Hajiya Atika suna magana,ta san mayar da yadda aka yi suke ya,bata ko yiwa sashen da suke tsaye kallo biyu ba ta shiga mota ta tayar ta fice daga gidan 





*HOSPITAL*

"Amra wannan wacce mahaukaciyar yarinya ce kika haɗa ni da ita take neman rayuwa ta?

Daga nuna mata hanyar daɗi kuma sai ta nemi kisa?"

Amra ta kalli Hassy da take wannan maganar ranta a matuƙar ɓace ta ce"ai ƴarinyar nan ta yi min wulaƙanci,amma wallahi bata ci banza ba,sai na ganar da ita kuskurenta,kafirar banza ƙazama kawai "

Hassy ta sauke ajiyar zuciya tana taɓa bandage ɗin da aka naɗe mata kai,a hankali ta ce"yanzu tana ina?"

Amra ta taɓe baki ta ce"oho!

Na dai bar ta a gida bayan na dake ta, gobe ta sake yi min wannan iskancin 

Itama karuwar ce fa,amma take nunawa duniya ita ba haka take ba

Abin haushi, yarinyar da criminal ce, nemanta ake yi ruwa a jallo amma zata yi min haka, sai na tona mata asiri a wajen yan sanda wallahi"Hassy dai bata ce komai ba, Amra ta cigaba da faffaɗar maganganu, saboda ranta a tsananin ɓacin rai da take ciki 





*ROXY*


A hankali take buɗe idanunta da take ganin dishi-dishi,ga jikinta ta ji ya yi sanyi babu ƙwari ko kaɗan,amma hakan bai hana ta yunƙurin tashi zaune ba tana sauke numfashi da ƙyar 

Ji ta yi an riƙe ta,an mayar da ita ta kwanta,ta dubi matar Oga boss da take riƙe da ita tana murmushi ta ce"sorry Ma'am!

Jikinki babu ƙwari, ba'a juma da cire bullet ɗin da aka harbe ki ba, relax ma'am "

Kallonta ta yi ta ce"ina Oga boss?

A ina ya gan ni?"

Matar Oga boss ta ce"a gefen hanya,da ƙyar muka gano ki,mun yi yawo sosai,sai kuma muka ganki a sume,shine muka dauko ki muka kawo ki nan,tun jiya da dare muka yi magana da likita ya zo ya duba ki ya cire miki bullet ɗin hannunki"Roxy ta kalli hannun nata ba tare da ta yi magana ba,ta sake dubanta ta ce"Azeema ina Oga boss?"

Azeema ta ce"yana parlour"

"Kira min shi"ta faɗa ba tare da ta kalle ta ba 

Babu musu Azeema ta juya ta fice daga ɗakin don kiran Oga boss, Roxy ta zauna sosai,ta lumshe idanunta, komai da ya faru yana dawo mata ƙwaƙwalwa tiryan-tiryan 

Ɗan murmushi ta yi tana tuna cin amanar da Amra ta yi mata,ta girgiza kai kawai,a ranta ita kadai ta san me ta shirya mata

Tana nan zaune su Oga boss suka shigo ɗakin,da sauri ya ƙaraso yana faɗin"sannu ma'am!

Ya jikin?"

Kallonsa ta yi ta ce"Oga boss wani aiki nake so ka yi min,amma da Azeema za mu haɗa!"

Waje ya samu ya zauna yana faɗin"okay ma!

Wanne aiki ne?"

Lumshe idanu ta yi ta buɗe, sannan ta fara yi masa bayani a nutse,a razane Oga boss yake kallonta, ba tare da shakka ko tsoro ba ta ce"eh haka nake so 

So nake na hukunta Amra,ina son a yau ta san wacece Roxy!"

Jinjina kai ya yi,ya dubi Azeema ya ce"za ki iya?"

Cikin bayar da tabbaci ta jinjina kai,ta ce"zan samu masu taya ni ma ranki ya daɗe 

Ke ce fa kika ba mu sutura, kika ba mu dukkan farin cikin rayuwa,raina ne kawai ba zan iya ba ki ba"

Cikin kwantar da murya Oga boss ya ce"amma kuma akwai haɗari a cikin wannan aikin ranki ya daɗe,ga na nakasarwa idan an samu matsala 

Ba za'a chanja hukuncin da wani ba kuwa?"

Kallonsa Roxy ta yi, cikin yanayin ɓacin rai ta ce "ka san wacece Roxy,babu wanda zai gaya maka halina ko da ace David da muke tare kusan koyaushe 

Ka san abin da na fi tsana,to me yasa Amra zata ci amanata?

Na san Amra cikakkiyar karuwa ce kuma ƴar lesbian,amma a haka nake tare da ita duk da ni bana ra'ayin hakan,amma meyasa dole sai ta yi forcing ɗina na yi abin da ban yi niyya ba?

Duk da cewa Amra bata cancanta ba amma ina girmama shekarunta,don na san ba ta kusa da sa'a ta ba ce,amma a ƙarshe ta zubar da ragowar girman da nake ganinta da shi ta ci amanata,amma kuma zan shayar da ita mamaki tabbas,na yi wannan alƙawarin!! 






#Nusy_bee